Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 17-18

Sponsored Links

_17-18_*

 

Miqewa yayi yana shirin shiga daki ta riqoshi ta baya tace “wai da gaske kunne na yakeyi kaine kake fadawa Mimee zakayi aure Aseem da gaske hakane? Please tabbatar min domin nasan tudun dafawa” kama hannunta yayi ya zaunar da ita yana binta da kallo yace “ba kamar yanda kowanne aure yakw nawa yake ba Mimee idan kika tashi hankalinki ke kikaga dama da kanki zan Aure ne domin ramuwa da daukar fansa, idan baki manta ba nataba baki lbrn wata yarinya data mareni ta fasamin yatsa kwanakin baya, to itane zan aura, a zahirinta ba ajina bace kuma ba tsarata bace ni kaina inajin kunyar hadaka ta da ita ina qyaqqyaminta wlh don an daina cinikin bayi ne da siyo miki ita zanyi matsayin baiwa ki rinqa morarta

Related Articles

 

Dakatar dashi tayi da sauri tace “shut up Aseem banason yaudara da zalimci ni zaka wulaqanta ashe dsma abinda ake fadamin gsky ne Wayyoh Aseem meye nayi maka da zakayimin wannan sakayyar….” Rufenta baki yayi yana girgiza mata kai yace “kada ki kawo komai a ranki ba haka nake nufi ba har abada kece zabina kece burina kuma kece zuciyata wlh da gaske yarinyar nan don ke na aurota nasan zata taimaka miki

 

Sake dagansa hannu tayi ta miqe da gudu ta nufi dakinta ya bita da sauri daqyar ya samu ya shawo kanta bayan yayi mata manyan alqawura masu wuyar cikawa yana qara rantse mata baso bane zaisa ya auri Asmah kawai gayya ce to ganin yanda ya zage yana rarrashinta yasata sakin jiki amma duk da haka kishin mijinta yana cinta a ranta duk da tayi ammannar bai isa ya wulaqantata ba kodon soyayyar da mahaifiyarsa takeyi mata dole yabi umarnin uwarsa saboda haka ta yanke shawarar binsa ta qasa zata hadashi da hajiyansa tasanta sarai bata hada hanya da takala balle kuma ta bari a kawo mata yar matsiyatan qarshen zamani matsayin suruka da wannan tunanin suka fita ko a hanya aikin rarrashin mimee yakeyi suna shiga harabar gidan yaji gabansa yana faduwa so yayi ya juya amma INA ya makara yana daga Kansa ya hango hajiyansa saman bene ta zubawa motarsa ido dole tasashi fita yabi bayan Mimee data shige gdan a qofar falon sukayi karo da Hajja ta daukeshi da mari ya dafe gurin da tafukan hannunsa yanajin zugin marin saman jar fatarsa yana dagowa ta sake daukeshi da mari tana kumfar bakin cewa yanzu Aseem har kayi qwarin da zaka nemi aure batare da ka sanar dani ba saidai naji a wajen qannenka…..”
Hawaye Mimee ta goge tace “ai dole bazai fada miki ba Hajja wai ya rasa dawa zai hadani kishi saida yar talakawa….” Dafe qirji Hajja tayi tace “na shiga uku ni Saratu yar talakawa Aseem ina ka samota me suka Baka suka sauya maka tunani ni zaka wulaqanta yanzu yaushe ma akayi aurenka da Maryam da har zaka tattagowa kanka aure kuma auren ma memakon kaci gaba sai kawai kaci baya to wallahi baka isaba dole ka hqr da wannan dan iskan auren naka ka zauna da matarka dana zaba maka”

 

Shidai tunda yayi qasa da Kansa bai dagoba sai yanzun yace “wlh Hajja ba haka bane kawai….” Buge masa baki tayi tace kawai Ubanka ka kiyayeni Aseem zanci ubanka wlh dama na lura shine yake daure maka gindi shi ko ubanme ya hanashi auren mace sama da dayan sai kai da quruciyarka zaka dorawa kanka wahala to indai na isa dole ka janye ban amince ba bakuma zan amince ba”
Juyawa tayi ta shige parlournta ta barshi tsaye itama Mimee tabi bayanta a sanyaye ya juya ya fice daga gdan yanajin zafin abinda Hajja tayi masa yanzu meye laifinsa don anyi masa ba daidai ba yayi shirin daukar fansa zaayi masa wata fassara ta dabam bandama abinsu shi meye zaici da wannan banzar yarinyar da bata isheshi kallo ba”

 

Da wannan tunanin ya nufi gdan Jabir yake fada masa abinda ke faruwa sosai shima Jabir ya jinjina abin ya dubesa yace “to kai tunda abin baiyi nisa ba ka hqr mana kasan dai halin Hajja shi kansa Dad hqr yakeyi da ita” girgiza kai yayi yayi murmushi yace “nifa babu abinda zaisa na janye akan qudurina saidai kowa yayi hqr kamar yanda nake haqurqurtar da zuciyata ta karbi auren idan na janye dama haka Asma’uh da nahaifiyarta sukeso farin ciki zasuyi nikuma ba burina suyi farin cikin ba saboda haka kawai aci gaba da tafiya a haka tunda Dad ya karba mgnr kowa ma kada ya karba” da wannan tunanin ya miqe ya nufi gdan Yayarsa Aseemah itace kadai me sauqin yanayi a wajenta yake tunanin samun mafita game da auren nasa yana zuwa ta tareshi da fara’a tana tsokanarsa nan yake zube mata abinda yake ransa sosai tayi murna ta tayashi fatan alkhairi yayi shiru kamar bazaice komai ba sannan ya dago yace.
“Banasonta Sister na rasa meye yasa na dage wajen Neman auren ta yar talakawa ce Allah ina qyaqqyamin kaina inajin kunyar nunata matsayin mata talauci yayi musu kanta nifa badon quduruna a kanta ba da tuni na hqr ko na samu nutsuwa”

 

Zubansa ido Aunty Aseemah tayi har saida ya rufe baki tayi ajiyar zuciya tare da murmushi tausayin Asmah yafi komai narkar da zuciyarsa duk da tasan cewa qarya Aseem yake yace bayasonta domin tasan zuciyarsa idan babu burbushin son babu abinda zai darsa masa son auren ta matsalar kafin ya aminta ya yarda yanasonta tasha wahala kawar dakai tayi tace “kaje kayita addu’a qila rabone tsakaninku kasan ba kowa ne yake da Baiwar gane abinda yakeso a qaramin lkc ba” sosai ta rinqa basa shawara wata yakan dauka wata kuma ya watsar da ita domin yasan bazai iyaba”
Baibar gdan ba sai bayan magrib ya nufi gdansa har lkcn Mimee bata dawo ba dakinsa ya shiga yayi wanka ya dawo ya kwanta a parlour ya kunna kallo.

 

**********

 

Tunda suka koma gda batada aiki sai tunani damuwa taqi damunta babban abinda yafi damunta shine yanda Sadiq ya manta da ita ko a hanya suka hadu sai ya kawar mata dakai koma ya buleta da qurar sabon lifan dinsa wannan Abu nayi mata ciwo gashi batada Wanda zata zauna tayi hira dashi taji dadi duk da zuwa yanzu sun daidaita da yan’uwanta so ta lura suma yan son zuciya ne har garama Dijangala ita ta fahimci akwai matsala tana tausayawa Asmah sosai musammam da taga kowa saurayinta yana zuwa gurinta suyi hira itakam Asmah Aseem tun ranar da aka sallamosu daga asibiti bai qara takowa gdansu ba saidai ya aiko Jabir duk ta rame abinka da mara jikin dama babu abinda kake gani sai dogon hancin da idanu duk rawar kannan da fitsarar Asmah tayi laqwas ko mgn wahala takeyi mata ana haka aka kawo lefen su Dija samarinsu sunyi qoqari sosai babu laifi a matsayinsu na talakawa kwana biyu tsakani aka kawo na Asmah ranar har wanda basa mgn dasu saida suka shigo ganin wannan lefe na al’ajabi

 

Lkcn bikin saura sati guda amma shiga shagalin biki itadai Asmah tunda aka fara bikin tana kwance a dakin da akayi musu na yaran gda batada aikin daya wucce kuka duk da fitsararta tasan haqqin Miji akan mace sosai yanzu indai ta bari aka daura auren nan shikenan ta zama nama duk yanda yaga dama haka zaiyi da ita? Hakan ba qaramin karyar mata da zuciya take ba ana saura kwana biyar tana gdan maqotansu tana kwance kasancewar ba Lfy ce ta isheta ba yaro ya shigo yace “wai ana kiran Asma’uh a waje” ajiyar zuciya tayi ta gyara kwanciya Jiddarh tace “ki tashi kije mana kinsan shima wannan dan Aiken ba qaunar jira yakeyi ba”
Tsaki tayi tace “kije kawai” sanin halinta ne yasata miqewa tace “bazakiyi mana buqulu ba yanzu haka kudin partyn aka kawo mana” Dija nayi mata dariya ta fice itadai bata tanka ba sai game da takeyi da wayar Hajar Matar gdan da suke yammatancinsu, da sauri sukaga Jiddarh ta nufo parlourn ta zauna tana Mayar da numfashi saida ta gama saita nutsuwarta tace “aikin babba ne Ma’uh yau me gayya me aiki ne yake tafe wlh yanacan saici mazu yakeyi kije yana jiranki” sosai taji qirjinta ya buga ta dago idanunta da suka kawo ruwa tace “don Allah kije kice masa bananan” zare ido tayi tace “ban isaba wlh ki tashi kawai kije” sharewa tayi ta koma tayi kwanciyarta daqyar tasheta shima saida Innah ta aiko da kanta sannan ta tashi tasa qaton hijjab dinta ta fito idanunta na fitar da ruwa ta nufi wajen ta jima tsaye kafin ya danna mata horn ta nufi inda motar take ya bude mata kamar taqi shiga sai kuma ta tuna maganganun Innah haka ta zauna ya mayar da qofarsa ya rufe ya juyo ya zuba mata ido tayi qasa da kanta tana wasa da yatsanta hawayenta na zuva saman santala santalan yatsunta,

 

 

Sun jima A haka kafin taji yaja Wata doguwar ajiyar zuciya ya furzar da iska yace “meye yayi saura?” Jan numfashi tayi me hade da majina kukan da take ta qoqarin hadiyewa ya qwace mata yayi saurin zubanta ido tare da kamo hannunta qirjinsa na bugawa da qarfi kukan yana masa kuda a kunne yace “ya….ya salam meye kuma na kukan?” Sake rushewa tayi da kuka gabadaya ya diririce baisan sanda ya hadata da jikinsa ba ya rungumeta sosai ta rintse idonta da qarfi ta sake qarawa kukanta sauti tace “nas….shiga ukuna wayyoh Innata ka sakeni don Allah banas…..” Numfashinta taji yana qoqarin daukewa ta shidewa tayi saurin bude idonta tsoronta ya nunku jikinta ya dauki rawa tunda take bata taba ganin dan iskan bayyane irin Aseem ba Shikam babu abinda yakeyi sai tsotsar lips dinta daqyar ta hada qarfinta ta tureshi tana jan zuciya tare da sanya hijjab dinta ta rinqa dirzar bakinta tana kuka me taba zuciya tace “Allah ya isana mugu kwarto kawai……”

 

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*

 

*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button