Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 6

Sponsored Links

*0?6?

*Wannan littafin na kudi ne meso ya karanta ya nemi wannan number 08030811300*

 

Washe gari ita mommy ta baiwa tsaraban yaran nata dake aure ta hadata da driver ta kai musu,duk da cewa tana da makaranta amma ita sam wannan ba matsalarta bace,damuwarta shine ta idar mata da nata aiken koma ya zatayi ba matsalarta bace,hakan ya sanya a gurguje taje ta miqa musu,ba wani zama tayi ba,ko dama can ba wani sabo ke tsakaninsu ba,tsakaninsu da ita idan bautarsu da tashi,gidan anty safiyya kawai ta dan zauna har ta sha ruwa,kasancewar duk ta fisu sakin fuska da janta a jiki.

Ranar bata shigo gida ba sai qarfe biyar na yammaci,duk da haka bata zauna ba sai data shiga kitchen ta shiryawa daddy abincin dare da taimakon inna laraba,data gama dinma dai ba zama tayi ba,kayanta ta soma hadawa wanda zata je gida gobe da su,tsaf ta shirya kayan nata cikin matsakaiciyar jaka,kaman yadda ta saba ta tsinci wasu daga cikin kayan nata ta zuba daban da niyyar yin kyauta da su kaman yadda ta saba.

????????

Tafe suke shida drivansa cikin motar tasa baqa wul,wadda kallo daya zaka mata kasan ba qananun kudi aka sanya aka sayeta ba,yana lafe bayan motar sanyin raba na kadashi,sanye yake da suit suma baqaqe wadanda suka dace da kalar fatarshi wadda ainihin hutu da jin dadi suka ratsashi,dirarsa kenan cikin qasar,wanda a yanzu haka yana hanyarsa ne ta isa gida,lokaci lokaci yakan lumshe kyawawan idanunsa dauke da zara zaran gashin ido,hakanan yake jin kasala da gajiya sun masa dabaibayi,Allah Allah yake ya isa gida yaga anninsa ya kuma kwanta ya huta.

A hankali qaramar wayarshi da bai wuce mintuna goma da kunnata ba ta dauki qarar qaraurawa,ko bai daga ba yasan wacece,ita kadai zata kirashi ta cikin wannan wayar,saboda don ita kadai ya saka layin ciki,hakanan daya bude yaci karo da tarin saqonninta tun na kwanaki bakwai da suka wuce,wato kwananshi biyu kenan da barin gidansu,kwana daya kuma da ganinta da yayi a wancan eatery din,wanda yayi dai dai da tafiyar data kamashi zuwa china sai a yau ya samu dawowa,a kasalance ya saka hannu ya daga wayar gami da karata a kunnesa
“Na gode da wulaqancin da ka yimin,duk ni na saiqa kaina koma meye ka yimin khalipha” idonsa ya sake lumshewa ya bude yana jin yadda taratsin maganarta ke ratsa kwanyarsa
“Afwan dija na”ya fada cikin qarfi halida danne bacin ranshi a kanta wanda ya haifar da sanyi a muryarsa,sanyin muryar da ta kashe mata jiki tare da sauke kaso hamsin cikin darin bala’in data so yi
“Ni baka da abinda zaka gayamin,wannan wanne irin cin fuska ne,tun ranar da kazo gidanmu na qarshe gaba daya aka daina samunka a waya,kuma kai baka neme ni ba,haka ake soyayyar?”boyayyen murmushi kawai ya saki,shi yasan ba wannan ne maqasudin fadanta ba,a baya bata taba nemansa ko damuwa da duk kwanakin daya dauka baije gidansu ko ya nemeta ba,idan ya nemeta falillahil hamd,idan ma bai nemeta ba duk daya wai mamaci ya karye
“ai nace kiyi haquri ko?,wayar tawa ce ta samu matsala,sai yau na samu na karbo daga wajen mai gyaran” ya qarshe maganar yana istigfari cikin zuciyarshi,daga can bangaren khadija dummm tayi,tana sake ji cikin zuciyarta da jikinta lallai muhammad din bai dace da ita ba sam,baiwar kyau kawai Allah ya masa,wanda bazata bari kyansa ya rudeta ba ta shiga gidan da bashi take da buri ba,wanne irin gyaran waya fisabillilahi,wayar tashi da ko tata wayar ta fita tsada,don ranar farko data fara ganin wayar sai data sake kallonta,gaba daya ba zata wuce dubu goma ba
“Kawai ka fadi me ya hanaka dawowa,ko babu waya ai qafafunka zasu iya kawoka,ko kudinne ba zaka iya bani ba shi yasa ka janye jiki?” Maganarta ta bashi dariya,baisan murmushin da yayi ya fito fili ba sai data ce
“Dariya na baka?” Cikin waskewa yace
“A’ah….ba haka bane,gani nayi kin kusa canko abinda ya hanani dawowa…..kawai dai kudin ne basu samu ba,kuma ina kunyar nazo miki haka” ranta yayi qololuwar baci,a haka zata aureshi?,mutumin da ya kasa mata kyautar naira dubu talatin kacal ina zai samu kudin aurenta,a gabanta kowacce cikin qawayenta suka dinga karbar alert na kudade daga samarinsu,mai qaramin kudi cikinsu itace wadda aka turowa dubu talatin,sai ita zata tashi a tutar baya?
“Kana nufin duk jiran da nayi ya tashi a banza kenan bazan samu ba?” Sake gyara kwanciyarshi yayi bayan motar sanyin A.C na ratsashi,cikin kwantar da murya kaman gaske yace
“Ni bance ba zaki samu ba,ai Allah shine mai bayarwa,shike kuma azurta bawa a duk sanda yaso,ina nan ina qoqari cikin satin nan ina saka ran Allah bazai hanani ba” shiruuu tayi bacin rai na ratsata
“Ai shikenan” abinda ta iya fada kenan ta katse kiran,wayar ya cire a kunnensa yana kallonta,ya sake sakin murmushi kawai yana girgiza kai,baiyi ko yunqurin nemanta ba ya aje wayar gefanshi saboda baison sauran hayaniya hutu yake nema kuma,har suka isa gida yana tunanin rayuwa da irin darussan daya samu masu tarin yawa dangane da halayyar ‘yammatan zamanin nan.

A nutse yayi sallama cikin parlourn alfarma wanda yake mallakin mahaifiyarsa,parlour ne daya wadata da dukkan wani nau’i na kayan morewa rayuwa,dattijuwa anni na zaune cikin daya daga cikin kujerun tana sauraron hadisai saga tashar talabijin ta saudi sunna tare da kallon masallacin ma’aiki da suke nuno lungu da saqonshi,a hankali ta cira kai tana amsa sallamar tashi fuskarta qunshe da fara’a,yayin da bakinta ke furta masa marhaban lale,cikin qauna irin ta d’a da mahaifi ya iso gabanta,suka shiga gaisawa cikin nunawa juna kulawa
“An dawo lpy”
“Lpy alhmdlh anni cike da nasara”
“Alhamdulillahi rabbil Aalamin” ta fada tana hade hannayenta waje daya kaman mai addu’a,kansa ya sake dagawa ya dubi saudi sunnah sannan ya kuma duban anni cikin murmushi
“Ko yaushe cikin shauqin wajen nan kike anni” murmushi ta sake masa mai sanyi irin na manyan dattijai sannan tace
“Banda abinka khalipha wannan waje ko sau nawa musulmi zaije ai bazai rabu da shauqinsa ba,ba zaiqi ya dawwama a nan ba har ranar mutuwarsa”
“Gaskiya ne,inaga ki soma shiri zan sa khalid ya shirya miki komawa can cikin watan nan,ko sati hudu kije ki sake yi” murmushi ya sake yalwata kan fuskarta,farinciki tare da alfahari da tilon dan nata ya sake mamayarta,bai wasa da duk wani abu data nuna tana muradi ko da iya kan fuskarta ya fuskanci haka,kwata kwata watanta uku cikin na hudu da dawowa daga umrar
“Ba matsala khalipha?” Murmushi ya saki
“Har abada anni ina fata mun tserewa matsala,ko sau nawa mike da buqatar zuwa ki fadi kawai,yaronki a shirye yake da ya kaiki,uwace ke da ba kowanne d’a yake dace sa irinta ba,har abada bazab manta sadaukarwarki garemu ba”
“Alhamdulillahil lazi bi ni’imatihi ta timmus salihat,Allah yaci gaba da yiwa rayuwa albarka,ya tsareka ya maka jagora,Allah ya zama gatanka kaida ‘yan uwanka,ya hadaka da mace ta gari”
“Amin ya Allah anni,Allah ya qara lafiya da nisan kwana”
“Amin amin” ta fada tana murmushi,ya bude bakinsa zai sake magana yaga shigowarta falon,hannunta riqe da wani kyakkyawan kwando kwanon tangaran,tana sanye cikin shadda gezner ruwan hanta wadda aka yiwa dinkin buba da ado mai kyau tun daga sama har qasa,tayi daurin zamani tare da buga kwalliya sosai,suna hada idanu ta soma jifansa da murmushi,janye idanunsa yayi a hankali ya maida kan anni yayin da take qarasowa kusa da su,ta aje kwanon gaban annin sannan ta zauna tana fadin
“Barka da dawowa ya khalipha”
“Yauwa,sannunki amal”
“An dawo lpy ya hanya?” Ta fada tana murza yatsunta kanta a qasa alamun jin kunya,ya sake dubanta ya dauke kai sannan ya miqe yana cewa
“Alhamdulillah,yasu momma?”
“Lafiyarsu qalau suna gaidaka”
“Ma sha Allah,anni zan shiga nayi wanka na huta” daga kanta amal tayi da sauri tana dubanshi
“Ya khalipha ga abinci can na shirya maka fa” ta fada a narke tana dubanshi
“Am ok,nafi buqatar na huta” ya fadi yana soma motsawa alamun zai wuce ne
“A’ah ai ba’ayi haka ba,kaje kayi wankan saita miqo maka ko a can sai kaci” cewar anni wadda bata so amal din taga kaman ya gwasale qoqarinta ne,saboda tunda ya kira annin yace mata sun taso take rawar qafa
“Ba damuwa anni” ya fada yana daukar safarshi daya cire yayi gaba.

Sai daya kashe wayoyinshi kaf sannan ya rage kayan jikinsa ya fada bandaki,mintina talatin yayi sannan ya fito,ya shirya cikin jallabiya mai gajeran hannu,yana cikin fesa turarensa ya jiyo knocking daga can qofar falonshi,ya aje turaren yana daukar wayarsa qwaya daya ya kunnata sannan ya fita zuwa falon.

Amal ce ita da mai aikin anni raliya,wadda ke dauke da kwanukan abinci,sakin qofar yayi,amal ta amshi kayan abincin daga hannun raliya ta shigo ciki,kasancewar ta sani baiso kowa na shigo masa bangare barkatai,a gabanshi ta dire kwanukan abincin a sanda yake waya da P.A dinshi,kafin ya kammala harta gana zuba masa komai ta samu gefanshi daya daga cikin kujerun ta hakimce tana satar kallonshi,ba qaramin so takewa khalipha ba,ji take kaman ta bude ido taga ya zama nata,komai nashi yayi mata,sak irin mijin data sha zanawa a mafarkinta,kyakkyawa mai qirar qarfi,mai aji mai kudi kana mai dimbin ilimi.

Hada idanu sukayi sanda ya dauki plate din data cika da fried rice da gasashshiyar kaza a gefe,daga cikin dabi’unsa sam baison kallo,a nutse yana juya abincin yace da ita
“Akwai wani abu da yayi saura ne amal?,kina iya tafiya” shagwabe masa tayi tana noqe hanci
“Haba ya khalipha,wanne irin na tafi bayan hira nakeso na tayaka?yaushe rabon da mu hadu don Allah,amma kai ko irin nunawa ma baka yiba” fararen idanunsa ya watsa mata yana tauna abincin bakinsa a hankali,sai daya hadiye sannan yace
“Indai zaman hira kika zo yi yanzu kam bazan iya ba,kinsan ban iya cin abinci ana min surutu ko?”kai ta sadda qasa
“Kayi haquri to” sai ta dan bashi tausayi kadan,banda ya riga ya gama da farke layarsu ita da mahaifiyarta bai tunanin zai iya tsallakewa tarkon ita yarinyar a yadda take binshi sau da qafa
“Is ok,kije ciki idan nayi bacci na tashi zan shigo,sai muyi hirar ko?”
“Tohm” ta fada tana miqewa tare da ficewa daga parlourn bayan ta ja masa qofar,kai ya girgiza yana ci gaba da cin abincinsa a hankali,har yau bai manta da mahaifiyarta ba wato momma zinat,har yau bai mance irin kyara tsana tsangwama da kallon qasqanci da ta dinga jifansu da shi shida mahaifiyarsu ba a wani zamani baya can da ya shude,sai gashi cikin qanqanin lokaci momma zinat din ta koma daya daga cikin gagga gaggan masoyansu,abun da mamaki da kuka daure kai a wajenshi,saida ga duk wanda baisan abinda ya faru shekara kusan goma sha biyar baya ba zaiyi zaton soyayyace daga Allah momma zinart din ke musu,da wannnan tunane tunanen ya kammala,a nan kan doguwar kujerar da yake kai ya miqe,kan wani lokaci bacci yayi awon gaba da shi kasancewar tafiyar da yayi bai samun isashshen baccin da ya kai awa hudu ko biyar

????????

Tunda suka shigo siririn titin da zai sadaka da ainihin qauyen nasu tunaninta ya rarrabu kashi kashi kaman yadda ta saba kowanne lokaci,ina zata sauka?,a wanne gida zata fara yada zango?,gidansu mahaifinta ko gidansu mahaifiyarta?,ko kuma gidan gwaggwo lami?,ason ranta gidan gwaggwo lami tafi sha’awar ta sauka,saidai hakan ka zama tamkar ta aikata wani laifi ne aduk sanda labarin zuwanta ya iske gidansu mahaifiyarta harma dana mahaifin nata,zasuyita mata fassara daban daban kaman yadda suka saba,duk da cewa ada bawai sun damu da rayuwarta bane,saidai a yanzun suna son nuna sun damu da rayuwar tata ko don dan qaramin alkhairin da take riqowa tazo musu da shi,wanda hakan ya dan sauya yanayin mu’amalarsu da dangantakarsu,sauyin da bai taka kara ya karya ba,sauyin kuma da bashi da wata ma’ana ko alfanu a gareta.

Itadai a baya tasan ba wanda ya damu da rayuwarta,babu wanda ya damu data rayu kota mutu,ba wanda keson ta rabeshi,kowa gani yake rab’uwarta da shi wani kayan nauyi ce,idan kuwa ya zama dole ta rabi mutum din yana ganin ya yiwa rayuwarta gagarumar alfarma ne,koda kuwa babu wani abu da yake iya tsinanawa rayuwartata

Umarni ta baiwa mai motar da ya daukota tun daga tashar takai saboda asma’u ta fice da motar da daddy ke fadin wai ya basu,wai mana tunda bata taba shigarta ba itakam,hakan kuma bai dameta ba,mommy kuma ta kasa bada koda qarama cikin motocinta biyu a kawota kasancewar babu idon daddyn,tun da sassafe ya sallameta sukayi sallama ya fita,tace drivan ya sauketa qofar gidansu mahaifinta,tunda duk tsiya da uba ake ado,yaran da sukayi tsaye gaban motar su suka daukar mata jakarta zuwa cikin gidan,sai data biya direban sannan tabi bayan yaran zuwa cikin gidan,lokaci lokaci gabanta na faduwa tare da tunanin me kuma zata taras wannan karon.

Kamar ko yaushe,kamar kuma kowanne lokaci irin wannan,dukkan matan sassa sassa dake gidan na gindin qatuwar bishiyar dake tsakar filin gidan,wadda kusan itace ta zama wajen hutawarsu a duk sadda rana ta qwalle a sararin subhana,nan ne dai wajen zaman,masu sana’a nayi,masu gulma da sa’ido ma duka suna yi,masu ayyukan gida ma duk sukan jibge a nan,wasu bisa shimfidar tabarmar kaba,wasu kan kujera ‘yar tsuguno,yayin da wasu ke a tsaye suna surfe ko wani aikin ma daban,bishiya ce da Allah ya mata yalwar inuwa da kuma iska,har wani bai takurawa wani,wajen zaman ya ishesu a wadace.

Tunda aka shigo da jakarta yanayin hayaniyar dake wajen ta ragu,kowa ya maida hankalinsa kan ganin shigowarta,mata ne a qalla sun kusa su goma kowacce idanunta a kanta tana qare mata kallo,ta saba da wannan kallon tun a sanda yake muguwar guba ce a rayuwarta,balle yanzu da kaifin wannan gubar ya ragu saidai abinda ba’a rasa ba,fuskarta a washe ta zauna gefan tabarmar da tatuwa take kai ita da faccalarta karime ke kai suna irga soyayyar tunkuza wadda da alama basu jima da kammala aikinta ba,saboda yanayin maiqon dake jikin zannuwansu da rigunansu,kowacce da yanayin data amsa mata,zuciyar kowannensu da abinda take saqawa.

Tsahon mintuna tayi a cikinsu tana tattambayar ‘yan uwanta dake gidajen aure da iyayenta maza wasanda dama ta tabbatar suna goba suda yaransu maza wadanda suka tasa sai qananu da aka bari a gida,matan kuwa matasan da basuyi aure ba na wajen talla,kana daga bisani ta tambayi kakarta wadda take mahaifiya ce ga mahaifinta hafsatu wadda suke kira da inna yelwa
“Tana rumfarta tana hutawa” cewar lami wadda ta maida tabaryarta cikin turmi bayan ta watsa dawar da zata surfa,tasan dama a rina,kasancewarta mace mai shegen mulki ga duk wanda ke qasanta da nuna isa,bata cas bata as cikin gidan,yawanci irin wannan lokutan tana rumfarta zaune saidai ta wurgo umarni kuma dole abi,walau ‘ya’yan nata ko matansu ko su kansu jikoki.

Ilai kuwa a sanda ta daga labulen dake rumfartata sai ta sameta zaune saman tabarmar karauninta,falon nata a share qal wanda tasan aikin daya daga cikin surukan nata ne,wanda duty duty suke,qafafunta miqe abinda,haule daya daga cikin surukanta tana murza mata goro a magogin qarfe tana watsawa bakinta,bawai don bata da haqora ba a’ah da saura,tsabar mulki ne da ganin dama.

Fuskarta a sake tayi sallama yayin da inna kululu ta dago kai tana dubanta
“Hala kinji zuwan waccar uwar taki shine kika kwaso qafa kika taho,bayan kin san babu abinda zai sauya,zuwanki banza zamanki banza” sosai kalaman suka soki zuciyarta,duk da cewa ta jima tana jin ire iren wadan nan kalaman daga bakin inna kululun,saidai har yau ta kasa sabawa,ta rasa sai yaushe wannan DAURIN BOYEN zai warware?,sai yaushe komai zai gyaru?yaushe zatayi dariyar farinciki da zata ratsa har qasan zuciyarta kamar kowacce ‘ya?.

Bata amsa mata ba har ta zauna gefan tabarmar da take kai tana gaida haule,ta amsa tana miqewa tare da gyara daurin zaninta da alama ta gama murza goron,kallonta inna kulu tayi
“Ki kiramin karime”
“Toh” ta amsa tana ficewa,sai data fitan sanann innar ta maida kallonta kan aysha
“Uwarki kika biyo ko?” Ta sake maimaitawa bayan ta amsa gaisuwar da ayshan ta mata,kai ta kada ranta na tabuwa
“Kibar wannan maganar inna yelwa,ni baffa nazo dubawa ance min baida lafiya”
“K’nnnnn,lallai Allah yasa da gaske kike,ya kika baro su sa’adatun,ince dai bakya musu wani mugun halin naki ko?” Ta fada tana tsareta da ido,ya ilahil Aalamina,daga durowarta?,ba’a tambayeta komai daya shafeta sai zancan su mommy?,koda yake hakan ba komai bane,abinda yafi hakan ma zata iya gani
“Suna lafiya lau,tana gaisheki”
“To madalla”.

Shiru ne ya biyo baya kaman wadansu baqin juna,ita innar bata ga damar sake magana ba har karime ta shigo ta fita,yayin da ayshan ta rasa abun cewa saboda ba wani sabo bane tun fil’azal tsakaninsu,bugu da qari tunanin daya rinjayi zuciyarta ta gefe guda najin mahaifiyara dake aure a lagos wai tazo,ba zata iya tuna yaushe rabon data sanyata a idanunta ba,idan zata tuna tun sanda zata bar qauyen zuwa gidan daddy rabonta da ita,shekara aqalla kusan takwas kenan,rabuwar da har yau tana tuna yadda suka yita,a duk sanda ta tunada lokacin sai qwalla ta cika mata idanu

Ta tafi tana roqon ta kalleta sau daya,ta tafi tana kukan ta kira koda sunanta sau daya taji da kunnenta,ta tafi tana kwadayin taji tayi mata addu’a ko sau daya ne tak a rayuwarta,saidai dukka wannan burin nata bai cika ba.

Sai qarfe biyu saura ta miqe daga zaman kuramen ta rataye mayafinta ta dauki butar inna kulun ta zagaya don kama ruwa da daura alwalar sallar azahar

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: ???? *DAURIN BOYE*????

*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(Home of expert and perfect writers)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button