Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 61

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

 

61

Related Articles

 

 

Farooq na fitowa parlon Abba ya tafi bangaren Mumy, Mumy ta fito daga dakinta jin sallamarsa yace “Bacci kike ne?” Tace “Aa ba bacci nake ba farooq, ya gajiyan hanya, jiya sai baka shigo ba har nayi bacci” Yace “Wallahi na gaji ne, i had issues with my car” Mumy tace “Haka kace, Allah Ubangiji ya tsare” Yace “Ameen” Mumy tace “Ka samu mijin Kamilar a waya?” Farooq yace “Eh na samesa amma bai daga ba kuma bai biyoni ba” Mumy ta ɗan yi shiru, can tace “Toh Allah ya kyauta, amma da ka je gida ka samesa ko?” Ya girgiza kai yace “Aa bazan je ba, duk yawancin abinda take masa dama ai ni yake kira, kuma sai dai in basa hakuri, so this time around ban san me tayi masa ba, tunda gashi har ya ga kirana bai biyo ni ba” Mumy tace “Kai abun ba dadi wallahi, Allah Ubangiji ya daidaita su” Farooq yace “Mumy dama Khalil ne ya kirani yace yau Mahaifinsa zai zo su gaisa da Abba….” Mumy tace “Yau din nan?” Farooq yace “Ehh, shine na shigo in gaya maki ko za ayi masu ko da snacks ne, tunda lokaci ya kure balle ace za ayi girki, yace min zuwa 11 za su zo and this is past 9” Mumy tace “Toh shikenan, dama Jamila na garin amma yau tace min zata koma, bari in kirata ko zata bari da yamma” Farooq yace “Ohk to, sai a karo drinks da ruwa” Mumy tace “Toh shkkn” Yace “Zan siyo drinks din da ruwa” Daga haka ya fita daga parlon Mumy ta dau wayarta ta shiga kiran Aunty Jamila, babu ɓata lokaci kuwa Aunty Jamila ta iso gidan suka shiga kitchen da Mumy, Hafsah na taya su, Umma ta fito ɓangarenta jin yanda kamshin soye soye ya cika gidan ta tsaya kofar kitchen tana kallon Mumy tace “Wai!! Sannunku da aiki, toh dai Allah ya sa su iya ci, yan kauye suka san wani Samosa da spring rolls banda abun ki Maryam, dama dai tuwo miyar kuka kika masu da wannan wahalan ai” Ko kallonta Aunty Jamila bata yi ba tana ci gaba da aikin da take, Mumy tace “Toh gashi nan dai muna yi, ya jikin Kamila?” Umma tace “Da sauki….” Daga haka ta juya ta bar kitchen din, sai a sannan ta tabe baki ta koma bangarenta. Nihad ta kasa hada ido da Aunty Maryam da Mami dake zaune Lounge din, sai Aunty Hassana da bata yi shawara da kowa ba ta dau gyalenta ta shige daya daga motocin Convoy, kuma daga Mami har Aunty Maryam babu wanda yace mata komai, Ita kuwa Hajiya Amina dama sai yanda Aunty Hassana tace mata to bata ce mata ta taho ba balle ta biyosu, Wani waje sak parlor Nihad ta hango Janar zaune da wani mutumi sanye da kayan soja suna magana, Nihad bata iya ta dago kanta ba, ta gaishe da su Mami a hankali, Mami ta amsa ba tare da ta kalleta ba, Aunty Maryam dae sae kallonta take bayan ta amsa gaisuwan, can ta nuna mata kujeran dake side dinta ganin gefe ta koma ta tsaya, a hankali Nihad ta karasa ta zauna kan kujeran, Aunty Hassana ta dinga kallon Nihad tana nazarin abinda Aliyu ya gaya mata, Khalil dama kin shiga Lounge din yayi, ya zauna a Departure Lounge din kowa da kowa… first class passengers suka fara boarding din plane din, wanda iyaka ahalin Janar ne a first class din, sai da Aunty Maryam ta nuna ma Nihad inda zata zauna cikin jirgin sannan ta zauna, kamar yanda Khalil ke ta avoiding eye contact da Mami ita ma haka ta dinga avoiding, wani kunyarta take ji, Khalil ne karshen shigowa ya zauna, Aunty Maryam ta taɓe baki ganin yanda yake wani sinne kai, ita kam ta gama tsorata da lamarinsa bata jin zata sake yarda da ko wani maganarsa, duk yanda take da shi amma ya boye mata wannan lamarin….. Karfe sha daya da kusan rabi jirgin ya sauka a Aminu Kano international airport, sai da suka fara sauka daga jirgin before the rest class, Nihad ta dinga kallon jerin motocin dake jiransu har da na sojoji da suka yi bake bake a airport din, tuni wani soja ya bude ma Janar da babban sojan dake tare da shi motar da za su shiga, Khalil dai sai nesa nesa yake da su kamar baya son a san tare suke, kai kace karere ne shi a wajen, Aunty Hassana kuwa sai daga kafada ake ana taku dai dai uwa ita ce matar Janar din, Nihad ta daga kai a karo na farko ta kalli Khalil tun barin su Abuja, taga ko kusa kusa da family din nasa bai son matsowa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, wasu abubuwan da tayi masa a baya ne suka hau dawo mata vividly, irin humiliating dinsa da tayi a gidansu, and even for once bai taɓa attempting nuna mata ya fi ta komai na rayuwa ba, yawanci duk abinda take masa sai dai yayi kamar bai san tana yi ba, bata san sanda hawaye ya kawo idonta, and because of him today she is among this elite, standing in the midst of them, kamar ya san kallonsa take shi ma ya kalli direction din da take, suna hada ido tayi saurin kauda kanta, Aunty Maryam ta bude daya daga motocin dake jere tana kallon Nihad tace “Shiga” Nihad ta shiga mota sannan ita ma ta shiga, Mami ta shiga wani motar daban, Aunty Hassana ta shiga motar da Mami ta shiga don me shegen tsada ne, nan suka bar airport din, Khalil da zai yi directing dinsu zuwa gidan ya hau motar dake gaba, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka iso Nasarawa GRA…. Nihad na ganin sun shigo layinsu gabanta ya dinga faduwa, Tuni Aminu ya taso da sauri yana leko gate jin jiniya kamar tashin duniya, ganin jerin motocin sannan ga na sojoji a gaba ya gwale ido yana jiran yaga sun yi gaba sannan ya ga gidan wa za su amma sai ya ga sun jeru dai dai kofar gidan, kan kace me sojojin sun sauka sun zagaye layin, a hankali Aminu ya tura gate din ya rufe ya saka lock yana zaro ido, to meye kuma suka tsaya masu a kofar gida, ko dai ɓatan hanya suka yi, A mugun tsorace Aminu ya kalli gate din jin ana bubbugawa, haba kan kace me sai ga Aminu har cikin parlon gidan ba tare da yasan ya iso ba, Inna da dawowarta kenan daga police station tana bada labarin yanda aka je har gidan Kamila ba a tadda tsinannen mijin ba, ta saki baki tana kallon Aminu tace “Me zan gani haka? waye wannan kuma??” Jiki na rawa Aminu yace “Hajiya wallahi sojoji ne sun fi hamsin a kofar gidan nan, yanzu haka su ke bubbuga gate din, ban san wa suke nema ba” Farooq ya mike yana kallon Aminu, Inna tace “Sojoji? Meye su din?” Umma dake zaune parlon ita ma tana kallon Aminu tace “Sojoji fa kace Aminu” Zufa na keto ma Aminu yace “Wallahi su Hajiya, da manyan bindigu na gansu sun sauka kofar gidan nan” Inna tace “Aa to ko dai bariki za su suka yi ɓatan hanya suka shigo ma mutane anguwa, da ba sai ka leka kace masu ba hanya ba” Abba ya fito daga parlonsa jin bubbuga gate din da ake ta yi ba kakkautawa, shi dai Farooq na ta tsaye yana kallon Aminu ya kuma kasa fita waje, ganin Aminu a parlon Abba yace “Lafiya” Aminu ya durkusa ya makale jikin kujera yace “Wallahi Alhaji sojoji ne sun kusa dari ban san wa suke nema ba, ni dai shine na kulle gate din na taho, ga su can suna ta buga gate din” Ai ko rufe baki bai yi ba Farooq ya nufi kofa da sauri, a tsorace Inna ta mike tace “Ina za ka farooq??” Umma ma ta daka masa tsawa amma tuni ya fice daga parlon, da gudu Inna ta bi sa tana kiransa a gigice, yana tafiya ya fiddo wayarsa dake ring a aljihu yaga Khalil ne ke kiransa, dagawa yayi khalil ya sanar masa suna waje, Farooq ya karasa bakin gate din ya bude, Khalil ne tsaye bakin gate din sai sojojin dake kewaye wajen ko wanne da bindiga a hannu, sai a sannan Janar ya sauko motar tare da abokinsa, Inna ta gwale ido uwa munafuka ganin Khalil ga sojoji sun zagayesa, sai kuma ta fashe da kuka ta saki salati tace “Dama sai da na fada, sai da nace ɗan kinnafa ne su Ibrahim suka gwaleni suka maida ni wawa…..” Sai kuma ta kalli Janar da sojojin dake wajen suna kallonta tace “wallahi ranka shi dade bamu taɓa saninsa ba, ce maku yayi ya san mu? Ɗan Nijar ne fa” Sai kuma ta juya da gudu taje ta gaya ma Abba ya buya, gaba daya ta rikice ta gigice, Farooq sai kallon Janar yake wondering if Lieutenant General Abubakar I Jikamshin da ya sani ne wannan yake gani a gabansa or just kamanni ne, shi dai Janar was patiently standing, su Mami kuma basu kai ga sauka daga motar ba, Khalil yayi kasa da murya yana kallon Farooq bayan ya shiga compound din da sauri yace “He is my Father” Muryan sojan dake tare da Janar suka ji yace “Is this how u treat ur guess?” Yana kallon Farooq yayi maganar babu yaɓo babu fallasa, Da sauri Farooq ya gaishesu a daburce yana welcoming dinsu ya bude gate din sosai ya basu hanya, nan su Mami da Aunty Maryam suka sauko daga motar, Khalil dai kansa na kasa, walking fast ya fara leading din Janar da abokin nasa zuwa entrance din main parlor ganin kamar Farooq ya rikice and at anytime Janar zai iya exploding ya masu kwarkwar gaba dayansu a wajen barin yanda aka barshi a tsaye, Nihad taji kamar taje ta rungume yayan nata, she is so happy seeing him, A balcony Khalil ya hadu da Abban Nihad, a bit confuse Abba ya dinga kallon Janar dake tahowa like the soldier he is, Abba ya kalli Khalil sae kuma ya sake kallon Janar with his friend, kamar Janar Jikamshi yake gani a gabansa, ko idonsa ne ke masa gizo, lokaci daya sojojin da suka biyo bayan Janar da abokinsa suka nemi each and every angle of the compound suka tsaya, hakan dai bai sa Abba ya fasa ba Janar hannu ba yana masa sannu da zuwa, sannan ya ba daya sojan ma hannu kafin yayi leading dinsu har cikin Main parlor, Saminu da Isiya sai wuwwurga idanuwa suke daga Chalet suna jiran suga an fara kwashe kowa na gidan har su, har sannan kuma Aminu na makale a inda ya durkusa a parlon tun dazu, Hajiya Inna kuma na can kuryan dakin Mumy bata ma san sanda ta isa nan ba tsabar gigicewa sai salallami take tana cewa ya cucemu ya cucemu, dama sai da nace masu ban yarda da shi ba hankalina bai kwanta da shi ba aka maida ni wawa…. Khalil ya daga kai ya kalli Umma da ta koma bayan kujera ita ma sai zare ido take a tsorace, Mumy na tsaye kofar kitchen da Aunty Jamila, ko wanne zaka ga Fargaba karara kwance a fuskarsa, sunkuyar da kansa yayi kawai, Bayan Janar da abokinsa sun zauna ya nuna ma Abba ganin bai zauna ba yace “Bismillah Alhaji” Abba ya kirkiri murmushi ya zauna yace “Barkan ku da zuwa, amma sai dai ban san me ke tafe da ku ba, ina kuma fatan Allah ya sa lafiya” Nihad ce ta shigo parlon su Aunty Maryam na biye da ita, duk suka zauna a parlon, Mumy da Aunty Jamila suka dinga bin su da kallo, lokaci daya gaban Mumy ya fadi, what’s happening??? Umma dai kamar idanuwanta za su fito tsabar yanda take gwalesu tana bin sabbin occupant din parlon da kallo, Farooq ne kawai ke ta masu sannu da zuwa a parlon da fara’arsa, ya tafi ya dinga jido pack din ruwa da lemo, Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta tafi da sauri ta rungume Mumy cike da farin cikin ganinta duk da basu wani dade da ganin juna ba, but she is having a new strong love for her mum now, Mumy ta hadiye wani abu da kyar, murya can kasa kasa tace “Su waye wa ennan Nihad? Why are they here??” Yanda zaka san kowa a tsorace yake ko gaida su Mami da Aunty Maryam babu wanda yayi a parlon ana dai jiran aji abinda ke tafe da su, most especially Abba da hankalinsa ya tashi sosai, kawai dai bai nuna bane a fuska, Muryar Janar dake kallon Abba suka ji yace “Babu wani abu dake tafe da mu sae alkhairi Alhaji, kuma muna me ba kai da iyalanka hakurin yanda muka shigo maku gida kai tsaye, may be without any notice…. and most important of all, i hope kai ne Alhaji Ibrahim??” Abba ya gyada kai yace “Kwarai ni ne” Janar yace “Sunana Abubakar Ibrahim Jikamshi….” A hankali Abba yace “Lieutenant… General…. Abubakar Jikamshi” Janar yace “Haka ne” Umma ta dafa kujeran kusa da ita tana sake kallon Janar da kyau kamar idanuwanta za su fito, kwarai kuwa sai yanzu ta ganesa, Ita kanta Mumy da Aunty Jamila kallonsa suke babu ko kiftawa with shock, Janar ya nuna ma Abba Khalil yace “Few abinda ka sani game da wancan mutumin nake son kayi briefing dina Alhaji…” Sosai gaban Abba ya fadi, ya daga kai yana kallon Khalil da ya sunkuyar da kansa kamar mara gaskiya, lokaci daya har hawaye ya kawo idon Mumy..mm Kasa cewa komai Abba yayi, Janar yace “Muna sauraronka Alhaji” a hankali Abba yace “Toh, ya dai zo gidan nan yau shekara daya da yan watanni, ya nemi aikin driving na kuma basa, yana kai min yarana makaranta, sannan duk wani aike na cikin gida ana aikensa” Cike da karfin hali Abba ke maganan, only Farooq is looking so calm a parlon, Janar ya gyada kai cikin gamsuwa yace “Shikenan?” Abba ya girgiza kai yace “Na kuma basa auren ‘ya ta, bayan da naga shi me gaskiya da rikon amana ne, sannan na yaɓa da hankalinsa da nutsuwarsa….” Janar ya dinga gyada kai, Shi dai Abba kallonsa kawai yake, Janar yace “Amma kai ta yaya kasan yana da gaskiya da rikon amana?” Abba yace “Ehh to, na sha gwadasa ta fanni daban daban akan abubuwa da yawa da suka shafi kudi, and i never find him guilty of any, a yanda ma yayi min maintaining motar da na basa ban taɓa driver da yayi min haka ba….” Janar yace “Nawa ne Albashin da kake basa?” Abba yace “Na kan basa dubu hamsin ko dubu sittin duk wata….” Janar yayi shiru sai kuma yace “Amma kai baka bukaci sanin iyayensa ba kafin ka basa auren yar ka?” Abba yace “Har wajen iyayen nasa naje a kauyen getso, kuma da yardansu na aura masa ‘ya ta ba kai tsaye aka yi hakan ba ranka shi dade” A tare Janar da su Mami suka daga kai suna kallon Khalil with surprise, shi ko ya ki dago kansa, Janar dai ya kasa daina kallon sa, wato har feigning iyaye yayi a kauye, Janar ya kalli remote dake gefen kujeran da yake zaune, dauka yayi lokaci daya ya harbi Khalil da shi, duk yanda Khalil ya so dodging remote din sai da ya taɓa sa, ni ko nace ya mance ba Major bane ya harbesa da yake kokarin dodging, Nihad ta rufe bakinta da sauri don wani dariya ne ya kusa taho mata, Khalil ya sosa kansa with a smile on his face, wai fa duk wannan abun da ake Inna na makale jikin kofa ta kasa fitowa, banda hawaye babu abinda take, ta tsine ma Khalil yafi sau hamsin, su Saminu da Isiya na tsaye bakin window ta waje suna jiyo komai, Aminu dai har ya gaji da gwale ido kamar wanda yayi ma sarki karya, Janar na kallon Abba bayan shirun few seconds da yayi yace “To ɗa na ne Ibrahim, ni na haifesa…. Ba komai kuma ya sa na xo nan ba sae don in tabbatar da gaskiyan lamarin auren nasa, ina kuma farin cikin hada zuri’a da kai Alhaji Ibrahim, na kuma ji dadin yanda ka yarda da shi har ka basa auren er ka, and I will forever be grateful for that” Ba Abba ba kowa na parlon sae da yayi stiff a inda yake for some seconds, da wani expression Abba yace “Ɗan ka kuma??” Janar yace “Ɗa na ne, and he is my only son” Aunty Hassana da ke ta girgiza kafa a parlon ta kalli Janar da sauri jin da tayi yace his only son, Abba ya daga kai yana kallon Khalil babu ko kiftawa, Aunty Jamila tayi saurin riko Mumy wanda ta ji wani jiri tayi baya kamar zata fadi, Aunty Maryam dai sai kallom Mumy take cike da tausayinta don taga kamanninsu da Nihad, Khalil bai iya ya dago kansa ba ya karaso har cikin parlon ya durkusa gaban Abba cikin sanyin murya yace “I am sorry i wasn’t truthful to you sir, i had no choice but to hide my identity…. Ina kuma neman yafiyarka, i never took u for a fool, bani da option ne….” Inna da ta kusa minti daya baki a bude ta fito parlon da sauri bayan ta goge hawayenta tana kallon Janar tace “Wai ɗan da ka haifa a cikin ka ko kuma yaron aikin gidanka kake nufi?” Janar na kallonta yayi murmushi ya nuna mata Mami yace “Ga Mahaifiyarsa can, ita ce uwargida na” Mumy da Aunty Jamila suka daga kai da sauri suka kalli Mami, hawaye masu zafi ne suka hau sauka idanuwan Mumy ta jingina jikin kanwarta saboda yanda taji tsayuwar na neman gagararta, ganin abubuwan take kamar a mafarki, Umma ta dinga bin kowa na parlon da kallo babu ko kiftawa tana ta wani irin murmushi kamar warce tayi recovering daga hauka, Inna ta rike kai tace “Habaa waaa, to kalleni nan” Janar dai sai kallonta yake, ta nuna masa Abba tace “Ni na haifi Ibrahim, kuma tsakanina da Allah tun da yaron nan Halilu ya xo gidan nan na gaya masu ba banza yake ba, wallahi tun ranan da na fara ganinsa hankalina ya kwanta na amince da shi, yaushe ake samun mutum da nutsuwa da ladabi da sanin ya kamata haka a zamanin nan, uwa uba ga kyauta, wallahi apple ya siyo min ranan ya fi na dubu biyar daga cewa yaje yaji nawa nawa ake siyarwa, Allah ne ya kaddara zaman sa a gidan nan amma ni ce sanadi, kuma ni na bada goyon baya aka aura masa jikata ka tambayi kowa, amma dai kai ko wani lalacewa ya sameka kamar me bakin uwa kana babban soja a kasa zaka bar ɗan ka a gantale? Yanzu da bai shigo hannunmu ba fa? Ayi magana ta tsakani da Allah fa” Juyawa duk suka yi da sauri jin an fadi timm a kasa, Mumy da Aunty Jamila da Farooq suka karasa gun Umma da sauri, Abba ya mike, Mami ta nufi wajen tace “Subhanallah, is she okay” Aunty Maryam dai ko motsawa bata yi ba don tuntuni take lura da yanayin da Umma ta shiga a parlon, kuma a kan idonta ta tafi luuu sannan ta fadi timm, tuni jini ya fara bulbulowa daga goshin Umma tsabar yanda ta buge da tiles, Farooq da Khalil suka yi waje da ita bayan Janar yayi instructing sojan dake bakin kofa a tafi da ita hospital with the convoy….

 

 

 

Waje aka yi da Umma za a saka ta a mota zuwa asibiti don jini ba na wasa bane ke zuba a goshinta kamar an bude pampo, Inna tayi gate da gudu tana ce ma sojojin dake bakin gate din su bude su bude, Kasake inna tayi ta bude baki ganin layin ba matsaka tsinke da jama’a, ke kya ce rabon daloli ake, Inna ta toshe hancinta da sauri don tear gas kawai sojojin ke sakar masu ba kakkautawa amma sun ki gudu, ashe duk yan Khaleesat palace ne da suko taho ayi komai a gabansu, shine sojoji suka hanasu shigowa gidan Abba, can na hango Mrs Bello ta ci damara, Mom twins da Aunty Zahrah rike da katon Banner an rubuta masu gudu su gudu, Daga daya bangaren kuma Chamo na hango tayi bake bake a gaba tana tura masu son mata overtaking ga Fu’ad goye a bayanta duk ta hada zufa, Deejah me lamurje kuwa sai bi take tana rabon lamurje a gora, ashe abinda yasa basa jin zafin tear gas din kenan, A kusa da Chamo na hango Aunty Inna sanye da hulan lauyoyi tana cewa sai tayi sue din sojojin idan basu bari sun shiga gidan ba, they have no right, turanci dai har da wanda ban taba ji ba a bakin inna in gaya maku, Sai kuma na hango Mardiyya rike da microphone cikin daga murya take cewa ita ewr jarida ce, ita fa ewr jarida ce, don haka tana da right din shiga ta dau wrahotu, they have no wright to stop her, Safiyya Usuman da Aunty Amzaj kuwa babu abinda suka mance basu gaya ma sojojin ba na cin mutunci ga hawayen tear gas sai zuba yake a idonsu, Damsel, Aisha Bela, da Aneesah da Mom Asas, kuwa na rike da speaker da ya cika anguwar da wakar rarara ta masu gudu su gudu, daga can bayan yan Khaleesat palace na hango yan Nihad conversation su ma suna ta nasu taɓarar su, a bayansu kuma ashe yan bati ne ko wacce da banner dinta a hannu, duk suka tare layi babu ta inda za a fitar da Umma dake ta zuban jini xuwa asibiti, ji kake tas tas tas tas tas a sama, kamar kiftawar ido layin ya dawo ba kowa sai gorunan Lamurje, warin takalmin jama’a da zanin goyon chamo a kasa, sai hular lauyoyin inna, sai banners din yan bati, sai a sannan aka samu aka yi asibiti da Umma….

🥸🥸

 

 

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

 

Ur evidence via 07087865788

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button