Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 3

Sponsored Links

0?3?

Tsaye yake cikin tafkekan dakin taron a gaban wani hamshaqin teburi wanda yake dauke da aqalla ma’aikata kimanin mutuk arba’in,hannunsa guda dafe yake da gaban teburin yayin da daya hannun yaketa wulwulgashi cike da gwanancewa duk da baisan yana yi ba,da alama bayanin da yakewa ma’aikatan da suka bashi dukkan nutsuwarsu ya dauki zafi,lokaci lokaci yana daga daya hannun nasa dake dafe da teburin yana duba agogon hannunsa,wannan kadai ya isa ya nuna maka mutum ne mai kiyaye lokaci da kuma alfanunsa.

“Is there any problem?….” Ya qarashe jimlar tasa ta qarshe yana duban fuskokin ma’aikatan,saidai kowanne ya gamsu girgiza kai suka dinga yi daya bayan daya,ganin haka ya sanya shi ya soma tattare kayanshi dake saman teburin tare da bada umarnin a rufe taron da addu’a kaman yadda yake a qa’idarsa.

Related Articles

Shine mutum na farko da ya soma fita,shahid ya rufa masa baya suna magana qasa qasa,a bakin hall din daya daga cikin mutanen dake tsaye a wajen ya karbi kayan hannunsa sannan yabi bayansa har cikin elevetor wadda bata saukesu ko ina ba sai hawan qarshe na kamfanin inda office dinsa yake.

Mahmoud ne kawai zaune cikin office din ya tasa computer a gaba da alamu wani aiki yake ragewa mai muhimmanci Hannu mahmoud ya baiwa shahid suka gaisa cike da alamun cikakkiyar sanayya a tsakaninsu bayan security din dake riqe da kayan khaliphan ya aje ya fice,yayin da khalipha ya wuce kai tsaye bakin freezer ya dauki ruwa ya sha bayan ya rage suit din jikinsa kana ya shige toilet,alwala ya daura sannan ya dawo cikin office din ya tadda shahid da mahmoud suna hira,wadda fiye da rabinta abinda ya shafi kasuwancinsu ne,daya daga cikin wayayoyinshi wadda ke dauke da lambobin dukkan mutanen daya baiwa muhimmanci a rayuwarsa lambarsu ke ciki,kai tsaye ya nufi bakin daya daga cikin windows din dake cikin dakin office din wanda kai tsaye zaka iya kiransu da qofa saboda kadan ne ya rage basu kai girman qofar ba,saidai glass ne zalla a jiki wanda hakan zai baka damar gano ainihin farfajiyar companyn daga sama har qasa.

Bugu biyu aka daga wayar,ya sauke ajiyar zuciya sallamar matar na ratsa kunnensa,cikin sanyin murya kaman yadda halittar muryarshi take ya amsa sallamar sannan yace”Anni…barka da warhaka”
“Barka kadai khalipha,kun fito daga taron ne?”
“Mun fito ammi,saidai aci gaba da yi mana addu’a Allah yasa mu dace”
“Ubangiji ya dafa,ya shiga lamarinku,ya zama jagora a gareku,ya albarkaci rayuwarku”. Cike da jin dadi yaketa amsawa da ameen,idanunsa lumshe yana shafa qirjinsa yana jin zuciyaraa wasai
“Ya jikin anni?,kinsha maganinki na rana,naga lokaci yayi”murmushi ta saki cike da qaunar yaron nata
“Khalipha kenan baka gajiya?,kaman ba awannin da suka shude muka gama waya da kai ba,jiki alhamdulillah,magani kuma ina gama sha kiranka ya shigo”cikin murmushi ya amsa
“Ya za’ayi na gaji da jinki anni….Allah ya qara miki lafiya mai dorewa”
“Allahumma amin khalipha,Allah yayi albarka”
“Ameen anni…sai na dawo”
“Allah ya tsare” ta sake ambata cikin nuna kulawa da qauna,ya amsa sannan ya kashe wayar yana murmushi,abubuwa da yawa na dawowa cikin kwanyarsa game da annin tasa,zai iya cewa baiga uwa irin tashi ba,kuma baya zaton za’a samu,anninsa da taban ce ko cikin halittun ubangiji,da wannan zancan zucin ya qaraso inda su mahmoud suke.

??????

Zaune yake gaban annin tashi cikin shigar qananun kaya na t shirt da trouser,qafafunshi tanqwashe gabanshi kuma plate ne wanda ke dauke da tuwon shinkafa miyar water leaf da ogu wadda ta wadata da ganda busashshen kifi da kuma tsokar nama,a nutse yake cin abinci gefe guda suna hira da anni,hirar dake nuna tsantsar shaquwa dake tsakaninsu,kallo daya zaka yi musu ka tabbatarwa kanka lallai akwai saboda da shaquwa mai qafi tsakaninsu
“Khalipha…” Ta ambata a hankali wanda hakan yasa ya dago kanshi yana dubanta sannan ya amsa
“Wai sau yaushe zan daina jiran ganin zuwam surukata?” Murmushi ne ya subuce masa,sai ya aje cokalin hannunsa ya fasa kai lomar da yayi niya,cikin kulawa da qauna yake dubanta sannan yace
“Kwanan nan anni,karki damu….addu’arki nake buqata kawai…ina son na kawo miki surukar da zata kulamin dake,surukar da zata daukeki a matsayin uwa….surukar da zakiji dadin zama da ita fiye dani yadda zanji” murmushi ya subuce mata,sai ta kada kai tana dubanshi
“Allah ya baka mace ya gari wadda zata zame maka majingina…..amma banda abin khalipha kana tunanin akwai irin wannan surukan yanzu?” Ta qarashe managanar tana dariya qasa qasa,don har ga Allah bata dauki burinta ta cillashi har haka ba,kullum dai addu’arta Allah ya bashi wadda zata soshi tsakani da Allah,nagartacciyar matar aure,dan marairaicewa yayi kadan sannan yace
“Anni,kin sha gayamin ba’a fidda rai da rahamar Allah”
Kai ta jinjina cike da gamsuwa tace”wannan haka yake,ubangiji ya maka zabi ja gari”
“Ameen” ya amsa yana daukar cokalinsa dinci gaba da cin abincinsa sannan yace
“Cikin sati na gaba haidar zai dawo gida hutu” murmushi tayi kaman ko yaushe
“Sun kammala jarabawar kenan”
“Eh sun samu hutu na wata biyu”
“Allah ya kai mana rai”
“Ameen” ya amsa yana daukar cup din daya cika da ruwa ya soma sha.

??????

Da sauri sauri take tafiya hadi da duba agogon hannunta,qarfe tara da rabi na safe dai dai,mintuna talatin zata qara ta makara wanda hakan dai dai yake da rasa lacture dinta har na tsahon awa biyu.

Turus tayi gabanta na dan dokawa ganin asma’u zaune dafa’an cikin falon sanye da kayan barci wanda hakan ke nuna ko wanka bata yi ba bare a kai ga shirin fita,hannunta daya riqe da cup na tea tana kurba a hankali,daya hannun kuma wayarta ce samfurin iphone 8 take latsawa,jikinta sanyaye ta qaraso gefanta ta tsaya
“Ashe baki shirya ba anty asma’u?” Sai data shaqi iska kafin ta amsa
“Eh….sai eleven”
“Gashi goma lacturer din yake shiga…” Ta fada adamuwance,saboda daddy yana gidan,kusan yasan lokutan fita lactures dinsu daya ne,tare suke fita su kuma dawo tare a iya saninsa kenan,idanu ta daga ta kalleta ta watsa mata wani kallo
“Naga alamun raini na son soma shiga tsakaninmu aysha duk don saboda sharing abun hawa da muke ko…to ki shiga taitayinki,ke kanki kinsan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,banda game game irin ja daddy da sunan zumunci saidai ki dinga hangoni ta cikin glass,to banson zura kai in zaki wuce kije ki hau abun hawa na haya ki wuce,dama dashi kika fi dacewa kuma dashi kika saba” tana kaiwa nan ta maqala earpiece a kunnenta da alama kira ne ya shigo mata zata amsa.

A kasalance take takawa a harabar gidan,zuciyarta cike fal da tunani,tana tsammanin kyautatawa na sanyawa kaso mutum koda baka sonshi,saidai ta gefan asma’u sam ba haka bane,mommy kuwa har yau ta kasa fahimtar a wanne aji take?,banbancin rayuwar data baro da wannan baya wuce sauyin muhalli,sutura da ilimi data samu ba,amma baya ga haka zata iya kiran yanayin da SAMMAKAL a wajenta
“A’ah,ina zaki a qafa aishatu?” Ta tsinkayi muryar daddy dake fitowa daga babban falonshi da yake ganawa da baqinsa,wanda sam bata lura da shi ba saboda zurfin tunanin da tayi,cikin hikima tayi qoqarin saisaita yanayinta,ta qaraso cike da girmamawa
“Ina kwana daddy…” Ta soma da gaisheshi,don yau duka basu samu damar haduwa ba,kasancewar jiya wajen goma na dare ya dawo qasar,ya kuma buqaci mommy ta tasota saidai tanajin sa’adda da tace masa ai ayshan tayi bacci,bayan idanunta biyu a sannan litattafanta ne a gabanta take dubawa,har lokacin data shiga dakin asma’u ta tadata kan ta fito daddynsu ya dawo amma asma’un tayi qememe tace ta gaji sa gaisa gobe,haka mommyn ta fito tace masa itama din tayi bacci
“Ina zaki aysha?” Ya sake jeho mata tambayar bayan sun gama gaisawa,bata da wata qarya da zata masa don kare asma’un wannan karon,saboda haka kai tsaye tace
“Makaranta” agogon wayarsa ya duba sannan yace
“Ina asma’un…..ina kuma drivern naku?”kanta ta duqar qasa sannan tace
” yau akwai banbancin lokacin fitar namu ne”
Kai ya jinjina,tun da can shi ba mutum bane mai yawan sanya ido da takura ba,hakan ya sanya abubuwa da dama kan gudana cikin gidan ayi musu kwaskwarima a sauya musu salo a bashi a haka ya karba ba tare da ya sani ba.

Dai dai sannan usama drivansa ya turo get din gidan ya shigo,saboda ga tsammaninsa a sannan zasu tafin,hakan ya sanya daddyn ya sallameta bayan ya miqa mata sabbin ‘yan dubu dubu guda biyar da sukayi saura a hannunsa wanda da alama ya gama sallamar masu neman taimako ne wadan nan suka rage,tasan baya kyauta a dawo masa da ita hakan ya sanya tasa hannu biyu ta amsa tana jero masa godiya.

Ko cikin motar tunanin karamci irin na daddyn take,har abada kuma har ta mutu ba zata taba manta alkhairinsa da karamcinsa gareta ba,qarar wayar usama ta dawo da ita hayyacinta,daga jin yadda yake amsa wayar cikin daburcewa tasan akwai magana
“Kiyi haquri ranki ya dade,yanzu zan ajeta na dawo,na dauka yau bazaki fita bane…kiyi haquri” kalmar yayita maimaitawa,saidai hakan bai hana asma’u yi masa tas ba harda alakoron zagi ta kuma katse wayar
“Kaga….ajjiyeni usama kaje ka daukota saina qarasa wani abun hawan” yana bala’in ganin qimar ayshan saboda yadda take girmamashi tamkar yayanta,hakan ya sanya yace
“Barshi kawai na qarasa dake aishatu,koda na ajekin ma na koma daukota ba tsira zanyi ba” kai ta kada
“Ka ajenin babu komai…laifin ai zai ragu idan kace mata ajjiyeni kayi ba kamar ka kaini ka dawo ba” haka ya gangara gefan titi bada son ransa ba ya ajeta ya juya ya koma,ta tsaida adaidaita sahu ya qarasa da ita,idan da sabo ta jima da sabawa da halayen asma’u,ta haddacesu tsaf,shi yasa ba komai ke bata ranta ba.

*mrs muhammad ce*??
???? *DAURIN BOYE* ????

*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(home of expert and perfect writers)?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button