Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 4

Sponsored Links

2:09 PM] Aisha Baby Novel: *Like i always say and always emphasize, things are not always what they seem, Duk abinda kake zargi karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike, ba ko wacce kishiya ko stepmom take kansa cewa azzaluma ko macuciyya ba.. Akwai masu zuciyar musulmi wanda babu tsatsa a cikinta, akwai soyayya ta gaskiya akwai ta algus, akwai mai tsayawa a rai akwai mai gundira..Never and never judge a book by it’s cover idan kuma ba haka ba you might spend the rest of your life regretting… Kuyi ta turo ƙudundunanniyyar dubu ɗaya amma kuna bawa mutum dubu ɗaya as free🤓to ai ko ɗan-gote akewa haka ya tafka zabgegiyar asarar balle Sarauta. Ni ba zan zagi ko Allah ya isa ba, ba kuma zanta surutu ba akan abu ɗaya ba, balle bakina ya yi tudu a barni da siyan mansileta.*

#Who is the husband?…
She looked at him with surprise and excitement baki buɗe take kallon Khalil She couldn’t believe that he was in front of her, because he was different from the Khalil she knew before, da sauri ta rufe bakinta tare da ɗauke Idanunta tana haɗe fuska sosai domin har cikin ranta bata ƙaunar sake ganinsa a rayuwarta. Abraham dake tsaye rungume da Baby Khalil ya ɗan ja baya kaɗan yana ƙare mata kallo frm head to toe, ta sauya bakiɗaya ta rame sosai idanunta ya faɗa, sai siririn hancinta da tsukakken bakinta da duk ya bushe, shap ɗin jikinta na nan daram musamman faffaɗan waist ɗinta dake kwance, ya ɗauke idanunsa a hankali kuma ya miƙa mata Baby Khalil ɗin, ta watsa masa harara mai nuna yadda take tsananin tsanar shi, shi dai bai ce komai ba kallonta kawai yake, because He has nothing to say, no words in his mouth. Ta saka hannu ta amshi ɗanta tana sauke ajjiyar zuciya ta rungume shi sosai, Abraham dai yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu Majeederh ta kasa yin shiru da bakinta ta ce “Stay away from me and my son, ban ce kada ka sake dawowa gare ni ba? Ka fita daga rayuwarmu tun kafin nayi maka baki, kasan kamar uwa nake wajanka da nayi maka baki zai bika” Ya yi ta kallonta Calmly ya ce “Ohk” Ta juya zuwa bedroom ɗinta sai kuma ta ƙara juyawa taga ba ita yake kallo ba wayarsa ya zaro daga aljihu yana dannawa a nutse ta ce “Ka fita daga gidan nan, kayi nisa damu, kuma ɗana bashi da alaƙa dakai hakƙin uba na yafe” bakinta dake motsawa ya zubawa idanu a hankali kuma ya miƙe tsaye yana mayar da wayarsu zuwa aljihu, walking slowly ya nufi inda take fuska ɗaure bata taɓa ganin fuskarsa haka ba, ta juya zata shige bedroom ɗin ya yi saurin cafko hannunta tare da bayar da ita baya zuwa jikin bango ya saka hannunsa a both sides ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious yana fita daga jikinsa, ya dinga kallonta ba tare da yace komai ba, tama ɗauka yabar wajan ta buɗe idanu a hankali taga fuskarsa dab da tata kamar zai haɗe fuskokin nasu, tana ɗaga idanunta taga bakinta kawai yake kallo tayi saurin ɗauke fuska gefe ɗaya, silently bakinsa na fidda ƙamshin Spraymintt mouth freshener ya ce “Ohk, kuma nace wajanki nazo? da wani mitsitsin bakin ki” Majeederh dai bata ce komai ba, domin bata son duk abinda zai haɗata da shi. Ya ƙara matsar da fuskarsa dab da nata murya can ƙasa ya ce “Kuma da zaki ce ba ruwana ɗana ke ki kai cikin? Ki biyani cikina da ƙwayayen haihuwata sai na bar miki shi” Cikin fusata ta ce “Ka matsa ka bani waje before I lost my temper” Ya dinga kallonta sai kawai ya juya da sauri tare da barin parlourn, yana fita tana sauke ajjiyar zuciya mayataccen turaren shi duk ya addabeta, ta shige bedroom tana zama saman gado idanunta akan Baby Khalil daya kwaɓe fuska Exlty yadda Abraham yake abinsa tun yana ƙarami ta lumshe idanunsa tana jin soyayyar ɗan ta har cikin zuciyarta, gabaɗaya yanzu bata son aure tana son ta rayu haka tunda Allah ya nuna mata ɗanta na cikinta, ta fahimci babu komai a cikin aure sai tashin hankali ba soyayya babu kulawa. Anti ce ta shigo ta sameta tana jijjiga baby khalil dake kuka yana harba ƙafa Anti ta ce “Au ke ya kawowa?” Majeederh ta kalli Anti bata ce komai ba ta ce “Ai tun safe Abraham ke gidan nan a part ɗin Jawaad ya dameni wai ina ɗan shi, na faɗa masa yana gidan Uncle Bello babu jimawa sai gashi rungume da yaron, wannan mugun kamar da Abraham yake da yaron nan ya ɓaci kamar shi ne yana ƙarami” Majeederh ta haɗe fuska tamau ta ce “Plx Anti ki daina haɗa my son with someone else” Anti ta riƙe baki ta ce “Au haba? Dole ya amsa sunan Ibrahim Ibrahim, ko kuma Ibrahim I Khalil kuma kin manta ke kika saka masa sunan? Kuma dole a cewa mijin iya baba ba zaki hana duniya faɗar cewa ɗan Abraham bane” Majeederh ta ce “Ɗana tsarkake ne, shi daban wancan daban” Anti ta gyara zama sosai ta ce “To Albishirin ki Abraham ya musulunta, yama jima da zama Muslimi ya sauya gabaɗaya daga yadda kika san shi, ke banda ya sauya tunda yazo gidan nan ai wajanki zai fara zuwa amma ko sunanki bai ambata ba balle kuma yace kina ina, he just asked where’s his son, kuma shi ma yasan ba zai sameki ba, da Jawaad yana basa labarinki bayan barinsa garin da kuma labarin mutuwar aurenk ko ƙala bai ce ba, ya kwanta tare da yin shiru kamar bacci, sallah bata taɓa shige shi akan lokaci da jami’i, so ki kwantar da hankalinki He didn’t come because of you, he came because of his son, Stop the small talk and shrug” Anti ta miƙe tsaye har taje bakin ƙofa ta tsaya ta ce “Uncle yana kiranki” Gaban Majeederh ya faɗi ta ɗan marairaice ta ce “Plx ki ce bana jin daɗi” Da wani irin kallo Anti ta ce “Tell him by yourself” Tana faɗin hakan ta fice, Majeederh ta runtse Idanunta tana zuciyarta na bugawa sosai tasan rabuwarta da Abuturab alheri ne tunda ta roƙi Ubangiji ya zaɓa mata mafi alheri, bata son ta shiga layin matan da za’a dinga lissafawa Aure, bata ji daɗin aurenta da his Excellency ba, bata san farin cikin dake cikin aure ba, ta gama karaya tasan bata da rabo da farin ciki bata da rabo na ladan dake gidan miji. Da ƙyar ta miƙe ta nufi parlour ta samu Uncle Isma’il zaune shi da Uncle Bello suna magana a hankali suna ganinta sukai shiru,ta zaune ƙasan carpet kanta a ƙasa bayan ta gaishe su Uncle Isma’il ya ce “Hawwa’u” Ta kasa amsawa sbd fargaba ya ce “Kamar yadda na faɗa zan ƙara, wallahi wallahi Allah a gobe zan aurar dake, daman furniture’s ɗinki da kayan kitchen da komai suna nan, abu ɗaya zan faɗa miki inma ki fitar da gwani a cikin su, Mai martaba Ajlaal Sultaan, Barrister Aliyu Sufyan, Engr Junaid, ko kuma Dr Ibrahimul-khalil, ko kuma na aura muki wanda ya fara zuwa ya saman wato Mai martaba” Majeederh ta rasa waye wani Dr Ibrahimul-khalil, idan ta auri Aliyu bata kyautawa kanta ba darajar Latifa a wajanta ta shige ta auri mijinta, idan ta ce Mai martaba kuma da wanne idanu zata kalli Ƙhulud Arzaan? Wacce ta ɗauketa matsayin ƴar uwa kamar Aaliyyah da Ruma da Raihana da su Sona, Du’a, Widad da Sahar? Idan kuma ta ce Engr Junaid bata san halinsa ba infact she don’t even know who he is? Uncle Bello ya numfasa ya ce “Kina da lokacin daga nan zuwa Subhi, ki yanke hukuncin da kike ganin ya dace dake Hawwa’u, ki dai sani a wannan karan zaki rayuwa da wanda yake son ki ne, kuma a yau kowa zai zo ya sameki ki bashi lokaci ku tattaunawa, but am sure you’ll like His Highness” Uncle Isma’il ya girgiza kai ya ce “Definitely” Ita dai bata ce komai ba suna zaune Jawaad ya shigo ya ce “Uncle na sauke shi a special parlourn gidan nan” Uncle Isma’il ya ce “Ok zata zo” Ya juya ya kalli Majeederh ya ce “Ga can Mai martaba kije yanzu ku gaisa” Majeederh ta marairaice ta ce “Uncle ni ban son auren please” Wata kyakkyawar tsawa ya daka mata jiki na rawa ta miƙe zata fice ya ce “A haka zaki? Idanu buzu buzu duk a jime” Ta ce “To ya ganni a haka” Uncle Bello mamakin Majeederh yake kwana biyu ta sauya ga saurin kuka ga magana kai tsaye, ko mene dalilin sauyawar nata? _Only God knows!_
A hankali ta shiga parlourn bakinta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta, ta shiga kanta a ƙasa bata yadda sun haɗa idanu da Mai martaba Ajlaal Sultaan ba. Shi kowa yana zaune hakimce saman kujera ya ɗan kishin giɗa, jikinsa da wata farar jallabiya ya ɗora hirami a kansa sai ƙamshin perfume ɗn Jean Paul Gaultier sai lumshe idanunsa yake, tunda kuma ta shigo yake kallon fuskarta a karo na farko har ya gaza ɗauke fararen Idanunsa duk da irin basarwa ta Mai martaba, maganarta ya dawo dashi daga tunaninsa da take cewa “Gani” Kamar bai jita ba haka ya yi shiru yana mai da idanunsa tare da rufewa, Malama Majeederh ta ɗago kai tana kallonsa tana mamakin girman kai irin na Mai martaban, ko da yake ba laifinsa bane jinin sarauta dake yawo a jikinsa ne. A hankali ta ce “Gani” ba tare daya buɗe idanu ba ya ce “Kewa?” Ya ja numfashi ya ce “Suwa suka kira ki?” Ta ce “Ohk Maybe mistake ne” Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta ji ya ce “Haw…wah” Cak ta tsaya a hankali ta dawo ta zauna, ya gyara ya zama yana buɗe ido calmly ya ce “Mun gani, mun yaba, muna son aura” Majeederh ta kasa Kallonsa sbd kwarjini ganin haka yasa ya ɗan gyara murya ta ce “Ƙhulud? ba zan iya mata haka ba” A hankali ya ce “Su waye haka? Oh Fulani kawai amincewar ki muke nema” Ta ce “Zan yi tunani” Ya jinjina kai he can’t stop himself wajan kallon riskarta Bai ce komai ba tasan ɗin bazai tanka ba, har zuciyarsa yake son Majeederh amma yanzu tunani kala daban daban ya shiga kansa, ya miƙe yana tafiya a nutse sai da yaje ƙofa ya ce “Kuyi tunani mai kyau”. Yana faɗin hakan ya fice ta bisa da kallo koman shi a nutse yake, ta jima kafin ta miƙe tana fita entrance na gidan taga Aliyu tsaye shi da yayansa Almustapha sun saka kaya iri ɗaya, Almustapha ne kawai yake magana amma hankalin Aliyu na kan Majeederh tayi kamar bata gansa ba, Almustapha ya ce “Assalamu alaiki” Ta tsaya tana amsawa can ƙasa bayan sun gaisa da Almustapha Aliyu ya ƙarasu inda take ya ce “Kin gama guje gujen?” Ta kame fuska bata ce komai ba ya marairaicewa fuska ya ce “I will ask for your help again and again, Hawwy, help my heart and accept me as your husband” Tayi shiru yana sauke numfashi murya kamar mara lafiya ya ce “Don Allah, don Allah ki taimaka mini ina son ki Jiddatul-khairy, bani da zaɓin zuciya sama dake tunda na fara haɗuwa dake har yanzu bani da ishasshiyar lafiya, bana cikakken bacci, bana cin abinci sosai wlh ko maƙiyina a duniyar ba zan so ya kamo da irin wannan son mai zautar da mutum da son kai shi kushewa ba, i loves you ina son ki” Wani irin tausayin Aliyu ya kamata domin kaf cikin su tafi tausayin shi yana da wata kalar zuciya mai sanyi da son kyautatawa mutum a hankali ta ce “Baka taɓa cewa kana so na ba sai yanzu?” Ya girgiza kai ya ce “Ba zaki gane ba, ki fara amince mini zan yi miki bayani amma ko Latifa darajarki take ci” Ta kalle shi sai ta ce “Thank you, yanzu ma taci gaba da cin darajata” Ya yi saurin durƙoshewa gabanta ya ce “Ki duba Allah ki tausaya mini, zan nuna miki cewa baki asara ba, zan baki farin cikin da kika rasa zan nuna miki so da ƙauna, ban miki al’ƙawarin fari na har abada ba, amma daga gareni zaki ta samun kwanciyar hankali, Ina son ki ina tsananin ƙaunarki, zan ma kira Hajia da Papa su baki hakuri, ga Yayana Almustapha he’s here to ask ur help, zan kira Anti Biba, Anti Rahmerh, da Antin Turkey su baki haƙuri kada ki wofintar dani Please” Idanunta ya cika da hawaye Almustapha ya ce “Plx Malama Majeederh a baya bana son tarayyarku amma yanzu na amince bana ƙasar ma sbd ke na dawo ki tausayawa Abokina aminina my younger brother idan wani abu ya sameshi ba zan yafe miki ba” Majeederh jikinta duk rawa yake ta ce “Am sorry ba zan iya auran mijin Latifa ba, wlh duk duniya zata haɗu ban iya auren mijin Bestie yadda Abbu ya haramta a gareni haka Aliyu, Am sorry” Tana faɗin hakan tai cikin gidan Aliyu zai bita Almustapha ya yi saurin riƙe shi sai kawai ya faɗa jikin yayan nasa yana wani irin kuka kamar zuciyarsa zata fito….. Anti ce tsaye waya kare a kunnenta ta ce “Yawwa duk yadda za ka yi kai ka sani ka tabbatar Abraham bai auri Majeederh ba, ka sanya masa soyayyar Sona a zuciyarsa, kamar yadda Alpha ya tattara kayansa yabar garin yace baya so kasan duk yadda kayi kasa Abraham yace baya son Majeederh, ai kace mini shi ɗin ɗan babba mutum ne? Yana da nasaba mai girma ga uban dukiya?” Magana akai ta cikin wayar can ta ce “Good, sau biyu aikin ka na bani matsala gashi Kuɗi dai ina baka sosai kamar hauka, nace ka saka Majeederh ta zaba karuwa ta ƙarfi da yaji amma kace ba zai ba, saboda ƙarfin addu’a da azkar ɗin da take, hakan yasa ƙaddara tazo ta sauƙi maimakon ta zama karuwa sai akai rapped nata, kuma….,” Da sauri ta ajjiya wayar ta ce “Jawaad how many zance ka daina faɗo mini without my permission eh?” Ya ce “Sorry Maa, dinner is ready” Ta haɗe fuska ta ce “Fice ka bani waje kai ta abu kamar zautacce” Ya fita zuwa dining room. Majeederh ta fito sanye da duguwar riga wacce ta bi jikinta sosai fuskarta fresh kana ganinta kasan akwai damuwa a tattare da ita dan dai jaruma ce kawai, kai tsaye ta nufi dining room ɗin cak ta tsaya ganin Abraham zaune ɗare ɗare akan kujera suna ta tafka uban musu da Jawaad Uncle Isma’il kuma na zaune yana ta musu dariya wannan yace shi ne babba wannan ya ce shi ne babba. “Majeederh ƙarasu mana” Tsit Abraham ya yi kamar bashi a wajan ya zaro wayarsa ya shiga dannawa fuska haɗe babu alamar fara’a kafin ta zauna Uncle Isma’il ya ce “To Antin bata ƙarasu ba, ki zuzzuba mana abincin” Ta yi jim sai kuma ta zubawa Uncle Isma’il ta zubawa Jawaad ta zuba nata kaɗan, tana neman wajan zama Uncle Isma’il ya ce “Wa zai zubawa Ibrahim ɗin?” Ta ce “Uncle..” Ya ce “Ranki zai ɓaci” Ta miƙe ta nufi gefen tare da ɗakko plate ta shiga zuba masa, shi dai Khalil wayarsa kawai yake dannawa Uncle Isma’il na kallon tulin abincin data zuba masa tare da nama da yawa ta ciccire albasa da tumatir “Ya kika cire masa kuma?” Tana ajjiye spoon ta ce “Baya ci” Kallonta Uncle Isma’il da Jawaad kawai sukai tana gamawa zata bar wajan a hankali ta ji muryarsa daidai kunnenta ya ce “Thank you” Ko su Uncle Isma’il ba su ji ba, Jawaad nata yi wa Khalil surutu daman haka yake shi kamar aku, Abraham daman baya wasa da cikinsa abinci kawai yake ci sai da ya cinye abincin tas ya sha ruwa ashe tuni Uncle Isma’il yabar wajan sai Majeederh dake ƙoƙarin tashi “Hawwa’u” Dam! Zuciyarta ta buga jin sunanta raɗau abakin Abraham, ta juya da sauri da tunanin ko bashi bane suka haɗa idanu ya harɗe hannunsa a ƙirji, Jawaad ya bar wajan tayi tsaki zata bar wajan ya ce “Kina barin wajan nan ni dake ne” Ta wani kalle shi ta ce “To sannu ubana” Ya girgiza kai ya ce “Ki zauna magana nake so mu yi, bana son kuma kai hannu jikin ki balle aja mini aya” Ta ƙara jan tsaki rai ɓace ta ce “Kai da jikina har abada yaro” Ya miƙe tsaye ya ce “Idan dai kika sake hannuna ya taɓa ki to ko Uncle I da Uncle B basu isa su ƙwace ki ba” Ganin yana nufuta yasa ta juya da sauri zata bar wajan ya saurin saka mata ƙafa kamar zai taɗeta ta faɗi da sauri kuma ya cafko gaban rigarta yana haɗuwa hatta bra ɗinta tayi kamar zata faɗa ƙirjinsa ya saurin ɗan baya ya riƙe waist ɗinta sosai ta ce “Zan baka abinda bakai tunani ba, sbd kai ɗan yau ne daman ance ka haifi yaro banda halinsa wlh…” Hannunsa yasa ya cafke lip’s ɗin nata tare da murɗewa azabar da taji yasa tayi saurin riƙe masa ƙugu da duk hannunta jikinta idanunta ya yi rau rau sai da ya murɗe mata bakin son ran shi kafin ya saketa ai kowa lip’s ɗin sukai jajur sosai suke mata azaba takaici yasa wani irin hawaye zubu mata, Abraham ya tallafo fuskarta kamar mai raɗa ya ce “It’s hot?” Ta yi masa shiru ya ƙara leƙa fuskarta silently ya ce “What??” Sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka na zallar takaici jawota ya yi jikinsa ya rungumeta zata ƙwace ya ƙara matseta a jikinsa gabaɗaya baƙin ciki ne yasata kuka gashi bata da wani ƙarfin kokawa dashi ta runtse Idanunta taja jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi “Gobe za mu yi aure, ni ba zan wani tsaya roƙanƙi ba kamar su dole ya zame miki yarda” Da dukkan ƙarfinta tasa ta hankaɗe shi, ta ce “Wallahi na tsaneka bana ƙaunar ganinka dana aureka gwara na zauna ba aure ko na auri wani, ko bakai mini komai ba kayi mini ƙanƙanta da zama mijina ɗan cikina sbd kai baka da kunya wani ɗan mitsi-mitsi dakai har kai ka isa yin aure ba, wlh bana ƙaunarka” Tana faɗin haka ta shige Khalil ya zube yana riƙe kansa fargaba da tsoran rasa Jee ya wanzu a zuciyarsa… Da asuba Uncle ya tambayi Majeederh me ya yanke? Sai ta ce masa ta amince da Ajlaal shi take so, Sosai Uncle Isma’il ya ji daɗi domin shi ma Ajlaal ɗin ne ya kwanta masa, daga nan ya kira Aliyu ya bashi haƙuri akan ba zai taɓa yiwa Majeederh auren dole ba, daga nan ya kira Khalil har Parlour shima ya kura masa bayani akan ya bawa Ajlaal Sultaan auren Majeederh, Khalil kasa magana ya yi sai jikinsa daya ɗauki rawa da sauri ya fice ya nufi hotel ɗin da Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauka, sosai ya dinga neman afuwa akan Ajlaal ya haƙura ya bar masa Jee ɗinsa amma fur Ajlaal ya ce “Sorry, i wishe you all the best da zan iya dana bar maka ita, but muma muna sonta” Abraham kamar zai zauce wani zazzaɓi ya rufe shi, shikenan ya rasa Majeederh ya rasa Ƴar Madara ya rasa Maluma da ƙyar yakai kansa gida…. Gidan Uncle Isma’il ya cika da ƴan uwa hadda Mami su Raihana da Ruma kowa na family Abbu ne kawai babu, kowa jira yake ji waye MIJIN MALAMA? Tunda duk basu san shi ba… A Masjid ɗin dake layin gidan Uncle Isma’il ake ɗaurin auren abun mamaki manyan mutane sosai ta ko’ina kamar wanda jima ana sanar da ɗaurin auren, cikin masallacin cike yake sosai da mutane, Aliyu Sufyan Alhassan yasha wata dakakkiyar shadda yana zaune gefe, ga Mai martaba Ajlaal ango ya shafa farar shadda sai ɗaukan idanu take, abin mamaki hadda Abuturab wanda da gayya Uncle Isma’il ya kira shi, Jawaad na gefe daga can ɓangaren Abraham ne durƙoshe yasha wata shadda fara tas kusan iri ɗaya data Mai martaba jikinsa duk rawa yake zuciyarsa na bugawa amma ya yi imanin Jee ba rabon shi bace Maybe Allah ya haɗa su don ya rabauta da addinin musulunci bawai dan ya zama mijinta ba hakan yasa ya haƙura…… Manyan mutane da liman ne suke magana a hankali Abraham ya miƙe da sauri zai fice daga cikin Masjid ɗin daidai nan Liman ya ce…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button