Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 58

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

58

 

Related Articles

Mami ta koma bangarenta da sauri ta shiga dakinta, Noor dake parlor ta bi ta da kallo ganin yanayinta ta mike ta bi bayanta zuwa dakin, zaune ta ganta gefen gado kamar warce taji wani mugun abu, she look shock, Noor ta karasa kusa da ita da sauri tace “Mami are you alright?” Mami ta kasa ce mata komai sai kallonta take, cike da damuwa Noor tace “Pls Mami ki kwantar da hankalinki kar ki fara rashin lafiya, everything will be alright in sha Allah, don Allah kar ki sa damuwa a ranki” Still dai Mami babu bakin magana, furucin khalil na karshe ne kawai ke ta yawo a kanta, she is trying all possible best tayi apprehending din furucin nasa, Noor ta zauna gefenta ganin kamar ma bata san abinda take cewa ba, ko kadan bata son ganin Maminsu cikin tashin hankali, Noor ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace “Plss Mami calm down, everything will be okay in sha Allah….” Sai a sannan Mami ta kalleta cike da karfin hali tace “Dauki wayata ki kira min Maryam….” Noor ta tashi ta dau wayar Mami dake gaban mirror tayi dialing number Aunty Maryam ta kai ma Mami bayan ya fara ring, Mami ta amsa tana kallonta tace “Ki je zan yi waya Noor” Noor ta juya ta fita daga dakin, Aunty Maryam na dagawa tace “Ya ake ciki Mami? Nayi ta kira baki daga ba, Is he alright?” Mami tayi karfin halin cewa “Maryam i wish kina kusa da ni….” Aunty Maryam da taji gabanta ya fadi tace “Lafiya Yaya? Hope all is well?” Mami ta kasa ce mata komai, she is just speechless, hankali tashe Aunty Maryam tace “Hello…. talk to me, me ya faru Mami?” Mami taji kanta ya sara mata, ta dafa kan tace “Zan kira ki Maryam” Bata jira me Aunty Maryam zata ce ba ta katse wayar kawai ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta fita…. Aunty Maryam ta gaji da kiran wayar Mami, daga karshe ta kira Noor, Noor na dagawa Aunty Maryam tace “Noor me ke faruwa?? Ina Mamin?” Noor tace “Wallahi ban sani ba, kawai tace min zata je wajen yayanmu a guardroom, kuma da ta dawo naga mood dinta gaba daya sae a hankali” Aunty Maryam tace “Ta samu ganinsa kuma?” Noor tace “Toh ban dai sani ba, kawai naga ta shigo wani iri, i asked what the problem is bata ce min komai ba” Aunty Maryam tace “Abban naku na gidan ne??” Noor tace “Baya nan tun jiya” Aunty Maryam duk hankalinta ya tashi, tace “Ina Mamin yanzu take?” Noor tace “Yanzun nan ta fita” Aunty Maryam tace “Kai mata wayar da sauri don Allah” Noor ta mike ta fita da sauri, har ta iso main parlor bata ga Mami ba sai Aunty Hassana dake zaune ta cika parlon da kas kas din cingam, Noor na fitowa compound ta gan Mami cikin mota za su fita with 3 soldiers, tsaye tayi tana kallon motar har suka fita daga compound din, Noor ta koma ciki ita ma duk jikinta yayi sanyi, ta kira Aunty Maryam tace “Aunty naga ta fita a mota kuma yanzu” Aunty Maryam taji hankalinta ya kara tashi sosai, ta ji kamar tayi tsuntsu ta ganta a Nigeria, Aunty Maryam tace “Kin tabbata kuma Khalil na guardroom din?” Noor tace “Da asuba fa suka shigo gidan nan, i am sure yana ciki, kuma na tambayi wani soja dazu yace min yana ciki” Aunty Maryam ta katse wayar kawai, babban damuwarta rashin maganar da basu yi da Mami ba har ta fita gidan, to ina zata? Ko gidan Hajiya Safeenah?
Gaba daya hankalin Mami baya jikinta har suka iso gidan Khalil, ta bude motar ta sauka tana kallon gate din gidan dake a kulle, daya daga sojojin ya karasa ya bude mata gate din da makulli, har bakin kofar shiga main parlor suka rakata, cike da karfin hali tana kallonsu tace “Ku jira ni nan” Suka tsaya bakin kofar ta shiga ciki tana bin parlon da kallo, mutuwar tsaye tayi ganin takalmin mace dake kofar parlon, she became weak lokaci daya, taji kafanta sun mata nauyi, banda faduwa babu abinda gabanta yake, tana tafiya a hankali ta nufi staircase dake parlon ta haura sama kamar me counting stairs din, ta fi second ashirin tana bin kofofin dakunan dake sama da kallo, master Bedroom din Khalil ta fara shiga taga ba kowa ciki sai pajamas dinsa dake saman gado, ta fi minti daya tsaye a dakin kafin ta juyo a hankali ta fito daga dakin, ta tafi ta bude wani kofar very gently, gabanta ya yanke ya fadi, komai ya tsaya mata cak ganin mace kwance saman gado ta takure cikin duvet sae dai ba a ganin fuskarta sbda ta rufe da duvet sae gashin kanta dake baje, Mami ta ji ta kasa ci gaba da tsayuwa zuciyarta ya dinga bugawa babu kakkautawa, is this for real or she is dreaming, yanzu abunda Khalil ya fada gaskiya ne kenan, ta juya da sauri ta fita daga dakin ta koma corridor ta dafa bango, bata san sanda ta fashe da kuka sosai ba tana furta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” yanzu da gaske aure Khalil yayi duk basu sani ba? aure yayi without the knowledge of his parent? What came over him? does that mean bai daukesu a bakin komai ba kenan, duk yanda take kokarin ganin ta kyautata masa saboda abinda ubansa yayi masa ta haka zai saka mata, yanzu abinda Khalil zai mata kenan, da bata san waye ɗan nata ba da sai tace karya yake kawai macen banza ya kawo gidan nasa ya ajiye, amma tasan halinsa tasan abinda zai aikata da wanda baxai aikata ba, tunda yace matarsa ce definitely matar tasa ce, amma a ina yaje yayi auren nan? Lokaci daya tunaninta ya tafi kan Hajiya Safeenah, da wani idon zata kallesu ma dai tukun? Kuka kawai Mami take ta rasa wani tunanin zata yi, wannan wani irin jarabawa ne astagfirullah, me ya samu khalil haka? how is everybody going to take this barin ma Abbansa, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ita kanta bata lamunta da auren nan ba kuma baxata taɓa lamunta da shi ba, bata taɓa jin takaicin ɗan nata ba sai yau, yau taji haushinsa da bata taɓa ji ba, yayi disappointing dinta ta yanda bata yi tunani ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, za kuma ta nuna masa yanda bai yi shawara da su wajen zuwa yayi aurensa ba haka babu shawaransu zai rabu da yarinyar cikin gaggawa ko ya ki ko ya so, idan ko ba haka ba sae dai ya nemi wata uwar ba ita ba, this time around she is going to show him bai isa yayi controlling dinta ba, she isn’t going to take it likely with him, ba don tasan babu ta inda yarinyar zata fita ba da kawai juyawa zata yi tace ma sojojin su mayar da ita gida yarinyar tayi ta dauwama a gidan, kuma bata ga dacewar fita tace ma sojojin su shigo su tasheta ba, da abinda xata yi kenan da dai ita ta shiga ta taso ta, ta share hawayenta zuciyarta na ƙuna ta koma cikin dakin tana kallon Nihad, ko motsawa Nihad bata yi ba a yanda take kwance, sabida takaici Mami taji baxa ma ta iya karasawa tace zata tasheta ba, she just can’t, kawai ta juya hawaye na sauka idonta ta fita daga dakin tana girgiza kai, downstairs ta sauka tana goge idonta ta tafi waje, har sannan sojojin suna tsaye balcony ta amshi wayar daya daga cikin sojojin ta koma parlor tayi dialing number Noor, Yana fara ring Noor ta daga, Cike da karfin hali Mami tace “Ki dau driver ku taho gidan Khalil yanzu” Noor da hankalinta ya tashi tace “Mami hope all is well?” Mami tace “Kiyi abinda nace yanzu, ina jiran ki” Daga haka ta katse wayar, Zaunawa tayi saman kujera a parlon zuciyarta a dagule, takaici baxai bari ta iya tashin yarinyar ba, gwara kawai Noor taje ta tasheta idan ta karaso, Mami na ta zaune lokaci lokaci hawaye ke sauka idonta, bata taɓa expecting haka daga Khalil ba, she least expect this from him, bayan kusan minti talatin Noor ta iso gidan, tana shigowa parlon ta karaso wajen Mami da sauri duk hankalinta a tashe tace “Mami me ke faruwa?” Mami tace “Tafi sama ki taso yarinyar dake daki a kwance” Noor ta zaro ido tace “Yarinya kuma? Me ya kawota nan?” Ganin Mami tayi shiru bata ce komai ba, fuskarta zar takaici, Noor ta nufi sama gabanta na faduwa, direct dakin da Nihad ke ciki ta fara budewa, ai ko taga mutum a kwance, still tayi bakin kofar gabanta na bugawa, can dai ta karasa cikin dakin tana tafiya a hankali tana kallon saman gadon, tapping gefen gadon tayi, Nihad ta bude idonta a hankali amma ta kasa sauke duvet din fuskarta don ko ina na jikinta ciwo yake mata na fitar hankali, ko kwakkwaran motsi bata son yi, a tunaninta kuma Khalil ne, Noor ta sake buga gadon amma Nihad bata motsa ba, hakan yasa tayi karfin halin yaye duvet din tana kallon fuskarta, bata san sanda ta mike a kidime ta dafe kirjinta ba tana zaro ido ganin warce ke kwance saman gadon, tana in ina tace “You????? What are you doing here??” Sae a sannan Nihad tayi kokarin daga kanta jin muryar warce take ji, Nihad ta kasa ci gaba da kallonta, Noor dai gabanta sai faduwa yake tana kallon Nihad, ganin abun take kamar a mafarki, wato Yayansu gidansa ya dawo da ita da zama ashe?? Wayar hannunta ya fara ring ta duba da sauri ganin number da Mami ta kirata da shi dazu ne ta kalli Nihad, tace “Ki tashi” Nihad ta kalleta amma she couldn’t say a word, Noor na ganin yanayinta ta ɗan yi jim, don daga lips dinta har idonta sunyi ja sosai, and she looks so sick, can tace “Are you okay?” Nihad bata ce mata komai ba, Noor na kai hannunta jikinta tayi saurin janye hannun, bata taɓa sanin temperature din mutum na irin wannan zafin ba, ta koma baya tana kallonta, sai ga Mami ta sake kiran wayarta, Noor ta daga daga daya bangaren cikin fada Mami tace “Uban me kike yi a dakin ne? Baxa ku fito a kulle gidan ba” Noor ta kasa cewa komai da farko ita duk tunaninta Mami tasan Nihad ce a kwance, Mami tace “Hello, baki ji na ne…” A hankali Noor tace “Mami she is very sick fa” Mami taji wani sabon faduwar gaba, tace “Sick? Toh baxata fito ba kenan?” Noor dai ta kasa cewa komai, Mami ta katse wayarta, Noor ta karasa saman gadon ta kamo hannun Nihad tace “Ki daure ki tashi, za a kulle gidan as instructed by our father” Nihad ta girgiza mata kai amma ta kasa cewa komai, Noor ta cire duvet din gaba daya wanda shi ma duk ya dauki zafi, dai dai nan Mami ta bude kofar dakin, and she met the shock of her life, don sai da numfashinta ya dauke na yan dakikai saboda bugun da zuciyarta yayi, ta dinga kallon Nihad da idanuwanta kamar zasu fito bata ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata cak, at yhe same time kanta ya kulle, zuciyarta ya canza bugun da yake yi, wait…. raina mata hankali Khalil zai yi?? wannan din ce zai ce ma matarsa saboda ya fara shan wiwi, dama gidansa ya kawota all this while, shine yake kokarin covering up yace matarsa ce tunda yasan babban laifi yayi, a fili tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, me zan gani haka?” Nihad dai ta kasa ci gaba da kallon Mami, Mami ta daka mata wani tsawa tace “Me kike yi a nan? Amma dai babu tantama daga sama kika fado babu iyaye….” Noor ta kalli Mami, sannan ta kalli Nihad, sai a sannan ta fahimci Mami bata ma san ita ce a dakin ba, da sauri Noor ta nufi Mami tace “Mami she is very sick” ko sauraronta Mami bata yi ba cikin bacin rai tana kallon Nihad tace “To zo ki fita….” Duk da Nihad na jin ko tashi zaune bazata iya ba, haka tayi karfin hali ta yunkura zata sauka daga saman gadon, abu biyu taji a lokaci daya, wani mugun jiri sannan kuma taji kamar ta taka allurai a kasan kafarta har zuwa laps dinta, bata san sanda ta fasa kara ba, sai kuma ta tafi luuu ta fadi kasan dakin, Mami dai sai kallonta take, controlling temper dinta kawai take kada ta fadi abu da zai yi affecting ɗan nata taje tayi masa baki, bata taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba, Noor ta durkusa gaban Nihad sai taga kamar bata motsi, ta kalli Mami da sauri tace “Mami kamar fa suma tayi” a fusace Mami tace “Dauki Hijab dinta ki bata ta fitar min daga nan, idan taje waje sai ta suma….” Noor ta mike ta kalli Hijab din Nihad dake saman gado ta dauka, kallon bedsheet ta dinga yi sai kuma ta kalli Mami dake kallon saman gadon ita ma, Mami ta karaso dakin tana kara kallon zanin gadon, Noor dai sai kallon Mami take, bayan few seconds Mami tace “Ajiye Hijab din kije ki ce ma sojojin nan they should be patient muna fitowa” Noor ta nufi kofa ta fita, Mami ta sake kallon saman gadon sannan ta kalli Nihad dake kasa, dukawa tayi gabanta cike da karfin hali tace “Me ya sameki?” Nihad ta bude idonta da yayi ja a hankali tana kallonta amma ta kasa cewa komai, Mami ta dake tace “Tashi zaune” Hawaye ya fara gangarowa idonta ta girgiza mata kai kawai, Mami ta kai hannu jikinta taji sa kamar wuta, ta dagota tace “Hau saman gadon” Nihad ta girgiza kai da sauri cikin muryarta da baya fitowa tace “Baxan iya tashi ba….” Mami ta kasa hada ido da ita, sai da ta fara cire zanin gadon sannan ta taimaketa zuwa saman gadon, kamar warce aka zare ma laka ta fita daga dakin ta sauka kasa tana kallon Noor dake zaune parlon tace “Kina da number Dr Rukayya?” Noor tace “Eh ina da shi” Mami tace “Kira min ita” Noor ta shiga neman number bayan tayi dialing yana fara ring ta mika ma Mami, Mami ta amsa ta kai kunne Dr Rukayya na dagawa suka gaisa Mami tace “Hajiya Fatima ce ke magana Dr” Dr Rukayya tace “Na gane Hajiya, ya yaran?” Mami tace “Alhamdulillah, pls za ki zo ki duba mara lafiya ne amma ba can gida ba, will send u the address right away” Dr Rukayya tace “Ohk Ma” Mami ta katse wayar ta tura mata address din gidan Khalil, daga haka ta mika ma Noor wayarta ta koma sama duk jikinta ya mutu, tsaye tayi corridor tunani kala kala na yawo a ranta, she is confuse, meye hakan ke nufi kenan? Tana safa da marwa a corridor din for almost 20 minutes don hakan kadai ke sata jin relieve din abubuwan da suka tunkushe a zuciyarta, har dai likitan ta iso gidan, Noor ta kai ta sama ganin Mami na corridor ta sauko kasa ta bar su, Mami suka kara gaisawa da Likitan sannan suka shiga dakin tare, likitan na kallon Nihad tace “Me yake damun ki yan mata?” Nihad dai kallonta kawai take ba bakin magana, duk gaba daya tayi laushi, Likitan tayi considering haka ta kalli Mami dake tsaye tace “Hajiya what’s wrong with her, and for how long is she sick, naga ta jikata da yawa…” Mami ta hadiye wani abu da kyar tace “I don’t know precisely Dr, amma dai ki dubata ki ga” Likitan na kallon Nihad cikin kwantar da murya tace “Just indicate duk inda kike jin ciwo….” Nihad ta nuna mata kanta sai kuma kafarta, Likitan ta dinga kallon kafar tace “Daga ina zuwa ina?” Nihad ta nuna mata daga lap dinta har kasa, Mami dai ta jingina da bango don tsayuwar taji yana neman ya gagaranta, Likitan tayi shiru tana kallonta, can ta kalli Mami tace “Is she a new bride?” Rasa abun cewa Mami tayi lokaci daya taji kamar ta fashe da kuka, Likitan ta na kallon kayan baccin jikin Nihad da kyau sai ta lura da few blood stain, Kallon Mami likitan tayi, kawai sai Mami ta juya ta fita daga dakin hawaye na zuba a idonta, hakan ya daure ma likitan kai ta kalli Nihad tace “Are you married??” Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Tashi likitan tayi ta shiga bandaki, tana ganin zanin gadon dake bandakin ta tabbatar da zarginta, ruwan zafi kawai ta hada a bathtub, ta fita xuwa wajen Mami tana kallonta tace “Za a samu gishiri Hajiya?” Mami tayi karfin halin girgiza mata kai kawai, Likitan ta koma ciki, dole ta ɗan ɗiga disinfectant dake bandakin sannan ta fito, sosai taji tausayin Nihad kafin su karasa bandakin, she is in so much pain, sai ta fara imagining where is the husband that is this heartless, wannan ma yana da imani kuwa, duk yanda tayi da Nihad ta shiga ruwan kin shiga tayi tana kuka kamar yanda tayi ma khalil jiya, bata mance wahalan jiya ba, Sun bata minti kusan biyar a haka likitan na fama ta shiga ta ki, likitan ta kara ruwan zafi a bathtub din ta fita daga bandakin taje ta samu Mami, tana kallon Mami tace “Tana bukatar ta shiga ruwan zafi, ban san ko zaki mata magana taji ba, she isnt co-operating” Mami was lost of words, kawai ta gyada ma Likitan kai, likitan tace “Zan fita yanzu in siyo mata drugs da allura” A hankali Mami tace “Toh” Daga haka Likitan ta sauka downstairs, Mami ta shiga dakin sannan ta karasa bandakin, ta fi minti daya tsaye kafin ta tura kofan, Nihad tayi da ta sanin da bata hakura duk azaban da zata ji ta shiga a haka ba, bata yi zaton Mami likitan ta tafi ta kira ba, ga kunyan yanda Mami ta shigo ta ganta, ta kasa yi ma Mami musu banda hawaye babu abinda take, haka nan ta shiga ruwan, bata san daga inda dauriya ya zo mata ba a wannan lokacin, Mami ta canza mata ruwan ya kai sau uku, daga karshe ta tara mata ruwan wanka, duk wannan abun karfin hali kawai Mami take amma her heart is so heavy, bata yarda su hada ido da Nihad all through ba, kamar yanda ita ma Nihad din bata iya ta hada ido da ita ba saboda kunya, Nihad na wanka Mami ta wanke bedsheet din ta fita daga bandakin, zaunawa Mami tayi gefen gado ta rike kanta, ita Khalil yayi deceiving haka? Tunanin abinda zata masa taji sanyi a ranta kawai take, ta ina za a fara wannan babban lamarin? Hawaye ya hau sauka fuskarta tana girgiza kai, she wish all this is nothing but a dream, daga karshe ta mike ta fice daga dakin ta shiga wani dakin daban, Nihad na fitowa bathtub din taji dama daman abinda take ji, amma har sannan zazzabin na jikinta, tana dingishi cike da karfin hali ta fito daga bandakin daure da towel ta kwanta saman gado ta takure waje daya tana jin sanyi.
Bayan wani ɗan lokaci Mami ta goge idonta ta sauka downstairs tana kallon Noor tace “Ki duba ko akwai yanda zaki dafa mata shayi a kitchen, idan babu kuma ki fita ko restaurant ne ki siyo mata abinci kafin likitan ta dawo” Noor tace “Toh” Mami ta juya ta koma sama tana jin jikinta babu dadi kwata kwata, kofar dakin da Nihad ke ciki ta bude ta ganta kwance har ta fara bacci, Mami ta karasa cikin dakin tana kallonta tunani iri iri na yawo a zuciyarta, press din dakin ta nufa ta bude taga babu kaya a ciki, ta kalli akwatinta dake dakin tana tafiya a hankali ta nufi gun akwatin ta bude tana duba kaya a ciki, wata doguwar riga ta fiddo mata da underwear sannan ta mike ta karasa kan gadon, bude akwatin da Mami tayi ya tada Nihad, Mami ta ajiye mata kayan a gefen gado ba tare da ta kalli idonta ba tace “Tashi ki sa” Nihad ta mike zaune, Mami ta fita daga dakin, hawaye kawai Nihad take, all her thought was that Khalil left her upon the condition she is in, bai duba halin da take ciki ba yayi tafiyarsa ya kyaleta haka, rabon da taji haushinsa yanda take ji yanzu tun farkon zuwansa gidansu…..
Har kusan azahar Nihad bacci take tun bayan da Dr Rukayya tayi mata allurai ta bata magani, ita ma Mamin maganin bacci ta sha don truly bata jin dadin jikinta, tasan da kyar idan jininta bai hau ba, nan spare room dake gidan tayi bacci har kusan azahar din ita ma, har a lokacin kuma Noor na gidan, ana idar da azahar Mami ta sauko downstairs tana kallon Noor tace “Zan kiraki zuwa anjima, xan je gida yanzu” Noor tace “Toh Mami, Allah ya kiyaye” Daga haka Mami ta fita tare da sojoji biyu suka maida ta gida, tana sauka compound direct Guard room ta nufa wani soja yayi saurin bin bayanta yace “Hajiya Oga ya dawo ai an fito da shi” Mami da gabanta ya fadi don sai da yayi magana taga motar Janar a gidan, ta juya tana kallonsa cikin karfin hali tace “Yana ina?” Sojan yace “Yana ciki” Mami ta karasa cikin gidan da sauri, tana shiga main parlor Aunty Hassana na kyabe baki tace “Plan din naku yayi aiki….” Mami ta kalleta sai kuma kawai ta tafi part din Khalil, bata gansa a dakinsa ba, ta fito kenan sai ga Mimi ta biyota, Mimi tace “Mami yana part din Abba, he is very sick” Mami tace “Me yake yi a can?” Bata jira abinda Mimi xata ce ba ta nufi bangaren Janar, bude kofar parlon tayi, taga Aliyu a tsaye Janar dake zaga Parlon yana ma Aliyun magana, don shi bai iya tsayuwa waje daya, Ta dinga bin parlon da kallo bata ga Khalil ba, Aliyu yayi kasa da kai yace “Ina yini” Mami tace “Where is Khalil” Wani kallo Janar yayi mata ya ci gaba da gaya ma Aliyu abinda yake gaya masa na zuwa Germany da zai yi akan wani business, Aliyu ya nuna mata inda Khalil yake, ta karasa ta bude kofar da sauri, kwance ta gansa saman gado yana bacci, ga allurai da drugs a kan bedside drawer, sai kuma drip da aka sa masa, har sannan kuma hannunsa daya akwai handcuff, ya bude ido a hankali jin an bude kofar dakin don baccin nasa sama sama ne, ganin Mami sai da gabansa ya fadi, ya mike zaune da sauri kusan a firgice, Mami ta dinga kallonsa kafin ta karasa cikin dakin ta tura kofar tana girgiza kai cike da takaici tace “Wato ni zaka raina ma hankali Khalil? Ni ka maida yar iska tsohuwar banza, ni zaka raina ma wayo kamar kai ka haifeni, ka ban mamaki wallahi, ka ban mamaki, dama kuma tun farko ni ce ban tsaya nayi nazari ba, amma da na tsaya nayi nazari da na gano cewar babu iyayen arziki da za su hada ‘yar su da namiji wai ya kai ta karatu, a da ina alfahari da tarbiyan da na maka amma banda yanzu, i can’t count on you now, ban taɓa tunanin akwai ranan da zaka saɓa ma Allah ta hanyar zina ba” Khalil ya katseta da sauri yana girgiza kai, zuciyarsa na bugawa yace “Keep on counting on me Mami, i am not a fornicator, ban taɓa ba, kuma baxan fara ba, i am sorry ban san ta yanda zan billo ma lamarin bane, amma Nihad matata ce ta sunna… Da aurenmu na kawota gidan nan, kamar yanda kika fada da ba don aure ba babu abinda zai sa iyayenta su bari in taho masu da yar su daga ni sai ita….” Mami kallonsa take babu ko kiftawa with new shock, lokaci daya ta fashe da matsanancin kukan takaici tana girgiza kai ranta na mata zafi tace “Sai dai in bayan raina zaka zauna da ita a matsayin matarka… amma matukar da raina a doron kasa to wllh babu aure tsakaninka da yarinyar nan, wallahi baza ka zauna da ita ba….” Tura kofar dakin aka yi Mami ta juya da sauri tana share Idonta, Janar na kallon Khalil with the expression of soldiers yace “Wacece matar taka???” Mami ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai tace “Ban taɓa dana sanin haifanka ba sai yau Khalil, kuma ina me tabbatar maka sai dai ka zaɓi ko ni ko yarinyar, baxan taɓa hada zuri’a da ita ba wallahi tallahi, this time around duk abinda ubanka zai maka yayi maka sannan nima ka jiraye nawa hukuncin, sai na nuna maka ni na haifeka ba kai ka haifeni ba” Daga haka ta fice daga dakin, zufa ya dinga keto masa yaji kansa yayi masa mugun nauyi, lokaci daya zazzabinsa ya dawo masa sabo, Janar dake ta kallonsa yace “Wace yarinya kenan take magana a kai??” Lokaci daya hawaye ya kawo idon Khalil idan Mami tayi masa haka waye kuma zai tsaya masa, yana kallon Abbansa ya kasa cewa komai saboda shock, Abba ya masa tsawa yace “I am talking to somebody” Khalil ya rike kansa with shaky voice yace “A gidan da na zauna a kano suka bani aurenta, ni kuma na amsa saboda sun amsheni a lokacin da aka nuna ba a bukatata a gidanmu, i can’t tell them no” Janar na ta kallonsa yace “So now, where is the girl?” Khalil ya kasa dagowa yace “Tana gidana” Janar ya hau safa da marwa a dakin kamar me pareti, can yace “Sai suka ce kuma ka boye mana ko?” Khalil ya dago a hankali yana kallon Abbansa with tears in his eyes, Janar na gyada kai yace “Zaka kai ni har kanon gidan iyayen yarinyar to make confirmation, and if i should find out u are lying sai na karya maka kafa i promise, idan kuma din da gaske matarka ce that’s fine….” Daga haka ya juya ya nufi kofa Khalil ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa…….

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don’t like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button