Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 17-18

Sponsored Links

17-18*

★★★~~~★★★~~~★★★

Zaman kusan awa biyu tayi kan sallayar ta rasa tudun dafawa hakanan gwiwa a sage ta tashi ta fita dinning ta tarar masu kula da ɓangaren abincin har sun shirya komai na dinner ta zauna ta buɗe tuwon shinkafa miyar zogale ta dauki mazubi zata zuba Beebah ta fito da sauri tana cewa “Ayyah Hajiyanmu yau kin manta nice zan haɗa Miki abinci tun dazun naketa leken jiran fitowarki”
Murmushi tayi ta gyara zama tace “To Beeban auta a haɗamin” kunya Hajiya ta bata ta juya zata gudu taji an riƙeta ta ƙyalkyale da dariya tace “Allah Hajiya kunya kike bani in kince Beeban auta dinnan waima kunyi waya dashi kuwa ya sauka ko har yanzun suna saman gajimare”
Tana mgnr tana langwabewa salon shagwaɓa Hajiya ta harareta tace “ai kin fini kusa dashi ba mijinki bane ki kirashi mana kiji lfyrsa” shiru Habeebatullah tayi da mgnr don batada kalmar ƙarawa itadai tasan yanda tsoron Bro ya ɗarsu a ranta bazata iya haike masa ba gara ma idan shine ya kira…..

Related Articles

 

Ƙirrr wayar Kilishi ta fara ruri bayan ta gama haɗa mata abincin suka kalli wayar a tare “Autana” sunan da Hajiya tayi saving numbersa dashi kenan suka haɗa idanu da Hajiya tayi saurin juyawa zata bar gurin Kilishi tace.
“Kai kajini da kitifaffiyar yarinya yanzun ki titsiyeni kina tambayata mijinki sannan ya amsa ya kira ki gudu” Turo baki tayi tace “Kayy Kilishi bafa niba ke yakeson jin….” Rankwashi ta zuba mata tace “Kaniyar me gardama ɗauki Ni kibani guri” ɗaukar wayar tayi ta danna accepted ta nufi ɗakinta ta kulle ta kara a kunnenta ya sauke numfashi yace “Matar da bata damu da ya mijinta yake ba” lumshe idanunta tayi tace “ya akayi kasan nice?” Wani gwauron numfashi ya sauke yace “zuciyata ce ta amshi saƙon mahaɗinta anya Beebah zan iya rayuwa Ni kaɗai a ƙasar nan Wlh ina cikin yanayi bansan Meye ke damuna ba nikam tunda aka sarƙamin rigar girma aka ɗaureni da igiyoyinki uku na fara fuskantar canji inajin kamar bazan iya cika alkawarin dana ɗaukar wa zuciyata akanki ba”
Abinka da ƙuruciya bata fahimci komai ba cikin kalamansa saima kwantar dakai da tayi tace “cikin kane yauma yake ciwo?” Fasali yaja yace kusan hakane gashi ina buƙatar bargo me taushi wanda yake numfashi kamar Ni Beebahta garin akwai sanyi waither ɗin su zata wahalar dani….”

 

Dariyarta ce ta katse masa furucin tace “Wai bargo me numfashi to a ina ake samun bargo me numfashi koda yake rayuwarku ta birni babu abinda bazaku iya samarwa ba ɗan birni nikam ina ganin tunda bazaifi ƙarfinka ba ka siya kada sanyin yayi maka illa” takaici ne ya sashi yin ƙwafa yace “shidai yaro kawai sunansa yaro bayan wanda nake dashi ƙarfi da yaji yafi ƙarfina kawai ki tayani addu’a kuma kiyi fatan kada a dawo Miki da gawar mijink…..”
Da sauri tace “Bari don Allah Bro banaso Wlh ina tsoron mutuwa saboda itace Ummul aba’isin komai na lalurar rayuwata na tabbata da ace yaya Tani bata mutu ba da yanzu aurena dakai bai zama silar tuɓe rigar albarkar iyayena ba Bro inasonka fiye da yanda nakejin kaina a zuciyata amma ina tsoron irin abinda kayimin jiya don Allah karka ƙara banaso Nima na mutu banga ƴaƴana ba…..”
Sosai kalmar ta ta ƙarshe ta bashi dariya yayi me isarsa sannan yace “is very funny My wyf kinajin tsoron matakin farko har kina roƙona karna ƙara sannan kuma kinason zuwa matakin ƙarshe to ta yaya wannan shirmen naki zai yiwu?”
Biye mata yayi sukayita shirmensu ko ba komai yana samun nutsuwa da muryarta sun ɗauki dogon lkc suna hira kafin suyi sallama yace ta kaiwa Kilishi ta fito takai mata a kunyace ta karɓa suka gaisa tanayi masa tsiyar yanzu tunda yabar zuciyarsa a gida ai ta rinƙa jinsa kullum…..

 

Itadai sulalewa tayi ta nufi dakin baccinsu ta tarar duk sun kwanta suna latsa waya taja bargo ta kwanta tana karanto addu’ar data sawwaƙa bacci yayi gaba da ita, sai asuba suka farka tayi wanka kamar yanda taga al’adar su Khaly da Hudah ta koma tana gyara musu ɗakin kasancewar itan ba sallah zatayi ba bayan ta gama ta nufi kitchen shegen karambani ne da ita Habeebatullah komai da ruwan ka kowa ya santa kuku har nemota yakeyi in zaiyi aiki saboda tace masa itama girki takeson koya har tana cewa ko ruwan tea ya dafa bai kirata ba wuta balbal aikuwa ranar Hajiya Kilishi da sauran yaran gidan sunci dariya wai wuta balbal shida aikinsa.
Dake tanada fahimta sosai babu wani abu da yake bata wahala indai taji a ranta zatayishi a wannan taƙin ne kuma Hajiya Kilishi tayi ruwa tai tsaki aka mayar da ita makaranta Dr Mas’ud yayi mamakin kwanyar yarinyar da akace masa daga kauye take SS one yasata sai gashi tana neman fin yan SS one ɗin ganewa saboda lesson ɗin da takesha a gida Hajiya Kilishi tayi mata Hudah da Khalisa suyi mata shima mijin ɓoyen idan ta saci jiki ta saci wayar Kilishi ta ƙule ɗaki yayi mata sukayi jarabawar zangon karatu na ƙarshe dake dama karshen shekara aka kaita da ƙyar bayan ankai ruwa rana ta samu na biyu don badon maths data samu matsalar maki ƙalilan ba ita zata karbe kambun first class aikuwa Ashe tun kafin ma a bayyana musu sakamakon Habeeb ya sani don result na Habeebatullah Habeeb ya jima a wayarsa.
Kowa Saida ta burge shi a wannan rana hatta Hajiyan soro dake lecturer ce Saida taji Habeebatullah ta mugun shiga ranta kyauta kuwa harda Mai martaba a bata gift gift na ban mamaki Mai martaba ya bata zoben gold da agogo yasa Hajiyan soro ta siyo mata masu kyau da tsadar gaske familyn yan boko sarakai kuma masu tashen hatimin nasara a Afrika ma ba iya Nigeria ba Allah ya jarabci wannan family da son mutum gifted yanzu darajar ka zata ɗaga.
Itakam Hajiyan soro ɗan kunnen gold ta siya mata babba, Habeebatullah banda hawaye babu abinda takeyi wai yau ita bamagujiya wacce take yawo tsirara² mara galihu wacce ake ƙyamata itace kowa keson gani da kuma ɗaukar hoto da ita.

 

Allah kenan tabbas idan ka rikeshi zai isar maka amma fah idan ta tuna ɓoyayyen matsayinta a gidan da kuma tsohuwar aƙidar mutanen family ɗin jikinta ya kanyi sanyi harta kasa katabus,
Ranar haka ta yini tulus babban tashin hankalinta yanda Mufeed yayan Rasheedah Turaki class met ɗinta Kuma ƙawarta ɗaya da tayi a ajinsu ya takura mata da kallo da hotuna duk inda tabi haskata yakeyi idan suka haɗa idanu yayi mata murmushi itakam tsoronsa ma takeji Mufeed Turaki Soja ne hutu yazo ya ishe bikin canjin ajin na ƙanwarsa rabon haɗuwa da ƙaddararsa yasashi jin shauƙin kasancewa a gurin.

 

Yaukam jinsa yakeyi kamar shine sarki Khalid saboda yanda zuciyarsa take haske yanajin tabbas yayi matar aure, hakanan taro ya watse suka nufi gda a motar Kilishi ita da kanta ke jansu Saida takaisu wani Gidan gyaran jiki aka gyara mata ƴammatan nata tayi musu siyayya sannan suka wucce gida suna zuwa Habeebah ko wanka ƙi tayi ta nufi dinning ta zuba abinci tanaci hanu baka hannu ƙwarya saboda yunwa sunata yi mata dariya Kawai jikinta ya bata ana kallonta ta daga kanta gabanta ya faɗi ta zaro idanu waje tace “Lahhhh Kilishi ya dawo…..” Bata gama isar da saƙon ba ta kwasa da mugun gudu ta haye saman ta ruƙunƙumeshi tana kissing nashi ta ko ina tana cewa “I miss you My Bro double miss you…..”
Mamaki ne ya cika Hudah da Khalisa ganin yanda ya wani lumshe idanu yana shafa bayanta da alama ma ya manta da akwai mutane a ƙasan ya ɗago fuskarta ya ɗora harshensa a lips ɗin ta ya sauke mata wani irin kiss me hucin bayyana sirrin zuciya ya janye ya ɗaga idanunsa da suke wani lumshewa kamar me jin bacci yace “Really My Wyf kinyi miss ɗina kamar yanda nayi naki?”
Dubanta takai ƙasa inda Mai martaba yake tsaye gabanta ya faɗi tayi saurin janyewa daga jikinsa ta nufi hanyar ɗakinta ya bita da kallo yana haɗiye wani mugun yawu gabaɗaya cikin watanni shida tayi mugun canzawa kamar ba Beeban sa ba wata ajiyar zuciya ya sauke ya fara taka step na benen ya sauko ya rusuna cikin ladabi da girmamawa ya gaishe da Mai martaba Sarki Khalil bai wani dami zuciyarsa da tunanin wani abu ba saboda yariga yasan dabi’ar family ɗin nasu da mazansu da matansu duk jinsu sukeyi abu ɗaya musamman Beebah yarinya me tsayawa a rai duk ɓacin ran da kake ciki indai tazo guri saita sanyaka dariya shiyasa bai damu da yanayin daya gansu da Habeeb ba.

 

Dafa kansa yayi yace “Autan Kilishi Meye ya dawo dakai ne wata uku na ɗauka sai kayi shekarar?” Shafa sajensa yayi yace “Allah ya taimakeka wani uzuri ne ya dawo dani amma ba daɗewa zanyi ba bazan wucce 2 weeks ba” murmushi yayi yace “Wato dakai zamu fara azumi kenan” shima murmushin yayi yace “Allah ya taimakeka mun sameku lfy?” Amsawa yayi yana fita yace “Dama kuwa inason mgn dakai da na bari sai bayan sallah idan nazo ziyarar aiki zamu tattauna to tunda ka dawo idan ka huta sai kazo inason ganinka”
Duk da gabansa ya faɗi hakan bai hanashi gdy ba suka gaisa da Kilishi da rashin kunyarsu ta sanyata daskarewa a zaune su Hudah ma da suka kasa gane lamarinsa da Beebah suka gaisheshi ya amsa musu babu wani annuri suka tashi sumsum suka fice daga parlourn ya matsa kusa da Kilishi ya ɗora kansa a cinyarta cikin shagwaɓa irin ta sangartattun yarannan yace “Hajiyata Help me please!”
Da rashin fahimta ta dubeshi tace “Name kuma Autan maza nayi zaton dai Beebah ce kuma gata taka ce” iska ya furzar ya shafa kansa yace “Hakane Kilishi amma….” Sai yayi shiru ta zubansa idanu gabanta na faduwa tace “Amma me?” Ƙasa yayi da kansa yace “Hajiya tun lkcn da jikina da ruhina suka karɓi canjin suna daga saurayi zuwa magidanci me iyali komai nawa ya sauya a baya bana wani damuwa da kaɗaici ko rashin abokiyar rayuwa, yanzun kam Wlh na fara gazawa ina buƙatar matata a kusa dani….”

 

Yanda Hajiya Kilishi ta tsura masa idanu ne yasashi haɗiye mgnr can ya nisa yace “Ki…ki fahimceni Hajiya wannan lamarin yamin tsauri ko bazaki bani itan ba ki amince min daga lkc zuwa lkc nake samun nutsuwa da it…..”
Dagansa hannu tayi tace “Ya isa Habeeb kul baka kiyayeni ba ban amince ba nace ban yarda ba kaje kaci gaba da hƙr da kuma azumin da kakeyi na nafila a baya zaifi maka amma gsky bazan baka Habeebatullah a wannan ritsin ba ko zan baka matarka sai komai ya daidaita banason son zuciya kaje ka jefa yarinya a matsala danginka da son kai babu me ganin laifinka”
Ya tabbatar Kilishi bazata fahimceshi ba tunda har taki fahimta hakan yasashi miƙewa yace “shikenan Kilishi idan na mutu kin huta….” Bata kulashi ba ta miƙe ta nufi sama ta shiga ɗakinta tayi wanka tayi sallar magrib tayi shirin kwanciya sannan suka fito dinner, harda Habeeb Beebah na ganinsa taji gabanta ya faɗi kamar ta juya babu dama ya kafeta da ido kwata² ta shafa’a da yana gidan rigar jikinta ta bacci ce airmles iya gwiwa ta kame gashin nan ta daureshi da ribbon tayi masa manyan tuka guda biyu ta sake shi a baya.

 

Ji tayi ranta yana faɗa mata ta juya ta ɗauko hijjab saboda zuwa yanzu tasan darajar suturta jikinta, kafin ta juya taga ya miƙe yace “ki kawomin coffee da cake”
Kallon Kilishi tayi itama itan ta kafe da idanu shikam bai jira me zatace ba yayi tafiyarsa ɗakinsa dakin da batamasan inda zata nemosa ba saboda tunda tazo gidan bata taɓayin bangaren da dakin samarin gidan yake ba.
Khaly ce ta miƙe tana cewa “shi Bro ya cika takura yanzun kuma ke ta gangano Wlh ya cika sa aiki bari nakai masa” harararta Hudah tayi tace “Allah yasa ya ɓalle miki ƙafa kazallaha ai yaganmu tun kafin ta fito baice mukai masa ba Saida ta fito ke nifa yau yanayin Bro tsoro yake bani tunda ya dawo sai wani kumbura yake kamar yiss” zama ta nemi guri zatayi Kilishi ta sauke fasali Allah ya sani batason shiga tsakanin mace da mijinta amma hakan shine maslaharsu ta lura idanun Habeeb rufewa sukayi ya manta abinda hakan ka iya haifarwa yanzu abin tsautsayi ba’a tara sani da lamarin ubangiji idan yaje yayi mata ciki kuma ya zasuyi?”

 

_IDAN KIKA KARANTAMIN LITTAFI BAKI BIYANI BA BAN YAFE BA._
[4/19, 9:14 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY

 

KIYIWA GIRMAN ALLAH KI BIYANI HAƘƘINA KAFIN KI KARANTA NORMAL 300 PC 600, KI BIYA TA WANNAN HANYOYIN ACCT DETAILS 0255526235 FAUZIYYA TASIU GTBANK KO KATIN WAYA MTN TA WHATSAPP NUMBER NA 09013718242 ƳAN NIGER ZAKU TURA KATIN AIRTEL 400CF TA WANNAN NUMBER +227 95 04 58 22 SAIKU TUROMIN SCREENSHOT NA SHAIDAR KUN TURA MATA NIKUMA NASAKU A GROUP.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button