Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 9

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA

Page 9

Arewabooks; Hafsatrano

Related Articles

****Sai da ta fara lekowa ta tabbatar babu kowa sannan ta fito ta jawo kofar kawai cikin sauri sauri tayi hanyar fita cike da tsoro da fargaba.
A tsaye yake kusa da gateman ya bada bayansa yana masa maganar wajen da yaga yayi ciyawa sosai yana so a gyara, saurin da take ya hana ta lura da mutane biyu ne har sai da ta karaso gate din sannan ta lura da wanda ke tsaye. Da sauri ta juya da nufin komawa daidai lokacin ya juya jin tafiya a bayan su.

“Dakata.”

Ya tsaida ta ganin ta juya zata koma, tsayawa tayi chak, bata juyo ba amma ta runtse idon ta kaman ta saki fitsari a wando. Takowa ya shiga yi hakan ya kara mata wani irin tsoro ta sake damke idonta sosai.
Wani irin daukewa numfashi sa yayi cikin yan dakikun da basu wuce biyu ba, runtse idon sa yayi ya bude su akanta, ba mafarki yake ba, still dai itace a tsaye a gaban sa.

_”how comes.”_ ya furta cikin madaukakin mamaki. Jin yayi shiru yasa ta bude idon ta dake kulle taga dalilin yin shirun nasa. Yadda yake kallon ta ne ya bata mamaki, da sauri ta durkusa kasa a tunanin ta ya gano abinda take shirin yi ne.

“Don’t, please.” Yace da sauri.

“Tashi, get up.”

Ya sake fada yana kallon ta fuskar sa na nuna wani irin yanayi. Mikewa tayi tana hade hannayen ta waje daya alamun yayi hakuri. Shi duk bata wannan yake ba, burin sa kawai suyi magana a yanzu. Menene ya kawo ta gidan su, wajen wa tazo kuma me take shirin yi?

“Follow me.” Ya samu kansa da furtawa sannan ya matsa yana nuna mata hanya alamun tayi gaba, ba musu ta wuce gaba ya bi bayanta har suka fice daga gidan, be san me yasa ba, kawai yaji a ransa ba zai sake bari ta kubce masa ba a wannan karon. Suna fita Saddam da driver na jiran su. Da sauri Saddam ya bude masa kofar, ya nuna mata da hannu alamun ta shiga, duk da tashin hankalin da ta shiga amma bata da zabi da ya wuce tabi umarnin sa, dan duk ita tsoron ta kar yaje ya sanar da Hajiya ya kamata zata fita, watakila ma yasan ina zata dan yadda tsaron gidan nan yake komai akace mata zai faru zata yarda.
Shiga tayi ta zauna ya rufe mata kofar da kansa sannan ya zagaya shima ya shiga ta dayan side din suka bar unguwar. Tafiya kawai suke a saman titi babu motsin komai sai yar karar da ac din motar ke bayarwa, wani irin mahaukacin sanyi take bayarwa wanda ya kara saka ta jin ta takura da wata irin fargaba hakan ya sakata matsewa sosai jikin kofar hawayen da ke makale fuskarta ya sauko a hankali zuwa saman kuncin ta. Yana lura da yanayin ta yana son ya gama karantar komai kafin su karasa in da zai ce su tsaya din domin tabbas akwai tambayoyi masu yawan gaske da yake so yayi mata.

“Stop crying, please.”

Muryar sa dake cike da amon sauti me dadin sauraro ta ratsa kunnen ta a daidai lokacin da tasa hannu zata share hawayen. Cigaba tayi da share hawayen wani yana bin wani. Hannu yasa ya bugi gaban motar ransa na baci saboda kukan nata da yake da yakinin yana da nasaba dashi, cikin hanzari yasa hannu ya jawo tissue a gefen motar ya mika mata sannan yace

“Wipe it, bana son kukan nan.”

Yadda muryar sa ta bada sautin yasa ta saurin hadiye kukan duk da bata karbi tissue din ba. Jefar dashi yayi a gefe yana sauke ajiyar zuciya jin tayi shiru dan dama kukan nata ba karamin damun sa yake ba. Daga dan gefen titin yace suyi parking, da sauri sukayi parking Saddam da driver suka fita ya zama sai su biyu a motar. Juyawa yayi gaba daya yana fuskantar ta, wani irin abu me karfin gaske na fizgar sa zuwa gareta, matse hannun sa yayi cikin kasa da muryar yace

“Kin daina kukan?” Da sauri ta gida masa kai sannan tace

“Dan Allah karka koreni, ba zan sake kokarin fita ba wallahi, zan zauna nayi aiki na kawai ba zan sake ba.”

“It’s ok, aikin menene kike? Me yasa ba zaki fita ba? Yaushe kika zo gidan? Dama kin san gidan? Wajen wa kika zo?”

Duk ya jero mata tambayoyin a lokaci daya cikin kaguwa da son sanin komai, kallon sa tayi kadan hakan ya haifar masa da wata irin kasala.

“Ya Allah!” Ya furta a kasan makoshin sa.

Shiru tayi, bata fuskanci komai a tambayar tasa ba, dan ita a tunanin ta yasan komai ne, kila ma gida zai maida ta wajen Baba, shikenan kuma ta rasa aikin ta.

_Na samu labarin tana aiki ne yanzu haka a wani gida, bansan wanne gidan bane ba dai, but zan bincika na gano.”_. Ya tuno da message din da Saddam yayi masa cikin bayanan da ya sashi nemo masa, nan da nan wani tunani ya darsu a zuciyar sa, da sauri yace

“Aiki kike a gidan?”

Kai ta gida masa, sai ya ce

“Aikin me?”

“Dafa abinci.”

“Damn it!” Ya dunkule hannun sa yana jin matsalar na ninkuwa akan wadda yake hange. Aiki take, a karkashin ikon AJI da Mummy.”

“Ya salam, Ya Allah!” Ya sake furtawa yana son daidai ta kansa da nutsuwar sa

“For how long kike aikin?”

“6month.”

“Shit!” Sai ya sake gyara zaman sa sosai yana fuskantar ta fiye da dazu

“Please ki bar aikin nan.” Ya samu kansa da furta mata yana ji da ganin hakan shine kawai mafita. Da sauri ta zaro idon ta, sai ga wani hawayen a jajjere, tasan dama abinda zai ce kenan, zamowa tayi daga kujerar zuwa kasa ta hade hannun ta biyu cikin muryar kuka tace.

“Dan Allah kayi min rai, wallahi aikin shine gata na da na mahaifi na, ba zan sake kokarin taka dokar da Hajiya ta saka min ba, na tuba dan Allah.”

“Tashi ki zauna.” Yace mata yana kawar kansa gefe, kin tashi tayi ta cigaaba da kukan tana rokan sa, abinda ke taba shi sosai har yake neman sashi loosing control nasa, cikin tsawa yace

“Tashi ki zauna!”

Da sauri ta koma ta zauna tana tsayar da kukan. Kiran Saddam yayi yace yazo su tafi zuciyar sa na tafasa. Shogowa sukayi yace su koma gida suka juya ba tare da kowa ya sake cewa komai ba.

***Awa kusan guda Asim yayi a tsaye yana jiran ta, wayarta a kashe tun yana kira yana tunanin zata shiga har ya gaji ya samu wani waje daga road side din ya zauna yana kallon hanya. Tunda yake a rayuwar sa be taba jin a damu da abu irin hakan ba, duk wanda ya wuce sai ya bishi da kallo ko da kuwa a cikin mota ne. Duk jikinsa yayi sanyi gashi ya kasa hakura ya tafi har sai da ya ga da gaske magriba na neman taddoshi a wajen ya hakurar wa zuciyar sa ya koma gida ya shiga part din su ya kwanta kawai zuciyar sa babu dadi.
Yana kwance Aneesa tayi knocking tace yazo Mum na kiran sa, kamar ba zai tashi ba haka dai ya karfafa zuciyar sa dan baya ko san zuwa part din Mummy din idan aka ce Ummita na gari. Tashi yayi jiki a sanyaye ya fito ya iske su a falon Mummy. Be ko kalli side din da suke ba ya wuce ya zauna a gefen Mum din yana marairaice mata fuska.

“Ciwon kan ne?”

“Gajiya ce kawai, sallah zanyi na kwanta na dan huta kafin Isha.”

“Sannu, dama wai system din Ummita ce take so ka duba mata, kaje idan ka huta amjima sai ta kawo maka ka duba matan.”

“Mum, kamar wani me gyaran computer, idan matsala take bata a chanja wata kawai.”

“Ba matsala bace ba fa, dan setting ne zaka mata, ko Ummita?”

“Eh mummy.” Tace tana murmushi.

Mikewa yayi yana zura hannun sa cikin aljihun wandon sa ba tare da yace komai ba, yayi hanyar ficewa daga sashen gaba daya. Sun zata masjid zashi basu san daga nan kawai mota ya dauka ya fice daga gidan ba, baya son alakar dole da Mum take chusa masa da yarinyar wanda ya riga yasan take taken su ita da AJI son hada su suke shi kuwa ko mata sun kare ba abinda zai da ita dan shi sam baya son macen da idonta ya gama wangalewa shiyasa sam baya son yarinyar daga ita har yayartata Laila.

***Yanzun ma tana gabansa yana bayanta har suka iso daidai dakin nata,ja yayi ya tsaya a wajen yana kallon ta, bata juyo ba duk da tasan yana tsaye a wajen tayi saurin shigewa a tunanin ta kar ya chanja raayi yace tazo ta tafi gida. Tana shiga ta zame a kasa ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, kamshin daddadan sanyayyan turaren sa da ya cika mata kofar hanci take ci gaba da shaka har lokacin, ji tayi kamar ma kwaso kamshin tayi saboda yadda take jin shi a ko ina. Tunanin Asim ne ya fado mata, wanda gaba daya ta manta shaf saboda yadda ta shiga firgici. Tashi tayi ta dauko wayar ta dake ajiye kasan pillow ta kunna ta, sai ga text message dinsa ya shigo.

_”Kina ina?”_

_”Gani a wajen.”_

_”please karki ki zuwa.”_

“Please ki bude wayarki.”_

Haka sakonnin suka dinga shigowa a jajjere. Ajiye wayar tayi jiki a sanyaye. Ya zatayi da wannan al’amarin da yake shirin faruwa da ita, idan har ta cigaba da magana dashi dole Hajiya zata gano, kuma tasan karshen zancen, don haka ya zamar mata dole ta nemi hanyar da zata katse duk wata alaka da yake shirin kullawa tsakanin su.

***Masjid Rafeeq ya wuce wanda ke makale a jikin gidan yayi sallah ya dan dauki wasu mintuna yayi tilawar alqurani me girma a ciki sannan ya fito yana duba time din a wayar sa, yayi daidai da lokacin da AJI yace yazo ya same shi. Yana tsaye yana koakrin zura takalmin sa motocin Ajin suka shigo gidan a jajjere. Saukar sa kenan ba kuma in da ya tsaya sai gidan. A wannan dawowar yana da plans da yawa da yake son ganin ya kammala su dan haka ne ma yake da plan din zama sosai har sai ya samu komai ya daidaita.
Jira yayi suka gama parking din sannan ya karasa wajen motar da yasan Ajin na ciki ya tsaya kaman minti daya sannan ya kama kofar ya bude masa. Dattijon da a kalla ya doshi shekaru sittin da doriya ya bayyana a gabansa, rike da sandar sa ta girma dake tare dashi a kowanne lokaci cikin shhigar babbar riga jamfa da wando sai rawani dake kansa irin nadin yan kasar Mali. Idon sa sanye da medicated glass kana ganin sa kaga tsohon dan boko me ji da kudi, mulki da kasaita. Babu in da Rafeeq ya baro shi sai a hasken fata wanda girma da shekaru suka janye wani kaso na AJIn. Babu murmushi ko na digo a fuskar sa sai wani irin kwarjini da cikar haiba da yake dashi wanda anan Rafeeq ya gado shi zam dan ko sau daya mu’amula ta hada ka dashi sai yayi maka kwarjini matuka hakan yasa duk wasu harkokin kasuwancin Ajin Rafeeq din ne dan yana da charisma sosai.

“Barka da zuwa.” Yace yana russunawa cikin matukar girmamawa.

“Barka.”

Yace a gajarce sannan yayi gaba Rafeeq din ya take masa baya yana bin sa a hankali har suka iso kofar glass din da zata sadaka da sashen Ajin dake da wani irin tsari da burgewa.

 

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button