Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 3

Sponsored Links

3*

Har dare Hammad haushin Jameel yake ji,dan shi a duniya ba abinda ya tsana irin a faɗawa stranger yana da ciwon ulcer,aganinshi kallon mayunwaci za’a masa.
Haka suka ci abincin se cika yake yana batsewa.

Koda gari ya waye,basu wahala ba cincin sukai ta ci da dublan.

Related Articles

Wajen azahar Hammad yafara jin yunwa,duk yadda yaso ya daure ya kasa dole ya isa ga Jameel wanda shima tun ɗazu yake kallon hanya yanaso yaga ta ina zata ɓullo.

“ya kamata fa kasamo wasu yaran abasu kuɗin suje su girko mana abinci ni yunwa nakeji”hammad ya faɗi sanda ya isa ga Jameel.

“karka damu nasan yarinyar jiya zata dawo,tabani tabbacin hakan,mu ɗan jirata kaɗan”Jameel ya bashi amsa cike da kulawa.

Hammad Juyawa yayi ya nufi cikim tantinsu,Bayan yaba Jameel ɗin wayarshi ya riƙe masa.kamar jira yana barin gurin Zahrau ta ƙaraso gun Jameel ɗauke da kwaryar nononta,ɗaya hannun kuma ledar abincin data dafo musu,shinkafa da wake dafadukan manja taji alayyahu da albasa se ƙamshi take.

Murmushi tayi tace”duk da baku buƙata ba amma na dafo muku wannan,sabida me ulcer nan”ta faɗi tana miƙa masa ledar da kular abincin take.

Da Sauri ya amsa yace”mungode sosai wallahi,shima yanzu yagama tambayarki,nace baku zoba tukunna”

Murmushi tayi batace komai ba,Wayar da Hammad ya miƙo masa ya riƙe masa ya ɗaga yasa camera yace”yakamata muyi hoton tarihi ko ƙanwata?”

Zahra’u murmushi tayi batace komai ba ya fara ɗaukarsu hotuna,tana dariya wani tana murmushi,har seda yagaji ya dena ɗaukarsu selfie ɗin.

Kwanikan jiya ya bata,dan dama suna ajiye agefenshi,sannan ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bata yace”ki ajiye wannan agurinki ki dinga yo mana girkin,in sun ƙare ki sanar dani zan ƙara miki,sati uku zamuyi anan mu tafi”

Amsar ƙuɗin tayi tana murmushi,ta juya tabar gurin ta ƙarasa inda suke siyar da nonon.

Ɗaukar ledar Jameel yayi ya nufi gun Hammad,da hanzari,dan yasamu yaci abincin.

Ganin jameel da abincin sosai ran Hammad yayi masa daɗi,matsowa yayi kusa dashi yana murmushi duk fushin da yake ya huce,yace”ta zone yarinyar?”

“Kana baro gurin tazo wallahi,yarinyar akwai kirki ga sanin ya kamata,kaga yau tun kan musa tayi tayo mana”

“naga alamar hakan”Hammad yace sanda ya ciko cokali da abincin ya danna abakinsa.

Lumshe ido yayi yana tauna abincin gashide ba nama akasa ba amma daɗin abincin ya wuce inda yake tsammani.

Jameel na janshi da hira ko sauraronsa bayayi ya maida hankali kan abincin seda yaji yacika cikinsa tab sannan ya ajiye cokalin.

Kamar daga sama suka fara jiyo ƙarar harbe harbe da guje gujen mutane ana ihu.

A hankali suka fito daga tantin ga mamakinsu ankashe mutane da dama agurin musamman ƴan talla da suka zo.

Harbin ne yafara yo ɓangarensu,da gudu suka nufi bayan wani dutse,hankali atashe,Jameel a firgice ya kalli hammad yace”ƴar filanin nan data dafo mana abinci tana gurin can,bari inje in taimaka mata kar wani abu yasameta”

Yayi yunƙurin zuwa harbin ya yawaita dole ya tsaya,guri yayi guri domin tankokin yaƙi aka fito dasu daga cikin barikin aka fara ɓarin wuta tsakanin sojoji da Ƴan bindigar da suka kawo hari garin,dan tuni sun shiga cikin rigagen sun ƙona komai sun kashe mutane,shine suka dawo nan bakin titin.

A gigice Jameel yaja hannun Hammad suka ruga da gudu zuwa cikin jejin domin su samu mafaka,sede ƙarar da jameel ɗin ya kwalla ce tasa Hammad tsayawa ya waiwayo yaga me ya samu aminin nasa,

Wayyo Allah harbinsa akayi agadon baya,rungumeshi yayi suka faɗi tare,ya tallafoshi yana ƙarajin kiran sunanshi,”No!!!!!!!! Jameel !!!!!!!! wake up!!!!”!!”yana ihun jijjigashi,Jameel wanda idonsa ke shirin lumshewa a hankali yace”ka kula da ƴarfilanin nan Hammad”yana kaiwa nan yafara salati jini na fitowa ta bakinsa.

A gigice yake jijjigashi amma ina jikinshi ya riga ya saki.

Ihu Hammad yake iya ƙarfinsa yana jijjiga aminin nasa,yana kiran sunanshi,amma shuru,

Harbin da ake yowa ta ɓangarenshine yasa ya miƙe da gudu,Ɗauke da Aminin nasa a kafaɗa ya ƙara nausawa cikin jejin,zuciyarshi na masa zafi.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button