Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 11-12

Sponsored Links

Tunda suka tafi sukabar Asma’u da sakakken baki kallon da Aseem yakeyi Mata ita da Sadiqu shine yafi Bata mamaki da Kuma dalilin zuwansu gdansu ganin ya damqawa Mal Husaini kudine yasata sake maida hankalinsu garesu amma sai taga ya dubeta yayi murmushi yaja motarsa sunbar Mal da kallon kudi cikin mamaki.
Mal Husaini na dagowa suka hada ido da Asma’u yayi saurin sanya kudin cikin hularsa tare da watsa Mata daquwa tayi saurin kawar dakai sukaci gaba da tsinkar furensu ita da Sadiqun ta Saida aka Kira magariba sukayi sallama ya nufi masallaci ita Kuma ta shiga gda ta dauki buta ta shige bayi ta Kama ruwa ta fito ta daura alwala daidai lkcn da taji Mal Husaini na cewa “ni Babu ruwana da inda Zaki Amina gdane saidashi zanyi dole kowacce ta nemi inda zata zauna kafin ayi bikin yarannan ku koma qauye ba Saida nace kada ku kuskura ku haifi Mata ba ku masu kunne qashi kuka haifesu ai gashinan basu kawo kudi ba sun kwamushe muku naku” cafkar kunnen Asma’u yayi yace “ja’ira da kanta tunna zuwa duniya saura naji kince wani Abu baki kamar gdan tsutsa tana tafe kamar allura” itadai tana samu ya sakar Mata kunne sumsum ta shige daki ta tayar da sallah tare da jan bakinta ta tsuke Abu daya ta iya tambaya shine meye ya kawo baqin gdansu? Inna tace Mata. Masu siyan gdansu ne daga haka tayi shiru da bakinta saboda batason subutar baki tasa tayi wata magana don Bata kuskura ta fadawa Inna tsiyar da tayiwa Aseem Shaheed ba.

 

Kwana Asma tayi tana tunanin dalilin da yasa Aseem yakeson siyan gdansu, a daren taci alwashin indai Allah ya hadasu gobe a hanyar makaranta sai taci mutuncinsa yanda zaiji bama ya sha’awar siyan gdan nasu, aikuwa tun asuba ta shirya taja ta zauna tana jiran lkc bakwai daidai ta fice daga gdansu ta nufi gdansu Jiddah suka dunguma suka tafi tana bawa jiddah labarin abinda ya faru jiya na zuwan Aseem gdansu a matsayin Wanda zaisai gdan zaiyi kiwon shanu”
Dariya sosai Jiddah tayi tace “kin gamu da qarfen qafa me wuyar kwancewa wato gayen nan ya shiryawa wasan so yake ya qure malejinki ya wulaqantaki Kinga idan ya siye gdanku ko haya ya baku ai babanku ya koma qarqashinsa balle ma tashinku zaiyi a wulaqance ya zuba shanu a gdan Kinga ya nuna Miki rayuwar shanunsa tafi taku muhimmanci. Nifa dama bangano Miki nasara a buga wasa da wannan mutumin ba da ganinsa kinsan yaci yatada Kai zai iya ramawa wulaqancin da zakiyi Masa ta duk inda yaso gara dai yan gujaru gujarun da muke tsokana Basu da yanda zasuyi damu sai tsaki sai harara”

Related Articles

 

Har sukaje makarantar Allah be hadasu dashi ba haka ta rinqa Allah Allah a tashi nanma Basu gamu ba taji haushi sosai so batada yanda zatayi dole ta hqr tana zuwa suka nufi islamiyya sai yamma suka dawo liqis dake laraba ce sunyi hadda a dakin zaure suka tarar da Mal Husaini da Mal Bala suna tattaunawa Mal Husaini sai dariya yakesu suka durqushe suka gaishesu da fara’a Mal Bala ya amsa inda Mal Husaini yace “Ina Ma’ulelena zonan dan qaniyarki” gabanta ya fadi tunda dama a tsorace take tana jiran abinda zaije ya dawo.
Matsawa tayi a darare ta zauna tana barin jiki don tasan ba wuya bane Mal ya maketa ba gyaran murya yayi yace “Ina kike Asma’ul Husnah?” Ajiyar zuciya tayi tace “gani Mal” Jinjina Kai yayi yace “yawwa Masha Allah dama wani umarnin gaggawa zan baki Kinga dai a yanda kuka taso a wahale a talauce to ke ki godewa Allah yasoki da arziqi yayi miki ludufi da ludufin da yakewa duk Wanda yaso cikin bayinsa jiya anzo ganin gida Ashe rabon aganki ne dan farin yaron nan Alhajin Birni eh wlh tallahi shine dai bayan sunga gda kinje kin gaishesu yagani yakeso harma yayimin alqawarin idan na bashi aurenki zai barmin gdana Kuma zaiyimin komai na auren Dijangala da Zabba’u keko yace ki cokali bashi buqata, kinji fah inda arziqi yake”

 

Tunda ya fara mgnr ta kafesa da ido cikin mugun tsoro da kaduwa ta gane waye yake nufi domin Zahran ba fari bane Aseem ne fari Anna sai tace “wa…waikace Mal Sadiqun fah?” Wata uwar harara ya buga Mata yace “Sadiqun0 ubanki yo ko Laminu ne uban Sadiqu ya dawo duniya ai bazai hanani cin wannan arziqin ba ke nifa bama shawara nake daku ba dagake har uwarki dama na dauka ke dake kin shafi zamani zakiba da hadin Kai to kema naga qwalluwar yar baqin ciki ce saboda haka tashi ware kauce karna makeki sauna kawai wadda arziqi ke binta tsiya ke dawo da ita baya”
Yana fadin haka ya miqe abinda yasata miqewa itama da gudu tayi cikin gdan tana rushewa da kuka tana cewa “wlh baa isaba bazaa taba cutata a hadani da wannan shegen azzalumin mutumin ba ai bani kadai aka Haifa a gdanba abashi wata Mana saini saboda an rainamin hankali….” Jin takun sawayen Mal Husaini yasata shigewa qarqashin gadon qarfen Inna tana kuka ya shigo dakin yana huci Yana cewa “kajimin mutane yan baqin ciki arziqi yazomin har gda Allah ya amsa addu’a ta Nima nakusa hutawa shine zakuyimin baqin ciki tabdi ai wlh baku isaba wannan aure me hanashi saidai mutuwa idan ma mutuwa zakiyi saidai ki mutu ja’irar yarinya kina tafe kamar ki karye saboda rama yo kika sake kika auri Wannan Dan gadon talaucin da ubansa tunda nasanshi da tàgiya daya nasanshi basai kin qwammace wannan makauniyar uwar taki barinki tayi ba”

 

 

Harya gama sababinsa ya fita Inna batace komai ba sai bayan ya fitane Asma’u ta fito tanata shassheqar kuka Inna tace “wai waye wannan ne daga zuwa Mal ya aminta dashi Babu binkice Babu komi?” Nan Asma’u ta yiwa Inna bayani Inna ta saki salati da sallalami tare da yiwa Allah kirari tace “naga takaina ni aminatu dama akan wannan kwasasshen mutumin Mal yacimin mutunci har Yana cimin alwashin aure Babu fashi aikuwa da fashi don baza’ayi wannan son zuciyar dani ba yaro shekara da shekaru Yana wahala Rana tsaka saboda son abin duniya Mal ya rufe ido yana cima mutane mutumci ai bake kadai ya haifaba yabasa wata Amma bake ba”

 

Dayin magariba kuwa saiga Kiran Sadiqu a qofar gdansu idanun Ma’u sun kumbura sunyi luhu² saboda kuka ta yafa mayafinta ta fito shima duk a hargitse yake yana ganinta ya riqo hannunta yace “Asma’u meye ne ke Shirin faruwa dazu Baffana yayimin kiran gaggawa naje yake fadamin Wai saqone daga Mal babuni Babu ke yayi miki miji hakanne da gaske Ma’u rabani zaayi dake?”
Kafin ta gama shassheqarta ta dago sukaji daga bayansu muryar Mal Yana cewa “eh hakanne babu Wai a ciki nama rabaku har abada indai nine mahaifin Asma’u to babukai Babu ita nayi Mata miji daidai da ita kaima kaje ka samu daidai dakai dama ai a rashin uwa ake uwar daki tunda uwa tazo kuwa dole uwar daki ta kauce soko kawai me hatimin talauci a goshi”

 

A sanyaye Sadiqu ya tsugunna gaban Mal Husaini yace “Kada kayimin haka Mal wlh idan ka hanani Asma’u kamar ka datsemin farin cikin rayuwa ne ka taimakeni kabarni da Asma’u nayi maka alqawarin Bata farin ciki fiye da Wanda kake hango Mata a Wanda kake Shirin aura Mata Mal baisan darajarta ba kamar yanda na San….”
Tsawa Mal Husaini ya buga Masa yace “kajimin yaro sakarai Shashasha aiyo wato Nima kana nufin kafini sanin darajar Asma’u ko to kaji in fada maka ba daraja ba ko alqabba ne Kai qarewar daraja Asma’u ba rabonka bace, kekuma munafuka na dawo kanki daga yau sai yau idan na qara ganinki da wannan faqirin yaron me riga daya saina Saba miki. Zaki shige gda kosai na karya qafafunki” a guje Asma’u ta fada gda tana kuka inda ta ishe Inna tana sallah fadawa tayi saman gadon qarfen Inna Mal Husaini ya biyota Yana cewa “wato Ni akeson a tozarta a garin nan a mayar dani sakaran uba da Bai Isa da gdansa ba ko to wlh baa isaba dole ne nasa doka abi ke Aminatu kin rainani Ina fada da babbar murya duk ranar dana qara ganin Ma’u da wani a Aseem ba sainaci mutuncinki wlh saikin gwammace baki sanni ba domin ranar ne zaki gane Nima namiji ne talauci ne yasani zama mace wawaye kawai masu qashin tsiya
[20/06 4:30 pm] Oum Hairan: *_ZARRAH_*

 

*_Oum Hairan_*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button