Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 24

Sponsored Links

Xxiv….
(24)

*MunayaMaleek is five hundred via 3200689860 Haruna Rukayya first bank.Evidence of payment to 07082281566 (Dan girman Allah idan baki shirya siya ba don’t chat me, masu tambaya idan suka siya sai dai na basu complete, toh bani da complete, munayamaleek is a ongoing novel, wanda bazai iya hakurin bin tafiyar ba should not buy please, babu gaggawa a wanna tafiyar, akace gaggawa daga shedan take, Bature kuma yace the patient dog eat the fattest bone, trust me you will gonna fell in love with munayamaleek in sha Allah, thanks for your patronage.)*

Kwana ɗaya, biyu, uku, har sati biyu ta shud’e ranar Shari’ar ta wuce Maleek bai je ba, bai kuma ji komai ba, domin yayi tsammanin *judge*(alkali) zai turo ayi arresting din sa kamar yadda akan yi wa ko wani mai laifi daya ki hallartar kotu. And then he remembered cewa Shakur ya ga takardar sammacin nan, ya san yayi wani abu akai, akwai dalilin shirun nan ɗaya ji ba hakan nan bane.
Ya ji wani irin relief a ransa sakamakon fasa shari’ar da akayi, ba dan komai ba, Saboda ya san maganar baza ta je kunnen iyayen su ba, dama fata da burin sa kenan.
Ya dauki wayar sa ya fara texting Shakur.

Related Articles

_Dear brother Thanks for always seeing troubles come my way before I could see them. an haife mu a matsayin yan’uwan juna, amma muna rayuwa tamkar abokan juna, i love You kid bro_

Bayan ya turo sakon sannan ya fara aikin sa cikin kuzarin daya rasa a yan kwanakin nan.

Shakur na hanyar sa ta zuwa gidan doctor Aaban domin yin godiya ta musamman a gare ta, dama ya karbi lambar doctor Aaban wajen Abbas ya masa godiya, domin tunda ya bar gidan a ranar bai kara komawa ba.
Ya shigo falon bakin sa dauke da sallama bayan an yi masa izinin shiga, ya tarar da barrister Abrar ce zaune da glasses a fuskar ta tana nazarin wani littafi, ya kalle ta, ya gaidata kana ya shiga godiya.
Ta girgiza kanta tana ajiye littafin wanda dama tun daya shigo ta daina karantawa, tace “bakomai Shakur, Ameen, but I’m sorry to say, put some sense into your brothers brain, fisabilillahi akwai dacewa kan abinda yake, Ni ba wai ina son sa anywhere closed to Munaya bane, ni da kai mun sani cewa Munaya bata son jin sunan sa balle haduwa da shi, amma he should show some concern kan abinda ya aikata”.

Shakur yayi kasa da kansa, Maleek! Maleek!! Maleek!!! Ya rasa yanda zai yi da shi, taurin kansa na bashi ciwon kai, addu’a kawai zai dinga masa domin baya jin magana ta Fatar baki zai narke stone heart din shi.

Ya kalli barrister Abrar kana yace “ayi hakuri in Sha Allah zan cigaba da yi masa, Nagode”

Ya yi shiru, sannan ya samu furta abinda ke ransa “Munaya fa, ban gan ta ba”

Barrister Abrar tace “Munaya na bacci, kasan tunda cikin ta ya tsufa bata iya bacci daddadare sai bayan asuba take samun bacci, Toh sai ta jima bata farka ba”

Yaji tausayin Munaya a ransa, yace “Allah Sarki, Allah Ubangijin ya raba lafiya”

“Ameen Ameen”

Zai mike kenan domin tafiya ya hango tahowar Munaya cikin taku da kyar, ya koma ya zauna bayan ya fahimci cewa shi ba’a zaune ba, shi Kuma ba’a tsaye yake ba.

Ina ma Maleek zai yarda ya biyo shi wata rana ya ga halin da Munaya ke ciki kila daya tausaya mata har hakan yasa ya gyara abubuwan da yake yi.

“Munaya har kin tashi?”

Barrister Abrar ta faɗa tana mata murmushi.
“Eh mami na tashi” ta fada da Muryar baccin da bai gama sakin ta ba, yunwa sosai ke kwakulan cikin ta shiyasa ta ƙasa cigaba da Baccin.

Ta kalli Shakur daya zuba mata ido da murmushi a fuskar sa, ta mayar masa da martani kana ta zauna a kasa, ta dago ta kalle shi tace “ina wuni ya Shakur?”

“Lafiya Lou Munaya, ya ƙarfin jikin ki?”

“Alhamdulillah!”

“Ki zauna mana a saman kujera, tiles da sanyi won’t You catch cold?”

A hankali tace “nafi jin daɗin zaman kasan ne”

Barrister Abrar ta mike da kanta domin kawo mata abincin ta kana Shakur ya samu yi Mata tambayar daya kasa yi ganin barrister a zaune, ba dan komai ba sai dan kada ta ga kamar sun gaza ne shiyasa yayi maganar.

“Munaya bakya bukatar komai, i mean Kudi, ko wani abu na ci, or anything?”

“A’a ya Shakur”

Ya sauke numfashi ya san kalar gidan da take ba karamin gida bane, ya san she won’t lack anything, amma yana so ya ga yana mata abubuwa saboda jinin sa (Maleek) ne ya ja mata duk wanna halin da take ciki, ya kara da cewa yace “ki cigaba da hakuri kinji munaya, Allah ya sauke ki lafiya”.

Tayi kasa da kanta, Da a ce kalmar hakuri na tsiro a jikin mutum da ya gama dabaibaye jikin ta saboda yanda a kullum kalmar ya Shakur din Baya wuce hakuri, ko a waya ko idan ya zo duba ta.

“Kin ji?” Ya kara fada ganin tayi shiru.

Ta jinjina masa kai da murmushin yake kan Innocent face ɗin ta.
Daidai lokacin da barrister Abrar ta kawo wa Munaya abincin ta.

Shakur ya mike domin tafiya, daidai lokacin ya ji karar shigowar massage wayar sa ya fito da wayar, ya bude sakon, cikin dakika biyar ya gama karanta sakon da Maleek ya turo, ya dauke kansa daga kan wayar ya kalli Munaya, ya ga itama ta kalle shi, yayi saurin dauke kansa, yayi musu sallama ya fita.

Barrister Abrar ta kalli kafar munaya dake mike a kumbure tsuntum ta dauke idanun ta daga kafar ta mayar da kallon ta kan fuskar ta tace “an jima idan kin huta sai ki dan fita compound ki taka kafar ki kin ji?”.

Munaya ta kalli kafar hawaye suka ciwo idanun ta, ta hadiye chips dake Baƙin ta, cikin damuwa da Kuruciya tace “Mami ya tara ruwa a ciki, kin gani har lotsewa take idan na taɓa”

Barrister abrar tayi murmushi fuskar ta na bayyana tausayin munaya, ta sauko kasa ta kamo kafar munaya ta shiga mamatsa mata tace “munaya ba ruwa bane a ciki, cikin ne ya sanya shi haka, idan kin haihu zai koma yanda yake”.

Kalmar haihuwa da barrister Abrar ta ambata sai ya karye zuciyar ta, taji kuka ya taho mata, duk yanda ta so hadiye shi kasawa tayi, tilas ta sake shi, ta shiga rera kukan, barrister Abrar ta ji kamar ta taya ta amma idan tayi hakan ai ya zama shirme, a matsayin ta na babba ya kamata ta zama jaruma domin lallashin munaya, ta kara matsawa kusa da munayan ta janyo ta gefen kafadar ta, ta shiga lallashin ta da kalaman masu sanyaya ruhin mai cike da damuwa, munaya tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jejjere, abincin ta da bata karasa ci ba kenan.

Bayan kwana biyu
da yamma doctor Abbas ya zo gidan, yayi wa su barrister Abrar sallama kan zai tafi Kano, kanin Mahaifiyarsa su ne ya rasu, suka masa taaziya da fatan dawowa lafiya, ya musu sallama kana ya mike ya kira miemie da hannu, a hankali yace “je ki kira min anty muyaya in yi irin ta Junior” miemie ta toshe bakin ta cikin dariya kana ta nufi dakin munaya da gudu.

Munaya na zaune a gefen gado ta ɗora kanta a pillow biyu, wani kan wani domin ya zama comfortable for her to lay her head on, miemie ta shigo tace “anty munaya uncle Abbas na kiran ki”

“Munaya ta gyada mata kai, gaba-daya bata jin daɗin jikin ta, kamar tayi ihun kuka haka take ji.

Ta mike a hankali tana cije labbanta saboda yanda taji wani ciwo na musamman daga kasan marar ta. Ta ɗauki dogon hijabi ta daura kan silky orange doguwar rigar da bai kai mata kasa sosai ba.

Ta shiga rarraba ido bayan ta fito tana neman sa a falon amma ta ga baya nan, barrister Abrar tace “ya fita haraban gida, tun dazu ya zo ai”

“Toh” munaya ta amsa tana nufar kofar fita, taji an riko hannun ta, ta juyo Junior ta gani, barrister tace “dawo ka zauna Junior yanzu zata dawo”

yaron ya makale kafada, ya kuma tabe baki alamun zai yi kuka.

“Munaya tace “mami ki bari na tafi da shi”

“Sai kun dawo” barrister abrar ta fada.

Munaya ta ɗora hannun ta a kansa ya shiga bin ta a hankali suka nufi waje.

Doctor Abbas ya mayar da wayar sa aljihu bayan ya hango fitowar su, ya zuba mata idanun sa musamman kafar ta, ya kuma kalli cikin ya ga yanda ya sauko kasa, a matsayin sa na likita ya san ta zuwan haihuwa, ya kawar da idanun sa daga kan cikin ya mayar kan fuskar ta.

“Assalama alaikum” tace cikin sanyayyar Muryar ta.

“Wa’alaikumu Salam, munaya hope you are fine?” Ya tambaya da kulawa.

Tayi murmushin yake tana jinjina masa kai, ya kalli Junior yana taɓa kumatun sa yace “Yaron anty muyaya”
Junior ya boye fuskar sa a jikin munaya yana dariya, ya taya shi dariyar kana ya dawo hankalin sa kan munaya yace “Kano zan tafi gobe in sha Allah”

Ta kalle shi tace “lafiya ko?”

“An mana rasuwa ne”

“Allah ya jikan mamacin” ta fada cikin sanyin murya.

“Ameen Ameen nagode”

Suka yi shiru for a while kana yace “shikenan abinda zaki ce min?”

Tayi kasa da kanta tace
“Ba zaka dade ba ko?”

Yayi murmushi yace “two days kadai zan yi in dawo”

“Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”

“Ameen Ameen nagode, me zan taho miki da shi tsara ba”

“Bakomi” ta amsa.

Yace ” ko da yake bai kamata ma na tambaye ki ba, dama na san bazaki fada min ba, na san abinda zai kawo miki”

Bata ce masa komai ba, ta jingina jikin motar sa yace “oops na manta, kin gaji koo? Sannu ki koma ciki, i will call you tomorrow morning”

Ta jingina masa Kai kana ta Fara tafiya…”munaya!” Taji Muryar doctor Abbas a kunnen ta.
Ta juyo ta ga yana kallon ta fuskar sa da murmushi yace “Na kusan fada miki wani abu dake nan din na”

Ta kalli inda ya nuna din, bata kowa komai a ranta ba, ta jinjina masa kai innocently labbanta na motsa wa da murmushi kana ta juya suka cigaba da tafiya.

Doctor Abbas ya sauke ajiyar zuciya ya
Cigaba da kallon ta har suka shige ciki, sai a lokacin ya shiga motar ya tada ta ya bar gidan.

“Alhaji ina son zan leka Hajiya maimoona ne na dawo.” Shiru Alhaji Dawood dake zaune a falo yayi da alama bai ji abinda tace ba.

“Alhaji!” Ta sake kiran sa wanna karon cikin dan daga sauti tana taba shi.

Ya dago da sauri ya kalle ta, ta zauna ganin yanayin sa, cikin kulawa tace “Alhaji lafiya dai?”

“Lafiya Lou Sa’adah”.

Duk da bata yarda ba amma bata kara tambayar shi ba tace “ina son zuwa gidan Hajiya maimoona ne”

“Hajiya maimoona kuma? Is it not shekaran jiya na ga tazo gidan nan?”

“Eh haka ne, bata da lafiya ne” tayi karya.

“Ayyah! Allah ya sauqaqe, kije din, my regards to her”

“Ameen sai na dawo” ta fada tana daukar handbag din ta ta fice.

Alhaji Dawood ya bi bayan ta da kallo, tunda ya dawo ya ga sauye-sauye masu tarin yawa a tare da Sa’adah din sa, mu’amalan su da komai ya sanja, hakkin sa bata son bashi sai yayi da kyar, babban abinda ya fi damun shi shine sunan MALEEK da ta kan kira a duk lokacin da suke tarayya ta aure yanzu, why MALEEK? Me yasa zata dinga kiran sunan dansa? Idan kuma ya tambaye ta tana da hujjoji masu karfi Domin ƙare kanta, ko tace masa bata faɗa ba, a iya sanin sa bashi da ear problem bare ace bai ji daidai ba, ko digo bai taba yi mata bahaggon tunani ba, kawai dai baya son tana ambatar wani idan suna tarayya ne, wani ma dansa a irin wanna lokacin, sam babu dacewa.

Anya ba zai je asibiti domin a tabbatar masa da lafiyar kunnen sa ba? Tabbas zai je. Da wanna tunanin ya sauke ajiyar zuciya.

Dariya suka kyalkyale da ita suka tafa, Hajiya maimoona tace ” Sa’adah ke done ce wallahi, Wato kika ce masa ba MALEEK kika ce ba, Abu Maleek ka….” Hajiya maimoona ta kasa ƙara sa maganar saboda dariya.

“Ni na rasa yanda zan yi na daina kiran sunan dan sa, kar asirina ya tonu ban shirya ba, shi yasa na zo takanas ki bani shawara ya zan yi, gashi kullum baya iya hakuri, shi ba abin kirki yake tsinanawa ba, amma ya dage sai dai ya bar ni da takaici, wallahi shi yasa ban so dawowarsa ba, duk ya takura min”

“Ki daure dai kina kama bakin ki, domin idan kika bari ya dago wani abin, toh zai mugun sanya miki ido har ki ƙasa aiwatar da plan din ki, ki iya takun ki Sa’adah domin komai ya tafi smoothly”

“kin san shi ma my boy kwana biyu na kasa gane kansa, hankalina ya tashi , sai da na sa aka duba min aka tabbatar min da cewa baya tare da wata mace ba kuma wata mace a zuciyar sa kafin hankalina ya kwanta, ke bari maimoon, zan iya taka ko ma wacece idan ta nemi shiga rayuwar Yaron nan, shiyasa tun wuri na saka aka duba min, kin San yanmmatan nan akwai kirsa kar taje ta lalata min raino”

“Huhuu mayyar MALEEK kawai”
Hajiya maimoona ta fada.

“Wayyo! baki zuciyata ba da kika kira sunan my boy” ta fada tana dafe kirjinta da kauraran yatsun ta Masu sanye da zobuna uku na danyen gwal.
Haka suka cigaba da hirar su, Hajiya maimoona na kara bata wasu tips din, har lokaci ya ja sosai basu fargaba, sai a lokacin Hajiya Sa’adah ta mike domin tafiya, ta ɗauki jakar ta, Hajiya maimoona ta rako ta har farfajiyar gidan, daidai lokacin da mota ke shigowa ciki.
“Wanna ba mijin ki bane?” In ji Hajiya Sa’adah.
Hajiya maimoona ta tabe baki tace “wallahi zai ma koma inda ya fito ne, ai yau ba’a gidana yake ba, dan na kira dan saurayina anjima zai zo ya kwana”

“Ina tsoron ki maimoona” Hajiya Sa’adah ta fada Cikin jinjina mata tana dariya.

Kan Hajiya maimoona ya ƙara fasuwa tace “ke tsaya wasa, ai shiyasa kika ga ba ruwana da waccan matar ta sa, saboda kin sani ba son sa nake ba, dole iyayena suka min aka raba Ni da masoyina, ai da ina kaunar mutumin nan da tuni na raba sa da waccan matar ta sa, zaman kudin sa nake ba aure ba”

“Yi shiru, yi shiru gashi nan” Hajiya Sa’adah ta fada kasa kasa ganin ya fito daga cikin mota.

Bafulatanin mutumin mai suna Alhaji Sooraj ya kara so inda suke da fara’a sa, cikin girmamawa Sa’adah ta gaida shi ya amsa, kana tayi wa Hajiya maimoona sallama ta nufi motar ta.

_amin afuwa, yan paid groups, dama wandan da nake tura musu ta PC. A duk lokacin da ba’a ga update ba, toh tabbas uzuri ne babba ya rike Ni, nafi kowa son ganin mun gama labarin nan, don’t rush please, ngd_💖

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button