Mijin Malama Book 1 Page 16
MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 1kne
Pay….0811923761617
Tafiya suke a nutse duk da ya yi mata nauyi a baya shekarun shi biyar a duniya amma yana da girma jiki ga shegen wayo. Ya ƙara shigewa bayanta ya ce “Mamina”
“Little babe” ya leƙo ta gefen fuskarta ya ce
“Mamina ke baki da mota? Me ya sa baki zo wajena ba, me ya sa kike mini faɗa ai nayi ƙarfi duka nakewa yara, I will fight, and I will win”
Murmushi kawai ta yi masa a zuciyarta tana mamakin yadda da yawan lokaci turanci ke zama a bakin shi, bai ci ace daga fara karatun shi ya fara turanci har haka ba. Jin ta yi shiru ya ce
“Get me down, Mami”
“No, little ba zaka iya tafiya ba” ya fara buga ƙafa a bayanta tare da ƙoƙarin sakin kuka. A hankali ta tsaya tana mai da numfashi kana ta sauke shi a ƙasa ya yi mata murmushi yana rufe Idanu tare da suɗe baki na daɗin ice-cream. Gani tayi ya durƙosa a gabanta ya ce “Ni ma zan rama muki, haka muke a school”
“What! wa zaka goya?’
Ya tura baki gaba ya ce
“Ke Ƴar madara, ai duk wanda ya goyaka kai ma kai masa haka ko Mami?” Ta tsora masa idanu surutun shi na bata mamaki ƙwarai ta sunkuya daidai tsayin shi ta shiga kaɗe masa gasar jikinsa tana shata samar kan shi daya hana a aske ta ce “To ai uwa duk abin da ta yi wa ɗanta daidai ne”
“Kyautatawa nada daɗi kin ce Mami?” Ta jinjina masa kai cike da jin daɗi tana faɗin “Shikenan ka bari idan ka sake girma ka goyani” ya dinga tsalle da murna zai goya Maminsa ƴar madara.
“Promise?” Ta miƙa masa hannu ta ce “Promise” ta kama hannunsa suka cigaba da tafiya tana jin zuciyarta daɗi ga wani farin ciki yau zata kwana da Little daman sabgar shagalin musabaƙa ya sanya ta kai shi can tunda ba kowa yake kula da shi a gidan nasu ba. Tun daga can har gida suka ƙarasu a ƙafa suna tafe yana mata surutu wasu ta gane wasu kuma kamar wani yare nada ban haka yake. A daidai ƙofa Majeederh taci karo da Latifa taja baya tana ƙara riƙe hannun Little dake ƙoƙarin tafiya wajan daya hango yara age mate ɗin shi suna faɗa. “Yanzu na shiga ake ce mini bakya nan” cewar Latifa. Ta lumshe Idanu cike da gajiya ga azumi don ma rana ta fara sanyi a gajarce ta ce “haka ne” Latifa ta ce “Ki ce ɗan rigima kika ɗakko daman tun da mu ka yi waya nake son tambayarki shi sai kuma naga you’re not on the mood na share” Majeederh ta ce “Ayya, muje” suka shiga cikin gidan a tare tana shiga ta jiyo muryar Uncle Isma’il ta faɗaɗa murmushinta tana sakin hannun Little ta shiga parlourn Abbu. Uncle Isma’il ne da Uncle Bello suna zaune suna tattaunawa akan maganar Widad da kuma kuɗin Ruma da za a kawo. Ya Uncle Bello ya dubi Majeederh ya ce
“Hawwa’u an dawo? Yanzu ake ce mana bakya nan” ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da ladabi ta ce “Eh Uncle, an yini lafiya” “Allahamdu lillahi” ya bata amsa yana mai jin tausayinta har ranshi sbd zurfin ciki da take da shi ga yadda duk al’amarin rayuwa yake jirkice mata. “Uncle..,” Uncle Isma’il ya yi saurin ɗaga mata hannu cike da ɓacin rai da damuwa ya ce “Kin kyauta tunda tsarin da ki kaiwa kanki kenan, ba bu abin da zamu iya ikon ki ne ke kike da kanki Hawwa’u” zuciyarta ta buga tsoro da fargaba suka risketa a wannan lokacin idan aka tsaga jikinta ba lallai a samu jini ba sbd tsabar fargaba. Amma sam fuskarka ko yanayinta bai nuna hakan ba. Cikin sanyin murya ta ce “Me nayi Uncle?” A hassale kamar zai daketa ya ce
“Ni kike tambaya me kika yi ko Hawwa’u? Yanzu yaron nan Imran kwanaki yazo yana son ki har iyayensa ya fara yunƙurin turawa, ban san mene ya faru ba naji maganar shiru, yanzu kuma na samu labarin zai kawo kuɗin Rumana na tambayi Abdul’aziz ya ce da kanki kika cewa Imran bakya son shi kada ki sake ganin ƙafar shi?”
Duk da sanyin shigewar hadari bai hana Majeederh jin wata zufa ta yanko mata ba, daga ina wannan al’amarin ya bayyana waye ya shirya mata maganar da bata san da ita ba, waye yake shirin wargatsa burinta?. Ta kasa cewa komai yawun bakinta ya maƙale ga ƙishin azumi ganta ya shiga juyawa. Uncle Isma’il ya gyara zama domin ya fi kowa zafi akaf familyn Khan.
“Duk abin da ya faru ki kuka da kanki, ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, itikafi rayuwa kaɗai zai sanya ki kai kanki tubalin tundun mun tsira, idan ba sukike rayuwar duniya ta baki naki kason ba, ina cewa akan idanunki aka haifi Widad? Sa’ar Aaliyyah ce amma aurenta za ayi, akan idanunki aka haifi Du’a Yaronta ɗaya ciki ne da ita yanzu, shi ne kin samu mijin aure zaki wasa da damarki akan wani karatu? Anya lissafi da burin zuciyarki da kwaɗayin ganin kin samu wadatacce ilimi ya miki adalci? Hawwa’u aure da haihuwa da arziƙi na Allah ne, kuma lokaci ke wanzar da samuwar su kada ki rufe idanunki akan wani abu wanda bashi da wani muhimmaci, ke ba a bin kunya bane ace saurayin da yake son ki ya koma wajan ƙanwarki, baban abin takaici ma wai ke ce da kanki kika lamumce masa auren Rumana, Goodness what noises? Meke damunki ne?” Majeederh ta fara shiga ruɗani da fara kokwanto anya ana sonta a gidan? Me ya sa ake shirya mata abin da bata sani ba? Ta ɗago kai a hankali tare da zare liƙab ɗin kanta, fuskarta ta yi jajur cikin muryarta mai sanyi kamar wacce take shirin yi musu shagwaɓa ta ce “Uncle ka yi haƙuri, ka zaɓa mini mijin ko a gobe ne” Rashin sani ya fi dare duhu, rashin sani baƙo ya sha ruwa wanka, sun kasa fahimtar ita kanta a ɓukace take da yin aure, babu abin da take sha’awa irin ta ganta gidan mijin babu abinda ke birgeta irin ta juya taga nata mijin a gefenta. Uncle Bello ya numfasa a lokacin ya ce
“A’a ba ayi haka ba, ai darajarki da kimarki ta shige a nema miki mijin aure, kaf yaranmu ba wanda muka sadakar ko zaɓawa miji ba zamu fara a akanki ba, kin yi kuskure tun farko sai ki gyara ki je Allah ya zaɓa mafi alheri” Uncle Isma’il ya ce “Wallahi kin ɓata rawarki da tsalle Majeederh iliminki bai amfana miki da komai ba…..” “Uncle Mami na kakewa faɗa?”
Siririyar Muryar yaron ta tsayar da Uncle Isma’il daga yin magana. Sai a lokacin Abbu ya ɗaga kai ya ce “To rasai yanzu za a san ka dawo, ko zaka rama mata?” Little ya dinga kallon Uncle Isma’il yana huci idanunsa suka kaɗa tare da yin jaa wata kalar zuciya ce da yaron kamar kuturu ya shiga surutu a ranshi bakinsa kawai ke motsawa.
Cikin sauri Majeederh ta kama hannun shi ta ce “Say sorry to him” ya yi shiru idanunsa ƙuri akan Uncle Isma’il ganin yadda ya sanya Maminsa a gaba yana mata faɗa gashi har fuskarta tayi jaa daman ta haka yake gane kukan zuci take. Majeederh ta finciko Little ta ce “Ka bawa Uncle haƙuri” ba tare daya kalleta ba ya ce “He is shouting at you”
“He’s my Father, am i your mother, na ce ka bashi haƙuri, say sorry to him” ya kafe yaƙi cewa hannu Majeederh ta ɗaga hannu ta zabga masa mari nan take yatsun hannunta ya bayyana a fuskar shi duk da kasancewar fatar shi baƙa. Cikin ɓacin rai ta jawo shi har gaban Uncle domin gani take idan bata hukunta shi ba a haka zai tashi da rashin kunya da shiga sabgar da babu ruwan shi.
“….Say sorry to him..”
“Uhm, Allah ya shirya ya kyauta, tun baki haifi naki ba kin fara dakon wahala Majeederh?” Cewar Uncle Bello Abbu ya ce
“Hankaka mai da ɗan wani naka kenan, kin kyauta kina riƙe wanda yake zagine yayyina”
Idanunta ya kaɗa sosai ta ce “Don Allah Uncle ka yi haƙuri ba zai sake ba”
Ta miƙe tana kama hannunsa lokacin Latifa ta gaji da jiranta har ta tafi gida. Ta samu Aaliyyah ta dawo daga makaranta tana shirya abincin rana lunch. Raihana na zaune ana waya da saurayi. Babu wanda ta kula sai Aaliyyah dake cewa “Sannu da dawowa Anti Jeederh” ta shige ɗaki tana jinjina kanta alamar “Yawwa” suna shiga ta saki hannun Little tare da ɗakko bulala ta waya ta kama hannunsa ta zirara masa guda ɗaya
“As form today na ƙara jin kayi magana da babba sai jikinka ya faɗa maka” ta ƙara zirara masa hannun ya taro jini amma bai motsa ba sai cewa ya yi “Faɗa ya miki ƴar madara” Majeederh ta ware Idanu tama rasa me za tayi sai kawai ta miƙe tare da shigewa Bathroom tayi wanka da Alwala ta wanke fuskarta sosai har jan fuskar ya daidaita domin ta fahimci sauyin fuskarta yake sawa Little ya fahimci halin da take ciki, bata taɓa ganin yaro mai fikira da shegen wayo kamar shi ba ga ɗan banzan wasa da shiga faɗan da bana shi ba. Duguwar riga ta sanya ash ta saka hijabi a kan idanunsa tayi sallah har sallar Asr tayi Asstagafirullah na lattin da tayi kana ta fara azkar na yamma ta dube shi fuska a haɗe ta ce “Sallah” da sauri kamar zai kifa ya shige bathroom. Babban abin da yake bata mamaki kafin ya yi sallah sai ya duba ko’ina yaga ita kaɗai ce a ɗakin yake yi jikinsa har rawa yake sbd tsoro ta rasa dalilin haka. Yana idarwa ta dawo kusa da ita a hankali ya ce “Sorry Mami”
Tayi shiru fuska haɗe sosai ya marairaice ya ƙara cewa “Sorry”
Sai a lokacin ta ce “Uncle zaka bawa” ya maƙale ka faɗa ya ce “I hate him, faɗa yake miki” wata kalar tsawa ta daka masa tare da nuna masa waje ta ce “Out”
Dai-dai lokacin Aaliyyah na shigowa ta ce “Mun shiga wannan tsaiwar ai ta sa na kusa sakin fitsari a wando, wai little kikewa tsawa haka?” Idan Majeederh ta gini ya motsa Majeederh ta motsa. Aaliyyah ta ja hannunsa suka fita yana tirjewa shi a wajan Majeederh zai zauna duk da tsawar da tayi masa. Har akai sallar Magriba Majeederh ta sha ruwa tai sallah Idanunta bai ƙara ganin Little ba, a wajan Mami take ji wai ko abinci yaƙi ci ya fito waje sun yi faɗa an fasa masa kai. Sosai tai mamaki babu yadda za a yi aci galaba akan Little a kullum ita take bada haƙuri ta tabbatar hakan baya rasa nasaba da faɗan da tayi masa. Tana son ta tambayi yana isa amma girman kai da nauyin baki irin na Majeederh sai kawai tayi shiru. Cikin dare wajan ƙarfe ɗaya taji saukar numfashi a jikinta, Numfashin mai ɗauke da zafi da buɗe Idanunta da suke ciki da bacci ganinta ya sauka akan Little dake rawar sanyi kayan safe ne a jikinsa har yanzu ta buɗe ido da kyau tare da taɓa wuyansa jikinsa zafi zau bakinta har ɓari yake ta ce “Little, little” ya buɗe ido yana ganinta ya ce “Sorry Jee Mami” bata kula shi ba ta ɗauki paracetamol na ruwa tare da ɗora shi a cinyarta zata bashi maganin ya girgiza kai ya ce “Ba zan sake ba ƴar madara, na daina Jee” jin ana ce mata Anti Jeederh shi kuma ba zai iya faɗa bakiɗaya ba ya sa yake cewa Jee, sai watarana data bashi alawar madara ya ce da Maminsa da alawar madarar suna kama tun daga nan yake cewa ƴar madara. Ta ɗauke kai ya ƙara sakin jiki yana kwaɓe fuska ya ce “Zan sake ba Mami, zan sake ba” ta saki fuska tana murmushi ta ce “Ok good boy I forgive you” da sauri ya shige jikinta ya rungumeta jikin nan nasa zafi sosai ta shafa kansa taji ya saki ajjiyar zuciya da sauri ta taɓa cikin shafal ba komai da alamar yadda yunwa ke damunsa ta ɗago shi za tayi magana taga har bacci ya ɗauke shi a hankali ta ɗauke ajjiyar zuciya tare da jansa jikinta ta rungume shi wani irin son shi na ƙara ratsa zuciyarta…