Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 18

Sponsored Links

18…

Bude motar Farida tayi ta zagayo ta bangaren Islam ta bude kofar tace “zomuje ku gaisa da superman dina” girgiza kai Islam tayi tace “sabida Anty Hindu ta hadamu ta mana rashin mutunci ko, nidai ban kudin Bala ya kaini na siyo” wani dadi ne ya kama Farida takama kumatun Islam taja sanan tamata peck tace “luv u Islam dina, idan kun siyo ko, kubiyo ku daukeni saimu koma tare” karban kudin Islam tayi tareda mata murmushi taja kofan motar ta rufe sanan ta kalli Farida yanda take washe baki yasa tace “at least adan rufe bakin ko ta superman” murguda baki tayi sanan tajuya security dake bakin wajen ya budemata ta shiga tana waige waige, babban wajene da sanyin ac ya cika ko ina, bangare daya gym ne sai dayan bangaren da ake saida any type of fruit salad da smoothies and fresh veggies da coffee. Waige waige tadinga dan wajen da dan mutane ga wani calm music dake tashi kadan kadan, hangoshi tayi akan treadmill machine yana gudu, karasawa wajen tayi ta zaga ta gabanshi ta tsaya ahankali tace “good morning Mk” saida yadanji tsoro daya ganta agaban shi kaman anjehota daga sama, wanan wace irin yarinya ne, murmushi kawai yamata batare dayace komiba yacigaba da gudu abinshi, wasa takama yi da bakin hijabin ta fuskar ta yay wani iri, yanda take wasa da bakin hijabin saiya tunamai da Eesha, ahankali yasa hannu ya kashe machine din sanan yadau towel dake kan kafadar shi ya share zufan dayayi sanan ya sakko yadan wuce ta ya dauko dumbell yadawo ya zauna akan kujera, kujeran dake kusa dashi ya nuna mata yace “sit” murmushi tamai ta zauna shikuma yacigaba da daga dumbell din da hannu, baki tasaki a bude ganin yanda jijiyoyin muscles dinshi ke tashi. Ajiye dumbbell din yayi akasa ganin yanda ta kafeshi da ido kaman zata hadiye shi yay folding hanunshi a kirji yana kallonta wani irin kunya taji hakan yasa ta kawad da kanta tace “dama nazo na gaishe kane kawai, naji kace you are here and I know dis place very well” murmushi kawai yamata batare dayace komiba yadau bottle dinshi yabude yana shan ruwan tace “Mk wai mesa bakason min magana ne?” cire bottle din yayi daga bakin shi da sauri ya kalleta, murmushi tasake yi tace “kagani bakason yima mutum magana, tell me about your sef to, kaman family, career and everything about you, I wanna know u more” wani waiter ne yazo wucewa yakira shi yazo sanan ya kalleta yace “me kikeso aka wo miki” wani irin dadi ne ya lullubeta tawani langabe kai kaman baby tace “anything of your choice” maida duban shi ga waiter yayi yace “bring one avocado smoothie and one strawberry smoothie” juyawa waiter yayi yatafi ganin yana daddana wayarshi kirar IPhone Xmas yasa tai wani iri kaman zatai kuka tace “Mk” dago kai yay ya kalleta tace “tunda you don’t wanna go first ni I will tell you about my self” ajiye wayar yay daidai lokacin waiter yakawo musu smoothies din a wasu cups masu kyau da straw aciki, daukan na strawberry yayi yabata shikuma yadau na avocado, wani irin murmushi tayi tace “yamasan fevorite dina” kaiwa bakinshi yayi ya zuko kadan sanan ya kalleta ganin shi take kallo yasa yace “am listening” wani dadi ne yakamata tana mugun son yanda bakinshi keyi idan yana magana, ajiye smoothie tayi akan tray sanan tace “my family name is maikano, Babana dan asalin Fulanin nan yola ne, yanada one sister yayar shice amma, mai suna Anty Hindu, Anty Hindu Allah yay mata baiwar masifa, abinda ma yarabata da mijinta kenan bata taba haihuwa ba. So daddy na nada two wives but tafarkon yanzu she is late, tarasu lokacin I think I was either 13 ko14 years old, yara biyu ta haifan ma baban mu Yaya Abdallah wanda yanzu yagama mechanical engineering yayi applying short service na soja, yama samu yanzu haka yana can kaduna suna training, sai yarta tabiyu mai suna Islam wacce muke age mate” murmushi tasake mai ganin yay paying attention yana jinta tace “amma fa na girmi Islam dinfa ni kaga an haifeni March itakuma December but the same year kagani ai na rigata shan iskan duniya ko?” gyada mata kai yayi, tace “mum dina itace second wife we are three, yayana Ibrahim yanzu yana hostel a zaria dan ABU yakeyi, saini saikuma my 5 year old brother mai suna Sameer yana basic 1 yanzu, so My mum ita tai training dinmu dukan mu ta lura damu sabida Mumyn Islam was always sick sikla ce, thank god Islam da yaya Abdallah ba sicla bane suba, anata fita da ita abroad ana mata magani” shiru tadanyi ahankali yace “sorry Allah jikanta” murmushi tamai tace “Ameen, so tareda Islam muka taso tundaga nursery ajinmu daya saiyanzu damuka shiga University ne nake Mass com ita kuma tana Home economics, kasan difference dinmu? Ni am free minded, am very free and friendly, Islam is friendly oo idan tasaba dakai but tanada zurfin ciki, she is my only friend and sister and am her only friend and sister, I love her so much and she loves me so much, my mum yar yola ce itama fulani, tana aiki lecturer ce anan AUN, tana koyar da yan food and nutrition, Mumyn Islam kuma yar Sudan ce daga chan dadyn mu ya aurota. So this is my story tell me yours” murmushi yamata daidai lokacin wayarta yay ringing, ganin Islam ne yasa tai picking “okay tace” fuskarta ya nuna alamun rashin jin dadi ahankali tace “I have to go su Islam na waje sunzu daukana, bye but next time is your turn u will have to tell me about yourself and your family too” murmushi yamata yace “okay” harta fara tafiya ta dawo da sauri tawani langabe mai kai tace “bazama karakani ba?” wayarshi ya dauka ya ijiye cup din smoothie dake hanunshi yace “okay” ita ke gaba yana biye da ita abaya.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button