Mijin Malama Book 1 Page 17
MIJIN MALAMA
Paid book
Book 1 and 2 1k
08119237616
Nimcyluv18
Baccin Little ya yi nisa sosai kafin ta miƙe tare da rufe shi da bargo ganin iska sosai na ɗaga labulen bedroom ɗinta. Wajan window ta ƙarasa tare da tsayawa ta sanya hannunta duka guda biyun ta ɗaga labulen Idanunta rufe a hankali iskar dake kaɗawa ta tasuwar hadarin dake kwance tun safe ta shiga ratsa ta. A duniya Majeederh tana so da ƙaunar taga ana ruwan sama, ko bata cikin yanayi na jin daɗi sai ta samu kanta cikin farin ciki nutsuwa ta saukar mata a lokacin duk wata damuwar data samu gurbi a zuciyarta take yayewa. Ƙara tura kanta tayi wajan window ɗin tana rufe ido fresh air ɗin na ratsa ta tana jinta har ƙasan zuciyarta damuwa da tunanin maganganun Uncle Isma’il ya goge a zuciyarta. Ta ɗauki wasu mintuna a wajan kafin ta ji motsi a bayanta ta juya da ɗan sauri tsaye ta gabashi daidai kafaɗarta ya jawo locker tare da hawa kai idanunsa na waje ita kuma tana kallonsa. Shi ma yadda ruwan zai sauka yake kallo yasan Maminsa indai ta tsaya a nan to ruwan sama za ayi, ganin ba ruwa sai gari take ta ihu da rugugi ga iska mai daɗi yatsuna fuska ya yi looking damn cute. Majeederh tayi masa murmushi taja baya ta ce “Ai kowa bani da abinci, waye yace ka kwanta kai kana fushi da Mami harda fita ai maka duka, thank God” kamar mai shirin rarrafe ya sauka daga kan locker tare da zubawa Majeederh Idanu yana kwaɓe fuska domin da gaske yunwa yake ji, ita kaɗai ke sawa ya nutsu duk rashin jinsa, daga yunwa sai faɗan da zatai masa idan ya yi abu. Ta ƙarasa kan gado tare da kwanciya tayi rigingine tana kallonsa tare da ganin zai haƙura ya kwanta ko sai ya yi rigimar yunwar. Bata kammala tunanin da take ba taji gabaɗaya ya haye cikinta tare da sanya mata kuka yana yarfe hannu. Ta zare Idanu da sauri ta miƙe da shi tare da ɗaukar shi a kafaɗa ta ce “Ai yau fa babu kai babu cin abincin dare salon kayi girman da zan kasa goyaka” Little ya ƙarawa kukansa ƙarfi ya ce “Mami Indomie”
“Sannu baban Indomie” ta ƙarasa da shi main parlour tare da shigewa kitchen yana goye a bayanta ya saƙalo hannayensa ta wuyanta. Ya dinga leƙawa. “Ok get down, zaka fasa mini ƙirji” ya saki dariya while hawaye na gangaro masa. A saman sink ta ajjiye shi ta kunna gas-cooker indomie ta dafa masa ba tare data saka attarihu ba domin baya son ya ji.
“Mami egg fa?”
“Babu” ya ce “baki da kuɗi?” Ta dube shi tare da girgiza kai ya ƙara cewa “baki da kuɗi?”. Ba zai taɓa barinta ba idan ba amsa ta bashi ba. Tana juye masa Indomie a plate ta ce “Kayi addu’a zan samu ƙarshen wata ya kusa” ya yi ta kallonta ya ce “Me ake a ƙarshen watan?” Ta sauke shi daga kan sink ɗin tare da tsugunawa ya hau bayanta plate ɗin abinci a hannunta ɗaya kuma bottle water ne guda ɗaya ta ce “Idan end of month ya yi zan samu salari kuɗin aiki kenan”
“To idan baki samu ba, ba zan ƙara cin egg ba, kuma ba zaki sai mota kina kai ni school ba?”
Daidai lokacin ta buɗe Ƙofar bedroom ta shiga ta mayar ta rufe tare da sauke shi. Ta zauna a ƙasan carpet yana zaune a cinyarta ta tallafo fuskarsa cikin kyakkyawan lafazi da magana wacce ƙaramin yaro zai fahimta ta ce
“Little ya sunanka?”
“Little” ya bata amsa
“Ba pronoun ba, asalin sunanka me ake ce maka” yadda yake kallon cikin Idanunta kaɗai zai tabbatar mata bai ma san akan me take magana ba, balle ya bata amsa. Majeederh bata son sunan Little ya bisa, lokacin data tsince shi bakin masallaci he just 3yrs bai san komai ba, ba zai iya tuna komai ba. Shekarunsa biyu a wajanta ciff da wasu watanni. Tana tsintar shi kuma kai tsaye ƴan sanda taiwa reporting amma sam yaƙi zama a wajansu tun a lokacin ya dinga ƙanƙameta yana cewa “Mamina”. Ganin yadda ya kasa sukuni ya sa ta buƙaci subar mata shi a duk sanda iyayensa suka bayyana zata bada shi, sosai aka sha faɗa domin Mami da Abbu idanunsu suka shafawa toka, sai dai Uncle Isma’il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu suka shiga cikin maganar. Aka je orphanage tare da cike komai da komai aka an mallaka mata shi abadan. Tun a lokacin tasu a sanya masa suna amma fur yaƙi cewa komai he just watching her face a duk sanda ta tambayi sunan shi. Har kawo yanzu da yake zaune akan cinyarta yana kallonta. “You don’t even know your name?”
“Little, ƴar madara”
Ta haɗe fuska tare da ɗaukan spoon ta shiga bashi Indomie yana ci yana gyaɗa kai tare da wasa da stone na gaban rigarta. Little na masifar son abinci, cikin abinci bashi da favorite sbd yadda yake mutuwar son food. Duk wasan shi da zarar ya fara jin yunwa yake nutsuwa ya sanyata a gaba da tambayar
“Mami food, I want to eat food” sau tari biyu take raba albashinta duk wata ta sai gatan ɗin Indomie da egg da kuma chocolate domin bata bashi ko sisi na makaranta zata haɗa masa breakfast box hadda chocolate ciki. Da kuɗin ta take biyan school fees bata son duk wani abu daya danganci maraya little ya yi kuka da shi. Da fari ta ɗauka rashin sanin sunan is nothing amma yanzu school sun matsa basa buƙatar wani little cikakken sunansa suke so, wannan dalilin ta shiga taraddadin sanin wanne irin suna zata bawa Little ɗin nata?
“Ƴar madara”
Ya dawo da ita daga tunanin ya watsa hannu ya ce “Na cinye”
“Zaka ƙara?” Ya girgiza kai ta ɓalle bottle water tare da tsiyaya masa a cup ta bashi bayan ya sha ta ce “Say Allahamdu lillahi” ya faɗi exactly abin da ta ce. “Mami zan siya miki mota babba irin ta Uncle Akeeth, zan baki kuɗi ki dinga siya mini Indomie da abin yin ƙarfi”
“Ƙarfi kuma?”
“Eh Mami, ina son yin ƙarfi na dinga dukan Uncle idan yana saki kuka” Nan da nan Majeederh ta haɗe fuska cikin tsoro da fargaba ya ce “Sorry Mami” ya faɗa yana kame kunnenshi.
Ta kama hannunsa ta ce
“Little zaka iya dukana idan ka girma?” Ya zare idanu ya ce “A’a”
“Why?” “You’re my mother” ta ce “Good, Uncle Isma’il mahaifina ne, duk abin da ya yi mini daidai ne yana so na, ba zai bari na wulaƙanta ba, ka zama good boy mai haƙuri da rayuwa ka rage zafin zuciya,na shiga uku ni Majeederh idan ka girma a haka da zafin zuciya wacce Mace ka ke tunanin zata iya zama dakai” da sauri ya ce
“You! Mami ke zaki iya zama” ta watsa masa harara ta ce “Yaro ba Mutum ba sai ya girma, daman duk lalacewarks ni ya zamewa dole zama da kai ok” ganin tana son sanya masa tunanin daba nasa ba yasa ta sauya topic ɗin da cewa.
“Muje bacci”
Gabaɗaya suka kwanta akan gado kanta akan pillow nashi kan a hannunta suka kalli juna lokaci ɗaya kamar yadda suka saba yin waƙar su a koda Yaushe suka haɗa baki wajan faɗin.
_“Darling promise you wait for me, i go think of you everyday my love”_
Little fararren haƙoran shi waje ya ce “I love you Mami” ta rungume shi tana faɗin
“I love you too sweetheart”
Tana kallon shi har bacci ya ɗauke shi yana riƙe da ita kamar mai tsoran ta gudu ta basshi, duk sanda zai bacci koda rana ne dole sai ta zauna ya dinga cewa “Mami ba zaki tafi ko’ina ba? Mami zaki iya tsaya ido ya buɗe?” Da yawan lokaci haka yake cewa ta fahimci har yanzu a ransa ji yake zata gudu ta barshi. Ta shafa sumar kansa tare da yi masa addu’a ta shafa masa a haka bacci ya ɗauke ta rungume da ɗanta Little. Kana ganinsu kasan soyayya ce da Ubangiji. Love for blood, love from God. Babu mai rabawa sai Allah.
Washegari ta su makara, an kusa idar da sallah ta farka tayi alwala tare da sallah tayi azkar. Tana kammalawa ta matsa ta shiga tashin Little amma kamar bai san me take ba, wani irin nauyin bacci ne da shi musamman idan ya samu yadda yake so, an kawo wuta ga iskar Subhi gata fanka. Sai a ɗauke shi a zura shi a buhu bai sani ba. Ɗaukar shi sai banɗaki acan ta dire shi ta sakar masa shower. Ya buɗe ido da sauri jin ruwa akan shi. Ta ɗauki ƙaramin towel ta ɗaura masa a ƙugu kana ta zare masa wando tana ji yana ta dariya yana jan gashin kanta tayi masa shiru. A haka tayi masa wanka da towel a jikinsa tana gamawa ta ɗauke shi ta shafa masa lotion ɗin shi ta taje masa sumar kan da mataji riga da wandon Adidas ta saka masa red and black suka amshi jikinsa kana ta sanya shi gaba ya yi sallah. Kasancewar cikin dare ya ci abinci bai nemi abinci sassafe ba. Fargaba ta risketa domin bata da raguwar wata Indomie, sai kawai taga ya kwanta ya juya mata baya bacci ya sake ɗaukan shi. Hamdala tayi a ranta tana fita daga cikin bedroom ɗin ta zuwa main parlour.
Ba kowa aciki ta nufi ɗakin Abbu yana zaune saman ladduma yana jan carbi ta tsuguna ta ce
“Ina kwana Abbu?”
“Lafiya lou Hawwa’u, ya ɗan naki?” Sosai tai mmkin yadda ba damuwa a fuska ya tambayi Little “Bacci yake” ya ce “to Allah ya yi albarka, Yaya Bilkisu na nemanki wai tunda aka fara sabgar biki bata ganki ba ko laifi akai miki?” Tayi shiru kawai
“Akwai damuwa ne?”
“Zani Anjima” hannu ya sa ya fito da ɗari biyu da hamsin ya bata ya ce
“Ki hau napep, ko Yaya Bilkisu zata baki na dawowa na ji ance fetur ya ƙara farashi”
“Na gode, Allah ya ƙara arziƙi” ya dubeta ya ce
“Daga nan ki je kiyi photo zan tura da wasu takardunki tafiyarki ta matso” yanzu bata data cewa burinta Ubangiji ya bata haƙuri da juriyar yadda take ji Allah ya tsare imaninta da mutuncinta na ɗiya mace
“Ki na ji na?”
“Eh, Abbu” ta ɗaga kai cikin sanyin nan nata ta ce “Me zan karanta acan? Shekara nawa zan?” Abbu ya ce
“Islamic studies, zai ɗauke ki shekara uku zuwa huɗu” kenan a lokacin tana da shekaru Ashirin da huɗu kafin kammala tunaninta ta ji ya ce “Sai ki juya zuwa Islamic language, zai ɗaukeki zuwa shekaru huɗu haka” lokacin shekarunta Ashirin da takwas babu lissafi aurenta gabaɗaya a maganar Abbu. Bata son musu da duk abin da Abbu ya shimfiɗa mata tana ganin hakan shi ne daidai tunda abin da ya hango ba lallai ta hango shi ba. Tana zaune ta ji Mami ta rangaɗa uwar buɗe wacce ta sanya Majeederh saurin rufe Idanu faɗuwar gaba ya sameta haka kurum. Mami ta shigo tana gyara ɗaurin zani ta ce
“Allahamdu lillahi, ma sha Allah ashe Rumana ƙashin arziƙi ce, shi ya sa ake cewa ko kana gudu haifi ka yar” Abbu kallonta yake yana jiran jin me zata ce ta zaune dab da shi ta ce “Yanzu Matar Isma’il Luba take shaida mini an kawo kuɗin na gani ina so na Rumana Dubu ɗari biyu har sanya rana, kai Allhamdu lillahi kafin nan da wata guda an kawo kuɗin Raihana kaga sai mu haɗe bikin waje guda” Majeederh ta miƙe tsaye tana jin jiri na ɗaukanta shikenan za su aure gori zai ƙara tabbata. Tana ƙoƙarin fita Mami ta ce “Babbar yaya magajiyar uwa, Majeederh Imran ne fa wanda kika ce bakya so? Shi ne ya kawo kuɗin ƙanwarki Rumana saurayin yaya zai zama mijin ƙanwa” Majeederh ta haɗiye yawu da ƙyar kafin ta tattaro abin da ya yi masa saura a baki ta ce “Allah ya sa albarka” “Amin Amin ke kuma Allah ya sawa karatu albarka”
A parlour ta samu Rumana na tiƙar rawa tana cewa “Ko anƙo ko an su aure ya ɗauro murna muke daga fuska har zuwa ranmu, zan zama matar Imran”
Tana rawa Raihana na yi mata rawa Aaliyyah na kitchen tana haɗa breakfast. Ƙosai take soyawa a lokacin da kunun gyaɗa. Hukuncin Ubangiji ne kawai ya kai Majeederh ɗakinta ta zube a bakin gado tana riƙe kanta da zuciyarta take bugawa. Little daya tashi tun ɗazo ya ce
“Mami kai ne? Ciwo?”
Ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya tana ƙaƙaro Murmushi ta ce “My little son” ya yi murmushi ya durƙosa a gabanta ya ce
“Good morning ƴar madara Mamina” ta ja hancinsa tana shafa sumar kansa ta ce “Ok jeka ka yi brush kafin na dawo” ya ce “Zani Mami”
Ta haɗe fuska ta ce
“Yanzu zan dawo ok” ya ɗaga mata kai ɗari biyu da hamsin ɗin da Abbu ya bata ta ɗauka tare da sanya hijabi har ƙasa ta ɗauki liƙab ta saka tare da ficewa ya bita da kallo. Katin dake kusa da gidansu Majeederh ta ƙarasa cikin muryarta mai daɗi da sanyi ta ce “Indomie zaka bani ƴar 170 sai egg guda biyu 60” ya ce “Malama Majeederh kuɗin ya kama 290 ne, kuma 250 kika bayar ta yi jim kafin ta ce “Ok bani ƴar 150” ya bata indomie ɗaya da ƙwai guda biyu. A ranta tana cewa sai dai na je gidan Yaya Bilkisu a ƙafa idan ya so sai na goya Little a baya…..