Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 64

Sponsored Links

Wuraren daya yatashi shima dan kiran sallan dayaji ne daurewa yay yamike ya shiga bayi wanka yasake yi sanan ya dauro alwala yafito ya shirya cikin dogon jean da sweater yawuce massallaci Koda yadawo Ihsan kadai yasamu afalo kallonshi tayi tace “har yanzu kan bai denaba kasha maganin kuwa Ya Khaleel wlh bakason shan magani? Bari nakawo ma abinci saikasha maganin ko” zama yay akan kujera yace “namiki booking
flight to Nigeria 10 nadare zaku tashi” murmushin dadi tayi sanna tawuce takawo mai breakfast dinshi kadan ya iya ci yature abincin yatashi daki yakara komawa ya kwanta batare dayasha paracetamol ba.
Kofa tabude ta shigo dakin ta tsaya atabakin kofa tana kallonshi dan taji lokacin da Ihsan kecemai yasha maganin, mayad da kofar tayi tarufe tazo kusa da gadon tadan rankwafo tana dan leken fuskarshi ganin ya lullube da bargo hada idon sukayi hakan yasa ta juyar dakai da sauri batare databar wajen ba ta tsaya tana wasa da yatsu, ajiyar zuciya yadan sauke yafito da hanunshi ya kamo nata zafin dataji yasa ta hayo gadon tana kallon fuskarshi murmushi yadan mata yace “kinyi kyau wife” Ya daura hanun nata akan kirjinshi yadan lumshe ido, dayar hanunta tadaura akanshi hakan yasa yadan bude ido yanda take kallonshi ne yasa ya janyota jikinshi ya kwantar da ita agefenshi ahankali yace “just headache I will be fine idan nai bacci tareda ke a kusa dani” murmushi yamata yadan rungumota jikinshi hakan yasa tai lamo tanajin yanda numfashin shi ke fita tun tana saurara har bacci itama yay gaba da ita.

Wuraren biyar da rabi Ihsan tazo ta kwankwasa musu kofan jinsu shiru gashi har anyi sallan la’asar shiya fara bude ido cikin bacci yace “come in” maganar shi ya farkar da ita hakan yasa tabude ido ta kallai suka hada ido, bude kofar da Ihsan tayi ta shigo yasa taji wani kunya yakamata tafara kokarin ya saketa dan ta tashi amma yaki, murmushi Ihsan tayi tace “Ya Khaleel shida saura fa niduk nakosa muje airport din saisa nazo natasheku” tabe baki yay yace “saima nahanaki tafiyar” dariya tai sanan tajuya tafita daga dakin ya juyo da kanshi ya kalleta yanda taketa mutsu mutsun ya saketa ta sauka, ahankali yace “muje kitayani yin wankan to, kinga yanzu am feeling much better dama dankin gudu jiyane kikasa ciwon kan dole ya kamani” dan murmushi tayi tareda boye fuskarta abayan hanunshi, dauke hanun yayi yadaura a bayanta hakan ya bayyanar da fuskarta yace “wai mesa kin cika kunya ne?” make mai kafada tayi hakan yasa yadan jawota kadan ya daura kanta akan kirjinshi yana shafa bayanta yace “inda ace Eesha na raye da hala ace ku yan biyune” dan dagokai tayi ta kallai hancinta ya lakata yace “zanbaki labarin ta wataran yanzu tashi muje muyi salla” tashi yayi yadago ta ya sauko da ita daga kan gado da sauri ta fizge hanunta ta shiga bayin ta rufo kofar ta dauro alwala ta fito tana nonnoke kai murmushi yay kawai ya shiga bayin shima.

Saida sukayi magrib sanan suka tafi airport din bayan sun biyata wani super market yasa tai shopping abinda takeso, koda zata tafi dan jirginsu yafara boarding ba karamin kuka Islam tayiba ta rungume Ihsan dan sosai taji tana sonta, daga musu hannu tayi ta tafi hakan yasa tafada jikin Khaleel tana kuka mara sauti da kyar ya lallasheta tai shiru sanan suka fito daga airport din suka taho gida.
Alwala duk sukayi shiya jasu Isha sanan yadan fita dan yayo musu take away. Koda yadawo bai sameta a dakinsu ba murmushi kawai yayi yawuce dakin Ihsan tana ganinshi ta tashi zaune dukta rude dan bata manta daren jiyaba, take away dayayo mata yabata sanan yafita daga dakin, budewa tayi taci shinkafar iya cinta sanan ta mayar ta rufe tasha ruwa tashiga bayi ta sake yin brush tafito ta kwanta abinta. Adaddafe yay nafila sabida wani sabon zazzabi da ciwon kai dayaji ya rufeshi.

Related Articles

Yunkurin amai dataji kaman amafarki yasa ta bude ido, hannu tadan mikar ta kunna wutar dakin tana kallon ko’ina takai dubanta ga agogom dake manne abangon dakin karfe uku da minti goma. kakarin aman data sakeji yasa ta mike tsaye da sauri kirjinta na bugawa tabude kofa tafita daga dakin, kanta ta daura akan kofar dakinshi adan rude tabude kofar ta shiga cikin dakin jin daga nan takejin karan, daidai lokacin ya bude kofar bathroom shima yafito adan duke ko tsakar dakin bai iya karasowa ba kawai taga ya zube akasa kaman ma ya suma ne, da gudu ta shigo dakin ta tsugunna a inda yake takai hannu arude ta taba goshin shi duka idanunshi alumshe suke ga jikinshi zafi sosai, arude tashiga jijjiga shi tana kuka, ganin ko motsi bayayi yasa ta tashi da gudu ta dauko wayarshi dake kan gadon budewa tayi hanunta na rawa number Dr Om ta Nemo a contact tai dailing number ringing biyu ya dauka “Hello Khaleel” bude baki tayi tana kokarin yin magana amma magana taki fitowa, wuyanta tashafa tana runtse idanu da karfi tana kokarin magana amma Ina takasa, sosai take kuka tana nuna Khaleel da dayan hanunta, daga ta dayan bangaren Om yace “Hello Khaleel kanajina kuwa, hello” iya karfinta take bude baki tana kokarin fitar da magana amma takasa saima wani irin zafi dataji makogwaranta nayi “Hello are you there, I guess d network is bad” katse wayar yayi hakan yasa ta jefar da wayar akan gado tana kuka jikinta har rawa yake dawowa inda yake tayi ta tsugunna tasa hannayen ta a kirjinshi tana jijjigashi sosai tana girgiza mai kai, tashi tayi da gudu ta shiga bayi ta debo ruwa a kofi tazo ta tsugunna ta yayyafamai amma ko motsi baiyiba, wani irin kuka tasake fashewa dashi tasa hannunta tana shafa wuyarta tana bude baki wani irin runtse idanu tayi sabida azaba tana nishi sosai “Ya’a’a'” tafada da wata irin murya, ahankali taga yadan bude ido dasuka kankance sukai jaa ya kalleta da sauri ta daura kanta akan kirjinshi jikinta har rawa yake sabida yanda take kuka, tashi tayi daga kirjin nashi ta taimaka mai ya zauna yajingina da bango yana kallonta da idanunshi dasuka xhanza launi, da dan gudu tafita daga dakin kitchen taje ta kunna ruwa a heater kettle nan da nan ya tafasa ta zuba a mug, tea ta hadamai mai kauri sosai ta dawo dakin ta ijiye agaban shi wajen drawer taje ta bude ledan magungunan ta tabude tana cicciro magungunan kwalin tana dubawa tana yarwa, paracetamol datagani ta dauko tadawo inda yake ta tsugunna tabaro guda biyu tasaka mai abaki yatsine fuska yay da sauri takai tea bakinshi hakan yasa yadan sha ya hadiye maganin, ahaka ta dinga bashi har yasha kusan Rabin kofin yadan mata murmushi kadan yace “am okay” sosai yaga tafashe da kuka tahau kan jikinshi ta shafa fuskarshi tareda mai alamun sorry da hannu, lumshe mata ido yay yabude hakan yasa ta rungume shi tsam tsam tareda sake fashewa da kuka, sunfi minti uku ahaka motsin dataji yanayi yasa ta ciro kanta daga kirjinshi ta kallai baki taga yana cijewa da sauri ta tashi daga jikinshi tareda kamamai hannu ta tadashi gado tasa yahau itakuma ta koma tadau mug din dayasha tea dashi tafita daga dakin takai kitchen sanan ta dawo dakin ta rufe kofar bayin daya bari abude, ahankali yake binta da kallo dayar pingilar rigar baccin dake jikinta. Kashe wutar dakin tayi sanan tadawo kan gadon itama tahau ta shige jikinshi sosai ta rungumoshi tasa hanunta tanata shafamai bata irin yanda akema yaro da baida lafiya dan hanun kuma tana goge hawayen dasuka kasa dena zuba dan wani iri taji tanaji mutumin dayake ta kula da ita ashe baida lpy kasa dena kukan tayi sai share hawayen take da bayan hannu hanunshi taji akan samar fuskarta ya share mata hawayen sanan ya rungumeta tareda matseta ba takawo komiba dan tazaci ciwon ne kesashi haka, ahankali yakai hanunshi bayan rigarta yadaura akan igiyar da ake kulle bayan rigan dashi ya warware.
[6/29, 11:47 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button