Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 13

Sponsored Links

🍇MunayaMaleek 🍓

 

_NoorEemaan_✍️📚

Related Articles

_masu tambaya na MunayaMaleek complete su sihirta min Please, ina zan gan shi fisabilillah? Yanzu fa nake typing din sa, ku dai ku zo muyi k’yakkyawar tafiyar nan tare da ku, abu daya na sani, sam babu ladama a wanna doguwar tafiyar tamu da ban taba irin sa ba a books dina. Patronize me, and follow my pen, for I assure you that you will gonna fell in love with MunayaMaleek_💖

 

Xiii…
(13)

Bayan su Shakur sun fito Daga masallacin, Maleek ya mike Daga kan dakalin daya zauna, yana jiran su karaso su tafi, Alhaji Dawood daya lura da fitar Maleek din daga masallaci ana sallame sallah yace “Maleek kana jira ana shafa addu’a da kai bayan ka iddar da Sallah, hakan abu ne mai kyau kaji ko?”

Ya shafa kansa kana yace “TOH daddy”

 

*Wacece Munaya*

Iyayen Munaya yan Asalin kasar Chadi ne, neman na kai ya dawo da su Nijeriya. A unguwar da talakawa suka fi yawa nan suka sauka a Abuja, suka samu dan karamin gida mai dauke da daki daya, banɗaki da kicin suka siya, inda ya kasance ginin jar kasa ce, dan ragowar kuɗin dake hannun Abba ya fara sana’ar burodi da shayi. nan suka cigaba da rayuwar su cikin rufin asiri, har Allah ya bawa Umma cikin Munaya, a kullum Abban Munaya bashi da zance sai na Umma ta haifa masa namiji, shi kam baya son mace, a kullum idan yayi wadandanan maganganun jikin Umma kan yi sanyi, domin ta fahimci mijin nata na daga cikin mazan da Tauhidi bai wadace su ba, domin duk wanda yake da sani, yake kuma aiki da ilimin sa ya kamata ya san cewa ya mace kyautar Allah ce, domin Allah subhanah wata’ala ya karrama mata, toh wane mutum da zai ce shi lallai sai d’a namiji yake so?
A takaice ranar da Umma ta haihu, ta ga tashin hankali, domin masifa da bakaken maganganun ya dinga mata kan me ta haifi mace tamkar ita ta bawa kanta, daga ranar Umma ta daina ganin dariyar sa, ko dan wasa da uba kan yiwa yar sa Abba baya wa yar jinjirar da aka haifa masa, ranar da ta cika kwana Bakwai, da asuba Umma ta daure ta tambayi mijinta kan wani suna ya zaba wa yarinyar, ganin tunda akayi haihuwar bai ce komai ba, a zafafe Abba yace babu ruwan shi da yarinyar, taje ta zabi duk sunan da yayi mata, a ranar Umma tayi kuka sosai, a karshe ta saka wa yar Maryam, sai dai tana mata inkiya da Munaya kasancewar sunan mahaifiyar ta mai rasuwa ne, ko rago bai yanka wa Munaya ba. a haka suka cigaba da rayuwa Cikin kunci har Munaya tayi shekara biyar Umma bata sake samun ciki ba. Kuma har zuwa wanna lokacin babu shakuwa tsakanin Abban da Munaya, domin sam baya mata wasa, saboda son namiji daya darsa a zuciyar sa.
Aka ce tsakanin miji da mata sai Allah, Munaya na da shekara tara, Umma ta sake samun ciki, wanna karon Abba ya dawo da kulawar sa ga Umma, har yake dan kula Munaya, domin ya riga ya gama yarda da kuma sawa a zuciyar sa cewa namiji Umma zata haifa masa wanna karon ko shakka babu, ita ma Umma tana addu’a a ranta cewa Allah ya bata namiji, duk da a ra’ayin ta ta fi son yaya mata, amma ganin ya fara kula Munaya sama sama hakan ya mata dadi ainun, tana kuma fatan ya daure, daurewar sa kuma na nufin ta haifi da namiji….

Sai dai Ubangiji ne mai kyauta, a lokacin da ya so, da kuma abinda ya so, sannan duk abinda Allah ya bawa bawan sa shakka babu shine mafi alkhairi a tare da shi, sai dai mai tunani kan gane hakan.
Cikin Umma na da wata tara da kwana shida ta fara nakuda, Abba da kan shi ya fita yace ya kira unguwar zoma. Babu jimawa ta sauka lafiya, sai da ta gyara Umma sosai da baby kana ta bude kofar, munaya da duk take a kage an fitar da ita daga dakin tayi saurin fadawa dakin cikin murnar jin kukan baby.
Abba kuwa jiki na rawa ya tambayi unguwar zoman me Umma ta haifa, cikin murnan matar ta ce masa an samu karuwar ya mace, dif jin Abba ya dauke, tsananin bacin rai ya bayyana a fuskar sa, haushin Umma ya cika zuciyar sa, a cewar sa ita ce bata iya haihuwa ba subhnanallah!
Bayan unguwar zoman ta tafi, fuskar Abba tamkar bakin haɗari ya fada dakin, inda Umma ke zaune kan yololuwar kafitar su tana shayar da jaririyar, yayin da Munaya ta sark’e hannun ta dana jinjirar tana mata wasa, Umma ta fara kokarin k’ak’alo murmushi, duk da yanayin fuskar sa ya sanya mata faduwar gaba amma bata nuna ba tace “Abban su ga yar kasa mata albar…”

“Babu Ni babu ke har abada Hadiza! Ba zai yu ki cika min gida da y’a’ya mata ba, akan me? Gwara tun wuri na nema wa kaina mafita, ga su nan na yafe su wa ke, idan ma ke baza ki iya ba na yafe wa duniya su” yana gama fadin hakan ya bar dakin fuuuuuu tamkar zai tashi sama tsananin ɓacin rai rubuce ƙarara a fuskar sa.

Umma bata tashi gane ma’anar kalaman da yayi mata ba sai da 11daren yayi ta ga bai dawo gida ba, hankalin ta ya tashi sosai, ga danyen jegon nan haka ta goya jinjirar nan ta rike Munaya da bata yi bacci ba suka fita zuwa neman sa, duk inda Umma ta san yana zuwa ta duba babu shi babu alamar sa, rumfar sa ta shayi ma ya cire, kusan babu komai a wajen sai murhun dafa shayin, jiki a mace suka dawo gida, a sammanin da fatan ta zasu tarar da shi a gida sai dai ko Inuwar sa babu, washegari shiru, babu shi babu alamar sa, Umma ta yi kuka tamkar zata shide, domin ta fahimci lallai guduwa yayi, ya tafi ya bar su saboda tana haifen ya’ya mata, wanda har yau babu shi babu alamar sa. (how cruel is Abba?!) Wanna karon ma
Umma da kanta ta saka sunan mahaifiyar Abba wa yarinyar Nabeelah, inkiya Amnah, tun Umma na kirgan kwanakin tafiyar Abba, har ta dawo shekara, daga lokacin ta tashi tsaye ta fara neman hanyar samun kudi domin kula da yanmmatan ta, ita ce shara da wankau wa mutane, har wata mata dake sana’ar abinci take tayawa girki, matar na bata dari biyar kullum, da haka take samun yan chanji a hannun ta wanda take kula da su Munaya.
Ranar da Umma bazata manta da shi ba, shine ranar da Amnah ta cika shekara daya, a kuma lokaci ne ta fahimci cewa Amnah na dauke da brain Cancer ♋ saboda yawan cutar da yarinyar ke yi yasa suka je asibiti, likita ya tabbatar mata da cewa yarinyar na da brain tumor, sosai abin ya dake ta, ta shiga damuwa mai tarin yawa, likita ya masu shawarwari da yanda za’a magance matsalar. Daga ranar Umma ta fara dan ajiye wani abu daga cikin kudin da take samu a aikatau din ta domin nema wa Amnah lafiya, domin kuɗaɗen ba kanana bane, burin ta shine Allah ya rangwanta Wa Amnah ciwon har ta samu ta tara kudin, Sai dai ko kwatan-kwata kudin bata tara ba Allah ya dauki ranta, daga wanna lokacin kulawar Amnah da komai ya dawo ga Munaya, ita ma ta ɗora daga inda ummah ta tsaya kan jajircewa domin samawa Amnah lafiya wanda a sanadiyar hakan ta rasa budurcin ta da Kuma tilon kanwar ta.
*wanna shine tarihin MunayaMaleek a takaice*

****

*Dawowar labari*

Hawaye cike a kwarmin idanun ta tace “Bazan iya ba doctor, baka san waye Maleek ba, Bama zai amince cikin sa ba ne, doctor banason abinda zai kara hada ni da Maleek har abada, bana kaunar sake ganin sa, dan Allah ka taimaka min, ya zanyi da cikin nan? wayyo Allah na” ta karasa tana fashewa da kukan tashin hankali.

Doctor Abbas ya yi shiru, jikinsa yayi sanyi domin yanayin yanda sautin kukan ke fita yafi komai kashe masa jiki da kara sanya masa tausayin Munaya mai yawa, ya Girgiza kansa, a nutse yace “ya isa toh, bazan tilasta Miki ba, amma kiyi tunani, ya kamata ya sani, even if bazai yi accepting ba, ya kamata ya sani cewa You re carrying his baby, kiyi tunani kan magana ta Munaya, zan dawo idan an kwana biyu, Please na roke ki don’t do anything stupid, kar ki yi wani abu domin zubar da babyn nan, ki sani cewa shi bashi da laifi komai, ki koma ciki, sai da safe” ya karasa maganar da barin gaban ta, yayin da yake jin wani abu mai kama da kishin Maleek din a zuciyar sa.

Munaya ta share hawayen ta da ba wai ya bar zuba bane, kana ta juya a hankali zuwa cikin gidan Kamar zata fadi saboda rashin kwarin jiki, tana zuwa ta fada kan tabarma ta cigaba da kuka Hadi da surutai masu ratsa zuciyar mai sauraro.

 

*MALEEK*
Saturday
_5:37pm_

Maleek ya kasa gane kansa tun daga ranar ɗaya raba Munaya da abin alfaharin ko wacce diya mace data san ciwon kanta, komai ya tsaya masa cak, bashi da nutsuwar zuciya ko kadan, a zahiri mutum zai dauka wata matsala ta rayuwa amma a badini ba haka yake ba, tunda abin nan ya faru a kullum sai tunanin ta ya fado zuciyarsa amma sai yayi ta maza ya kawar da ita, ya kan gaya wa kansa cewa bata da matsayi ko kwayar zarrah a cikin zuciyar sa, tunanin ta ma zai daina ne, ya san dalilin abinda ya faru tsakanin su yasa taki barin zuciyar sa, tunanin ta ma zai daina fado ransa ne. A hankali ya sauke ajiyar zuciya kana ya mike tsaye, cikin shigar Jersey armless da wando Mahadin Jersey ne a jikin sa, duka na Company’n *mike*. He looks handsome, giant and strong as ever, hanyar barin dakin ya nufa domin ya San kowa na falon kasa tunda yau weekend ga kuma Alh. Dawood na gari, cikin natsuwa heavy footstep ɗin da ke bada sauti yayinda yake taka matata kalar bene, duk suka juya suna kallon sa Kada ma Sa’adah ta ji labari, gaba-daya hankalin ta ya raja’a zuwa gareshi, dame a matse take da son ganin sa daurewa kawai take, ji take Kamar ta mike domin zuwa gareshi, domin wani kyau na musamman yayi mata a yayinda take kallon sa. Alhaji Dawood kuwa kallon dan nasa yake cikin alfahari, fuskar maragayiyar bilkisun sa yake gani, kalar fatar sa ce kawai Maleek din ya dauka…
Maleek kuwa sai daya karaso inda suke ya dauke idanun sa daga kan wayar sa, ya mayar aljihu, ta zauna close to Shakur, Yace “Barka da hutawa mum and dad” sai a lokacin Sa’adah ta dawo nutsuwar ta, murmushi tayi, ta wayance yayinda take amsar gaisuwar kamar yadda Alhaji Dawood ya amsa. Ta kasa hakuri yayinda ta shiga kallon sa kasa-kasa cikin salon da ba wanda zai lura, burin ta a yanzu ta kashe ƙishirwa data ɗebe shekaru masu yawa data diba, ta kuma samu hanyoyin data san zai Kaita ga cin nasara, saidai kash Alhaji Dawood ne matsalar ta a yanzu, so take yayi ya tafi ta samu aiwatar da kudirin ta hankalin kwance wanda ta san Maleek bazai iya tsallakewa wanna karon ba.
Maleek da Shakur Hirar su suke wanda yawanci maganar kan business din Maleek ɗin ne, Alhaji Dawood na dan sa musu baƙi, a hirar ya kara jin daukaka da cigaban da ya’yan nasa suka samu, musamman Maleek dayake business, and that makes him more proud of his boys.

 

 

 

*Wandanda suka yi payment ina sane da ku, zan yi adding din ku a group soon, Ngd jazakallahu Khair.*

 

MunayaMaleek is 500 via
3200689860 Haruna Rukayya first bank, shidar biya ta WhatsApp number na 07082281566

 

#Munayamaleek
#M square
#paidbook
#NoorEemaan

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button