Mijin Malama Book 1 Page 21
MIJIN MALAMA
Via this number….. 0811923761623
Duk inda ta sanya ƙafarta sai taga ana matsawa tare da jan jiki baya, Majeederh was Shocked ta yi saurin saka hannunta ta shiga shafa fuskarta ko wani abu ne ya sameta, amma bata ji komai ba, bata iya shiga razani ba sai numfashinta ya fara sauka da ƙarfi ciwonta ya fara neman tashi, wani saurayi ya dinga kallonta daga nesa ganin attention ɗinsa yana kanta ya sa ta nufesa duguwar rigar jikinta na neman yarda ita sbd tayi mata yawa sosai. Tana zuwa wajan saurayin taga ya yi saurin rufe idanunsa a fili ya shiga faɗin “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Ya subuhanallahi!” Kalamansa da salatin da yake na neman taimako daga Ubangiji ya ƙara firgita Majeederh da jirkita duniyarta idanunta da sukai jajur ta buɗe akan saurayin ta ce “Don Allah mene ya samu fuskata? Me ya sa kowa ke kallo na?? Me ya sa maza suke guduna?” Sosai muryarta ta razana shi amma ya dake deep down na zuciyarsa addu’a yake na neman tsari ya dai daure ya ce
“But are you a Baha’i?” Majeederh ta dinga kallonsa ya ce “Ina nufin ke Bahaushiya ce?”
Ta jinjina masa alamar eh ya ce “Ki dai bincika amma duk wanda ya ganki zai ci Aljana ce, kyanki ya yi yawa ni ma dauriya kawai na yi” Yana faɗin haka ya bar wajan da sauri jikinsa na rawa. “Aljana??” Majeederh ta tambayi kanta tana nuna kanta da yatsa a fili ta ce “Is this really happens to her?” Ta zube saman kujera tare da dafe kanta “Wai meke faruwa? Ni ce Majeederh ko wata new Majeederh? Ko dai gaske Aljana ce, Innalillahi” da ƙyar ta iya jan jiki tare da ɗaukan liƙab ta mayar a fuskarta tana fita Aliyu ya shigo wajan shi kansa bai san mene ya kawo shi ba….. Gabaɗaya suna zaune a parlour Hajia ta gyara zama speaking calmly ba faɗa ta ce “Sannu fa, ai zata aikata duk me aka ce ta yi bana doubting” Hajiya Rahmerh ta ce “I don’t think so, amma dai ta ce komai zai daidai In sha Allah” Hajia ta girgiza ƙafa kawai hankalinta yana ga Aliyu-haydar da har yanzu ba taga shigowar shi ba. Anti Biba mai bin Hajiya Rahmerh ta ce “Ni wai ina Autanki ne Hajia? Babu shi ba Almustapha?” Kafin ta yi magana Aliyu ya shigo muryarsa mai ɗauke da damuwa ta ɗan baiyana a parlour. Daga Mahaifiyarsa Hajia har ƙannenta Hajiya Rahmerh da Anti Biba suka dubi Aliyu. “Kai lafiya kake? Wannan idanun kamar mai azumin Kaffara?” Ya nemi waje kusa da Hajiya ya ce “Am Good, ya hanya Aunties?” Anti Biba ta ce “Lafiya, lawyer sarkin ƙarya” Bai ce komai ba ya shafa kansa feeling better ganinsa kusa da Hajiarsa “Aliyu” Aliyu ya kalli Hajiya Rahmerh har sai da gabansa ya faɗi ta ce “Aliyu, Aliyu, Aliyu how many times do I call your names?” Ya yi ƙasa da kansa ta ce “Ok na kira na ji daɗin bakina ne ko mene? Eh?” A hankali ya ce “Afuwa” Ta gyara zama ta ce “Kana da gata, kana da kuɗi, kana da ilimi ka fara aiki zaka gina kanka to me ka ke jira? What are you waiting for??” Shi dai bai magana ba ta ce “To ka fita daga cikin idanuna, ku biyu kawai Allah ya bawa Hajiya Laylerh ai yana da kyau yanzu zuri’a su fi haka yawa, bari na buɗe maka zancan a faifai maganar aure nake maka” Ya yi shiru daman ya san abin da zata ce kenan ya ce “To” ta ce “Ba wannan nake son ji ba, cewa zakai to Hajiya Rahmerh zan yi nan da wata kaza ka gane, ni a kawo maganar ba ga can ƴar uwarka ta ƙare karatunta a London Buhayyerh talk to her ina da tabbacin zata amince maka” Ya cira idanunsa ya kalleta ya ce “She is not strong enough to be my wife, I need someone stronger” Ta ce “Are you kidding me, right?” Ya yi shiru, Hajiya Rahmerh ta shiga faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba har tayi masa tas bai ce komai ba. Ya miƙe tare da shigewa part ɗinsa, yana shiga Anti Biba ta bi bayansa ta ce “baka kyauta ba Aliyu” ya riƙe kansa ya ce “Goodness, me na yi?” Ta ce “Ba haka ya dace ka bata amsa ba, ana iya yin ƙarya domin kare kai wannan ya halatta a mazahabar malam Bahaushe, ana iya lashe rai ɗaya domin kare rai dubu” ya yi shiru for some seconds ya ce “Kawai sai a haɗa aure? Kamar an daina wannan abun an shige ƙarnin tun tuni” Ta yi Murmushi kawai ya ce “Ina Antin Turkey?” Anti Biba ta ce “Sun sauya sheƙa an yi mijinta transfer na wajan aiki” Yana kwanciya tare da rufe idanu ya ce “Zuwa ina?” Ta ce “Ban san ƙasar da take ba, tana ta complain dai bata so sbd karatun yaranta baya yake dawowa” Ya mirgina ya ce “Tana da gaskiya” Hira su ka yi sama tana lura da yadda ƙirjinsa ke ɗagawa sosai da ramar da ya yi sai ba tayi masa magana ba…. Washegari da safe Innati ta dira gidan Abbu lokacin duk suna karyawa ta dubi Abbu ta ce “Audil azizu saɓon Ubangiji kake amma ba zaka gane ba” Da damuwa sosai ya ce “Saɓo Innati?”
“A’a, Allah na tuba ai duniyar gajere ce kaje ka yi bance komai ba, amma zaka sha mamaki da izinin Allah ka kuma shirya” Kalaman Innati suka daka Abbu cikin shakku na rashin sanin abinda ya aikata har haka da zai gani? Innati ta kalli Majeederh data raƙube gefe ɗaya kamar ba gidan Ubanta ba ta ce
“Babu komai, jarrabawa ce amma ni kaɗai na san abinda idanuna ke gani akan ki Kululu ki yi ta addu’a takanas na zo wajanki tunda na ji ance jirgi zaki hau ki bar duniyar”
“Ƙasar dai ba duniyar ba” Aaliyah ta faɗa tana kallon Majeederh wanda ko kunun ta kasa sha. Kamar daga sama kuma su ka ji ta ce “Inna da Aljanu nake kama?” Innati ta zare idanu tana dafe ƙirji ta ce “Yanzu to mene haka? Ina ruwanki da zancen Aljanu da sanyin safiyar nan don Allah? Allah ya yafe miki” A raunace kamar bata son yin magana ta ce “Na taɓa ji kince na tsorataki” Innati ta ce “To bance komai ba, ke kuma kwaɗayayyiya wacce ta sha nonon maita ki ke idan wancan yaron ne zaki gani, abin da naga komai ina kan gani” Ta faɗa tana nuna Ruma da hannu ita kuma ta tura baki gaba, ta juya kan Mami ta ce “Ban yi mamaki ba, haihuwar Legas ce ke sai abinda Ubangiji ya ƙaddara za mu gani, duk ƴan iska ne Legas ɗin ai” Abbu dai bai ce komai ba sbd yasan halin mahaifiyarsa kamar wacce take da matsala idan tana abu sai dai kawai su dinga jinta. Majeederh ta yi shiru a ɗakinta inda take kwance akan gado sai juyi take, bata san meke damun zuciyarta ba, wacce kullum ke ƙaryata ta akan zata iya samun wanda zai aureta ya rusa zuwanta Egypt.
Ta juya a hankali tana ƙanƙame pillow jin tsigar jikinta na tashi wani abu yana mata yawo a jiki, wanda ta kasa sabawa da jinsa a kullum, yanzu ko ta ɗauki azumi ma sai ya karye bata san meke kawo wannan abun ba, ta ƙara juyawa tana kiran sunan Allah ko zata daina jin abin amma ina, ruwan saman da akayi ya ƙara haddasa bayyanar abu a jikinta kamar cin wutar kara. Miƙewa tayi ta nufi toilet tana zuwa ta dinga sheƙawa kanta ruwan sanyi a hankali ta durƙoshe akan ƙafafuwanta duk yadda ta kai da haƙuri, juriya, da miƙa lamura ga Ubangiji sai da ta fashe da wani raunataccen kuka har da shassheƙa. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta, ta farka da wani irin zazzaɓi ta juya tare da kallon Mami dake zaune bakin gado ta zabga uban tagumi ta ce “Kin farka?” Majeederh ta miƙe zaune tana mistake idanunta da suka kumbura “Mami”
“Kuka ki ka yi Majeederh?” Ta yi shiru domin bata ƙarya Mami ta sauke numfashi ta ce “Hawwa’u, kina ji cewa a ranki bana kyautawa ko?” Majeederh couldn’t speak Mami ta ce “Majeederh bani da iko dake, haka kullum mahaifinki yake ce mini, shi ya sa na tattara komai na ja bakina nai shiru, to na ce me? Ina tofa tawa zai ƙullace ni, mun sha samun saɓani da shi akan ki amma ya ce ba ruwana ƴarsa ce ke ba wani ya haifa masa ke ba, hatta tafiyarki ba a son raina ba dana faɗa masa gasky cewa ya yi zan yi ta igiyar aurena, ni kam mene ya yi mini zafi? Ƙatuwa dani ina shirin kai ƴa ɗaki na samu jika da yawon zawarci?” Ta ja numfashi ta sauke ta ce “Allah yana gani na fara gajiya yana neman shafa mini baƙin fenti” Murmushi kawai Majeederh ta yi ta ce “Ba komai”
“Da gaske babu?” Ta jinjina kai ta ce “To Allah ya iya mana, ko can ɗin kika je kiyi ta addu’a, ki riƙe mutumcinki har zuwa shekaru takwas ɗin” Kanta a ƙasa ta ce “Na gode” Mami ta miƙe tsaye tana cewa “Maza ki tashi ki shirya wani sa’ilin ke kike mai da kanki baya ayi mace ba kwalliyya? Ba kwalli ba powder, fuska kullum a rufe da wata ƴar malafar uban duguwar riga, kamar matar mamaci ko wacce aka koro daga Saudiya? Fuska a maiƙaci sai farin bala’i kamar an kwara miki man ɗanyar gyaɗa haba Majeederh? To ai shikenan” ta saka kai ta fice abinta.
Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya, wai ta yi kwalliyya? Ai bata da wata sauran dama ta riga ta sallama, ta yarda ta amince domin ta yi ilimi da bautar Ubangiji take raye, ta yarda ita ta rako mata duniya ko me za ta yi a rayuwa ba zai taɓa sauya abin da zuciyarta ya yarda da shi ba, ko fata za a sauya mata ba zata taɓa samun mijin aure ta yarda za ta yi karatu zata zama cikakkiyar Malamar addinin Musulunci zata fafata da duk wanda zai ja da wata ɗiyya mace zata zama jaruma mai yarda da suke abin da Ubangiji ya zo mata da shi, yarda da ƙaddara ta zama feminist. Ta buɗe wayarta tare da kunna network ta shiga facebook, abin ya bata mamaki ganin ta samu mabiya da yawa sosai kamar jira ake ta buɗe. Ta shiga wajan timeline ta yi rubutu ta ce “ITA MACE, BA BAIWA BA CE, KO A GIDAN MIJI” tana gama rubutawa hannunta na rawa ta yi posting ɗinsa, Just now amma over 100 comment ta duba sunan wani Bilal-Habib ya ce
“Uhm ke ba aure ba, kuma zai kashewa wasu? Shi aure ne ba bauta ba? To uwarki ne?” Tana gama karanta idanunta ya sauka akan wani da ya rubuta.
“Malama Majeederh ki bari ki fara auren ko? Ai wannan maganar bata yara ba ce” Da sauri ta yi wurgi da wayar bayan ta kashe datar zuciyata na harbawa. Ta daɗe kafin ta samu nutsuwa. Mami da maƙociyyarta na zaune suna hira Latifa Omar ta yi sallama ta shigo cikin wani lace mai kyau ta sha kwalliyya ta ce “Ina yini Mami?”
“Lafiya lou Latifa ya Maman taki?” Ta ce “Ta ce a gaisheki, Majeederh fa?” Da hannu ta nuna mata hanyar ɗakin Majeederh ta shiga da sallama ta sameta zaune ta ce “Ya naganki zaune ba kyan gani? Kamon ba?” Ta yi shiru idanunta akan waya tana da Research more than 2hrs tana abu ɗaya “Amma dai baki isa ki ce ba zaki ba ko? Bikin Widad ƴar uwarki ni ma zani balle ke?” Ta ce “Mene amfanin zuwa? Ana zuwa domin farin ciki ni raina ke ɓaci Latifa Omar ki bari kawai karatu zan yi” Latifa ta zauna ta ce “Mene ya faru?” In brief ta faɗa mata komai, Latifa ta yi jigum ta ce “Kamar wata mujiya, Majeederh anya lafiya?” Majeederh ta yi murmushi ta ce “Lafiya lou, i believed Ubangiji ke komai i trust ni mutum ce ba Aljana ba….