Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 15

Sponsored Links

🍇MunayaMaleek🍓

 

_By NoorEemaan_📚✍️

Related Articles

Xv….

(15)

Duk wanda ya ga Munaya a Yanzu a kallo daya zai fahimci Akwai juna biyu a tare da ita,
gaba-daya ta kara lalacewa saboda cikin mai laulayi ne, ga karancin shekaru uwa uba babu mai zama ya kula da ita, baka hango komai sai cikin, Bawai saboda girman ba, sai dan mugun ramar data yi yasa cikin nuna kansa, a kullum idan ta kalli yanda cikin ke girma sai ta fashe da kuka, gaba-daya ta dawo wata kala babu kyawun gani.

Kamar yanzu zaune take ƙishirwa take ji sosae, makogwaron ta a bushe take jin sa, domin har wani kaikayi yake mata, gashi babu ruwa a gidan, domin na rijiyar ma ya kafe, ta tuna doctor ya bata kuɗi zuwan sa na ƙarshe, ta zari hijab ta saka, ta ɗauki dari biyu Cikin kudin ta fita zuwa kantin, hannun ta boye cikin hijabi saboda mutanen unguwa, da son samu ne da babu inda zata fita domin fitan ta babu abinda zai ƙara mata sai damuwa, musamman yanxu daya kasance rana ne. mintuna shida ya Kaita katin ta siyo pure water hadi da dawowa, har ta sha leda daya a wajen mai kantin domin ta kasa hakurin zuwa gida, ji take Kamar zata mutu, sai dai tana daf da zuwa kofar gida ta ga wasu yara ƙanana na wasa suna kallon ta, suna dariya, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya. Ta tsaya cak dalilin jin abinda yaran suke cewa, bugun zuciyar ta ya karu, tamkar zata faso kirjin ta ta fito “Munaya! Tayi cikin shege, Munaya! Tayi cikin shege” abinda suke maimaitawa kenan suna tafa hannu cikin sigar waka, har mutane sun dan fara taruwa, hawaye masu zafi suka zubo mata, bata juyo ba ta ruga cikin gidan da gudu tana kuka, yaran suka biyo ta har soro suna cigaba da fadin “Munaya! Tayi cikin shege” abin mamaki yara ƙanana sun san mace mai ciki, babu haufi iyayen su ke gulmar suka ji, sun jima suna yi, kana Muryar wani babban mutum ya daka musu tsawa hadi da kore su, ya kuma jawa kofar langa_langan su, hakan ya saka ta huta da jin abinda yaran ke faɗa, sai dai babban fami maganar su ta yi mata a ciwon dake zuciyar ta, ta cigaba kuka Kamar ranta zai fita, tsanar cikin da shi kan shi Maleek da a kullum yake daduwa a ranta, amma tafi jin tsanar su a yanzu fiye da ko koyaushe, ta shiga buga cikin da motsin sa ya yawaita tun data shiga 15weeks, take kanta ya fara ciwo tamkar zai rabe, kuzarin kukan ma ba da ta shi, hakan yasa ta yi shiru ba dan kukan ya daina zuwa bane, ta shiga sauke ajiyar zuciya, har bacci ya dauke ta a zaune tana sakin shesheka a cikin baccin.

***
Mita yake cikin zuciyar sa domin tun dazu masu bada hannu a titi suka tsayar dasu, gaba-daya a gajiye yake, yayinda a gefe daya na zuciyar sa tunanin yanda zai lallaba Munaya ta amince ta fada masa in da wanda ya Mata lalata mata rayuwa yake, domin ya kamata ya sani, ko dan jaririn ko jaririyar da za a haifa ya san da baban sa, amma ya ga kwata kwata bata son ayi maganar sa, ba kuma ya son hankalin ta ya dinga tashi, ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mafita, kamar ance ya kalli sama ta gefen hagun su ya hango wani katon gini mai kyau da tsari, a saman an rubuta *A.A DAWOOD MOTORS* ya ɗan kankance ido yana son tuna a ina ya taba ganin irin wanna sunan amma ya kasa tunowa har aka bada hannu, ya daga kafadu yana tabe baki, sai dai sunan dake saman building ɗin ya ki bacewa a zuciyar sa, ya shiga tuki a hankali, har yayi nisa, can yace “yes Munaya!” Tabbas a jikin ledan da Munaya ta saka kudin asibitin Amnah ya gani, tabbas hakan ya gan wanna sunan, ya juya yana son sake kallon rubutun amma ya ƙasa saboda nesan, yayi gaba kadan ya ga wani U. Turn hakan ya saka ya juyo da saurin sa.
Bayan ya iso kofar gate din ya danna horn, Nura mai gadi ya fito zuwa wajen doctor Abbas ya gaida shi, Ya amsa cikin sauri, wata zuciyar na tunasar masa da cewa ya aka yi ka tabbatar da cewa shine, what if ba shi bane, amma zan tabbatar yanzu domin Munaya na yawan faɗin na tsani Maleek, bana kaunar ganin sa. Ya saki. numfashi kana ya leko da kansa ya kalli Nura yace “Maleek na nan kuwa?” Ya faɗa freely tamkar dama ya san shi.

“Eh boss na nan” Nura ya karasa fada hadi da nufar wajen gate domin buɗe masa, ajiyar zuciya Abbas ya saki, yana hamdala da Allah ya kawo masa komai cikin sauki, duk da ba zai so wata alaƙa ta haɗa MunayaMaleek ba, amma zai so ya san cewa Munaya na dauke da cikin sa, yana hakan ne saboda yaron ya samu gatan da duk wani da yake samu, duk da yaron bai zo ta hanyar da ake so ba, amma pure soul ne, bai ma zo duniyar ba ɓalle ya girma ya aikata zunubi, dan me za’a hukunta shi da laifin uban sa? da wanna tunanin ya hau benen kamar yadda aka kwantata masa, kwatancen ne ya kai shi floor din da office din Maleek yake ya ga an rubuta *CEO OFFICE* da kyakkyawan rubutu, kansa tsaye ya tsaya a kofar glass din har ya buɗe kansa sannan ya shiga, ya hango zaratan samari biyu masu kyau, aji da haiba a zaune, aka shiga kallon kallo a tsakanin su, shi doctor yana tunanin waye Maleek a cikin su, su kuma na tunanin waye wanna da zai shigo kan sa tsaye???…

*Mummy*
Tsaye take a kitchen, tana girkawa Maleek one of his favorite food Bolognese spaghetti jollof daya ji minced meat, farinciki bayyane a fuskar ta domin sabon malamin tsubbun ta ya tabbatar mata wannan karon matuƙar Maleek ya ci girkin nan babu abinda zai hana bai nime ta da kansa ba,
Hakan yasa jiki na rawa ta shiga tsara girkin na sa, domin already ta saka masu aiki yin girkin da sauran mutanen gidan zasu ci, saboda yanda ta kagu ya dawo a yi komai a gama, sai da girkin ya rage kadan ya yi ta fito da wani ƙaramin kwalba daga cikin bra din ta, wani abu ne cikin kwalbar wani abu mai dan kauri da maiko kalar maroon mai turuwa, ta saki murmushi tana tuno yanda aka ce maganin zai yi aiki, lallai ta yarda ta kuma tabbatar domin tana wajen karbar maganin wasu mata na zuwa suna fada masa yanda aikin da yayi musu ya ci kamar yankan wuka, hakan ya saka mummy kara yarda da aikin sa, ta buɗe kwalbar ta juye cikin spaghetti Bolognese din ta saka spatula ta jujjuya da kyau, seconds goma kacal ya kara ta sauke abincin hadi da juyawa cikin warmer mai daukar ido, ta kai dakin ta, domin so take ya zamana itace zata bashi da kanta yaci, domin bata yarda ta bar abincin a dinning ba, tafi son ya zama ita ce zata gabatar masa da shi da kanta domin aikin yafi ci tamkar yanda mutumin daya bata maganin ya fada, domin bayan wahalar zuwa wajen da ta yi domin a wajen gari yake, ga makudan kudaden data kashe kafin ta mallaki karamin kwalbar nan, amma bata damu da kuɗin ba, domin cikar burin ranta Worth kuɗin da ta kashe…

****
A nutse shakur ya ce “lafiya gentleman, who are you please, wa ka ke nema?”

“Maleek! waye Maleek among you two?” Doctor Abbas ya fada fuska a turbune.

“You didn’t answer me, i said waye kai?” Shakur ya fada yana kallon sa.

Cikin dan fada-fada doctor Abbas yace “ban zo nan dan in gabatar maka da kaina ba, important issue ne ya kawo ni nan, who’s Maleek here” ya faɗa yana rarraba idanun sa kan su.

Maleek dake cike da jin haushin Abbas musamman irin amsar da ya ji yana bawa kanin sa ya kara haɗe girar sama da ta kasa, har tsakiyar girar ta tattare yace “ba za a gaya maka waye Maleek ba, har sai ka fadi waye kai, You even have the guts ka shigo min office kan ka tsaye babu neman izini? now live my office” ya fada hankali kwance, irin na cikakken namiji daya iya boye bacin ran sa, sai dai fuskar sa kadai zaka kalla ka tsorata.

Doctor Abbas ya tako zuwa dab da Maleek yace “oh i see….you most be Maleek, because you are so arrogant and proud” shima doctor Abbas ya mayar masa cikin jin ciwon halin da ya jefa Munaya a ciki.

Maleek ya mike a zafafe zai isa gareshi, sai dai jin abin da doctor Abbas ɗin ya fara faɗa ne ya saka shi tsayawa cak.

“barin fito maka a mutum, domin kimar ka bata kai ayi magana ta fahimta da kai ba, Innocent girl da ta sanadiyyar ka take cikin kuncin rayuwa ne dalilin zuwa nan wajen nan da kake ikirarin office ne, i swear ko ta wacce hanya sai na bi wa Munaya hakkin ta, wadannan sune takardun asibitin ta, she’s carrying your baby, tana dauke da cikin ka dan wata hudu” Dum! Dum!! Daram!!! Kirjin Maleek, Shakur da shi kan shi doctor Abbas din dake maganar ya yi lugudan bugu, sai dai shi nashi na ɓacin rai ne, shiru ya ratsa office din, tashin hankalin Shakur kuwa bazai misaltu ba, domin muraran ya nuna a fuskar sa kasancewar bai iya boye abu ba, ya mike cikin sauri ya kamo hannun Abbas ya zaunar da shi, domin ya dauka y’a’yan ta ne, cikin rawar Murya da damuwa yace “kayi hakuri, na san kana cikin ɓacin rai, ka kwantar da hankali ka, ka cire ɓacin rai a Muryar ka ka mana bayanin da zamu gane”

“Shi wanda yayi aika aikar ya san komai ai”

Shakur ya yi imanin Maleek bai san da zancen cikin nan ba, Toh ina ma ya ga Munayan balle ya sani?”

Kamar doctor ya san tunanin da Shakur yake yace “ya san ciki na shiga ai, kafin ya aikata son zuciyar sa” ya faɗa yana wurgawa Maleek wani mugun kallo.

Shakur ya dafa kansa kana yace “kayi hakuri dan Allah, ka sanar da Ni, You have no idea of yanda nake neman ta kullum tunda d abin nan ya faru”

Doctor Abbas ya kasa musawa Shakur domin yafi Maleek saukin kai nesa ba kusa ba, ya kuma lura kamar Maleek din bai gaya masa komai a yanda ya faru ba, sai daya kara watsa wa Maleek wani kallo mai kama da kishi kana ya kalli Shakur ya fara cewa “a watan march ranar 25 ga wata ita ce ranar da Munaya ta kawo kanwar ta Amnah asibitin da nake aiki….”

Maleek ya runtse idanun sa, har abada bazai taba manta wanna date din ba.

Doctor Abbas ya ɗora da cewa “ban taba ganin yarinya karama cikin rayuwa irin ta Munaya ba, so a ranar i was wondering Ina iyayen ta da zasu bar karamar yarinya da wahalar zuwa asibiti, so ganin halin da yarinyar da take ciki yasa na karbe ta na bata gado hadi da yin duk wani taimako dana san zai taimaka wa Amnah, bayan na saka mata drip, aka kawo min tests Dana sa aka yi running mata na gane cewa yarinyar na dauke da cutar daji ta ƙwaƙwalwa wanda har ya kai stage wanda bazai ji magani ba fa ce surgery, Munaya cried to my office, na mata bayanin cewa ga halin da kanwar ta ke ciki, ta durkusa gabana tace dan Allah na taimaka na yi wa Amnah aikin zata nemo kudin a duk inda yake, she even told me that a fara yi wa kanwar ta aikin ko da bazamu sallame su ba, ta yarda mu cigaba da rike Amnah har sai da biya kuɗin ita dai burin ta kanwar ta ta warke, na Girgiza kaina nace Mata hakan bazai yu ba saboda dokar asibitin ce haka ba a fara aiki sai an ajiye kudi kuma kudaden kimanin miliyan uku da dubu dari tara ne, so nace mata ayi gaggawar samun kudin asibitin domin yarinyar na cikin ciwo sosai, nace mata taje ta sanar da dangin su domin a samu mafita, dana sani ban bari ta fita ba, saboda dalilin fitar ta yayi sanadiyar halin da take ciki yanzu”

Doctor Abbas ya kara shiru, na wasu seconds yana jin dama hannun agogo ya dawo baya da tabbas bazai bari Munaya ta rasa budurcin ta ba.

“Fitar Munaya daga asibitin da mintuna talatin kanwar ta ta rasu bakin ta na kiran sunan yayar ta Munaya, hakika a ranar na ji mutuwar yarinyar duk da ban san su ba, amma nayi matukar tausaya musu, after some hours like two Munaya ta dawo asibitin da leda mai dauke da kudaden nan kimanin miliyan uku da dubu dari tara, i was so shock ta Ina ta samu kudi cikin ƙalilan din lokaci haka? Amma ban tambaye ta ba, duk da tarin damuwa dake kwance a fuskar ta amma kanwar ta ce first on her mind, tace min likita ɗan Allah ka tashi ka yiwa Amnah aikin ta warke, ga kudin nan, jikina yayi sanyi sosai na shiga tunanin ta yanda zai sanar mata, daya baya sanar mata cewa kanwar ta ta rasu, fadin tashin hankali da damuwar data shiga bata lokaci, domin a lokacin data yi tozali da gawar Amnah din suma tayi, hakika ranar har kwalla na zubar saboda tsananin tausayin Munaya, saboda tayi kankanta sosai da fuskantar kalubalen rayuwa iri wanna, a takaice bayan an binne yarinyar, da kwana biyu, na je mata ta’aziyya, na ga ta fara fita a hayyacin ta, na mata nasiha kan ta kwantar da hankalin ta, sai da zan tafi nace mata ga kudin ki nan, kasancewar i office dina ta barshi ranar rasuwa, hawaye ya zubo Mata ta karɓe ledar mai dauke da tambarin wannan Company din, wanda shi ya taimaka zuwa wajen nan, har ta juya zata tafi nace Munaya a ina kika samu kudade masu yawa irin wanna, her answer melt my heart, tace i sold My virginity doctor, na siyar da budurcina domin samawa Amnah lafiya, alhalin na manta cewa babu wanda ya Isa ya bawa wani Lafiya ko kara masa tsawon rai face Allah daya hallaci wanna bawan, a ranar na kasa bacci domin ban taba jin mutum dake shan gwagwarmayar rayuwa haka kamar ta ba, na ji haushin ta data amince ta bayar da budurcin ta, sai daga baya na mata uzuri, domin akwai karancin shekaru a tare da ita, bayan kwana biyu nace gidan su na sanar mata cewa ya kamata ta fada min ina ne address din inda Maleek din yake, na ga ta shiga sabon tashin hankali tana kuka tace ita bata son haduwa da Maleek har abada bata son ganin sa, ta tsani Maleek ta cigaba da cewa ranar da abin nan ya faru wajen Shakur ta taho da niyyar ta roke shi ana cirewa cikin albashin ta, sai dai bata samu Shakur din ba, Wanda from all indication na tabbatar kai ne, Maleek ta samu yace mata yana da kudade masu yawa ga su nan ta dauka amma ita ma sai ta bashi jikin ta in return, tace ta roke shi ya yi hakuri ya dinga cirewa a kudin aikin ta ita bata taɓa yin komai ba, bata san komai ba, yace karya take babu Mace virgin a yanzu” idanun doctor Abbas ya kada, ya kalli Maleek yace “i hope yanzu ka tantance cewa ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, duk lalacewar Duniya ba’a rasa na gari ɓalle ita ƙaramar yarinya” ya karasa maganar yana jefan Maleek da harara wanda ke tsaye kekam har yanzu cikin yanayi mai wuyar fassaruwa…

“Tun daga wanna lokacin na yi alkawarin kula da Munaya, musamman dana ji labarin ta rasa iyayen ta duka, gashi su ba yan kasar nan bane ya Chadi ne, har raina ina jin ta kamar kanwata ta jini, na kuma yi alkawarin shigar Mata kan abinda danuwan ka ya mata, sai dai duk lokacin dana mata maganar Maleek din kan ta bani address din sai ta fara kuka, akwai lokacin dana je wajen ta ta shiga amai, na Kaita asibiti Mafi kusa domin na ga ta galabaita aka tabbatar min da cewa tana dauke da ciki ga hawan jini, abin ya daga min hankali sosai Domin karamar yarinyar da ciki ga kuma hawan jini, lokacin data san tana dauke da ciki hankalin ta yayi matukar tashi tace dan Allah na taimaka na zubar mata dashi, Ni kaina nayi takaicin samun cikin nan na ta, sai dai zubar da shi din wani karin zunubi ne domin kashe rai ne, na fahimtar da ita cewa kar ta zubar da cikin domin Allah zai yi fushi da ita, lokacin zuwa lokaci ina so ta sanar dani address din Maleek din, amma taki, abinda bata gane ba Ni kaina bana son ta da Maleek din, amma ina so ya sani cewa akwai cikin sa tare da Munaya ina yin haka ne saboda darajar babyn da bai san komai ba, amma ban samu hadin kai ta faɗa min ba, ganin kuma duk lokacin dana fadi sunan Maleek din hankalin ta na tashi ya saka na bar yi mata maganar, amma a raina ina neman mafita. dazu bayan naje duba wani mutum wanda nine family doctor din su danger ta tsayar dani a tsallaken nan, a nan naga sunan company *A.A Dawood MOTORS* sai na shiga tunanin ina na san wanna sunan, and then I remember cewa cikin ledar da Munaya ta kawo kudin asibitin Amnah na gani, jikina ya bani cewa nan ne wajen, hakan yasa na juyo, da haka na gano nan wajen, saboda haka Maleek wait for it, ni zan samawa Munaya Justice, i don’t care da tarin dukiyar ka Allah yana tare da mai gaskiya, domin idan Munaya yarinya ce bata da wayo kai fa? meyasa zaka yaudare ta da kudi ka keta mata haddi, idan bazaka iya taimakawa mata fisabilillahi ba meyasa baka bar ta ta tafi ba, You could have allow her go, Amma saboda son zuciya ka garara yin Hakan, saboda takamar ka kudi? Toh ka saurari tsammaci daga kotu “…. doctor Abbas ya karasa maganar da mikewa domin tafiya, Shakur yayi saurin goge kwallan tausayin Munaya domin Baya son a gani, Sai dai fuskar sa ta nuna yayi kuka domin ja da dan kumburi da suka yi, ganin da gaske doctor zai bar office din yayi saurin rike hannun sa yace.

 

 

_wandan da suka yi payment duk ina sane da ku, nayi saving number’s din ku, zan kuma yi adding din ku a grp da xaran na gama free pages in Sha Allah._
_Sannan Promo da nayi ya kare, kudin littafin ya dawo dari biyar din sa, duk wanda ya kara turo 300 TOH ya sani cewa kuɗin shan lemo ya bani a kyauta😂🙌👏_

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566
Thanks for your support, Allah ya ƙara muku budi a hanyoyin samun ku🥰

 

#MunayaMaleek
#Heartouching
#MMSquare
#disflowering
#arrogance
#selfishness
#virginity lost
#painfuldeath
#NoorEemaan
#Paid book

07082281566

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button