Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 8

Sponsored Links

💖💖 *NIHAAD* 💖💖

 

 

Related Articles

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

8……

 

Throughout the day’s lecture mood din Nihad was so dull, gaba daya she wasn’t her self, Husnah tace “Nihad mu je mu ci abinci ni dai na fara jin yunwa” A takaice tace “I am not hungry” Husnah tace “C’mon babe, wai me ke faruwa ne? Gaba daya you look dull today, don Allah ki gaya min me ke faruwa” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Wai har ni mutumin nan xai ma walakanci ya ajiye ma makulli ya wuce Husnah?” Husnah ta ja wani dogon tsaki tace “Ohh this? Wai wannan ne ya canxa maki mood throughout? Lallai ma, To wai meye abun damuwa, kika sani ko barin aikin ma yayi? Ni na fi tunani ya ajiye aikin ne, ba gashi da kika tambayesa wa ya bar ma motar yace maki masu shi ba, probably yayi quitting ne” Nihad dake ta kallonta tace “Sai ya rasa wanda xai ajiye ma aiki sai ni, me yasa bai kai ma Abba makullin ba, salon ayi xaton ni ce na koresa? dama babu wanda ke considering dina a gidan banda Umma, kawai so yake ya kara ja min bakin jini wajen Mumy” Husnah ta ja tsaki tace “Soo what? Idan ma ajiye aikin yayi ai hakan ke kika fi so, abinda kike ta so ne ya faru fa, karkari su gama surutunsu na kwana biyu su yi shiru, sannan a samo wani driver din wanda xa ki juya yanda kike so, ba shikenan ba?” Nihad ta taɓe baki ta mike tana harhada material din karatunta tace “Xan tafi gida” Husnah tace “Gida kuma? Da wuri haka? Ke da nace maki xa mu je guest inn din su Bill yanxu, Kai Nihad yau da kike da full control din mota an bar maki kiyi yanda kika ga dama shine xa ki wuce gida da wuri, haba yan mata, ki bari wajajen six ki koma gidan mana” Nihad tace “Ni kawai gida xan tafi duk raina a bace yake” Husnah ta juya ido tace “Toh ai shkkn, bari in raka ki gun motar” Tare suka isa inda motar yake, Nihad ta ajiye jakanta da kayan karatunta a bayan motar, sannan ta zaga ta shiga driver seat, Husnah na tsaye har ta tada motar ta fara tafiya….. Nihad na isa gate din gidansu tayi horn, mai gadi ya fito da sauri ya bude gate din, ta shiga gidan tayi parking, sannan ta kashe motar ta sauka, kallon inda mai gadin yake tayi, ta ga shi kadai ne a wajen, ta nufi cikin gida ba tare da ta dau material din makarantar ta dake bayan mota ba, Mumy na xaune parlor da Nihal, sai Umma dake parlon ita ma duk suna kallo, ta gaida su xata wuce, Mumy tace “Bani makullin da kika amsa wajen driver daxu” Tsayawa tayi cike da mamaki tana kallon Mumy tace “Mumy wa yace ni na amsa makullin?” Umma tace “Atoh, nima dai nace baxa kiyi haka ba, amma shi algungumin yace kin amshi makulli, kuma sun yarda” Nihad tayi narai narai da ido tace “A yaushe na amshi makulli wajensa? Wllh Umma sharri yayi min” Mumy tace “Ban tambayeki ba’asi ba, makulli nace kawai ki bani, xa kuma mu hade a daki” Nihad ta fashe da kuka tace “Ni wllh Allah ya isa wannan sharrin da yayi min, Allah ya isa tsakanina da shi munafuki kawai, ajiye min makullin fa kawai….” Throw pillow Mumy ta dauke ta jefa mata tace “Tafi ki bani waje, ga ki nan munafuka, wllh tunda haka kika xaba xa mu sa kafar wando daya dake a gidan nan, kuma daga yau kika sake driving da kanki sai dai ki canza wata uwar bani ba” Umma tace “Wai ya kike haka ne Maryam? Shikenan kai da ɗan ka baxa ka ja sa jiki ba komai ya fada maka sai ka karyatasa baxa ka goyi bayansa ba, me yasa kike fiffita bare akan naki? Wannan wace irin rayuwa ce? Ki bar ta tayi bayani ma kin ki sbda rashin adalci” A fusace Mumy tace “Bana son bayaninta, wani bayani xata min sai kace bani na haifeta ba, ko kuma ban san halinta ba, wllh daga ni har ubanki babu me irin wannan mugun hali naki don ma kiji, in har kince ke sai dai ki tuka kanki to wllh ki nemi wata uwar, kuma ai kin saba cewa a baki makullin ba wnn ne karo na farko ba, don haka babu abinda xa ki gaya min in yarda” Kuka kawai Nihad take xuciyarta na suya, ta ajiye makullin motar nan saman kujera tace “Allah ya isa karyan da ya laka min, Allah ya isa tsakanina da shi…” Tashi Mumy tayi, Nihad na ganin haka ta wuce sama da gudu, Mumy tace “Tsaya dai ki min rashin kunya” Mikewa Umma tayi ta fita daga parlon, tana fita compound ta kwalo ma Aminu kira ya taho da sauri, tace “Ina dreban nan yake?” Mai gadi yace “Ya fita ya ɗan amso abu” Tace “Toh xai dawo ya sameni” Daga haka ta juya fuu ta koma ciki. Nihad na shiga dakinta ta sa makulli ta dinga rusa kuka ta dau wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing ya daga yace “Hello Dear, ina meeting i will get back to you” Ta fashe da kuka tace “Abba ni dai kawai a canza driver din nan, bana son ganinsa kuma, i can’t withstand the sight of him any longer, kawai ni dai Abba ka sallamesa” Abba ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Why did u ask him to hand over the key to you da ya kai ki makaranta?” Nihad ta xaro ido tace “Abba wllh sharri ya min, ta yaya xan ce ya bani makulli, wllh karya yake min ni ban ce masa haka ba” Abba yace “Idan na dawo gida xa mu yi magana yanxu muna meeting ne” Daga haka ya katse wayar, kuka ta dinga yi, nobody is getting her banda Umma, wato dawowa gida yayi ya laka mata wannan uban sharrin gashi kowa ya yarda, number Farooq tayi dialing, yana dagawa shi ma ta rushe masa da kuka yace “Lafiya??” Cikin kuka tace “Yaya dama Abba ne ya dau wani sabon driver, yaya tun da ya fara aiki yake laka min sharri iri iri, yana sa Mumy na kara tsanata, wai daxu ya kai ni schl shine ya ajiye min makulli yayi wucewarsa, da ya dawo gida shine ya je yace ma su Abba da Mumy ni nace ya ajiye min makullin” Farooq yace “To ai halinki ne wannan, amsan makulli a wajen drivers kiyi driving da kanki, ke ko wani driver sai kin samu matsala da shi, haka Habibu farkon da ya fara aiki a gidan nan, why are u always having issues with everybody? Me yasa ita Nihal bata ce an mata ba” Lkci daya ta hade rai, yace “Shi wannan din yaushe ya fara aiki har kika fara samun matsala da shi Nihad?” Kin cewa komai tayi, yace “Ki min magana ko in kashe wayata” Murya can ciki ciki tace “Sallah xan yi” Katse wayar yayi, ta jefar da nata wayar, wato nobody is even supporting her, then xata dau action da kanta. Tana kwance bayan tayi wanka tayi sallah wayarta ya fara ring, ta jawo wayar ganin number da ke kiranta ta mike zaune ta daga tana wara ido tace “Shine baka ce min xaka dawo ba bayan ko jiya mun yi magana” Yace “How are you?” Ta lumshe ido tace “I am fine, ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, yaushe za mu hadu? I will be leaving for Abuja next tomorrow” Tace “Wai yau kake nufi xa mu hadu?” Yace “Toh shikenan tunda ba yau ba” Da sauri tace “Noo ba haka nake nufi ba, i only asked, okay yanxu xan shirya in fito in sha Allah” Yace “Where are we meeting?” Tace “U suggest” Yace “How about Royal park…” A hankali tace “Kasan fa an canza mana driver” Yace “Ohh really, when?” Tace “Kwanan nan” Yace “So u are not use to the new one ko?” Ta taɓe baki tace “Aa wannan dan rainin hankali ne, i don’t think we can eva get use to each other” Yace “To yanxu ya za mu yi? Sbda ke na sauka kano fa” Tace “For now pls mu hadu ko a wellcare ne, dama xan ɗan yi shopping…” Yace “Nahh, baxan iya fita don kawai in je wellcare ba, kina nufin a tsaye xan ganki sannan mu rabu?” Tace “No pls, after today i will plan where we will be meeting, ba kace next tomorrow xaka koma ba” Yace “Karfe nawa xa ki wellcare din?” Tace “Kawai shiryawa xan yi yanxu” Yace “Drivern ne zai kawo ki?” Tace “To ya xan yi shi din xai kawo ni, dama kuma Abba ya bani kudin shopping kawai dai ban je nayi ba ne har ynxu” Yace “Okay idan xa ki fito ki kirani” Tace “Tohm, i will call you” Daga haka ya katse wayar. Sosai taji xuciyarta yayi sanyi duk wani bacin rai dake tare da ita ta nema ta rasa kawai muryarsa da ta ji. Bayan ta shirya ta fito ta tafi bangaren Mumy, Tana tsaye a parlon tace “Abba ya turo min kudin shopping, cream dina da sabulu sun kare, ina son xan je in siya yanxu, sai driver yayi dropping dina a can” Mumy tace “Gobe Nihal xata je shopping xata koma makaranta, sai ki bari ku tafi tare” Nihad da gabanta ya fadi tace “Mumy bani da cream din da xan shafa ne fa, let me get even if it’s just the cream today idan ya so goben sai mu je tare, ina gama siyan cream din xa mu dawo gida” Mumy tace “Allah ya tsare, sannan kuma ki yi masa abinda kika saba, ki tabbatar tare xa ku dawo gidan nan da shi” Nihad dai bata ce komai ba ta juya ta bude kofar dakin sannan ta fita. Tana fita compound taga bata ga drivern ba, ta tambayi mai gadi yace “Yanxun nan ya bar nan, ya shiga can bangarensu…. ” Chalet din ta nufa, ta hangosa zaune saman matakalan dake wajen waya kare a kunnensa, yana hangota ya katse wayar kuma ya ki kallonta, ta karaso babu yabo bbu fallasa tace “Hey idan ka ga dama zaka ajiyeni a well care yanxu yanxu” tana fadin haka ta juya ta bar wajen. Da ido ya bi ta, sai kuma ya mike ya ciro makullin a aljihunsa ya bi bayanta, tana tsaye compound din ta kira Aliyu, ta sanar masa gata nan xata fito, bayan ta gama wayar ta karasa ta shiga bayan motar, sai da suka hau saman titi sannan yace “Kwatance xa ki yi” Ta hade rai tace “Kai ko ina sai kace baka sani ba sai an maka kwatance, baka da Google map ne??” Yace “Ban da” Tsaki ta ja, haka ta dinga gwada masa inda xa su bi har suka iso well care, parking yayi a space da ake parking din, tayi dialing number Aliyu, yana dagawa tace “Are u inside?” Waige waige ta fara yi jin abinda yace, tace “I am also outside, where did u park?” Sauke glass tayi, lkci daya ta hangosa, murmushinsa me kyau ya sakar mata yana kallonta, xata katse wayar yayi saurin cewa “Waitt” sai ta fasa kashewa tana sauraronsa, yace “What if idan an ɗan basa wani abu mu ce ya jira mu a nan, mu je eatry… i am jet hungry” Rasa abinda xata ce masa tayi, don ta ce ma Mumy baxata dade ba, can ta saci kallon Khalil ta ga idonsa a kan Aliyu yake ko kiftawa bai yi, duk da glass din a dage yake, kuma tinted ne ba me duhu can ba, a ranta tace wannan ma yayi kama da wanda xai amshi abu idan an basa, bude motar tayi ta sauka ta nufi inda Aliyu yake, shi dai Khalil bai daina kallon Aliyu ba kamar ya ga wani halitta na daban, tana karasawa gun motar Aliyu dake ta kallonta underneath his breathe yace “Waow, baby kin kara kyau fa, tell me what is d secret” Tayi masa murmushi wanda har dimple dinta sai da ya lotsa, sauke idonsa yayi kasa, can ya zaro dollar 100 a aljihunsa yace “In bashi wannan ya jira mu a nan?” Tana kallon kudin tace “Toh kasan dai ba wai mun saba da shi bane, snn bashi da kirki fa wllh” Aliyu yace “Kudi ne baki fara basa ba shi yasa baku saba ba, yana ganin wannan yanxu xaki ga kun dawo kun dai daita kun saba” Bude motar yayi ya fito, walking majestically ya nufi motar, Nihad ta bi sa da kallo, Waige waige khalil ya fara yi da sauri, as if looking for an alternative kafin Aliyu ya karaso gun motar, lokaci daya kawai yayi locking motar kafin ya iso, Aliyu na karasowa ya bude motar yaji a kulle, kwankwasa glass din motar yayi, Khalil ya kauda kai duk da Aliyun ba ganinsa yake ba, Sau biyu Aliyu na kwankwasawa kafin ya daga kai ya kalli Nihad, ta buda masa hannu alamar i told u dama, mamaki ne ya cika Aliyu ya dinga kallon motar, can ya sake Kwankwasa glass din, tace “Dear just leave him ka bar wajen kawai, ba nace maka ɗan iskan yaro bane” Aliyu da ransa ya gama baci yace “Who did he think he is, da driving din da yake yi ake biyansa yake takama ko me? Waye shi yana matsayin just driver xai kulle mota yana jin ana kwankwasawa ya ki budewa, kuma ba wai bai gan ni bane” Nihad tace “Ai ban ta6a ganin mutum me karfin hali irin yaron nan ba” Aliyu yace “Look Nihad idan kika shiga school gobe xa mu hadu, i can’t stand here any longer, mood dina ya baci seriously, ba a ta6a ci min fuska irin yau ba” Nihad tayi shiru tana kallonsa duk jikinta yayi sanyi, don kana ganinsa kasan ransa yayi mugun baci da gaske, tafiya ya fara yi kawai ya koma gun motarsa ya shiga ya tada yayi zoom off, da ido khalil ya bi sa har ya hau saman titi, Nihad ta dinga kallon motar tana jin kamar ta rushe da kuka ko xata ji sauki a ranta, mutumin da tayi wata da watanni bata gani ba, shine wannan drivern xai 6ata ma rai har ya tafi?? Ta fi minti biyu tsaye kawai kallon motar take with different thought running her mind ga wani kullutu da ya tokareta a makogwaro sbda bakin ciki da takaici, a duk abubuwan da yake mata bata jin akwai wanda ya mata ciwo ya ta6a har karshen xuciyarta irin wannan, she is trying her best not to cry, don har idonta ya cicciko, kiris ya rage ta fashe da kuka a wajen, Khalil dake ta kallon duk expression da reaction dinta ya shafa kansa, sai kuma ya sauke both glasses yace “Naga kamar kin fasa siyayyan, kuma ga hadari, ni kuma bana tuki cikin ruwa ko in baki makullin in yi tafiyata??” Wani matsiyacin shegen kallo tayi masa, ta bude back seat ta shige motar ta kulle da karfi tana kara danne kukan dake cin ta, tada motar yayi, yayi reverse ya dau hanyar gida, har suka isa gida Nihad danna kukanta take, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta tafi gun driver seat ta tsaya tana nunasa da yatsa tana huci tace “Sai kayi da ka sanin abinda kayi min yau wllh, kuma ni ce sanadin barin ka gidan nan, banza mahaukaci kawai talaka” Kashe motar yayi ya sauka yana kallonta ya kara mata kunne gaba yace “Kamar kina magana?” Da wani bakin ciki ya mamayeta bata san sanda ta cakumo kwalarsa ba duk da uban tsayinsa tsaurin idonta bai sa taga hakan ba, tana jijjigasa da duk karfinta hade da kunduma masa wani mummunan zagi, mai gadi dake ganin komai ya karaso da gudu jikinsa na bari yana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Subhanallahi… ” Khalil dai kallonta kawai yake baya ko kiftawa, cikin nutsuwa yace “Cika ni” Ta buga wani uban tsawa tana dungure masa goshi tace “An ki a cika ka din, kayi uban da xaka yi in ga, kai har ka isa kana aiki ƙarƙashinmu kana matsayin Drivern gidanmu ka dinga kawo min raini? Ni ce ma zaka raina? Kasan wa ka walakanta daxu?? To wllh ko kaff zuri’arka xa a siyar idan har Aliyu ya daureka kudin da aka siyesu bai isa yayi bailing dinka ba” Nihal ta fito cikin gida da kawarta xata mata rakiya ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri xata ta janye Nihad tace “Nihad what’s this u are doing, don’t u have manners? Meye wannan kike yi?” Nihad na huci ta bangajeta a fusace tace “Eh ban da shi, sai ki ara min naki ke me shi, a kan matsiyacin nan xaki ce min bani da manner, kin san abinda yayi min ne?” Nihal na kallon Khalil cike da damuwa tace “Don Allah kayi hakuri” Yana warware rigarsa da Nihad ta cakuikuye yace “Ba komai… fita xa ki yi ne?” Nihal dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, yace “Ko ba fita xa ki yi ba?” tace “Aa Kawata xan raka bakin titi” ya kalli kawartata dake tsaye ita ma tana kallon abun mamaki, yace “Ohk to, ta hau sai na ajiyeta a gida, xan jira ta a waje….” Yana fadin haka ya koma motar ya tada ya bar wajen, mai gadi ya tafi da sauri ya bude gate, Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ba, da hanzari ta shige cikin gida tana kuka sosai. Bayan ta ci kukanta me isarta ta dau wayarta ta kira Aliyu, har ya katse bai daga ba, ta kuma kiransa nan ma no response, hawaye ne ya dinga sauka idonta, bayan kusan awa daya ta mike ta gyara idonta ta fita, bangaren Mumy ta tafi sai taga kamar tana da bakuwa, hakan ya sa ta bar wajen ta tafi gun Umma, Umma tace “Lafiya me ya sami idonki Nihad?” Cikin rawan murya tace “Umma Aliyu ne ya dawo shine muka yi da shi xa mu hadu a wellcare, bayan mun hadu sai ya sauko daga motarsa yace bari su gaisa da driver ai ko in gaya maki mutumin nan yayi masa walakanci mafi muni, ya kulle motar ya kuma ki ya sauke glass, banda Abba da ya ja mana ina Driver xai ma tsaya same place inda nake balle Aliyu? Yasan waye uban Aliyu a kasar nan, kaskantar da kansa fa yayi ya tafi su gaisa maimakon shi drivern ya sauko ya taho har inda yake ya gaishesa amma ya masa wannan mugun walakancin” Umma dai sakin baki tayi tana kallon Nihad, can tayi kasa da murya tace “Wai har yanzu kuna tare da Aliyun nan ne dama?” Nihad ta gyada mata kai tana matsar kwalla, Umma tace “Ba kince min kun rabu ba kwanaki?” Nihad tace “We came back together 1 month ago” Umma tace “Ke dai bakya ji Nihad nace ki fita harkan yaron nan, ba mutunci ne da familynsu ba kin ki, nace ki rabu da shi in kina son sama ma kanki mutunci kina son ki tsira da mutuncin ki, ina ke ina Aliyu banda dai yaudaran kai Nihad? Kika san wasu irin yan mata yake hulda da? ‘ya yan shugaban kasa yake hulda da fa” Nihad taki cewa, Umma tace “Gaskiya kar ki sake kulasa ni dai na gaya maki, yana son ki ne ko sau daya bai ta6a takowa ya xo gidanku ba? Sai dai soyayya a titi da makaranta, kema kinsan yaudaran kanki kike don Aliyu ya fi karfin ki, me ma xai kawosa gidan nan? waye ubanki a inda ubansa yake, inaa ai nisan ma yayi yawa, balle ma duk yan iska ne yaran masu kudin nan wa enda idonsu ya yage har kunne, banda lalata yara da bata masu rayuwa babu abinda suke” Nihad still ta ki cewa komai, Umma tace “Kin min alkawarin xa ki rabu da shi kiyi blocking dinsa kamar yanda kika yi blocking din Ahmad yanxu?” Nihad ta turo baki tace “Ni dai ina sonsa Umma, shi ma kuma yana so na ai, da baya so na baxai dinga kirana ba har yace mu hadu a wani waje, dama ce maki xanyi xan je gidansu Baffa ko da Mumy ta tambayeni” Daga haka tayi ficewarta daga parlon Umma ta bi ta da ido ko kiftawa babu, Nihad na sauka downstairs ta fito compound, fuskar nan nata a murtuke ta nufi gate, mai gadi dai ya kauda kai da sauri don tare suke da Khalil, shi dai ya rasa kan wannan abinda ke faruwa tsakaninta da Khalil, yana mugun ganin karfin halin Khalil da baya nuna shakkarta kamar su, har ta fita gate ta dawo tana kallon mai gadi fuskar nan nata babu rahama tace “Kai in ji dai kuna kula min da tsuntsaye na? Don idan har wani abu ya samesu wllh kaf gidan nan duk sai kun raina kanku ban cire kowa ba kuma” Da ladabi yace “Ko daxu sai da naje can da kaina Hajiya” Ficewa tayi daga gate din bayan ta maka ma khalil da bai ma san tana yi ba harara, Mai gadi ya kalli khalil yace “Sai fargaba nake kar tace xaka kai ta wani waje” Khalil yayi murmushi yace “Meye a ciki, sai a kai ta ai…” Da yake babu wani nisa da kafa Nihad ta bi ta cikin anguwanni har ta isa gidan yayan Abbanta, Hamid na xaune compound tare da wani abokinsa, kallo daya tayi masu ta kara gaba abunta, Abokin nasa yace “Wannan ba cousin din nan taka bace, naga ta wuce bata ce maka komai ba, and kamar kuna good time da ita ai” Hamid yace “Noo, step sisters dinta ne muke good time, wannan ai yar iska ce” Abokin yace “Shit but sun yi kama sosai, kamar har ya wuce misali” Hamid yace “Toh wannan da kake gani ji take da girman kai da rainin wayo, sannan runz girl ce…” Abokin ya wara ido yace “Waow dai dai mu kenan, ka hadu mu to” Hamid ya masa wani shegen kallo yace “Ai da manyan mata ake runz ba kwailaye ba, kwailar ma fitsararriya irin wannan” Tuni Nihad ta shige gidan, direct part din Kakarta ta nufa, tana bude kofar dakin ta shiga, inna tace “Aa, daga ina haka, Ibrahim din ya shigo ne” Nihad tace “Ni kadai ce” Inna tace “Aa naga sai ya taso keyarki kike xuwa shi sa abun ya daure min kai, ina ce tare ku ke” Nihad ta nemi waje ta xauna, Inna tace “Baki da lafiya ne?” Nihad ta fashe da kuka kamar jira take tace “Inna wani sabon driver Abba ya dauka, yaron ba shi da kunya ya raina ni inna, ba irin rashin mutuncin da baya min” Inna da ta saki baki tace “Shi Dreban?” Nihad ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Inna tace “Ko ba wani gansameme ba yana tafiya gansan gansan?” Nihad tace “Shi” Inna tace “Toh ai Ibrahim din ya kawo sa har nan ya gaisheni, amma ni na xata ɗan arxiki ne, don har kasa ya duka ya gaida ni” Nihad tace “Wllh na munafurci ne….” Nan ta labarta ma inna abinda ya faru kamar yanda ta gaya ma Umma, Inna tace “Ba lafiya, shi dreban??”

 

07087865788✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button