Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 37

Sponsored Links

37*

 

“ke har yanzu baki girma da haye min cinya bane?”mummy ta faɗi tana shafa kan zahra.

Related Articles

Dariya tayi sannan ta ƙara gyara kwanciyar tata,tace cikin shagwaɓa”kai mummy,nawa nike gaba ɗaya na,naga har yaya ma hawa yake wani lokacin”

“ay duk kun dena hawamin,ku kawomin jikokina su hau”mummy ta faɗi cikin nishaɗi.

Shuru zahra tayi,batace komai ba se murmushi.dan batun ya bata kunya.

Suna nan zaune a falon daddy ya shigo falon se ƙamshin turare yake irin nasu na manya,yana ganin zahra yace cikim fara’a “yau ,zahran tawace agidan nan ah lalle mina da babbar baƙuwa”

Zahra wacce tun shigowarshi data shaƙi ƙamshin turarenshi zuciyarta ta fara tashi daurewa kawai takeyi,

Guri daddy ya samu ya zauna,sakkowa zahra tayi domin gaisheshi,amma ina aman daya yunƙuro mata be bata damar yin hakan ba.

Tuni ta gama ɓata gurin da aman,hankalin mummy da daddy ne yayi mugun tashi,mummy riƙe take da ita,daddy na jero mata tambaya”zahra me ya sameki dama baki da lafiya ne?”zahra ba baka se ido,ga wani sabon yunƙurin aman tanayi,

Kamata mummy tayi ta kaita ɗakinta,kai tsaye ruwan wanka ta haɗa mata,ta rakata har toilet ɗin ta rufo mata ƙofar.

Masu ayki mummy tasa suka gyara gurin,daddy kuma ɗakinshi ya wuce yayo wanka,yasako jallabiya sannan yadawo ɗakin mummyn.

Ay yana shigowa zahra taji ƙamshin turaren da gudu ta kuma komawa banɗakin,ta fara kyalaya amai,bin ta mummy tayi da sauri,ta riƙeta har ta gama,ta wanke mata baki da fuska,sannan ta kamota da nufin su fito.

Cogewa tayi a toilet ɗin ta marairaice fuska tace “mummy ki barni anan turaren daddy ne bana son ƙamshin shi,shine yake sani aman nan”

Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar mummy wanda rabonta da jinshi tun lokacin data samu cikin surayya,wanda har a fuskarta seda ya bayyana.

Sakinta tayi ta fito bakinta a washe,daddy dake zaune zaman jiran fitowarsu kallon rashin fahimta yake mata, yace”hajiya ina ɗiyar tawa kika barota kikazo nan kina min dariya?”daddy yayi tambayar cikin ɗaurin kai.
Dariya mummy tayi sannan tace”Alhaji to ay kai jikan naka kaine baya yi dakai,dan turarenka ne ke sawa yake wahalar maka da ƴar taka”

Janyota yayi jikinshi,yana murmushi yace cike da faraa”kina nufin zahra ta cikine da ita?”gyaɗa mishi kai tayi tana dariya.

Rungume mummy yayi cike da faraa,yana sumbatarta a goshi yace”tukuicin wannan albishir hajiya,zan sauya miki mota”

Sosai mummy ke godiya,daga haka sakin ta yayi yabar ɗakin,fanka mummy ta kunna,ta buɗe windows,turaren yagama fita,sannan ta kashe fankar ta kullo windunan,ta koma toilet ɗin ta kamota suka fito,ta kwantar da ita akan gado.

Abinci mummy tasa aka kawo mata taci,tasha ruwa,sannan mummy ta ɗibi jininta sannan ta bata ƴat kwalba tayi fitsari aciki .
ɗakin data ware a mazaunin asibitin tafi da gidanka ta nufa,taje ta gwada komai dan ta tabbatar da hasashenta,ayko sakamako na fitowa cikinne.

Sosai mummy ke godiya ga Allah daya ara mata tsawon rai na ganin wannan lokaci.

Hammad ko nacan cikin abokai anata chapter,jikinshi ne yaji be masa daɗi kewar matarshi duk ta dameshi,hakanne yasa yayi musu sallama gefin magriba,ya tuƙo motarshi zuwa gidan iyayen nasa.

Muje zuwa

 

Surbajo for life.
[1/7, 12:29 PM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*SHIMFIƊAR AURENA,na fara posting free page,wanda zanyi daga ɗaya zuwa page 15 duka free,kiyi ƙoƙarin biyan kuɗinki akan kari,kar ayi babu ke,ze nishaɗantar,faɗakar,wa’azantar,daku masu karatu,shikaɗai ne irinsa beda na biyu, shi ɗin na musamman ne 500 kacal*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 a turo shaidar biya tanan*

*masu tambayar ta littafi,ko sabo ko tsoho shima ki biya 500 din zan turo miki,masu cewa insasu a group shima ki biya 500 ɗin zan saki😊*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button