Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 8

Sponsored Links

8….

Kara zaro idanunta tayi duka tana kallonshi tana wani irin kallon abincin daya kawo bakinta yanajira tabude yasamata aciki, dan lumshe ido yayi yabudesu ahankali ya sake daurasu akan white oily eyes dinta, cikin wani irin dense voice yace “open your mouth Jewel” ja baya tafarayi akan gadon arude yana binta rike da spoon din harsaida takai bangon gadon tafashe da kuka tana kare fuskarta da hannu, ahankali ya zauna kusa da ita ya mika hanunshi yakama hanun datake kare fuskan dashi yakai spoon din mouth dinta yana wani irin kallonta batare dayay magana ba, da sauri ta bude bakin yasaka mata rice din ta karba zata fizge hanunta yakara rikewa gam gam, ahaka yacigaba da bata abincin hartaci kusan 5 spoons sanan ta kauda kai tace “na..na koshi” rufe abincin yayi ya ijiye a inda yake yadau bottle water yabata, ahankali ta karba tasha kadan tabashi ya karba ya ijiye yana kallon yanda gefen bakinta ya baci da oil din food din, hanunshi ya zira a aljihu yaciro clean white handkerchief dinshi mai taushi da kamshi yakai saitin bakinta yana wani irin kallonta, arude ta yunkura zata koma baya da sauri yasa hanunshi yakama waist dinta yana wani irin kallonta, kwalalo ido tayi tana wani irin kallonshi adaburce kaman wacce ke shirin suma, ahankali batare daya yanke eye contact dinsu ba ya daura handkerchief din gefen bakinta yana share mata ahankali harya gama yana kallon kwayar idanunta, zare handkerchief din yayi batare daya saketa ba yana rike da ita har lokacin yace “what’s your name Jewel?” kulle idanuwanta tayi da sauri dan bazata iya jure kallon dayake mataba, ita tunda take bata taba ganin namiji mai eyes irin nashiba, yatsarshi yadaura kan nose dinta yana kallon long eyelash dinta yace “what’s your name Jewel?” wani irin nishi tayi dan sosai yatsarshi ke mata wani irin sanyi a hanci hakan yasa tasaki wani irin ajiyan zuciya tace “Amatullah” murmushi yayi sosai dayawani irin karamai kyau maidan sauti hakan yasa ta bude idanunta, kallonta yasakeyi yace “your name is very cute just like you Ama” sake ware idanunta tayi ta kalleshi adan tsorace, gyadamata kai yayi yace “yes, you’re beautiful Jewel” saukar da idanunta tayi kasa da sauri hakan yasa ya sanya hannu yakama habarta ya daga fuskarta ta fuskance shi, sosai zuciyarta ke neman dena aiki sabida yanda yake kallonta, da sauri ta sanya hanunta tana tura nashi daya rike mata habanta dashi muryanta na rawa sosai tace “s…stop touching me” da sauri yace “why?” tabe baki yayi yace “ba kyau ko? In UK is a normal thing” shiru yayi yana kallon yanda har lokacin hawaye ke fita daga idanunta and he could feel yanda jikinta ko’ina yake rawa sabida riketan dayayi ahankali yace “kinaso na sakeki?” da sauri ta dagamai kai batare data kalleshi ba, dan murmushi yayi yace “okay to stop crying and listen to me, I wanna talk to you, inba hakaba I will hold and touch you again” da sauri ta sanya hannu ta share hawayen nata tass tadan kalleshi irin kallon nan na antursasani ne, ahankali yajanye hanunshi daga waist dinta ya saki habarta yadan koma baya da ita kadan dan yasan inhar yana kusa da ita he will touch her again and yanaso he wants her to be comfortable, gyara zama yayi ya kalleta murya chan kasa yace “Amatullah” da sauri ta dago kai ta kalleshi dan sosai yanda ta kira sunan ya daki ranta danko kadan a gida ba’a saba kiranta da Amatullah a gidaba dan sunan Kaka ne, babu wanda ya isa yakirata da sunan. “where are you coming from, tayaya kikai drowning? Kinje Beach ne?” shiru tayi tana kallonshi kafin cikin siriruwar muryanta tace “bikin Anty Ayush” da sauri yace “who’s Anty Ayush?” ahankali batare data kalleshi tace “My sister” “aruwa kuke bikin?” gyadamai kai tayi tace “yes d husband is navy a jirgin ruwa suke party” da sauri yace “to tayaya kika fada ruwa basu ciroki ba?” cikin wani irin muryan kuka tace “jiri” da sauri yace “jiri kika dinga gani?” gyadamai kai tayi batare datai magana ba, shima shiru yayi yana kallonta, dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido da sauri ta saukar da kanta tana share hawayen daya zubomata tace “I thought na mutu ma” murmushi yayi yace “no, I was the hero, I saved u Jewel, am your superman Jewel” batare data kalleshi ba tace “my name is not Jewel stop calling me that” murmushi yayi maidan sauri yakamo hanunta yace “you’re my Jewel, I found you a water, and bazan barki ba Jewel, I just li…” hawayen dayaga tana sharewa yasa yadanyi shiru yana kallonta, dago kai tayi ta kalleshi adan tsorace ahankali tace “zan kira Mama na” dan yatsine fuska yayi kaman wani karamin yaro yace “I don’t want them to come and carry you now Jewel” duka hannayenta tadaura kan fuskarta tana share hawayen dake zubo mata sosai wanan wani irin mutum ne haka, wani asibiti ne wanan, tasan su Anty Lami da Ayush kowama ana chan ana neman ta, tasan hala yanzu ma har an kira su Baba da Mama harma Kaka duk an sanar dasu ta bace, hanunta taji yakamo ya matsa. “Jewel stop crying pls, zakiyi magana da Mum dinki?” gyadamai kai tayi hakan yasa yaciro wayarshi daga aljihu ya mika mata dan dago kai tayi suka sake hada ido, karban wayan tayi tasaka number Mama tai dailing, harya katse mama bata dauka ba, ana biyu ne ta dauka muryanta yadan shake alamun taci kuka tace “Assalamu Alaykum, waye?” jin muryan Mama yasa taji hawaye yazubo mata da sauri tace “Mamaa” tashi Mama tayi daga kan gado datake kusa da Abba dake lallashinta, dafe kirjinta tace “Hamida, Hamida kene?” gyadamata kai tayi ahankali tace “uhm nine Mama” kaman Mama zatai kuka tace “Hamida ina kike? Ina kikaje su Ayush hankalin su dukya tashi anata neman ki, Hamida I promise bazan kara turaki kije wani waje idan bazakije ba kinji, fadamin inda kikaje, inkika boye? Anbicika jirgin kakap ba’a gankiba, ina kika boye Hamidana nakira su Ayush nafada musu suzo su daukeki ki koma gida gobe sudawo min dake nan kano tunda bakison chan, kina ina Baby na? and wanan wani number ne kika kirani dashi naga banaki bane, da number wa kika kirani, ina kika boye eh Hamida na fadamin?” Mama tai maganan muryanta narawa sosai hankalin ta atashe, dama ance yaro mai matsala yafi shiga rai, bala’in son Hamida take bana wasaba, ko Ihsan auta tabiyo bayan son datake ma Hamida, ahankali Hamida tace “ruwa nafada Mama” “innalillahi wa innailaihi raji’un ruwa Hamida? Wanan babban rafi da manya manyan jirgin chaina kebi kika fada? Ru kika fada Hamida? Are you fine? Kina ina yanzu?” ganin yanda tabi ta rude ko’ina najikinta na rawa yasa Abba karban wayan daga hanunta yakara a kunne yace “Mamana kinajina” gyadamai kai tayi tana kuka murya chan kasa tace “eh” anatse yace “yanzu kina ina?” ahankali tajuya ta kakkali dakin cikin kuka tana lankwashe kai kaman tana gabansu tace “asibiti” da sauri yace “subhannallah asibiti? Garin yaya? Waya kawoki asibiti?” fashewa tai da kuka tace “nima ban sanshiba Abba” da sauri Abba yace “da wayanshi kika kiramu to” gyadamai kai tasake yi cikin kuka tace “eh shiya bani wayan” da sauri Abba yace “bashi wayan nai magana dashi” ahankali ta dago idanunta dake cike da hawaye ta kalleshi hada ido sukayi ya rungume hanunshi yamata kuri da ido yana kallonta kaman zai cinyeta, mikamai wayan tayi tace “Abba na zaima magana” kallonta yayi kafin ya kalli wayan yasake kallonta, sanan ya karbi wayan yakara a kunne a natse yay sallama kaman bashiba sanan yajuya yafita daga dakin tabi bayanshi da kallo, yakai kusan 10min awaje sanan yadawo dakin, gyangyadi yaga tanayi a zaune, kujera yaja ya zauna hakan yasa tabude ido da sauri ta kalleshi da idanunta dasuka dan kankance sabida bacci tace “za’azo a daukeni?” gyadamata kai yayi yace “amma saida safe za’azo nafada musu sunan asibitin” wani irin bakin ciki taji ya tsaya mata a wuya dan bataso kara koda minti daya da wanan mai shegen kallon ba, ahankali ta kwanta kaman marainiya ta juyar da kanta dayan side din tana danne kukan daya wani irin taushe mata makoshi.
_🌹 IN BANI 🌹_

 

Related Articles

_M. Shakur_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button