Amatulmaleek Hausa NovelHausa Novels

Amatulmaleek 10

Sponsored Links

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

10
Badan mum Aisha taso ba dole ta Bada dama likita ya duba maamah a asibitin sai gata itama anbata gadon sbd sosai jikinta ya rikice.

Related Articles

Bayan likita ya gama komai akan mamah din ansamu tayi bacci yayiwa mum Aisha bayanin ciwonta da hutun datake buqata ya tafi.

Babu abinda mum Aisha take tinanin tsayawa tayiwa maamah din Dan haka ta dawo gida saima data huta tayi sallah taci abincin ta Tina da maamah din tasaka khaltume ta hada Amatu dame aiki Daya aka kaisu asibitin gurin maamah.

Amatu karan farko tana ganin halinda mahaifiyarta take ciki Jin tayi komai nata yayi sanyi sbd Koda sukazo tayi Amai Amma Babu kowa adakin bare ya taimaka mata harta koma bacci ahakan.

Share hawayenta dasuka gangaro tayi ta qaraso tafara kokarin tsafatace maamah din batareda wadda aka hadota da ita ta taimaka mata ba duk da qarancin shekarunta ita kadai ta tsafatace mamanta ta gyarata zuwa lokacin jikin maaman ya sake rikicewa Dan kuwa kaman Wanda beso aka zo asibitin ba.

Tsoro dukkaninsu suka shiga sbd Dena numfashin da maamah tayi hakama yanda take fizga tini suka kirawo likita Yana zuwa akace su fita.

Suna fitowa dole Fatima ta tausayawa Amatu itama jikinta yayi sanyi sbd itama marainiya ce tasan suna rasa mamansu a yawon aikatau Kila Suma zasu qare.

Zaman Jira suka dasa a wajen dakin har likita da sauran nurses suka gama duba maamah din suka fito suka wuce Babu Wanda yace musu komai sbd ganin basune sukeda iKon Jin komai ba sai mum Aisha tazo itada ta kawota.

Ciki suka koma suka zauna shiru Babu me magana sai kallan maamah da Amatu keyi a Kai Akai.

Anan Amatu ta kwana tareda Maamah ita kadai sbd ana kawo musu abincin dare aka koma da ita.

Husnah ma taredasu Abdul da Haydar akazo dasu suka duba mommynsu da maamah din suka koma.

Acikin kwana biyu da wuni biyu maamah ta zabge itama Takoma kaman ba itaba ciwo ya sauyata,
Amatu ma sosai ta Dan sake figewa sbd Bata iya ko sabawa da dawainiyar asibitinba dukda Babu abinda sukasan ma Yaya ake biyansa komai Kai tsaye cikin bill na familyn ASH yake shiga.

Madame abeeda kuwa jikinta itama dai sai ahankali har lokacin Dan haka aka fara shirye shiryen fita da ita waje Amma saita farfado Dan haka ana Saka ran farkowanta kowane lokaci.

Maamah Saida tayi kwana bakwai tana jinya me wahala kafin sauki yafara zuwa lokacin Abeeda ta farfado itama jikin nata yafara sauki Kuma baa sanar mata maamah na asibitin tana jinya ba sbd kada a qara mata damuwa.

Koda Maamah tafara samun kanta dauriya da qarfin hali ta Saka sosai ta warware aka sallameta sai alokacin taje ta dubo Abeeda wadda ramarta ta bayyana sosai,
Ita kanta Abeedan dataga maamah sai data tambaya cikin sanyi da rashin qarfi cewan ko maamah din tayi rashin lafiya ne sbd yanda duk ya qanjame itama.

Murmurshin karfin hali maamah ta saki tana girgiza kawai tana qarasa zama a kujeran gaban gadon tareda Dan dafa bakin gadon tana kasa kallan fuskan Abeeda ta tambaya Yaya jikin nata.

Numfashi Abeeda ta sake ahankali tana Dan lumshe idanuwanta sbd gajiyan datake ji ta gyada Kai ahankali tana qure kallanta akan maamah din wadda take kasa kallanta.

Amatu ma da Bata samu zuwa duba mommyn ba sbd dawainiyar kulawa da maamah sai alokacin tayi mata sannu tana fatan samun lafiya.

Zuwansu Husnah tareda su Haydar ya Saka dakin Dan daukan hayaniya kadan sbd murnan ganin iyayensu sun samu sauki kowacce tana zaune da kanta sabanin yanda suke zuwa ganinsu a kwance Babu me sauki.

A Nan dakin suka wuni sai dare suka tattara suka koma gida gabaki daya sbd an sallami maamah,
Suna dawowa gida wanka maamah din tayi Amatu ta Sakata Shan maganinta kafin taci abinci ta kwanta hakama Haydar da Husnah na dakin nasu anan sukai dare kafin suka koma can cikin Mansion suka nufi dakunansu suka kwanta.

Washe gari wankin kayansu Amatu tayi nata Dana maamah Dana Abdul,
Bata gama ba sai Rana Dan haka tana gamawa sallah kawai tayi taci abinci itama ta kwanta ta samu baccin Hutu.

Sai yamma sosai ta tashi tayi sallan laasar lokacin maamah Dan karfin hali tabi masu zuwa asibiti zuwa dubo madame,
Amatu bataji dadin fitar maamah ba a halinda take ciki Amma Kuma batada abin cewa sai kawai tayi fatan samun lafiyansu su dukan.

Sai dare maamah ta dawo cikin ikon Allah tareda madame din suka dawo anyi sallama.

Madame din tareda daddynsu Husnah ta dawo Dan haka babu Wanda ya ganta sbd Kai tsaye bangarensa aka ajesu Kuma sun shige Dan haka Babu Wanda ya ganta sai washe gari Shima washe garin Se yamma ta fito sbd Babu abinda Babu acan da zata buqata,
Masu Kai abinci ne kawai ke shiga sashen Se masu gyara Suma suna gama abinda yakaisu suke fitowa.

Kowa yaje har palonta na kurya ya gaisheta ya mata sannu da jiki da fatan samun lafiya Mai dorewa kafin kowa ya fito aka barta dasu Husnah sai mum Aisha data shiga itama.

Maamah da Bata gama warwarewa ba haka ta ringa yawon kulawa da ita sbd Abeedan tafison maamah a kusa da ita akoda yaushe,
Tafi Jin sauki da qarfin jiki takeji idan maamah ce take kulawa da ita.

Ita Kuma maamah Sam bazata iya fadawa Abeeda batada lafiyanba tinda harta Nuna ita takeson ta kula da ita to tabbas zata danne tayi mata komaima.

Amatu a zuciyarta bataji dadin Hakan ba sbd maamah din kullum dare itama haka take kwana jikin Se ahankali.

******Da wannan kacokam lalurar kulawa da Abeeda ya dawo hannun maamah wadda har tsaftan bangaren Abeedan gaba Daya mum Aisha tasaka aka bar mata Dan haka sai maamah ta koma tamkar itace me aikin Madame abeeda a gidan.

Tafiyan da akaso yi da Abeedan ganin ta warware yasaka ta buqaci ASH din ya barta taci gaba da ganin likita anan,
Shawara yayi da likitoci qwararri suka ce zaa iya barinta Nan din duk ba matsala Suma sunada likitoci cancer masu kyau,,Hakan ya Saka ya barta din Badan hankalinsa ya kwanta sosai ba sbd bayyanar cancer a tareda Abeeda ya jijjiga duniyarsa da duk abinda yake cikinta sbd a ransa Abeeda wata haskensa ce da baya fatan rasawa a kusa Yana fatan su tsufa tare su mutu tare.

********
Amatu da Abdul sun sake komawa bakin karatunsu da suka bari a Nan din sedai wannan Karan harda Boko aka sakasu makaranta me kyau da tsada Amma ba wadda su Husnah keyiba.

Amatu Sam batajin kunyar girman data Dan Fi Yan ajinsu ba tace tafison tafara daga Js 1 din Daya kamata Dan haka anan aka Sakata akan idan anga kanta na budewa sosai sai idan zata shiga Js 2 a jefata Js 3 kawai.

Abdul ma nursery aka sakashi duk da yayi girma kamata yayi ace an sakasahi primary 2 ko 3 Amma dai sbd baida komai na karatun dole aka sakosa daga can.

Daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya damu da girman da yayiwa Yan ajinsu su farin ciki ma sukai da Hakan Dan haka suka dage tareda Maida himma musamman Amatu datasan wahalar mahaifiyarsu ce suke mora da karatun Dan haka bazata bari uwarsu tayi wahalar banza ba Dan yanzu aiki bana madame Abeeda kawai takeyiba kusan aikin gidan Rabi yana rataye ne akan maamah din Dan haka tsufa na dole yafara rufarta ga ciwo shiyasa kowanne dare a wahalce take bacci gari ya waye Takoma aikin kamar engine.

*****Fara karatunsu ya Saka sosai Amatu ke sake wayo da Jin damuwan mahaifiyarta da Babu ranarda bata kwana da abin,

Ta bangare daya Kuma Husnah na taimaka mata sosai da karatunta hakama Haydar shima Yana taimakawa Abdul Dan haka abin yake zuwar musu da sauki suna ganewa.

Madame abeeda kuwa jikinta yayi sauki sosai Kuma har lokacin Babu Wanda yasan Menene ciwonta daga ita sai ASH Wanda Shima a qurarran lokaci ya sani Dan haka a yanzu koyaushe cikin ganawa da manyan likitoci yake ana masa recommending qwararrin likitocin Cancer na qasashe da ze Kai Abeeda ayi treating dinta.

Maamah dai a taqaice Takoma chief maid ta gidan Dan kuwa yanzu hatta abincin da masu gidan ke ci itace take girkawa Dan takanasa aka ringa koyar da ita bisa ga umarnin mum Aisha Dan haka tana qwarewa aka sallami chiefs din Dake girka abincin ASH TALBA maamah tayi replacing dinsu Dan haka ta sauya sosai ta sake manyanta ba kaman Abeedan Dasuke Aminai ba ita duk da tanada boyayyan ciwon da Basu saniba jikinta yananan me kyau da Hutu kamar yarinya take sake komawa.

**AmatulMaleek karatunsu yayi Nisa ta sake zama Yan mata Dan ma karatu na cinyeta sosai sbd yanda ta qwallafa masa Rai,
Kamar yanda aka fada idan anga tana ganewa zaa mata jumping to lokacin nayi Akai nata tsallake maimakon tayi Js 2 Kai tsaye Js 3 aka kaita wadda har sunyi jlc tayi SS 1 hakama yanzu tana Ss2 lokacin Husnah tagama harta shiga university.

***Ita rayuwa tana zuwarwa bawa ne a yanda ubagiji ya tsaro masa bawai Kaine kake tsarowa kanka ba,
AmatulMaleek matashiyar budurwar Dake tasowa a lokacin,
Wata irin rayuwa ce take gudanarwa ta kadaici da kamun Kai a cikin gidan dasuka Dade da zama ‘yan gida Kokuma tace gidan da suka Dade da zama ‘yayan me aikin gidan Dan kuwa ayanzu ba ‘yar uwa ko Aminiyar madame ake kallan maamah ba matsayin shugabar masu aikin gidan ake kallanta,matsayinta Daya da masu aikin,guri Daya da masu aikin gidan suke rayuwa,abinda ake bawa masu aikin gidan shi ake Bata,bambamcinta da masu aikin gidan shine Bata karban albashi hakama dauke ake da nauyin karatun yayanta Wanda zata iya qarasa rayuwarta a wannan wahalar sbd ‘yayan su samu gobensu me kyau duk da har Koda yaushe duk abinda takeyi na wahala da abinda ake mata a gidan bata taba Jin haushi ko damuwa ba sbd Dan Allah takeyi dakuma kaunar datakewa Abeeda wadda itama zata iya dawwama a wannan wahalar datake mata batareda taji komaiba.

AmatulMaleek zuciyarta ta taso ta Ginu da damuwa da Jin radadin irin rayuwarda mahaifiyarta ke ciki wadda a yanzu ko tausayi Babu bare kauna a yanda yake treating maamah a gidan,
Hatta dawainiyar Husnah data Haydar itace takeyi Wanda Hakan ke sake lullube zuciyarta da tausayin mahaifiyarta wadda har lokacin zuciyarta me tsafta ce Bata Jin qyashi ko gazawa.
#MAMUH#
#MERAH HERBS

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button