Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 50

Sponsored Links

Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta tace “Faree da gaske kin yafemin dan Allah?” dan murmushi Farida tayi tace “how about nadafa miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina” cike da murna Islam tace “to tashi muje mu dafa” ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi Farida tayi tace “ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati Teejay tai posting” da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta kalleta tace “inane kitchen din? ” nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace “tashi tashi kici” ta mika hannu ta karbi wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace “Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne saisa yake kirana nadawo” Islam tadan tabe fuska tace “to Indomie mufa bazaki tsaya muciba” hararan ta tayi tana murmushi tace “sabida nai missing flight dina ko” tashi Islam tayi tsaye da sauri Farida ta maida ita ta zauna tace “dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so kici da kyau bye” murmushi Islam tayi tace “Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye” fita Farida tai daga dakin tana daga mata hannu.
Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace “kaman wari warin kalanzir” hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace “kodai akwai kalanzir agidan nanne” exotic din ta dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button