Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 18

Sponsored Links

MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 (1k)
08119237616
Nimcyluv19
Lokacin data koma gida ta same su duk suna breakfast Mami ta ce “Majeederh danƙi baya cin ƙosai shi ya sa ban kira shi ba” Majeederh ta san babu abin da Little baya ci kawai dai bata taɓa gwada bashi ƙosai bane balle ta ce. A hankali ta jinjina kanta kawai alamar “Eh” kana ta nufi cikin bedroom ɗinta. Ta samu Little a tsakiyar gado ya yi ɗai-ɗai tare da langwaɓe kai kamar mara lafiya ta yi murmushi tana ɗauke kai ya ce “Mami yunwa ina ji” a taushashe cikin sanyin murya ta ce “Na sani, bani 10 minutes”
Ya ɗaga mata ta fita wajan 15 minutes ta dawo hannunta ɗauke da plate ɗin Indomie gefe kuma ta soya masa ƙwai sai ƙamshi suke. Yana ganinta ya miƙe tsaye yana kyakkyawan murmushi tare da tsalle ya ce “Idan na yi kuɗi zan baki kuɗi da yawa”
“Aikin me za ka yi” ya ɗaga kai sama alamar tunani kafin ya watsa hannu baya ya ce “Zan samu kuɗi, naiwa duk wanda ya saki kuka duka” “Allah ya shirya ka ya yi maka albarka”
Ya yi murmushi da kyawawan haƙoran shi ta shiga bashi Indomie a baki yana zaune akan cinyarta. Bashi abincin kawai take amma a zahiri tunanin yana wani wajan daban ita kanta ba zata iya lissafa inda tunanin nata ya je ba,idan ta tafi wazai kula mata da Little? Wazai jure rigamar shi da ɗakko mata magana da yake? Tana wannan tunanin ta ji yatsun shi biyar a cikin bakinta ya tura mata wainar ƙwan data soya masa, ta zare idanu cike da maɗaukakin mamaki ta kasa magana sbd ya yi mata yawa a baki Little ya dinga tun tsire dry. Ta ɗaga hannu kamar zata dake shi ya yi saurin rungumeta yana cewa “Sorry Mami” hugging nasa back ta yi tana shafa kansa tana gama bashi ta miƙar da shi tsaye akan gadon ta kama hannunsa ta marairaice fuska ta ce “Little” “Mamina”
“Za mu gidan Uncle Isma’il yanzu” nan da nan ya haɗe fuska kamar bai taɓa dry ba zuciyarsa ta motsa ya yi ƙasa da kansa. Ta yi murmushi domin ta san za a rina an saci zanin mahaukaciya.
Ta leƙa fuskarshi ya yi saurin rufe Idanu ta ce “Ba zaka ba?” Ya ɗaga kai da sauri ta ce “To ni zani, ka zauna a gida”
Ya maƙale ka faɗa ya ce “Mami mu zauna a gida” “Dole za mu, ai Uncle Isma’il ɗin baya nan ka ji kuma a bayana zaka goyaka zan” ya yi saurin cewa “Baki da Kuɗi?”
“A’a kawai tafiyar ƙafa akwai daɗi” Ta tallafo fuskarsa ta ce “Don Allah banda faɗa ka zama nice har mu taho yau ɗin zan zan maka siyayya harda motar da ka ce”
“Har bindiga?” Ta kame fuska tana ɗauka shi zuwa toilet ta ce “A’a, ko soja zaka zama?” Ya yi mata shiru. Ruwan wanka ta haɗa kana ta ɗaura masa towel ta cire masa kayan tayi masa wankan tana mamakin baƙar fatarshi kamar ƙara mata baki ake amma baƙin irin mai kyau ɗin nan da ɗaukan Idanu. A wajan saka kaya ma faɗa sosai shi baya son manyan kaya dole ta saka masa wata brown ɗin t.shirt mai photon tiger a jiki sai wando 3gauter kayan su kayi masa wani irin sahihin kyau tare da amsar fatar shi. Tana gyara masa sumar kai ta ce “Ka tsaya na shirya ko ka fita parlour” ya ce “to”
Tana shiga wanka ta ya fita parlour ya leƙa yaga Aaliyyah ta ce “Big boy yau sai ina?” Ya lumshe idanu ya buɗe ya ce “Da Jee zamu” Aaliyyah ta ce “To daman ka isa ka fita kai ɗaya? Zo na yi maka photo” ta tsayar da shi a gabanta ta shiga yi masa photo suna tsaye Raihana ta fito ta ce “A’a ɗan baƙi na Anti Jeederh, kaga yaro mai uwar rana” bai kalleta ba daman jininsa bai zo ɗaya da ita ba. Little yana da wanne irin hali ga shegen wayon masifa kamar wassafa masa wasu abubuwan ake. Duk wanda suke takura rayuwar Majeederh ya haddace su tar kuma baya kula su. Raihana har ranƙwashin kansa tayi ta ce “Miskilin banza, daga gani uwarka fama tayi dakai kafin ya ɓata” “Mamin?” Ta ce “Uwarka na ce, ko an faɗa maka MAJEEDERH ita ce Uwarka?” Ya yi shiru kawai domin baya fahimta gabaɗaya. Suna nan yana yiwa Aaliyyah surutu yana itama zai siya mota bayan ya siyawa Maminsa ƙatuwa “Wato dole sai ka nunawa kafi son Maminka, to ai Mamin taka tafi so na” ya maƙale murya ya ce “A’a” Aaliyah ta yi masa gwalo ta ce “Ohho, wooo Mami ta fi so na akan ka” nan da nan ya haɗe fuska duk da yaro ne amma ya tsani ace Mami bata son shi. Aaliyyah za ta yi magana ya ji an sakar mata ranƙwashi akanta. Ta kwaɓe fuska ta ce
“Kai Anti Jeederh akan Little zaki dakeni” Little ya yi tsalle sosai ya ce “Mamina” Majeederh dake tsaye sanye cikin shigarta as usual abaya ce mai kyau da ɗaukan hankali ta yi rolling kana ta ɗora liƙab. Cikin wani sabon yanayi data samu kanta ta ce “Ki kiyayeni Aaliyyerh” Aaliyyah ta tura baki ta ce “To Anti Jeederh ai da gaske kin fi so na” Little ya kalli Majeederh yana jiran ya ji me zata ce. Sai bata ce komai ba ta kama hannunsa zuwa bedroom ɗin Mami ta sameta zaune ana ta buga waya ana faɗawa ƴan-uwa an kawo kuɗin Rumana Dubu ɗari biyu cif. A sanyaye ta ce “Mami na ta fi” Mami ta ce “Zuwa ina?” “Gidan Uncle Isma’il, Yaya Bilkisu na kirana” Mami ta ce
“To to na ji, yanzu Ruhuma zata wajan Widad maganar ankon biki Imrana ne zai kaita na ji ma ta ce yana hanya ki bari ku ta fi tare, kici arziƙin ƴar-uwarki ko?”
Bata son musu sai kawai ta ce “To” tana fitowa ta ja hannun Little su ka yi waje. A bakin ƙofa taci karo da Latifa cikin shigarta riga da skirt na atamfa ta yafa mayafi ta kalleta sosai sai bata ce komai ba. Latifa ta yi dry ta ce “A’a fa yadda kike takura kanki da zafi cikin duguwar riga da liƙab ni ba zan iya ba, shi imani a zuciya yake” Majeederh ta ce “Wane ya yi maganar imani?” Latifa ta ɗaga kafaɗa ta ce “yanzu zaki fara faɗar na bayyana tsaraici ki shiga kawo fatawa kala-kala, ke dai ka san ko a malamai tsaurin ra’ayi zaki” Ita dai Majeederh bata ce komai ba Latifa ta sake cewa “Sai ina?”
“Gidan Uncle Isma’il” “mu je na rakaki” tafiya suka fara a hankali Latifa ke surutu ita ɗaya domin Majeederh idan ka ji maganarta Little ne ya ce wani abu ko da Aaliyyah da suke Uwa ɗaya Uba ɗaya bata fiya hira da ita ba, sai dai faɗa idan ta yi kuskure akan abu. Tun da ya karyo kan motar shi idanunsa ya sauka akanta, wani irin maganaɗisun abu ya shiga fisgarsa zuwa gare ta. Ya tsorawa yatsun hannunta idanu wanda suke ɗauke da Little dake kafaɗarta a hankali yake lura da juyawar Idanunta tana bubbuga bayan yaron tafiyar a hankali mai cike da ɗaukan hankali wani abu ya ratsa zuciyarsa irin abun nan da ake kira da soyayyar fari, har suka zo daidai motarshi bai kula ba sai da suka gilma kaɗan ya sauke numfashi tare da buɗe motar shi ne ya fito. Kyakkyawan matashin saurayi mai fama da rufin asiri daka gani yanzu yake ji da samartakar shi. Fari ne kyakkyawa mai matsakaicin jiki nutsuwa da ilhama a tare da shi, yana sanye cikin kyakkyawar shigar dake nuna kamalar shi. Amy green ɗin shadda ce a jikinsa ya murza hula saman kansa zai ƙamshin turaren (Thierry mugler). Ƙamshin dake narkar da dukkan wata zuciyar ƴa mace. Ya ƙarawa tafiyarsa sauri harya tarar da su tunda ba wani sauri suke musamman tafiyar Majeederh wacce take kamar an zare mata laka. “Assalamu alaikum” Cak suka tsaya tunda sun san darajar sallama babu cancantar suna tafiya kuma wani na binsu. Ƙamshin Thierry mugler bai firgita Majeederh ba, deep down na zuciyarta addu’a take Rabbil izzati ya sanya wa’adin zamanta a gidan Abbu ne ya zo ƙarshe, addu’ata take Allah ya sa mai rusa zuwanta karatu ne ya bayyana, Al-hakkamu sarki kowa da kowa ya ƙaddarta masa ikonsa a yanzu nan, Allah ya da mai yaye mata damuwar dake sanyata azumi ne ya zo. Ta rufe Idanunta tana jiran ƴar manuniyyarsa ta tsaya akanta. “Wassalam” cewar Latifa tana duban matashin wanda ya amsa komai na kamalar mutum. Ya dinga kallon Majeederh ba zai ce ga kalar kyan fuskarta ba, amma yatsunta sun bayyana wace ita abubuwa da yake ji game da ita sai ya ji sun ninku ainun kamar zubar ruwan sama ya yi da hadari ya ƙara kankame. Cikin wani irin al’amara da gilamar wasu sabbin ƙaddarori masu wahalar fasaltasu ba tare da sanin abin da yake faɗa ba ya juya gabaɗaya kan Latifa ya ce “Amincin Allah ya tabbata ga ma’abociyar kyau da kwarjini, fatan san samu number wayarki ganin akan hanya kuke” a baɗini kalamar direct domin Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Ya zayyana su amma a zahiri tubalin ginin maganarsa da yadda ya zayyana su ya nuna mai fahimta da ganin komai cewa da Latifa Omar yake. Latifa ta yi jim ta ce “Ni, ko ita?” Ya ɗan tafe baki kaɗan ba tare sanin ainahin abin da yake ba ya ce “No, dake nake kyakkyaw” Dam! An koma. Zuciyar Majeederh ta bada sauti ta ƙara rufe Idanunta Allah ya sa zalamarta bata fiyi ba balle ta kunyatar da ita. Majeederh ta ƙara lamuncewa zuwa karatun nan nata na daga cikin ƙaddarorinta masu girma. Latifa ta ce “Amma sauri muke” “Kuyi mini alfarma ba don na isa a yi mini ba, sai dai ta yaku kare mutumci ku shiga na ƙarasar daku” ya faɗa yana haɗe hannu bibbiyu. Latifa ta juya ta kalli Majeederh ta ce
“Malama Majeederh ke ce me matsala Kinga Little har ya yi bacci ki zo mu je” Bawai fuskarta suke gani ba,amma ta ƙara kame kanta bata da wani kuzarin yin magana. Ya juya a hankali da ɗan sauri kuma ya buɗewa Majeederh ƙofa ta shiga a nutse da addu’a bakinta. Ya buɗewa Latifa Omar gaban motar ta shiga. Tafiya suke a nutse ya gyara zama ya ce “Sunana Barrister Aliyu Sufyan Alhassan” “Nice” Aliyu ya shafa gemu ya ce “A gida more especially Hajia suna ce mini Zaki, am the second born of my parents, ina da babba yaya Almustapha, mahaifina sunan shi Sufyan Alhassan yana nan tare damu, ya su nayi aikin jarida na ƙi, to ya na iya abincina yana ga Shari’a, sai mahaifiyata we call her Hajiya, I love my mother more than anything dake duniyar nan tamu, na yi karatu mai yawa akan Shari’a now an working with Shari’a court of appeal ban jima da fara aiki ba” Tunda ya fara magana Latifa ta rufe Idanu sosai har cikin zuciyarta Aliyu ya kwanta mata irin mijin da take so daka gani zai yi haƙuri sosai. Har suka isa gidan Uncle Isma’il Majeederh ko tari ba tayi ba ta rungume Little kamar zata mayar da shi ciki, lokaci zuwa lokaci Aliyu ya dinga kallon Majeederh ta madubi, duk sanda ya kalleta sai ya sauke numfashi a ɓoye. Suna tsayawa ta buɗe ƙofa ta fita ta shige ciki, da sauri kamar wacce wani abu ya biyota. Innati dake maƙale a bayan labule ta buga tsalle tana faɗin “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, wahala haula wala ƙuuwata, uban waye a wannan wajan?” Majeederh ta shiga tana sauke numfashi Innati ta ce “Amma dai Allah ya isa Kululu, Allah ya isa saura kaɗan na saki gudawa ɗaukan hakƙin nan har ina? Ashe ƙatuwar jahila muke zaune da ita kinsan alhakin da kika ɗauka? To wallahi ba wani yafewa nayi ƴar banza da fuska kamar karas” Majeederh ta tura baki tare da kwaɓe fuska ta ce “Ki barni” Innati ta riƙe haɓa ta ce “Na barki ba? Idan na barki a duniyar nan Kululu na kama ubanwa? Wa kike da shi daga duniya har lahira wanda ya shige ni?” Majeederh dai ba tayi magana ba ta ɗaga liƙab ɗin fuskarta Innati ta zabga sallati ganin yadda fuskar Majeed ta yi jajur kamar jini ya kwanta. Innati ta kwasa a guje zani na faɗuwa ta shiga faɗin “Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Isma’ila masifa ta faɗo mana uban kowa ya yi ta kansa Aljana mai kama da Kululu a ɗakina….

*A yi karatu a nutse, a fahimta a ilmance, a nishaɗantu. Muna nutsawa a labari zaku kasa bacci da sukuni. Soyayya ce mai wahalar gogewa, ƙaddara ce mai wahalar fahimta. Babu batun sadaukarwa faɗa ne akan Soyayya!*

Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a yi weekend cikin farin ciki…. 08119237616

Related Articles

Nimcyluv20
“Masifa da bala’i, Kamarni har wata Aljana ta isa ta firgita? Ina Isma’ila ya zo ya yi mini iyaka da wannan Aljanar tun kafin raina ya ɓaci” Innati ta faɗi hakan jikinta gabaɗaya rawa yake na fargaba da tsoro, tuni ta yi wurgi da zanin jikinta sai ɗan tofin daya rage mata banda haka tsirara za ta yi.
Uncle Isma’il daya fito a hargitse sbd jin kiran shi da Innati ke yi ya sa yana zuwa ya ce “Innati lafiya dai? Mene ya faru?”
Ta girgiza kai ta ce “Lafiyar kenan, maza maza a haɗa mini kayana yau sai gidan Bello, ba zan zauna matarka da kasheni ba, ina sane ita take tura mini Aljanu” Uncle Isma’il ya kusan tuntsirewa da dariya amma babu hali duk abin da ya kuro ɓera da ga wuta, ya fi wutar zafi. “Majeederh ta ƙarasu?” Ta zare idanu ta ce “Wata abace haka? Ka je dai kaga turan da akai mini da wata Bafullatanar Aljana” Uncle Isma’il ya bar Innati a tsaye, tare da nufar ɗakinta. Yana shiga ya samu Majeederh durƙoshe a saman gwiwoyinta ta dafe kanta da hannu bibbiyu wanda yake bazaranar rabe mata gida biyu sbd tsananin ciwon da yake mata, ta rufe idanu sosai sbd komai bibbiyu take ganinsa a cikin idanun nata. Uncle Isma’il ya zuba mata ido cike da tausayinta yasan duk abin da zai sanya Majeederh cikin wannan yanayin ba abu ne mai sauƙi ba. Ya dubi Little dake tsaye ya ɗora kansa a bayanta ya saƙalo wuyanta tare da yin lamo, yanayin Mamin tasa ya taɓa kuzarin yaron. Ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake ɗakin na Innati, cikin kulawa ya ce
“Hawwa’u!” Ta yi sauri ta ɗago kanta tare da ƙaƙaro murmushi ta ɗorawa fuskarta matsayin dole. Cikin sanyin murya kamar kullum ta ce “Ina yini Uncle?” Ya ce
“Lafiya” ya yi jim kafin ya ɗora da “Ke kika firgita mini uwata ko?” Ta ƙara yin murmushi kamar ba za ta yi magana ba ta ce
“Da Aljana take haɗani fa” Ya yi murmushi ya ce “Dole ta haɗaki da Aljanu, ni kai na mamakin kyan da Ubangiji ya yi wa ƴata nake, sai yanzu nake ƙara ganin cancantar suturta fuskar da kike”
“To ALLAH ya isa, Allah ya isa shi kaɗai zai isar mini idan ka yafe Allah ya tsine” Innati dake bakin ƙofa tana leƙowa ta furta hakan lokacin data tabbatar Jikarta ce Majeederh Abdul’aziz Khan! “Ki yi haƙuri Innati”
Innati ta fashe da kuka sosai tana face hanci ta ce “Wallahi ba dani kike ba, ba kuma ni ki kaiwa ba, Ubanki mai faɗin ran nan da manyan Idanu Audil azizu shi kika tsoratar” Majeederh dai bata kulata ba, domin tunaninta baya wajan gabaɗaya zuciyarta tana wani birgire wanda kullum take ganin kanta acan, a cikin mafarkanta na kullum.
“Majeederh wa kika bari a waje? Na ga mota” Uncle Isma’il ya faɗi hakan cike da zumuɗin jin Majeederh ta ce wani ne ya kawota, addu’a yake Allah ya sa nata rabon auren ne ya zo.
“Latifa Omar ce”
“Ayya to, Allah ya amfana” Ya gyara zama sosai ya ce “Hawwa’u ki faɗa mini gaskiya, mene hujjarki na barwa Rumana saurayin dake son ki yake son aurenki a lokacin baya, sai yanzu kwatsam! Reshe zai juye da mujiya wai kin fasa auren shi ya auri ƙanwarki Rumana anya akwai ƙamshin gaskiya? Domin na lura da rashin nutsuwarki, A can gidan” Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar Uncle ɗin nata, ita yanzu a yadda take ji ko sa’an mahaifinta Abbu aka bata matsayin miji da gudu zata amsa, koda ha za ta yi farin ciki ba da zama da shi muddin zai ɗauke buƙatar ta, wacce ke damunta take sanyata rama da ibadar dole.
“Ina jinki, kin fi ganewa ki zauna duka ƴan-wanki su yi aure ke kina gida? Kin fi ganewa ki gansu da mazajansu gwanin sha’awa suna yin soyayya da rayuwar aure mai tsafta? Su haifi ƴaƴa wanda ko wanne mai rai yake muradi, inma namiji inma mace? Zuciyarki ta yi rayuwarki adalci? Anya Hawwa’u-Jidderh?”
“Ka yi haƙuri Uncle, Idan da rabo zan yi auren”
Maganarta ta narkar da zuciyar Uncle Isma’il, kalamanta sun nuna karaya zahirin fuskarta kuma ta amshi ƙaddarar tare da godewa Allah bisa tarin Ni’imar da ya yi mata, tasan yana sane da ita bawai barinta ya yi ba. “Shikenan, ALLAH ya yi miki Albarka ki je wajan Luba” caraf Innati ta ce “Wacce masifar ce Luba? Ka fita daka idanuna Isma’ila matar taka da ban gama sanin zuciyarta ba ita zaka turawa Kululu? Ƴar Gombe? Wato ta tsaface ta bayan kasan yadda Fulanin Gombe suke?”
“Allah ya baki haƙuri Innati, zan shige taron da ake yau babu mamaki na samu dacewa da aiki mai kyau” “A to! Ya dai fi maka, kamar tsiya akan ƴaƴana ta kare kowa fama yake da kansa da azababben talauci, In sha Allah tsalelen miji Kululu zata aura na tarkata na koma gidanta” Murmushi kawai Uncle Isma’il ya yi tare da shafa kan Little ya ce “Yau ba magana?”
“Mami kakewa faɗa”
“To ɗan Maminta Allah ya baku haƙuri kai da Mamin” Yana fita Innati ta yi ƙasa da murya ta ce
“Munafuki, ai duk tsinewa matarsa da nake to ta shi nake, daga shi har Ubanki Audil azizu sai na kai su hisba uban kowa ya huta, turmin atamfar ankon wannan yarinyar Wifat fa na ce ya siya mini wai bashi da shi?” Ta ƙara girgiza kai ta ce “Hoo! Ƙasa Ubangiji ya baki miji mai kuɗi wanda zai so ki”
Majeederh ta marairaice fuska sosai ta ce “Innati bar maganar auren nan”
Innati ta riƙe haɓa ta ce
“To ba zan bari ba, Annamimiyya ina nan watarana idan ban mutu ba sai mijinki ya sunkuya ya miki doki-doki dake da yaran da zaki haifa, wallahi ko bana raye sai kin tuna wannan maganar tawa, zaki haifi zuri’a mai yawa zuri’ar da babu Uban wanda ya taɓa haifarta a cikin ƴan-uwanki da iyayen naki” Majeederh ta lumshe idanunta a zuciyarta tana tona tsayin shekarun da zata ɗauka kafin tabbatuwar hakan! Innati ta fashe da kuka ta ce “Allah ba zai barki haka ba, wallahi halin Uwarki Fulani kika ɗauka, har tsinannen kyan da kike da shi duk nata ne, ki rubuta ki ajjiye watarana sai labari ni dai ki sani ina son ki ba zan baki gurguwar shawara ba, amma dai Allah ya yi ɗaiɗai da zuciyar Rumana” Surutun Innati ya hau wa Little ka, daman ba daɗi yake ji ba ta shagwaɓe fuska tare da fashewa da kuka ya faɗa jikin Majeederh ya ƙanƙameta “Mami gida”
Majeederh ta yi saurin rungume shi tana shafa kansa yau ɗin gabaɗaya ta rasa meke damunsa ga kanshi zafi kamar mai zazzaɓi. “Innati kin firgita mini yaro” Innati ta riƙe baki ta kasa cewa komai sai can ta ce “Ba zan ce komai akan yaron nan ba, amma dai a guji gobensa akwai abubuwan Al’ajabi cikinta” Majeederh ta ɗauke ɗan ta tare da rungume shi sosai a ƙirjinta tana ji yana sauke numfashi ya ƙanƙameta.
Latifa Omar ta yi murmushi mai kyau tare da kallon Aliyu ta ce
“Kana da abin dariya”
Aliyu Sufyan Alhassan ya ce “Uhm Latifa Ina son ki, bana son a ɗauki lokaci ki bani dama”
“Daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi?” Ya yi murmushi kawai kana ya ce “Bani labari”
“Na me? Akan wa?” Latifa Omar ta tambaya. Ya ce “Your friend”
Ya nuna ƙofar gidan da Majeederh ta shiga. Latifa ta juya idanunta ta ce “Oh, Sunanta Majeederh Abdul’aziz Khan! Iyayenta suna yawan ce mata Hawwa’u, ƙannenta musamman Aaliyyah tana ce mata Jeederh. Mun yi makarantar primary lokacin ɗaya, amma ta fini ƙoƙari ne sa ba kusa ba, da yawan lokaci ina hana kai na bacci ganin na zama ita, sai na fahimci iliminta baiwa ce, daga Allah. Biye ɗaya takewa ayar Alkur’ani ta hadda ce ta, tun muna primary ta rasa mahaifiyarta, she left her, at the same time ta yi saukar Alkur’ani, ni kuma na maimaita aji, a lokacin da ta zama hafiza a lokacin na yi sauka ta farko” Ta yi jim,tana rayuwa da step mother ɗin ta, kishiyar babbar ta, ilimin Majeederh ya sa Manyan mutane na primary school ɗin mu suka shige mata gaba wajan samun scholarship a matakin secondary school, ta samu makaranta mai kyau tun a lokacin Karatun ta a ɓangaren Islamic yake, yanzu maganar da nake maka ranar Candy ranar ta zama Gwarzuwa a ɓangaren musabaƙar Alkur’ani, wannan shi ne kashi na wajan uku na dai manta Makarantarmu Ahlul Madar tana bada sunanta matsayin wacce zata jagoracemu, yanzu haka sunanta yaje ko’ina duk wata gasar karatun Alkur’ani indai Kano zamu shiga to ita za ta yi” Ta ja aya tana sauke numfashi. Tunda ta farar maganar idanun Aliyu a rufe yake ruf ta ce
“Lafiya?” A taushashe ya ce “Ina jinki”
“Majeederh ta zama malama a Ahlul Madar duk wata suna bata albashi, da albashin take kula da yaron daka gani a wajanta” Ya ware idanu da mmki ya ce
“Yaro? I heard you kin ce single take, not house wife” ta ce “Eh, Tsintar yaron ta yi, kuma tana son sosai banda kada na yi maka ƙarya bayan iyayenta babu wanda take so kamar Little, tana iya haƙura da cikinta ta bashi ya ci, kuɗin Makaranta, kayan sawa duk da albashinta take masa, kuma a ciki take taimakon Abbu da abincin gida, by the way yanzu tana shirin tafiya ƙasar waje Africa, ta samu scholarship za ta ɗora University ɗin ta a can ɓangaren Islamic and Arabic studies”
Ta yi shiru ganin kamar Attention ɗin Aliyu baya kanta ta ce “Ya dai?”
“Wacce ƙasa?” Ya faɗa yana murmushinsa mai kyau da aji. “Misira”
“Ok Egypt, Allah ya taimaka” Latifa Omar ta ce “Amin”.
A can cikin gida Hajiya Luba ta kalli Majeederh ta ce “Yanzu karatun zaki?” Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya a fili tare da jinjina kanta alamar “Eh, Mama”
“To Ubangiji ya sa rabokin ke kiranki, Allah ya baki ikon cinye ƙaddarorinki mutane ne kawai da basu son zama lafiya gabaɗaya nawa kike balle ƴan-uwanki shekaru Ashirin bai ci har a fara gorantawa mutum bai aure ba”…
“…… Allah ya kyauta”
Ta ci-gaba da bata haƙuri da ban mamaki. Har Latifa Omar ta shigo suka ta fi gidan Yaya Bilkisu domin acan ake Sabgogin bikin Widad ɗin. Ko! Da ta je bata iya zama ba ƴan matan familyn Khan, suka shiga sauke magana. Kusan duk akan Idanunta aka haife su sbd rashin aure ya sa girmanta ya zube. Tana zaune kiran gaggawa ta sameta zuwa Orphanage for young children, kira ne daga kai tsaye daga Akeeth. Yaya Bilkisu ta bata kuɗin napep daman tuni ta ce Latifa Omar ta tafi kawai. Tana gab da zuwa ta sake kiranta.
“Assalamu alaika”
Majeederh ta furta cikin muryarta mai sanyi daɗi a kullum. Akeeth ya amsa ya ce “Am sorry Majeederh,na samu meeting na gaggawa idan na gama ko kiranki ne zan yi” Jikinta san yi ƙalou ta kashe wayar ba tare data ko amsa masa ba.

Unguwar Darmanawa
Idanunsa rufe yake kallon selling ɗin dake cikin bedroom ɗinsa, lokaci na farko a rayuwa da ya yi nauyin baki wajan furta abin da yake so. Ya juya kaɗan yana sake mirginawa hoton idanunta kawai suke gilmawa cikin nasa idon, ganin abin bazai goge ba sai ma ƙaruwa da yake ya sa a hankali ya miƙe ya shiga bathroom tare da sakarwa kansa shower yana riƙe ƙugunsa bugun zuciyarsa na ƙaruwa gabaɗaya Latifa Omar ba tsarin aurensa ba ce, me ya kai shi? “Density” Shi kansa bai adadin lokacin daya ɗauka a bathroom ɗin ba, sai da ya ji ana knocking ƙofar part ɗin shi ya fito ɗaure da towel a jikinsa.
“Meke damun ɗan autan Hajia yau da bai yi dinner damu ba?” Aliyu ya shagwaɓe fuska sosai autar ta motsa daman rauninsa da wuri yake fallasa asirin zuciyarsa. Ya ja baya yana zama kan kujerar dake kusa da gadon shi, ɗan ƙasar Turkiya. “Hajia”
“Na’am Autan Hajia” Hajia ta amsa tana jiran ta ji dame yau kuma ya zo, domin shi Aliyu baya rabo da issues sbd tsabar taɓara gashi kyakkyawan ajin farko sai ka ɗauka Half-caste ne. Looking so classic. “Aure zan yi, na samu mata” Ya faɗi hakan domin a tunaninsa shi ne mafita ga abin da yake ji, wacce zai aura daban, wacce ta yi zuciyarsa kamo daban. Ko mene hakan hakan? Only God knows.
Sosai Abbu ya yi wa Majeederh faɗa don me bata ƙarasa ta karɓo form ɗin ba? Ita dai bata ce komai ba ita kaɗai ta san abin da take ji. Yau ɗin ma sai da ta yiwa Little wanka ta sanya masa kaya masu ɗan sauƙi bata son ya kwana da zazzaɓi. Ta tsora masa idanu a hankali ta ce “Little zaka manta dani?” “Me?” Ta tambaya domin bai fahimta ba.
Ta ce “Idan na ta fi karatu, karka manta dani ka ji? Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana” Ita kaɗai take magana ita kaɗai kuma take fahimtar me take cewa. Ya shafa laɓɓanta da suke jajir ya ce “Mami ni ma irin naki”
Ta yi murmushi tana ɗaukar shi tare ta ɗora a cinyarta ta ce “Until you grow up” Ya shiga buga ƙafa da yarfe hannu shi a dole sai laɓɓansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce
“Ok Shafi kaɗan, da safe sai koma red” Ya yi murmushi yana tsalle ya ɗora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta ɗauke shi tana dungure masa kai, ƙara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya. Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki. Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani. Wani irin kuka take da dukkan ƙarfinta wanda yake tasowa tun daga ƙasan zuciyarta. Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai. Da ƙyar ta rarrashe shi suka kwanta bacci. Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son taɓa jikinsa ta ji ko da zafi. Wayam! Ta buɗe idanu taga babu Little a kan gadon ta miƙe da sauri idanunta ya sauka akan ƙofar ɗakinta dake buɗe bayan har rufewa ta yi. Da sauri ta ce “My Son, Little?….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button