Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 4

Sponsored Links

Dankakaren falon gidan su acike yake dam da yan uwa dan yau Alhaji Ismail wan baban Khaleel wanda suke kira da Abba ya iso daga Yola tareda yaranshi da matayen shi biyu, Hajiya Amina wacce itace babba yaranta uku Mustapha babban danta da yanzu yay aure matar shi bata haihuwa, sai Yusuf shine na biyu shine saan Khaleel tare suka taso sun shaku sosai, sai autar su Fa’iza wacce ke SS3 a boarding school. Amaryan Abban Kuma Mujiba yarta daya wacce takeda shekara daya aduniya, gabaki daya falon ya kachame da hira idan ka gansu gwanin ban Sha’awa.
Yusuf ne ya kalli Khaleel dake danna waya yana shan tea yace “kai tashi muje mu amso dinkin mu, and su Shareef na jiran mufa a barrack dinku” yatsine fuska yayi sanan ya maida wayar aljihu ya harare shi yace “muje” tashi sukayi Yusuf yace “Abba zamudan fita” da sauri Ihsan tace “Ya Yusuf ku dawo dawuri fa, 4:30 daidai ne walimar babu afircan time” ta kalli Fa’iza da Ilham tace “ku tashi muje gidan su Aisha ma, nasan amma fara lallen tanata min flashing” Car key Khaleel ya dauka suka fita dukan su tare.
Karfe 4 aka fara tafiya da kawayen amarya wajen event din ganin su Eesha basu fitoba yasa Mama ta shiga dakin nasu, su Ihsan ne da wata kawar Eesha wacce suke aji daya anan University Abuja. Kasa magana Mama tayi ganin yanda Eesha tai mugun kyau abunka da wacce bata saba kwalliya ba, murmushi su Ihsan sukayi, Ilham tace “Mama tai kyau ko, Fa’iza ce tamata makeup dinan” murmushi kawai Mama tayi tajuya tabar musu dakin, ahankali Aisha ta dago kanta ta kalli fuskar ta a madubi murmushi tayi sabida taga tama kanta kyau, Khadija ce ta dagata tace “tashi muje, yau idan Khaleel ya ganki na tabbata hmmm” dariya sukayi bakaramin kunya taji ba ta turesu tafita daga dakin da gudu, binta sukayi nan suka shiga motar da aka barmusu driver ya jasu zuwa wajen venue walimar.
Wa’azi aka musu mai ratsa jiki, mai sanyaya rai mai kara Imani, sosai kowa yay hawaye, barinma amaryar, bayan angama aka rarraba kyaututtuka akai ciye ciye sanan aka fara kawo motocin komar dasu gida. Gaban wata babar jeep Khadija ta kaita kirar Brabus, bude marfin motar tayi ahankali ta shiga sanan ta mayar da kofan ta rufe juyawa tayi da sauri ta wuce ta shiga wata motar daban. Kin dago kanta tayi dudda taji yanda kamshin turaren shi ya bude motar, cikin wani irin calm voice taji yacema driver mutafi. sundan jima suna tafiya kafin ahankali ta dago kanta ta kallai karaf suka hada idanu hakan yasa ta juyar da kanta da sauri tana murmushi.
Parking motar taji anyi anbude gaban motar anfita matsowa yay kusa da ita kadan dawani irin murya chan ciki yace “wife” duk yanda taso karta kallai hakan ya gagara samin kanta tayi da juyowa ta sauke mai kyawawan idanunta akanshi, ganin kallon dayake mata yay yawa yasa ta huramai iska a fuskar murmushi yayi, ahankali tace “Mesa kake kallona haka?” takarashe maganan tana turamai baki, murmushi yasakin mata kafin yakara matsowa kusa da ita, da sauri tai yunkurin matasawa hannunta yarike yana wani irin kallon fuskar ta, jikinta ne yafara rawa ta bude baki zatai magana, dayan hanunshi ya daura akan lips dinta yana girgiza mata kai da idanunshi dasuka xhanza launi kaman basuba, ahankali yadaura goshin shi akan nata lumshe ido yayi jin yanda take numfarfashi, dawani irin murya yace “ina sonki sosai my Eesha” Ahankali ya dago da kanshi hannu yasa yay cupping fuskar ta sauke idanunshi yay akan lips dinta dake shining sabida Jan bakin dasuka ji wani irin abu ke fizgar shi ahankali yakai bakin shi zai daura da sauri ta kawad da kanta kirjinta na mugun bugawa dan tunda take dashi baitaba mata hakaba, wani irin hawaye ne ya zubo mata tai sauri ta share sanan tadan kalli fuskar shi wanda ita yake kallo da idanunshi dasuka kankance kofa ta bude da sauri tafita ta bude gate ta shiga gidan su. Yafi minti uku a zaune kafin ya bude kofar ahankali yafito front sit yakoma ya kunna motar yaja yabar wajen.
Gaishe da kawayen Mama tayi dake falon a kunyace ta wuce sama, su Khadija da Ihsan ne ke gwada kayan ankon su da aka kawo musu, zama tayi a gefen gado tana yatsine fuska tace “wash Allah wlh nagaji” dariya duka yan matan sukayi Khadija ce tace “ai dole sannu kinji” yanda tai maganan yasa Ilham ta kwashe da dariya tace “ai Yaya Khaleel shegen naci shi bazaima bari gobe tayiba yawani…” hararan ta Eesha tayi tace “yan sa ido Yaya Khaleel dina baida naci duk cikin sone” kama baki dukan su sukayi suna kallonta cike da mamaki, Ihsan ne tace “iyye kike karemai muma Allah bamu mai sonmu” dariya tayi tareda cire doguwan rigan jikinta ta yarage saura shimi da dogon sket, ta ninke ta ijiye akan gado, murmushi tayi ganin fuskar Khaleel namata gizo, hannu tasa ta cire dan kunnen kunnenta ta ijiye agaban mirror sanan ta juyo ta kallesu ganin duk ita suke kallo yasa tasake murmushi tace “bazaku gane yanda nakeson yayan nan naku bane, inama Ya Khaleel son da ina ganin ko bayan namutu banjin son zai mutu ba, Ya Khaleel namijin tal da har yau banga irinshi ba, mutum ne mai tausayi, kirki ga amana da addini, nasan yanada matsalan zuciya da yawan fushi but alkairan shi sun mamaye wanan, sabida Ya Khaleel ne Auta ke raye da yanzu ya mutu, kuntuna randa gidan mu yakama da wuta duk anfito damu but Auta na ciki, Ya Khaleel was d one daya koma duddu uban wutan nan yaje ya dauko Auta, saida ya kone a hannu garin hakan, haryau tabon na jikin shi” share dan guntun hawayen daya zubo mata tayi ta mikama Ilham da Ihsan hannu tace “Yaya Khaleel dina is my everything bazan taba son wani sama dashi ba” murmushi tayi ta sake su ta wuce bayi danyin wanka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button