Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 34

Sponsored Links

Arewabooks;hafsatrano

Page 34

***Driving yake cike da nishadin kasancewar su tare, a hankali yake tukin yana rik’e da hannun ta cikin nasa ya dora shi saman gear har suka karasa gidan. Gate din aka bude musu suka shiga ya samu gefe yayi parking sannan ya zare seatbelt din yana kallon ta.

Related Articles

“Kinyi kyau.” Ya sake maimaita mata a karo na barkatai yana jin kamar suyi ta tafiya a haka daga shi sai ita yana jin kusancin ta sosai a tattare dashi.
Tare suka fito daga motar ya zagaya side din da take yana gyara mata veil dinta sannan ya kama hannun ta suka wuce ciki. main living room din suka wuce dan yasan a chan zai samu Mummy idan yaso bayan sun yi sallar sai yaje yaga AJIn. ce ta fara ganin su sanda suka shigo ta fito falon da gudu ta koma ta shige dakin ta,ta rufo dan bata son haduwa da Rafeeq din. Ya ganta sarai amma sai ya dauke kai suka karasa shigowa ya nuna mata wajen zama ta zauna yace mata yana zuwa. Part din su ya wuce ya shiga dakin sa ya duba wasu takardun sa dan kar ya manta sannan ya dauki sim pack da international passport dinsa ya fito.
Yana fitowa mummy na shigowa itama suka hadu, wani kallo tayi masa kafin tace

“Kun karaso kenan.”

“Eh mun karaso.”

“Yayi, ina surukar tawa, ko ka kasa fitowa da ita saboda kana kunyar nunawa mahaifin ku ita ne?”

“Akan me? Matar da kika zaba min da kanki? Idan ma wani abu ne ai ke zai tuhuma,tunda ke kika shirya komai.”

“Sai ki shirya amsar da zaki bashi.”

Sai yayi gaba kawai ya barta a wajen mamakin maganganun sa sun haanata motsawa. Da kyar ta daure wa zuciyar ta, ta bi bayan sa zuwa falon ta same shi tsaye a gaban Noor din yana mata magana.

“Surukata.”

“Ina wuni?”

Tace tana daga zaune bata motsa ba, bare ta sauka kasa ko ta nuna tsorata kamar yadda take a baya. Wani dan jim Mummyn tayi kafin ta masa tana zama kawai

“Ashe tare kuke, na dauka ai ya barki gida.”

Murmushi kawai Noor din tayi bata ce komai ba , shine yace

“Ina Aneesa?” Yana duban mummy din

“Tana dakin ta, kasan ta sarkin zaman daki.”

“Taso.” Ya mika mata hannu ta kama tana dakewa suka wuce zuwa dakin Aneesa. Knocking yayi ta taso ta bude ganin shine tayi saurin juyawa amma sai ya rikota da sauri yana murmushi

“Ga amanata nan, zatayi sallah kuma wallahi ko kallon banza kikayi mata sai kin gane baki da wayo.”

“Allah ba zan ba Yaa, shigo.”

“Shiga kiyi sallah, zanje nayi sallah na dawo nima.”

“Ok.”

Tace ta shiga shi kuma ya juya ya fice ko kallon in da Mummyn take zaune bakin ta bude ta rasa abun yi.
Toilet Aneesa ta nuna mata, ta shiga tayi alwala ta fito ta samu ta shinfida mata abun sallah da hijab akai, dauka tayi ta tada sallar ita kuma ta fice daga dakin. Bayan ta idar ta ninke komai ta ajiye mata a gefe sannan ta yafa veil dinta ta bude kofar ta fito. Ita kadai ce kwance a cikin kujerun falon sai Noor din ta samu waje ta zauna babu wadda tayi ma wata magana a ciki ita Aneesa tana jin tafi karfi ita kuma rashin sabo da fuska ya hanata ce mata komai.
Suna zaune shiru wayarta tayi kara, dagawa tayi tana karata a kunnenta abinda ya bawa Aneesa damar ganin wayar sosai ta bude baki da mamaki tana kallon hannun Noor din. 15promax? Yaushe har yar talakawa ta kai rik’e waya kamar wannan? Ko ita 14 ce a hannun ta, tana taso ta chanja Mummy tace mata ta bari a kwana biyu amma shine yar talakawa zata yi ta ita tana zaune. Tashi Noor din tayi bayan ta amsa wayar tasa yace mata ta fito compound din ta same shi.

“Waye ya baki wayar nan?”

Aneesa da ta kasa hakuri ta tambaye ta tana tashi zaune.

“Mijina, ko kina da matsala da hakan ne?”

“Miji, miji? Ya Rafeeq?”

“Akwai wani bayan shi ne?”

“Lafiya na ganku a tsaye Neesa?”

“Mummy kalli hannun yarinyar nan, 15promax fa! Na tambaye ta waye ya siya mata wai har tana da gut din ce min mijinta.”

“Miji? Ah lallai yarinyar nan, wuyanki ya Isa yanka.”

“Mummy wallahi duk laifin ki ne, ke kika bata wannan matsayi gashi tana nemar zaman maki karfen kafa.”

“Barta, zanyi maganin su dukkan su.”

Ficewar ta, tayi ta barsu tsaye dan takaici, kukan bakin ciki Aneesa tasawa mummy tana bubbuga kafa ita ma dole a chanja mata waya a ranar. Takaici ya hana Mummy magana kawai tabi bayan Noor din dan tana so duk abinda AJIn zai yi yayi a gabanta.
A compound ta same shi jingine da mota yana amsa waya , kusa dashi ta tsaya tana jiran ya gama, sai da ya kai karshe sannan ya katse yana mata kallon tsaf sannan yace

“Kin shirya?”

“Me zamuyi?”

“Wajen AJI zamu je, yace yana son ganin wadda ta sace zuciyar dansa.”

Rufe fuska tayi tana dariya.

“Emana,baki yarda ba?”

“Ni yaushe na sace maka zuciya?”

“Muga?” Ya daga hannun sa kamar me lissafi sannan yace

“Shekarun da yawa, tun kina yar ficika.”

“Ni din?”

“Da gaske, zan baki labari but ba yanzu ba, yanzu muje kafin ya sake kira kinsan AJI baya son delay.”

“Ni tsoro nake ji.”

“I’m with you, kar kiji tsoron komai.”

“Tam.” Ta gid’a kanta.

Ta zata tunda yace wajen AJI zasu, ba zai rik’e hannun ta ba amma sai taga ya kama hannun ya rik’e gamgam, har suka dangana da sashen AJIn da ya kusan fin kowanne part a gidan girma da tsaruwa. A kofar ta cije ta kwace hannun ta,dan ta lura idan ta biye masa zai iya kunyata ta, ita ko zaman da tayi a gidan bata taba ganin me gidan ba, shiyasa yanxu ta cika da tsoron yarda zai karbe ta, addua duk wacce tazo bakin ta, ta dinga yi har suka kutsa falukan sa biyu suka isa babban falon in da yake zama da family dinsa idan bukatar hakan ta taso.
Yana hakimce a kan wani lallausan carpet ya kishingid’a akan tuntum yana kallon new a aljazeera sannan gefen sa bakin shayi ne da yasha kayan kamshi yana ta tururi. Yana jin sanda suka shigo ya amsa sallamar amma be dago ba har suka karaso suka zube gaba daya a kasan.

“Barka da dare AJI.”

Sai a sannan ya dan kalle su kadan sannan ya amsa

“Barkaa.”

Cikin dakiya ta tattaro yan kalmonin ta gaishe shi a ladafce tana kankan da kanta.

“Kuna lafiya? Ya bakunta?”

“Alhamdullillah Baba.”

“Madallah, komai lafiya dai ko?”

“Lafiya lou Alhamdullillah.”

“Toh toh, Masha Allah.”

“Naje office din dazu na duba ayyukan.”

Shigowa Mummy tayi, hakan ya hana aji bawa Rafeeq din amsar maganar sa. Tare take da yan aiki biyu dauke da tray manya suka ajiye sannan suka fice da sauri.

“Wannan kayan duk a chan ya kamata ki sauki bakuwar taki ai.”

“Naga suna ta sauri sauri suzo wajen ka ne, shiyasa.”

“‘Yar tawa me kunya ce, ba zata iya sakewa anan ba, ki dauke ta ku koma ciki, zanyi magana da shi.”

Zafi goma da ashirin, ba a son ranta ba, ta mike Noor din ma ta tashi tabi bayan ta suka bi wani hallway suka koma part din su Mummy din.

Suna fita ya maida kallon sa wajen Rafeeq din yana mikewa zaune sosai

“Ganin da nayi wa yarinyar nan sai ta tuna min da mahaifiyar ka, haka take da kunya.”

“Uhmm.”

“Nayi bincike na gano Alhaji Isma’il bashi da yarinya mace kamar ta, yaransa dukka maza ne. Tun farko ban gamsu da karbar ragamar auren ka da babarku tayi ba, haka kawai naji hankali na be kwanta ba dan duk abinda take yi ina sane. Wato ni mutum ne me matukar saka ido a duk harkokin gidan na, ina sane da duk wasu al’amura dake faruwa dan haka ne ma na saka akayi min bincike, har na gano komai na kuma kara yarda da shiri ne ta shirya maka, cikin rashin sani itace yarinyar da ka dade kana bibiyar rayuwar ta, ina katse ka. Ni da kaina nasa aka tashe su daga ainihin gidan su, suka koma wani shima na saka akayi ma mahaifin ta sharrin da ya raba shi da kowa. Duk dan ina ganin baka dace da ita ba, kuma soyayyar da kake mata tayi yawa zata hana ka cika min buri na dana saka a raina. Bahaushe yace ba’a wa Allah wayo, sai Allah yaa barmu da halin mu ya kuma nuna mana ikonSa, a lokacin da muke ganin mun isa da mu yi duk abinda muke.”

“Haka ne.”

“Halinka na kwarai ka cigaba da shi, ka kuma rike matar ka da kyau kar kayi wasa da zuciyar ta, har kazo ka rasata kamar yadda na rasa mahaifiyar ka rashin na har abadah.”

“Nagode Allah ya saka da Alkhairi, in sha Allahu zanyi abinda ya dace.”

“Na sani bana jinka, Allah yayi muku albarka.”

“Amin.” Ya amsa yana dukar da kansa, wani irin yanayi mara misaltuwa ya dinga shigar sa, a yau ya tabbatar da waye AJI, ya kuma gane kalar rayuwar sa da yadda yake gudanar da abubuwan sa. Tunda ya taso yake ganin kamar yana takure shi da yawa, yana matsa masa fiye da Asim da Aneesa. Sai a yanzu ya gane gata yayi masa, hakan yasa ya zama jajirtacce, ya zama managarci me cike da tarin hikimomi da sanin ya kamata, ashe taimakon sa yayi, ashe gina rayuwar sa yayi dan da ace ya nuna masa kauna a baya da tabbas Mummy ba zata taba barin sa ya kai yadda yake a yanzu ba.

***Kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna haka ya baro sashen AJIn cike da farin ciki. Ita kadai ya samu a falon tana kallon TV, zama yayi a daf da ita yana kallon agogon dake manne a jikin bangon falon, tara har da rabi, gida kawai zasu wuce sa je gidan Baban daga baya ko gobe

“Ke kadai?”

“Umm.” Ta bashi amsar a gajarce zuciyar ta babu dadi saboda maganganun da mummy ta gaggaya mata, tun dazu take son yin kuka amma tana daurewa shiyasa ta kafawa tv din ido tana kallo sai gashi ya shigo, tana ganin sa sai taji son yin kukan amma ta daure tana kin hada ido dashi. Ya lura akwai damuwa ya kuma dama san Mummy sai ta mata abinda zai bata mata rai tunda baya wajen. Juyo ta yayi suna fuskantar juna idon ta da ya ciko da kwalla tayi saurin maida ta amma ya gani.

“Kuka? Me ya faru?”

“Ba komai, kamar bacci nake ji amma.”

“Ba wani, gashi nan.”

Ya nuna mata idon ta. Kamar wanda aka tunkudo haka hawayen suka sakko tayi baya yayi saurin rikota ya rungime ta yana bubbuga bayanta

“Ki bari muje gida please, karki kuka nan.”

“Na kasa rikewa ne.”

“Tashi toh.” Ya dagata tsaye sannan yasa hannun sa yana goge mata hawayen da ya zubo.

“A ah kalou? Kun gama da baban naku ne?”

“Bana son kina zubar da hawayen ki me tsada akan mutanen da basu dace ba, mutanen da basu san komai ba sai son kansu, so karki sake please. Bana son gani.”

Gid’a masa kai tayi tana share hawayen da bayan hannun ta itama, ta goge sannan tayi murmushi shima ya maida mata

“Good, be strong.”

“Zamu wuce, AJI yana son ganin ki.”

“Sai ka gama wulakancin da mace sannan zaka gaya min kiran da yake min, wai Rafeeq yaushe ka lalace haka ne wai ni? Ko duk dan ka bakanta min rai shine zaka saka yarinya ta raina ni? Idan wannan abubuwan zaku dinga yi a ko ina ai sai ku zauna a gida ku cinye kanku.”

“Mu kwana lafiya.”

Yaja hannun ta suka fice kawai. Kicibis sukayi da Asim dawowar sa gidan kenan duk bashi da walwala tun abinda ya faru gashi ya dauki wani tunani ya dorawa kansa gaba daya rayuwar bata masa dadi. Da gaske yake son ta dan be gane haka ba sai da ya tabbatar ya rasata.

“Asim…” Rafeeq ya kira shi ganin ya dauke kai zai wuce su. Be tsaya ba bare ya saka ran zai amsa, sai sauri ma da ya kara ya shige yana jin zuciyar sa kamar zata hudo ta fado ta cikin kirjin sa. Wani irin zafi da suya da yaji tana yi masa, yana shiga yayi saurin wucewa zuwa dakin sa, Mummy na kiran sa amma yayi kamar be ji ba itama ya shige. Da sauri tabi bayansa tana kwala masa kira dan ta tabbatar sun hadu da Rafeeq ne a waje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button