Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 16

Sponsored Links

MunayaMaleek

✍️

 

Related Articles

Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks: nooreemaan

 

Xvi…
(16)

“Dan Allah ka saurare ni, na san an cuci Munaya, cuta mafi muni, ka fada min inda take, wallahi muna neman ta, tun ranar data dawo da kuɗin nan muke neman ta, but she’s no where to be found, karka duba zafin abinda dan’uwana yayi, saboda Allah ka nuna min inda take, na dade ina neman ta domin in bata hakuri, but trust me brother dina baya cikin hankalin sa ya aikata abinda yayi da ita wallahi, You may not believe” doctor abbas ya kara jinjina sauki kai da sanyin hali irin na Shakur, domin sam daukaka ko arzikin su bai rufe masa ido ba , yayinda haushin Maleek ya cika shi, ganin ko kala mai bai ce ba bare bada hakuri, shi da yayi laifi amma ya kasa bada hakuri sai wanda ba ruwan sa ne ya damu, ya lura Shakur na matukar son dan’uwan sa sosai, ba kuma zai yarda cewa Maleek baya hayyacin sa ya keta wa Munaya haddi ba, mahaukaci ne da shi da bai san abinda yake ba ko mene, kawai ya yarda da abinda Hausawa suka ce so so ne amma son kai yafi yawa.

“I don’t think zaka samu Ganin ta yanzu, domin bata ma san nazo nan ba, tace bata bukatar ganin dan’uwan ka, ni kaina bana son ciwon ta ya tashi….” Doctor Abbas ya kara maimaitawa domin yana son ran Maleek ya ƙara ɓaci.
Cikin sauri Shakur ya katse shi da cewa “ni zaka kai, nice nake son ganin ta Please”

Numfashi Abbas ya sauke, mutuncin Shakur ya saka yake kasa yi masa musu, ya ce “zaka ganta but not today, lemme have your contact, zan mata bayani first, idan na ga babu tashin hankali sosai a tare da ita zan kira ka muje gidan na su” cikin sauri Shakur ya shiga karanta masa lambar wayar sa, sannan suka yi musabaha, Shakur ya jaddada masa cewa ya kira shi ɗan Allah, kallon daya doctor Abbas ya kara watsawa Maleek mai cike da jin haushi hadi da kishi kana ya fita.

Bayan fitar doctor Abbas Shakur ya kalli Maleek dake tsaye har yanzu fuskar nan tayi ja jijiyoyin kansa sun fito rudu-rudu, kai tsaye mutum bazai iya fassara yanayin na sa, a zahiri Shakur ya fishi shiga damuwa sai dai from the inside, Maleek kadai ya san abinda yake ji, tsabar jarumta ce irin ta sa.

” You kept quiet, You didn’t say anything Maleek, meke damun ka ne, ka san irin tawayar da ka yi wa yarinyar nan kuwa,, and yet ka yi shiru baka ce komai ba, duk abubuwan nan sun faru amma ka zabi boye min wasu daga ciki sai yanxu nake ji, na kasa yarda dan’uwana ya aikata wanna munana ayyukan, Maleek what came over you?”

“Is that why kake bashi hakuri? meyasa zaka bashi hakuri, who is he da zai zo ya fadi abinda ya ga dama wa mutane, yaje ya kai maganar duk inda zai kai, i don’t bloody care!”

Tsabar haushi Shakur ya dauki ƙwallin serviette dake kan table ya jefi Maleek da shi ya daki kirjin sa, a fusace ya isa gareshi yace “You still have mouth to talk huh? Kana da bakin magana bayan tarin rauni da tawaya da ka yi wa diyar mutane, dan ka ga bata da kowa ko me, toh ka sani in dai maganar nan yaje kotu i will back Munaya, ko kana tunanin dan kana jinina zan goyi bayan karya, no i won’t, da kuma dukiyar ka zan diba in bi mata hakkin ta”

Idanun Maleek suka sake kadawa, yace “You know I’m not afraid of anything in this world right, ko ina zaku kai ni ka san bana jin tsoron komai, ba kuma zan fara kan wannan maganar ba”

“Eh na san cewa zuciyar dutse ce dakai baka shakkar komai, amma ka shirya yi wa mummy da Daddy bayani? Ni ne na yarda da cewa baka cikin hayyacin ka kayi wa Munaya haka, kana tunanin kowa zai yarda da hakan? Huh tell me” Shakur ya faɗa kamar zai kai mishi duka.

“Tun ranar farko da yarinyar nan ta shigo rayuwar mu na san ba alkhairi a tare da ita, gashi ta haɗa mu fada, abinda Bama yi, raina ya sosu da har za ka bar ni jininka ka goya wa wata can baya, taya bazan tsani yarinyar nan ba? kamar yadda ta tsane ni, haka nima i hate her, more than she does” yana gama fadin haka ya fice daga office din domin har an fara kiran magrib, basu taba kaiwa wanna lokacin a office ba, Shakur ya ɗan ji ba dad’i, musamman kalaman Maleek din ya ɗan saka jikin sa yin sanyi, shi ma ya san fadi yake kawai, tabbas bazai bari Munaya ta Cutu ba, ba kuma zai bar gefen dan’uwan sa ba, tun yarinta suna tare, ba kuma zasu rabu ba sai mutuwa in sha Allah”
A sanyaye ya fita shima yana fatan Allah ya warware musuz matsalolin su.

Yana zuwa haraban Company’n ya hango Maleek zaune cikin mota ya haɗe girar sama da ta kasa, duk da damuwar da yake ciki ya ɗan ji sanyi a ransa, dama ya san Maleek bazai taba tafiya ya barshi ba, ya shige motar, Maleek ya ja suka fice Nura mai gadi ya musu fatan sauka lafiya amma babu wanda ya kula shi, a yanda yake sharara gudu zai tabbatar maka da cewa ransa ba dad’i, Shakur ya dinga mamakin karfin hali irin na yayan na sa, kai ne da laifi amma kai ne da yin fushi.

*Mummy*

A dame ta dinga kallon agogo ganin shiru basu dawo ba, Domin basu taba dadewa irin haka ba, hankalin ta yayi matukar tashi, domin a wanna karon kam hakurin ta ya kusan karewa saboda yanda ta Kai kololuwa a bukatar Maleek, asirin ta zai iya tonuwa if care is not taken, ta rasa dalilin daya sa bai dawo ba, a yau ta zauna tayi wa kanta wanna tambayar, meyasa sai ranar data shirya cimma burinta a kansa ake yawan samun matsala in one way or the other?
Kasa da awa ɗaya mummy na zaune jugum har makeup din da ta yi domin Maleek ya fara lalacewa saboda gumi, duk ac din dakin amma zafi take ji, tana zaune haƙa taji horn din mota da karfi, bata kawo komai a ranta ba ta saki kayataccen murmushi, yayin da tashin hankali da damuwar data shiga na gushewa a hankali, tana cikin tunanin yadda al’amarin zai kasance tsakanin ta da maleek, har wani lumshe idanun ta take murmushi bai gushe daga fuskar ta ba… Budewar kofar falon data ji ne ya dawo da ita tunanin ta, Maleek ne a gaba, yayinda Shakur ke bayan sa, dukkanin su babu walwala ko digo a fuskar su, fuskar Maleek ma yafi bata tsoro, wani yawu mai kauri ta hadiye, ta dake hadi da mikewa tsaye tana faɗin “welcome home my son’s” ta fada da irin sigar da takan musu wasa ko Maleek zai saki ransa domin shine damuwar ta, shi kadai take gani, ta kama hannun Maleek zata zaunar da shi a kujera ya zame hadi hannun sa ya raba ta gefen ta ya nufi hanyar dakin sa cikin sauri tamkar zai tashi sama…

Shakur ne mai karfin halin sakar mata murmushi yace “thanks mummy, ya gida?”

Shima zai bi gefen ta ya wuce ta tare shi da cewa “lafiya meke damun my boy, kunyi fada ne?”
Mummy ta fada not minding halin da shi Shakur yake ciki, wanda shima akwai damuwa mabayyane a fuskar sa…

“Babu komai mummy” shima ya bata amsa da barin gaban ta cikin sauri, domin bai san sauran abinda zai ce mata ba kuma.

Mummy ta koma da baya kwaraf ta zauna kan kujera, ga koshi ga kwanan yunwa, dama ta san Shakur bazai fada mata ba, tun suna ƙanana basu fadin sirrin junan su bare yanzu da hankalin su, tunanin mafita kawai take yanzu, can ta mike zumbur kamar wacce aka mintsila ta nufi hanyar dakin Maleek da abincin data shirya masa, ta san yana jin maganar ta, da wanna damar da zata yi amfani, bugu da kari kuma bazata so tayi asarar wahalar ta da kuɗin ta ba, dole ne yau ta kasance da Maleek, ta kuma kashe ƙishirwar ta, ta san na yau ne da wahala, amma daga baya shi zai dinga neman ta da magiya, ba kuma zata yi masa yanga ba ko ja masa rai wurin bashi kanta ba, saboda tsananin so da kaunar da take masa, har hango hakan take a idanun ta, she can’t wait for that day, tayi wani irin juyi tamkar yar budurwa bayan ta ajiye tray din a gaban dakin sa, sannan ta shiga kwankwasa masa kofar a hankali.

*MunayaMaleek is not for free, Its 500 via 3200689860 First bank, shaidar biya ta WhatsApp number na 07082281566, thank you for your patronage, Noor tace madallah da masoyanta na gaske*

( na san da yawa kun zata free pages ya kare ne a nan ko? TOH ku duba kasa akwai sauran❤️)

Sai dai shiru, ganin bashi da alamar buɗe mata yasa ta shiga kiran sunan sa cikin kwantar da murya, yanda babu wanda zai jiyo ta sai shi Maleek ɗin, amma ko motsin sa bata ji ba, duk wata dabara ta gwada, hatta kuka ta saki, domin ta san baya jurar kukan ta, baya kaunar damuwar ta, ta san dole zai zo ya buɗe mata, sai dai bata ci nasara ba, mamaki ya kamata, yaushe Maleek din ta ya fara share damuwar ta? hankalin Mummy ya kara tashi, tana jin cewar bata cikin masu Sa’a a Duniya, hakika bata ci sunan ta ba Sa’adah ba, ta bar kofar dakin sa jiki a sanyaye musamman da ta ji motsin buɗewar Kofar dakin Shakur alamun zai fito, ba kuma ta son ya ga halin da take ciki.

*MALEEK*
A haukace yake hargitsa sumar kansa, gaba-daya ya rasa meke masa dadi har yanzu, shi ba tsoro ba, shi ba farin ciki ba, yanayi ne mai matukar wahala ya riske shi, gaba-daya ji yake Baya son ganin kowa, ya tsani kowa, he just want to be alone without anyone by his side, not even Shakur, shiyasa duk kira da kukan da mummy tayi masa bai bude ba, duk da kukan na ta ya daki kirjin sa, amma baya bukatar kowa a tare da shi, ya mike a zafafe, yana naushin iska, tamkar kuma mai yin fada ya shiga kiciniyar cire rigar sa, yayi saura daga shi sai dogon wando, ya nufi had’add’en babban toilet din sa, ya sakar wa kansa ruwa yayinda dogon wandon ke jikin sa still, hannun sa dafe da bango yana sauke numfashi a jejere tamkar wanda yayi tseren gudu, yayinda ruwan shower din ya cigaba da dukan jikin sa, ko kusa bai ji sanyi a ransa ba, duk da sanyin da Ruwan ke da shi, idanunsa sun yi matukar kadawa, idanunsa kuri a waje ɗaya baya ko kifta su, lallai ba karamin abu bane ke damun zuciyar Maleek din.

*MUNAYA*

Kamar kullum tana zaune tayi zurfi cikin tunanin data saba yi, ta ji sallamar yaro, ko ba a faɗa ba ta san doctor Abbas ne yazo, ta cire tagumin data zabga, ta mike tsaye, ta kalli yanda cikin ta ya fito ta cikin hijabin ɗin ta, ta saka hannu ta cikin hijab din, domin kare cikin, a sanyaye ta taka zuwa waje domin isa wajen shi, ta kuwa tarar da shi tsaye jikin motar sa sanye da kananan kaya da suka yi matukar kar bar sa, ya kura Mata ido cikin tausaya wa, tabbas Munaya bata dauki shawarar da ya bata na cewa ta cire damuwa ba, domin kullum kara ramewa take, halin kuma da ya ganta a ciki ya kara masa kaimi wurin aiwatar da abinda da yake ganin shine zai rage mata damuwa da kadaicin da take ciki.

“Ina wuni” ta ce cikin Siririyar Muryar ta mai cak’ude ta tarin damuwa, hakan ya kara masa tausayin sa, ya yi taku uku zuwa gare ta kana ya ja ya tsaya, ya rungume hannunsa a kirji yace “munayaaaaa! Bakya jin magana ta ko? Don’t take life too seriously. You Will never get out of it alive, challenges are what make life interesting, and overcoming them is what makes life meaningful, ki sani cewa Allah didn’t promise days with pain, laughter without sorrow, sun without rain. But he did promise strength for the day, comfort for the tears, and light for our way, Dan haka na roke ki, ki bar damuwa, everything is goona be alright ok?”

“Ok” ta amsa tana share siririn hawayen da ya zubo mata.

“Baki ji abinda naci Miki ba kenan, meyasa kike kuka again?”

“Ba…bani nake basu umarnin zubowa ba, su kan zubo ne a duk lokacin da suka ga dama
ya Abbas!” Ta karasa tana fashewa da kukan da take kokarin hadiye wa ta durkusa kasa ta rufe fuskar ta da hijab.

Sosai yanda ta kira shi da ya Abbas ya yi matukar sanyaya masa rai, domin yau yaji ta taɓa kiran sunan sa na ainihi, and that means a lot to him, wani yanayi na musamman yaƙe ji a kanta, ya sauke ajiyar zuciya, ya shiga kwantar mata da hankali har sai da ya tabbatar tayi shiru, sannan yace “mu karasa kan dakalin can mu zauna, akwai magana mai yawa da zamu tattauna karki gaji” ya fadi hakan ne, domin yasan ko yace ta shiga motar sa bazata shiga ba, bugu da kari kuma yana lura da Wani kallo da yan unguwar ke bin sa dashi, kallon wanda ya lalata wa Munaya rayuwa, hakan kuma bai dame shi ba, tunda Allah ya ga niyyar sa, ba musu Munaya ta yi gaba, ta zauna, shima ya zauna, Tsawon dakika biyar kana ya numfasa yace
“I meet Maleek and Shakur yau a ma’aikatar sa ta siyar da motoci” ya fada da zuba mata idanun sa domin ganin reactions din ta.
A zabure ta dago kanta, ta zuba wa doctor Abbas idanun ta, hawayen data samu ya fara kafewa ya sake tara ruwa cikin kwarmin idanun ta, a rayuwa bata son jin wani abu ɗaya danganci Maleek, domin babu abinda hakan ke kara haifar mata face karin damuwa, cikin rawar Murya take son fadin wani abu doctor Abbas ya dakatar da ita, cikin tattausa murya yace “Munaya i understand, Amma yanda kike so bazai yiwu ba, dole ya san da cikin nan, because he’s responsible, in gaya miki wani abu? Ina jin nafi ki tsanar wata halaka ta shiga tsakanin ku, because i hate him, duk abinda kike ga ina yi, ina wa babyn dake kwance a mahaifar ki gata ne, dole ya tashi ko ta tashi ta san uban ta, zaki so ya amsa sunan Bara Uba a duniya, for how long Zaki cigaba da yin shiru, gwara ya Sani tun yanxu, domin a gaba bai zama lallai ya amince ba, kina tunanin idan abinda kika haifa ya girma ba zai nemi Sanin waye baban sa ba? Komin dare gaskiya zata bayyana, Domin jini ba wasa ba, blood is thicker than water Munaya, zan iya kula da ke da babyn nan, har ya girma ya zata nine mahaifin sa, amma hakan ba mafita bace, ba mu yi wa babyn adalci ba, saboda innocent soul ne bai san komai ba,so meyasa zaki yi punishing din babyn da laifin baban sa? Kuskure da zunubi an riga an tafka ta, sai neman tafiyar Allah, saboda haka ki bani hadin kai domin yin abinda ya kamata, kin sani na dauke ki tamkar yar kanwata, bazan taba cutar dake ba kin ji?” Cikin gamsuwa ta jinjina masa kai, kima da darajar sa na sake samun mazugunni a zuciyar ta.

Ganin ta ɗan nutsu ya sa ka ya bata labarin yanda ta kaya tsakanin sa da su Shakur, bata yi mamakin halin ko in Kula da Maleek din ya nuna ba, she’s knows zai iya yin fin haka, ta kuma ji dadin yanda Shakur ya nuna damuwarsa ga halin da take ciki, ta sauke numfashi daidai sanda taji doctor Abbas ƴace “that Maleek guy is so arrogant, Sam Babu alamun damuwa a tare da shi, but I’m glad brother din sa na da kirki sosai, sannan abu na karshe ina jin it’s time da zaki bar gidan nan, akwai abokina *doctor Aaban* da matar sa hadi da ya’yan su, suna nan Abuja, can zaki koma har ki haihu, domin kin shiga stage din da kike bukatar kulawa da sanya idon babba a kanki, anything can happen ba fata ba, bana jin zan samu matsala da AABAN because na san shi sosai, sai gobe zan je na gabatar musu da maganar first, kin ga hakan ma zai rage Miki kewa da damuwa”

Shiru Munaya tayi, ita kanta zata so hakan, zata so ta yi nisa da nan, duk da abinda ya faru a watannin baya bazai taɓa fita a kwakwalwar ta ba, amma chanjin muhalli zai iya rage wani abu, Musamman da mutanen unguwar suka fara saka Mata ido, sai dai bata son ta zama takura ga kowa, cikin sanyin ta tace “amma doctor baka ganin zan takura musu, in ba damuwa zan iya cigaba da zama a nan din in Sha Allah babu abinda zai faru dani”

“Nima bana fatan wani abu ya same ki Munaya, ina da abokai masu iyali, amma ban ambaci kowa ba sai doctor Aaban saboda ina da tabbas a kan shi, karki damu babu wata matsala in Sha Allah”

A sanyaye ta dire gwiwowin ta a kasa, tace “Nagode sosai, jazakallahu khair, Allah ya faranta maka duniya da lahira, dan Allah ya zan maka godiya, saboda ina ji kamar kalmomin dana yi amfani da su sun yi kadan” ya saki murmushi, yanda ta karasa maganar ya sake fito da kuruciyar ta sosai, cikin jin dadin addu’ar data masa yace “tashi tashi ki Zauna, You said it all, Allah ya amsa Nagode” da haka dai suka yi sallama ya fada mata cewa zai iya zuwa gobe ya fada Mata yanda aka ciki, idan kuma bai samu ba sai jibi, yan Kayan kwamulashen da ya siya Mata ya bata, ta karba ta yi masa godiya ta koma cikin gidan su wanda ita daya ke rayuwa a cikin sa yanzu.

____★★★____★★★

Washegari daya kasance Lahadi da misalin karfe biyu a cikin hadaddiyar falon daya kawatu da kayan k’awa na zamani wani kyakkyawan magidanci ke kwance a kujerar three sitter, Wata kyakkyawar mata chocolate color ke kwance a saman kirjin sa, duk da sun yi nisa a bacci amma hannun su na sarke dana juna, daga yanayin kwanciyar tasu zai tabbatar wa Mutum cewa akwai tsaftataciyar soyayya, da fahimta a tsakanin su.
Can cikin baccin magidancin yaji karar wayar sa alamun shigowar kira, yamutsa fuskar sa yayi, kana ya ɗauki wayar dake saman kujerar zai kashe domin baya son Matar sa ta tashi, sai dai number’n daya gani na yawo a screen din wayar ya saka shi dakatawa, a hankali ya furta “Abbas!” Kana ya latsa kore, cikin murya mai cike da bacci yace “Assalamu alaikum”

Daga dayan bangaren doctor Abbas yace “ooops kar dai na maka kasalandan, na kira a lokacin da bai dace ba, ooh sorry na manta yau weekend” ya karasa cikin shakiyanci irin tasu ta abokai.

Murmushin daya tsaya a iya labban sa ya saki, ya leka fuskar matar sa ya ga tana bacci, hannun sa daya ya dora a kan Bayan ta, yace “gulmame kawai, toh bacci muke”
Daga dayan ɓangaren Doctor Abbas ya saki dariya yace “toh gani a kofar gate din ku”

“Toh shigo” yace yana katse kiran, kana ya sake kallon matar sa yana tunanin yanda zai ɗauke ta ba tare da ta farka ba domin yana son tayi bacci sosai, kasancewar tun safe bata huta ba tana dawainiyya da su, cikin dabara ya tashi da ita a jikin sa ya mike, domin ya ji an bude gate wa Abbas, sama inda dakunan baccin su yake ya nufa, a hankali ya kwantar da ita kan makeken gadon shi, zai mike kenan ya ji ta tsarkafo hannun ta ta zagaye wuyan sa tana buɗe idanunta daya dan kumbura, ya saki murmushi dama ya san sai ta farka, goshin ta ya sumbata yace “decent one kina bukatar bacci fa, kwanta doctor Abbas yazo barin je”

Ta girgiza kai tana mikewa zaune, bai ƙara magana ba ya shige toilet ya wanke fuskar sa da bakin sa ya dauki face towel ya goge fuskar sa kana ya fice zuwa kasa in da Abbas ke zaune, musabaha suka yi, kana suka zaune suna taba hira a tsakaninsu, bayan mintuna biyar matar ta sauko sanye da jar hijab har ƙasa, a mutunce ta zauna kusa da mijin ta tace “lallai yau za ayi ruwa da ƙanƙara, doctor Abbas ne a gidan mu, yaushe rabo?” ta karasa cikin zolaya, mijin ta na rike da hannun matar sa ya kallon jan lallen hannun ta daya fara fita yana sakin murmushi kadan kadan.

Dariya Abbas yayi yace “nine Barrister Abrar, na same ku Lafiya, ina yaran?”

“Lafiya Lou alhamdulillah, suna islamiyya”

“toh Masha Allah, ai yanzu zan dawo yin zumunci” ya fada daidai lokacin daya ga abokin sa na sumbatar hannun matar sa, wanda hakan ba bakon abu bane, duk wani abokan su su san Aaban ya kan rike hannun matar sa ko sumbatar hannun a gaban ko waye, soyayyar su na burge mutane sosai, domin tun ana tunanin zasu daina da zarar sun fara haihuwa, a madadin hakan tamkar kara musu son junansu ake.

“TOH Allah ya sa” ta fada tana zame hannun ta, kicin ta je ta dauko masa lemo, ruwa, da samosa data yi yau da safe” kana ta koma ta zubo masa abinci ta jere masa a dinning, ta dawo cikin falon ta ce “Bismillah ga abinci” ba musu ya mike yana fadin “kamar kin san ina jin yunwa kuwa, Allah ka aurar da mu, ko ma samu gata irin ta abokina” ya karasa yana daga hannun sa sama, suka yi dariya, shi kuwa ya nufi dinning table ɗin.
Yayin da matar da aka kira da Abrar ta zauna suna hira da mijinta kasa kasa suna dariya, duk yanda Abbas ya kware a son jin me suke cewa ya kasa, har ransa yake fatan ya samu soyayya irin ta abokin sa da matar sa idan ya yi aure, domin rayuwar su abar sha’awa ce mai cike da ilimi da tsafta…

Bayan ya gama, ya dawo falon, Abrar ta je tayi clearing inda ya ci abinci ta gyara, bayan komai yayi daidai ta fito daga kitchen din tace “ni zan koma sama” ta fada tana yin hanyar step, domin idan mijin ta yayi bako ta kan basu wuri su tattauna.

“Ammmm ai yau wajen ku na zo duka barrister, har dake kina da hakkin sani” tsayawa tayi cikin ɗan mamaki, ta Kalli mijin ta ya mata alamar ta zo ta zauna, ba musu ta dawo, tana fatan su ji alkhairi.

Bayan ta zauna, doctor Aaban ya yi gyaran murya yace
“muna jin ka doctor Abbas”
Abbas ya gyara zaman sa, ya fara da cewa.

 

In Sha Allah anan na kawo karshen free pages, duk wanda yake son cigaba da karanta MunayaMaleek ya yi payment domin ya More karatun sa, domin ba’a fara komai ba.

Ya rayuwar Munaya zata kasance?

Shin Maleek zai amince Cikin sa ne ya kuma karbe sa?

Me kuke tunanin kan Shakur da doctor Abbas?

Sannan su doctor aaban da barrister zasu amince su karbi Munaya kuwa?

Wani irin rawa zasu taka a rayuwar Munaya?

Ya labarin mahaifin Munaya, shine yana raye ko ya mutu?

Munaya na sake yin tozali da Mahaifin ta ko kuma baza su kara haɗuwa ba har karshen littafin?

Shin rayuwar Munaya zai sauya ko kuwa?

Ya mummy zata ji a yayinda labarin cikin Munaya ya riske ta?
Alhaji Dawood fa?

Waye zai ci nasarar Mallakar Munaya? Ku manta da cewa sunan littafin MunayaMaleek, ba’a nan take ba, tabbas Munaya deserve someone special, waye kuke tunanin zai yi nasara a cikin samarin?

Shin mummy na samun cikar burin ta kan Maleek kuwa? Kun san yar banza ce bazata taba hakura ba sai ta samu nasara, lallai Hakan zai tarwatsa zuciyoyi da dama.

Bari na dakata a nan da sauran tambayoyin dake ranku makaranta, domin suna da yawa, duka amsar ku na ga cikin book din, ki biya ki More karatun ki hankalin ki a kwance kada ku jira na bati.

Masu cewa basu da banki na iya zuwa pos, idan yaso a cikin dari biyar din sai ya dauki charges din shi, ina jin baya wuce 20 ko 50.

Yan Nijar da suka shirya biya zasu iya min Mgn ta Whatsapp number dina dake kasa.

Waɗanda kuma basu da banki ko kuma basu da mai pos a kusa, ku turo katin Airtel na 500.

 

MunayaMaleek is not for free it’s five hundred (500) via 3200689860 Haruna Rukayya first bank contact 07082281566 for more information.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button