Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 12

Sponsored Links

MM

Xvii
(17)

 

Related Articles

 

“Alfarma nake so kuyi min, ko na ce taimako” ya fada yana kallon su, a yanzu da yake gaban su, sai yake jin nauyin sanar da su, gani yake tamkar taimakon da zai nema yayi yawa.
Ganin yayi shiru, suka ce “muna jin ka” alamun a kage suke da son jin wani taimako suke son yayi musu.
Doctor Abbas ya numfasa yace “Some month back nayi wata patient a asibitin da nake aiki, kafin na fadi taimakon da nake so ku min zan so ku San wani abu, ita yarinyar marainiya ce bata da kowa, sannan she’s 5 month pregnant a yanzu haka, abinda zai karya wa mutum zuciya shine she’s only 14years going to 15”

“Innalillahi wa inna ilahirin raju’un” barrister Abrar ta fada tana rufe hannun ta da baki.

A nutse doctor Abbas ya shiga basu Labarin tun farkon haduwar sa da Munaya har izuwa ƙarshe, kana ya dora da cewa “ina neman alfarma ta zauna a gidan nan har ta haihuwa, domin saura few months haihuwar, tana kuma bukatar sanya idon babba, domin komai zai iya faruwa idan babu idon babba a kanta ba fata muke ba, kaf na duba abokai na masu iyali ku kadai zuciya ta ta aminta da shi, na san halin ku na taimako shiyasa na kawo muku wanna maganar, ina fatan zaku amince”
Sai a yanzu ya lura da yanda barrister Abrar ta kwantar da kanta a kafadar doctor Aaban tana kuka sosai, bai san dalilin ta na wanna kukan mai yawa ba, amma yana tunanin tausayin Munaya ne ya cika zuciyar ta.
Doctor Aaban kuwa ya san komai, ya san dalilin ta na wanna kukan, labarin Munaya ya tuno mata da ta ta irin rayuwar ta baya da irin wahalhalun da ta sha, duk da akwai bambancin tsakanin rayuwar Munaya da doctor
Abrar…(read mijin Ammi na ne sila by NoorEemaan)
A hankali doctor Aaban ke fadin “decent one ya isa Please, kukan ya isa haka”
Jinjina masa kai take, a hankali yanda shi kadai zai ji take faɗin “pure heart ta bani tausayi, ka tuna tawa rayuwar ta baya, i was 17years then but still na Sha wuya, what about yarinyar nan da akwai tarin kuruciya a tare da ita, ga ciki kuma”
Ta share hawayen fuskar ta da kyau, kana cikin daga sauti tace “zan yi Shari’a da shi, zan maka shi kotu sannan zan kwatar mata yanci, kila yana tunanin ba tada gata ne, shiyasa yake tunanin yaci bulus, but he’s mistaking, in takamar sa dukiya gidan ya zo” ta juyo ga mijin ta”Please pure heart let’s take her, mu taimaka mata, i can feel and understand her pain” daga haka ta mike cikin sauri ta haye saman bene, doctor Aaban ya bita da kallo, zuciƴarsa ba dadi, ya tsani ganin ta Cikin damuwa haka, numfashi mai dumi ya furzar yana lumshe idanun sa.
Doctor Abbas kuwa sai ya ji ba dad’i, musamman ganin yanda hankalin matar abokin sa ya tashi, ya kuma lura da daci a Muryar ta, sai yake ganin kamar shine silar damuwar su.
A nutse ya ce “I’m sorry, ban san maganar zata daga hankalin barrister Abrar haka ba da ban yi ba, duk da ban da matsaniyyar abinda ya sa ta damuwa ba, but I’m really sorry for…”

“It’s ok, baka yi komai ba, kana Iya kawo yarinyar duk sanda ka shirya” doctor Aaban ya katse shi.

“Nagode sosai abokina, Ni zan wuce Sai ka jini “. Ya fadi hakan ne saboda ya lura hankalin doctor Aaban din na wajen matarsa, bai kuma yi karya ba, domin ko haraban gidan Abbas bai bari ba doctor Aaban ya haye saman bene.
Zaune kan tiles ya tarar da ita tana kuka sosai, ya ya ji ransa ya kara ɓaci, a hankali ya rufe kofar, hakan ya saka barrister Abrar Ankara da shigowar sa, tayi saurin hadiye kukan ta, saboda ta san ya fi kowa tsanar ganin zubar hawayen ta, bata kuma yi masa adalci ba matukar ta cigaba da nuna halin kuncin da ta shiga domin ya wuce miji a gare ta, shi din rayuwar ta, wanda ya sadaukar da abubuwa da dama domin ta, cikin dabara ta goge hawayen fuskar ta, tana murmushi tace “har ya tafi doctor Abbas ɗin?”
“Don’t give me that fake smile decent one” ya karasa maganar yana zubewa gabanta yayi irin zaman da tayi, ta kamo hannun sa ta sumbata tace “I’m sorry, ban yi kuka dan na bata ranka ba, amma ban taba jin labarin daya karya min zuciya irin haka ba, ashe har yanzu akwai Mata da suke fuskantar irin wanna kalubale da wahalhalun, i just can’t bear it pure heart….” Ta karasa tana zubewa jikin sa, wani kukan na zo mata, ya rungume ta da kyau ya shiga kwantar mata da hankali da soyayyar sa mai zafi gareta da bata tsufa, cikin kankanin lokaci tayi shiru, ya dago kanta yace “karki kara zub da hawayen ki, banaso kina tuna baya, komai ya wuce, i have spoken to Abbas already za’a kawo ta, so stop carrying my little girl”
Dan dukan kirjin sa tayi tace “kai na fa girma yanzu, sai dai a cewa miemie little girl ”

Yayi dariya yace “no you re my little, har yanzu ina kallon ki like the 17years old you were when I first meet you, Babu abinda ya Sanja, shagwaba da rigimar ma karuwa tayi”. Tayi dariya sosai tana gyara kwanciyar ta a jikin sa.
Bangaren doctor Abbas kuwa, bai samu yaje wajen Munaya a ranar ba, domin bayan barin sa gidan doctor Aaban ya samu kira daga asibitin su ana bukatar sa cikin gaggawa.

Sai da aka yi kwana biyu da misalin ƙarfe biyu na rana ya samu isowa gidan su Munaya, ya aika kamar kullum aka kira masa ita, iddar da sallar ta kenan yaron ya shigo, tun Kafin yayi magana ta riga ta san doctor Abbas ne domin babu mai zuwa neman ta sai shi, bayan yaron ya fita, ta bishi a baya a hankali, domin ta fara nauyi, ga jikin mai Yawan motsi, ikon Allah kenan, domin bata motsa jiki ko zuwa awọ ko yin duk wani abu da ake bukatar masu ciki su yi, amma yaron cikin ta lafiyayye ne, daga yanayin motsawar da yake zai tabbatar wa mutum da hakan, a nutse ta yi masa sallama yana lura da girman da cikin ta ya kara, gashi bata wani Sanja yanayi ba ko kalar fata irin yanda wasu masu cikin kan yi, sai uban ramar data yi
“Are You ready?” Yace mata.
Cikin rashin fahimta ta kalle shi, yace “kar dai ki ce min kin manta maganar da muka yi dake last zuwan dana yi”

Ta ɗan lumshe idanunta, kana ta bude, Har ga Allah ta manta.

Yayi murmushi yace “Toh muje, idan kuma akwai abinda kike bukatar tafiya da shi dauko muje, ko kuma bana jin zaki bukaci wani abu, duk wani abun bukata akwai shi a can, so let’s go”
Dan jim tayi kafin tace “akwai abinda zan dauka, ina zuwa” ta fada tana juyawa a hankali ta koma cikin gidan.
Wani madaidaicin jakar ratayawa ta dauka, ta zuba yan hoton su, kana ta dauki rigar Amnah guda daya da bata yi sadakar sa ba, da takalmi, su kaɗai ke ɗebe mata kewar tilon kanwar ta da bata wanna duniyar tamu mai cike da kalubale, duk da tana jin radaddi a duk lokacin data tuna cewa Amnah bata tare da ita, amma tayi hakuri, domin Allah yafi son ta shiyasa ya karbe abar sa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo Mata, ta share su cikin sauri, i hankali ta furta “Allah ya jikan ki Amnah ta, Allah yasa ki cecemu ranar gobe kiyama, nayi matukar kewar ki, kin tafi kin barni a wanna rayuwar mai tarin kunci, ba ke, ba umma, sai doctor Abbas da Allah ya aiko yake taimako na…” Kasa karasawa tayi sakamakon wani mugun kuka daya taho mata, amma tayi saurin rufe bakin ta tana kokarin hadiye shi, tsawon mintuna uku kana ta zuge zip din jakar ta rataya ta dauki wani tsohon kwadon su daya sha tsatsa, ta fito daga dakin, ta tsaya a dan tsakar gidan na su tana kallon gidan tunani mabambanta na zuwa ƙwaƙwalwar ta, ta tuna wanna gidan mutane hudu sun taba rayuwa a cikin sa, a hankali suka dinga gushewa har ya rage ita ɗaya, a yau ita ma zata bar shi, “what a life” ta furta tsakankanin ƙananun labb’anta, ta share hawayen daya zubo mata, kana ta nufi hanyar waje, ta saka kwadon nan ta sakala kofar langa-langan su domin yaki datsuwa saboda tsatsar da yayi, yana zaune a kujerar driver sai dai kofar na buɗe, Wajen motar ta karasa a hankali, doctor Abbas ya zuba mata ido, ya san tayi kuka, amma ba zai ce komai ba, sometimes yana da kyau mutum ya rage wani nauyi da yake ji ta hanyar kuka, sai dai she’s too small for such a dark sorrow-ridden Amma bazata iya tsallakewa ba, domin hakan na cikin kundin kaddarar ta, ya kuma san dole tayi kuka domin zata bar in da ta rayu tsawon wasu shekaru zuwa wata muhalli da bata saba ba, bare sanin wani.
A nutse ya tayar da motar ya bar layin, yana lura da yanda wasu ke magana hadi da mika wuya domin ganin su da kyau, abin ka da ghetto area unguwar da jama’a, duk da babu dadi ana wa mutum bahaggon kallo ko tunani, amma bai damu ba, domin Allah ya ga kyakkyawar niyyar sa kan Munayan, ya kuma ji dad’i daya dauke ta daga unguwar, saboda hakan zai kara mata damuwa musamman masu gulmar ta a fili, shiru motar tayi babu mai magana, har suka iso unguwar da gidan doctor Aaban yake, manya manyan gidaje ne, kowa na cikin gida sai securitys dake waje, horn ya danna mai gadi ya leko ya ga shine yayi saurin wangale masa gate din, ya tura hancin motar sa ciki, a lokaci Munaya ta budi baki ta yi magana “doctor kana ganin zasu iya zama da ni? I’m scared” ta karasa cikin murya mai bala’in ban tausayi.
Doctor Abbas ya kalli fuskar ta dake bayyana tsoro da damuwa, ya sakar mata murmushi yace “i promise you zaki ji dadin zama da barrister Abrar da iyalan ta, they are the most kindhearted people i have ever seen, Zaki bani labari da kanki” ya faɗa yana ɓalle murfin motar bangaren da yake zaune ya fito, ya xagayo dayan ɓangaren da take ya bude mata, ta sanya kafar ta kasa a hankali ta fito.
Gaban ta na bugawa amma hakan ta daure ta bi bayan sa har suka iso kofar da zai sada mutum da falo ya tsaya Hadi da danna alarm dake manne gefe a bango, tsawon dakika bakwai suka ji alamun ana buɗe kofar, doctor Abbas ya ɗan yi taku biyu baya, a daidai lokacin da aka buɗe Kofar, wata kyakkyawar yarinya yar shekara shida ta bayyana ta washe haƙoran ta tace “lah uncle Abbas, sannu da zuwa” kana ta daga murya tace “mami uncle Abbas ne!” Sam bata lura da Munaya dake bayan sa ba, doctor Abbas yayi murmushi yace “miemie how are you?”

“I’m fine uncle” ta amsa tana barin bakin kofar zuwa Cikin falon, doctor Abbas ya juyo ya kalli Munaya dake rarraba ido ya mata alamun ta biyo shi, ji take kamar ta ruga ta koma gidan su, amma ta daure ta bi bayan sa zuwa Cikin falon yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa.
Doctor Abbas yace “zauna Bari matar gidan ta fito” sai a lokacin miemie ta lura da Munaya, tayi mata kallon rashin sani kana tace “ina wuni” Munaya ta dago kanta ta kalli kyakkyawar yarinya da zata yi Sa’a daya da Amnah din ta, sai dai ta fi Amnah girman jiki, ruwa hawaye ya kwanta a idanun ta, ta daure bata bari ya zubu ba, ta sakar mata murmushi tace “kina lafiya?”
Miemie ta amsa da “lafiya lau” tana kallon ta.
Doctor Abbas yace “ina junior da hammad?” Ban gan su ba”
“Suna daki suna wasa, ya jinjina kai ba tare da ya kara cewa komai ba, idanun Munaya ne ya kai kan wasu frame masu kyau da daukar hankali, wanda mutanen cikin hoton ya ja hankalin ta, wani kyakkyawan mutum da wata kyakkyawar Mace ta gani, wanda ta aiyana sune iyaye ga miemie, sai wasu da suka yi su biyar, a taikace dai family picture ne, suna a haka ne suka ji takun barrister Abrar dake saukowa daga saman bene cikin abaya maroon color da mayafin sa, munaya ta kasa dago kanta ta kalle ta, ji take kamar matar zata tsane ta idan suka hado ido, barrister Abrar kuwa sai data kai karshen stepcase ta ja ta tsaya, hawaye suka cika idanun ta suka zubo, sosai Munaya ta mata yarinta da daukar ciki, a zahiri tafi yarinta fiye da yanda doctor Abbas ya basu labari, idanun ta ya kai kan cikin daya fito, duk da ƙoƙarin boyewa da Munaya take domin kar a gani, cikin dabara ta goge hawayen da ke kokarin bata fuskar ta, ta karaso tsakiyar parlon tayi sallama hadi da zama kusa da Munaya, ta kirkiro murmushi suka gaisa da doctor Abbas, tace “miemie baki kawo musu abin sanyaya makoshi ba kika ishe su da surutu ko?”

“Allah mami ban yi surutu ba, ki tambayi uncle Abbas ma ki ji, kuma Allah mami kice wa Abbi ya kawo yan aiki, haka da muka je gidan k’awata na ga maman su ta kira yan aiki suka kawo mana lemo da snacks, kuma gidan mu yafi nasu kyau, kuma mun fi su kudi wallahi” ta fada cikin yarinta.
Doctor Abbas ya saki dariya, yana mamakin surutun miemie, barrister Abrar data rufe bakin ta saboda dariya tace “TOH ke ya aka yi kika san mun fi su kudi, muna da yan aiki mana, idan sun zo da safe sun yi ayyukan su sai su tafi, Abbin ku baya son zaman yan aiki a gidan sa, maza je ki kira kanin ki su gaisa da uncle din ku”
Ba musu ta mike ta tafi da gudu Domin kiran na su.
Barrister Abrar ta juyo ga Munaya data takure waje ɗaya, tace “sannu ko, kina lafiya?”
A sanyaye Munaya ta dago kanta ta kalli Abrar sai ta ga Kamar hotunan su dake bango Ya rage mata kyau, tace “ina wuni” tana kokarin zamewa kasa, barrister Abrar tayi saurin rike ta tana girgiza mata kai, kana tace “ina zuwa” ta mike zuwa kitchen, kamar ko ta san zasu zo yau ta yi girki da dan yawa, bayan ta shirya musu komai a dinning ta dawo ta zauna tace “ga abinci a dinning”

Shi kam doctor Abbas ya mike abinsa zuwa dinning din, domin Baya bakunta a gidan, ta kalli Munaya tace “Munaya ko?” Ta gyada kai alamun eh, ta kara cewa “toh je ki ci abinci ki zo muyi hira” ta fada domin Munaya ta saki jikin ta.

Ta gigirza kai tace “na koshi”

“Me kikace da kika koshi?” Ta tambaye ta.

“Na ci abinci kafin mu taho” tayi karya.

Barrister Abrar bata kara matsa mata ba, ba dan ta yarda ba, sai dai bata son takura mata.

Hammad daya sauko da sauri ya nufi wajen doctor Abbas, yayinda miemie ke rike da hannun junior suka ƙaraso falon, yaron ya kurawa Munaya ido Kamar ya santa, abin mamaki kuma sai ya nufo inda take ya kwantar da kansa a cinyar ta, murmushi ta saki, domin tana son yara sosai, amma banda na cikin ta, yanda yaron ya kwantar da kansa a cinyar ta melt her heart domin Amnah na yawan mata haka musamman idan ciwon ta ya matsa mata, a hankali Munaya ta saka hannunta ta shafa sumar sa, barrister Abrar tayi murmushi cikin mamakin junior domin sam Baya yarda da kowa, amma ikon Allah karon farko daya ga Munaya ya yarda da ita har da zuwa wajen ta.
Hammad daya ƙaraso cikin falon bayan sun gama surutu da doctor Abbas yace “Mami wacece wanna?” Ya fada yana nuna Munaya.
Ta masa wani kallo daya san ma’anar sa, yayi saurin cewa “I’m sorry mami, Ina wuni” ya fada yana kallon Munaya hadi da dan rissinawa kamar yanda mami ta koya musu.

“Lafiya kalau” Munaya ta amsa, tana sakin boyayyen ajiyar zuciya, fargaban ta ya ɗan ragu.

“Toh Mami wacece?” Ya kara tambaya.

“Anty din ku ce, she will be staying here with us”

“Yeeehy Mami, Ina son ta” hammad yace yana murna, miemie ma sai washe haƙora take, yaran akwai son mutane.
Bayan doctor Abbas ya gama cin abincin ya yi musu sallama, hadi da cewa yanzu zai je hospital din abokin sa wato doctor Aaban. Ya kalli Munaya yace “su Munaya inyee an yi Kani” yanda yayi maganar ya Basu dariya, amma ita murmushi tayi, zata iya cewa tun sanda Amnah ta rasu bata kara murmushi sai yau, real smile ne a fuskar ta yau, ba fake ba, lallai jama’a ma Rahama ne.
Bayan doctor Abbas ya tafi, Munaya tayi kokarin daukar junior zuwa cinyar ta Sai ta ga Ashe yayi bacci, barrister Abrar dake kallon su tace” bacci yayi kenan, dama baccin yake ji tun dazu yaki yi, kar ki daga shi ya kara Miki gajiya, bari naje na kwantar da shi” ta faɗa tana mikewa Domin zuwa daukar sa, sai dai tana daukar shi ya fasa ihu yana k’ok’arin komawa jikin Munaya, mamaki ya kara kama barrister Abrar tace Allah mai iko” Munaya ta dauke shi ko nauyinsa bare na cikin ta bata ji ba ta kwantar da shi a jikin ta, a dai dai lokacin wayar barrister tayi ƙara, ta duba ta ga Aminiyar ta ce barrister Hanan, kuma kanwa ga mijin ta, ta ɗauki kiran tana barin falon.
Munaya ta bi ta da kallo, komai na matar ya burgeta, musamman kirkin ta da fara’ar ta, a hankali ta sauke numfashi, daidai lokacin da dan cikin ta yayi wata irin juyawa tamkar zai tsaga cikin ta ya fito, tayi wata karamar kara da babu wanda ya ji tana cije labbanta, hawaye ya zubo mata tayi saurin goge wa.
Bayan kamar mintuna goma barrister Abrar ta sauko tana fadin “afuwan mun barki ke kadai ko?”

“Bakomai” Munaya ta fada cikin Siririyar Muryar ta mai cak’ude da tarin damuwa.

“Tunda yayi nisa a bacci barin dauke shi, ki samu ki ci abinci, kuma karki ce min kin koshi, babu kyau ki zauna babu komai a cikin ki a yanayin da kike ciki” ta fada tana daga junior a hankali daga jikin Munaya wacce tayi shiru ta kasa yi mata musu

Bayan barrister Abrar ta kwantar da junior ta haɗa wa Munaya abinci ta Kuma ce ta taso taci, bata jin zata iya yiwa matar musu, hakan yasa ta mike zuwa dining area din, duk kyau da dandanon abinci amma bata ci da yawa ba ta rufe, sai ruwa data dan sha mai yawa, Bayan ta kammala barrister Abrar ta kai ta dakin da ta ware domin Munaya tun daga lokacin da doctor Abbas ya basu labarin ta, daki ne mai dan girma mai haɗe da toilet had’add’e, cikin dakin na dauke da madaidaicin gado, comfortable for one person to lay on, sai wardrobe mai four door hadi da dressing mirror, sai madaidaicin plasma, decoration din dakin gold and brown color ne, a takaice dai dakin ya hadu kana babu tarkace a ciki, Barrister Abrar tace “Munaya this this your room, i hope you like it?” MUNAYA ta kasa magana saboda ko a mafarki bata taɓa tunani zama a muhalli irin wanna ba, lallai Wandannan mutanen da ta shigo cikin su na da zuciyar zinare, ta jinjina kai tana fadin ” Nagode sosai, Allah ya sa ka muku da gidan aljanna” ta karasa tana zubewa kasa, Abrar tayi saurin riko ta tace ” karki kara durkusa min, nima mutum ce kamar ki, ki yi wanka, ki sanja kaya lokacin sallah ya matso, ga wardrobe din ki nan akwai komai da zaki buƙata, kafin mu fita a sake siya Miki wasu Kayan” Abrar ta gama maganar tana ficewa a dakin, Abrar ta bita da kallo tana fashewa da kuka sosai, bata san meyasa ba, amma she feels so emotional right now, sai da ta yi kuka mai isar ta kana ta shige toilet din domin yin wanka.

 

MunayaMaleek is not for free, it’s five hundred via 3200689860 HARUNA RUKAYYA FIRST BANK.
Thanks for your patronage.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button