Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 65-66

Sponsored Links

*65-66*_

 

 

Related Articles

_*End! End!! End!!!*_

 

Wata ajiyar zuciya yaja me qarfi ya daga yarinyar saitin fuskarsa yayi mata duk abinda ya cancanci uba yayima yarsa ya rungumeta a jikinsa yanajin qaunarta na ratsa zuciyarsa lallai ya yarda qaunar da da mahaifi daban take tunda yake baitabajin qaunar wani abu kamar wannan yarinya ba numfashi ya sauke a ransa yace “yanzu da sakaryar can tayi nasara fah da tuni bai sameta ba” Asmah ya duba yayi mata murmushi ya miqa mata babyn Hajja tayi maza ta karba tace “kawota a gyarata mana kun barta tinqi sai zagawa kukeyi da ita” ita da kanta ta wanke yarinyar ta shiryata tsaf Aseemah da Nasmah na tayata ana gama shiryata ya fara zubanta hotuna ko kunya babu Inna dake shigowa itakam yar kallo ta zama daqyar Hajja ta qwaceta a hannunsa ta bawa Inna ita Inna tayi murmushi tace “kamar zare kamar Allura Aseem hankali ya kwanta ubangiji yabada lfyr tarbiya da nemo Abinci don da ganin wannan bakin zaiyi ci”

 

Murmushi yayi ya fice daga dakin ya nufi gidansu dashi da masu aikin gdan suka gyare gidan tsaf sannan ya debar musu kaya ya fita ya koma asibitin sai dare suka dawo gida da rikici aka taho wai zasu tafi da ita gida yayi tsalle yace shikam baa isaba dole suka qyale sai Inna ce ta zauna a gurinta wannan yarinya tayi goshi Zulaihat yasa mata sunan Kakarsa Sukece mata Ammi gatakam Ammi da mamanta sunganshi bayan suna komai ya lafa Badon inna naso ba haka ta zauna har arba’in sannan ta tafi su Mimee harda zuwa barka taga yarinyar ji takeyi dama itace ta haifa masa yarinyar sosai take nadamar biyewa zuciya data rinqayi har takaita ta baro gashi tayi uku babu ba surukar babu Mijin babu Haihuwar.
Gashi wacce takeso taga bayanta din ta zama itace take mulkar gdan wannan abu nayi mata ciwo, ranar da sukayi arba’in washe gari kuwa ya dauke matarsa suka bar qasar duk yanda Mimee taso ta shawo kansa abin ya faskara hakanan ta hqr ta zubawa sarautar Allah ido kullum mahaifiyarta cikin goranta mata take ta kaso aurenta tazo tana sa musu ido a gda itakam batada bakin mgn saidai idan sun guma mata ta shige daki tayi kuka tayita kiran Aseem baya dagawa dole ta hqr ta sallama mawa Asmah mijinta donta fahimci yanzu hankalinsa baa kan kowa yake ba sai matarsa da yarsa tana ganin status dinsa kullum daga matarsa sai Amminsa sune a status dinsa idan tayi masa mgn ma baya budewa, tafi tafi har shekara guda Aseem yayi gurin zama A Sweeden yaqi dawowa shekarar Ammi guda ta sakejin labarin Asmah ta qara haihuwa.

 

Ta haifi Mukhtar Sunan Mahaifinsa kenan Suna kiransa Anwar tuni ta zubar da makaman yaqinta ta koma lalubar Asmah tana gaisheta tare da tambayarta yara da farko bata saurarenta sai daga baya ta saduda take amsa mata suke gaisawa sosai tayi nadama da kanta take bawa Asmah hqr take roqonta ta taimaka ta bawa Aseem hqr ya daina gaba da ita wlh sharrin zuciya ne da tsautsayi.
Saida Asmah taji dam a ranta ta saba rayuwarta daga ita sai mijinta yanzu kuma ace wata tazo ta shiga wannan abu ya girmi tunaninta bazata iyaba, Suna chat da Jiddarh take fada mata halin da suke ciki nan Jiddarh take bata shawara akan ta manta da komai tayi domin Allah Allan bazai tabar da itaba nan take fada mata halin da Mimeen ke ciki a gdansu na tsangwama da wulaqanci kasancewar Qanwar Mimeen Zahra qawarta ce.

 

Jikinta ne yayi sanyi ta nutsu ta fara tunanin itama hakan zata iya faruwa da ita idan akaqi taimaka mata bazataso ba kuma duk wanda ya taimaki wani tabbas Allah zai taimakeshi, da wannan nazarin ta danni zuciyarta ta runkari Aseem din da maganar yakoyi funfurus yace bayada raayi,
Haka ta rinqa binsa da magiya da komai yamaqi sauraronta balle tasaran zai dubeta gajiya tayi ta yima Inna mgnr itace ta nemesa akan ya dawo da matarsa ai tayi hankali yaso yayi mata gardama amma mutuncinta da yake gani yasa yace mata shikenan zaiyi nazari.
Lkc yayita tafiya baice mata qala ba har saida aka qara daukar wata shekarar ta qara sunkuto masa da namiji a wannan karon ne tayi nasara da Inna ta qarasa baki ya amince ta dawo amma ta nutsu ta kama kanta idan yaga wani abu sabanin hankali tabbas zata koma inda ta fito kwanan Jamal Goma a duniya jirgin Mimee ya sauka da gaske gabadaya tayi sanyi batada wani katabus ta cire komai ta kama Allah tasan shine kawai yanzub zai iya mata bayin kanta ba.

 

Yaran ta kama ta riqe tun Asmah bata saki jiki da itaba har ta sake mata suka rungumi junansu komai ya wucce kamar baayi ba anan Sweeden Asmah taci gaba da karatunta na likitanci bayan ta gama ya nema mata aiki anan din itakam Mimee tace bazata iya wani karatu ba sai jari daya bata take kasuwanci itama Asmah tana aikinta tana sarar jakankuna da takalma yan Sweeden tana turawa 9ja ana siyar mata haka nan rayuwa taci gaba da tafiya lkcn da asmah ta samu cikin hudu itama Mimee ta samu sosai ansha wahalar cikin nan dake allah yayi me taka qasa ne ta haifi yaranta biyu mace da namiji sati biyar tsakani Asmah itama ta Haifi nata guda biyu duk maza itakam Mimee mahaifar ce ta lalace dole aka cireta itakuma Asmah haihuwar ce tazo da tangarda saida akayi mata Cx aka cire yaran aikam tace itafa ta gama haihuwa a shekara shidda yara biyar to shima bai zafafa ba aka daure mata mahaifar sukaci gaba da rayuwarsu suna kula da yaransu idan ka shigo gdansu bazaka taba bambamce wace ta haifi wane da wane ba saboda shaquwar da suka samu da Mimee kusan ma basu samu da Asmah ba.
Rayuwa tayi dadi tayi albarka lkcn da Ammi da Anwar suka gama secondary ne suka shiga Jami’a lkcn ne sukuma suka koma 9ja ya gina musu qaton gda A NSRW G.R.A ita kuma Asmah ta gina qaton Asibitinta ta mayar da hankalinta akan kula dashi kusan ginin shine yayi mata kayan aiki kawai ta zuba, itama Mimee ya bude mata shagon saida kayan mata da yara………..

 

 

_*Tammat Bi Hamdullah*_

_Nan na kawo qarshen wannan labari Ina fatan kuskuren da yake ciki ubangiji ya shafe abubuwan amfanin dake ciki Allah yasa Mu amfanesu ya bamu ikon bin daidai da kuma aikata daidai ubangiji yasa ayyukanmu su zama hujja garemu ba hujja akanmu ba_

_Kada ku manta JUHUD shine littafi na gaba dana fara sakinsa ranar 7/7/2021 duk da kasancewarsa na kudi ina fatan masoyana zasu karbeshi domin nasan tabbas banako tantama zai nishadantar daku fiye da tunaninku kuma zai ilimantar daku zaku qaru matuqa a cikinsa._

 

_Ina roqon duk wanda yakeda shirin bibiyar labarin JUHUD da yayi hqr da yanayin labarin domin tun a tallansa na fada Romance ne akwai……… sosai a cikinsa duk da cewar insha Allahu zanyi amfani da hikima wajen kyautata harshe, to nima inason uzuri daga gareku._

_Domin sharhi shawara ko qarin haske zaku iya nemana ta WhatsApp a wannan number 09013718241_

_Taku ta kowa me burin nishadantar daku da kawo muku abubuwan da suka shigenku duhu koda wasunku zasu kasa fahimta_

 

_*Oum Hairan*_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button