Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 9

Sponsored Links

Washe gari jirgin Rana sukabi suka koma yola, haka gidan ya dawoma Ammi da kanen Khaleel wani iri, ba karamin wani iri Ammi takeji ba da kyar ta lallaba kanta ganin zazzabi nason kama su Ilham.

Yau kusan watan shi daya kenan a yola, yana zaune a dakin Goggon wacce ta hadamai fura take bashi abaki, yana sanye da farin t-shirt wacce ba karamin dambe suka sha da Yusuf ba kafin yabari asamai, ahankali Goggo ta ijiye kofin furan, tadau handky ta share mai bakin shi da rigar jikin shi dan gabaki daya fura zubewa yake wanda ya shiga bakin shi ne yake lashewa, Abba dake tsaye akansu ta kalla tace “Sama’ila ni ni wlh jikan nan nawa tausayi yake bani, ace yaro yafita daga hayyacin shi baima sanmuba yanzu” kecewa tayi da kuka sosai ta kwance bakin zani tana share fuska zama Abba yayi yace “to Mama idan kina kuka haka mumuce mene, namayi magana da baban shi dazunan, jibi zamu fitar fashi waje saudiyya zamu, akwai wani likita dana sani a wajen yace mukawoshi in sha Allah zai sami lpy har magana zai fara” da sauri Goggo tace “dagaske Sama’ila” gyada mata kai Abba yayi tace “Alhamdulillah” shafa kan Khaleel din tayi tace “Allah nagode ma, dazaran ya warke zan nemo yarinya yar kirki mai hankali da natsuwa na auramai hakan zaisa ya wartsake” tashi Abba yayi yace “bari nadan fita” “adawo lahiya” part din Mujiba yatafi a uwar daki ya sameta tana kan gado tana watsapp baiko kalleta ba ya bude wardrobe babban rigar shi ya dauka yasa sanan yace “kihada min kaya jibi zamu fita da Khaleel waje” adan zabure ta kalli Abban tace “Alhaji maisa zaka wani kashe kudin ka Yaron nan yariga ya haukace bazai taba warke wabafa” wani irin kallo dayamata yasa tadanyi murmushi ta kwantar da murya tace “bahaka nake nufi ba, ni gani nayi tayaya treatment din zaiyi progressing bayan baya cewa uffan balle asan meke mai ciwo daka bari yafara magana tukun, duk kawani damu saikace Yusuf ne baida lpy” wani irin kallo ya watsa mata ya nunata da yatsa cikin fushi yace “ki kiyaye ni Mujiba, ki kiyayeni fa, and Yusuf da Khaleel basu da bambanci awurina duk yayana ne, baki isa kiraba kan family naba kinajina ko” fita yay daga dakin ranshi abace, sosai abin ya konama Mujiba rai, ai wlh yanda naso kaninka yakini, dasonshi nake wahala da dawainiya, bankara ganin farin ciki ba, haka danshi ma zai wahala bazai taba samin farin ciki ba arayuwar nan ba, ko Allah ma nabaya na, ai saisa ya kashe yarinyar batare danai komiba, warke wa dai bazaiyi ba bi’iznillahi, koma ya warke farin ciki yakare mai arayuwa. Tsaki tayi ta wurgar da wayar ta tashi ta shiga bayi.

Saudiyya.
Ba karamin cigaba aka samu a treatment din Khaleel ba, dan yanzu dazaran yaji kiran salla zai tashi yay alwala yayi, magana ne idan anmai saiyaga dama zai amsa, gabaki daya ya chanza ya dawo shiru shiru kaman ba Khaleel mai rahan nan ba, idan Ammi tabashi abinci zaici kadan ya ijiye mata, idan yagaji ya kwanta ya daura kanshi akan cinyar ta ya lumshe ido, sosai aka dage damai addu’a dudda haka sunji dadin yasoma samin cigaban nan. Dr yahana amai maganan Eesha ko kadan. Ganin cigaba sosai yasa Dr ya sallame su suka dawo Nigeria Ammi da Daddy suka wuce Abuja, Baffa da Yusuf suka wuto dashi nan yola.
[6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Related Articles

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button