Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 43-44

Sponsored Links

 

Cikin ƙunan zuciya ɓarin jiki da tashin hankali ta miƙe tsaye idanunta na ganin duhu ta nufi wardrobe domin ɗauko kayanta tasa Hajiyan ƙofa tace “Matsiyaciya ubanme kikazo dashi da zaki ɗauka? Ina haka akazo dake a cikin tsumma zaki wani buɗe wardrobe kinga maza zo kama hanya kafin dare yayi Miki” lumshe idanunta tayi ta juyo ta dubesu ta girgiza kai zuwa yanzu furucinta ya ƙare batada wata kalma da zata iya furtawa domin kare kanta tabbas komai nisan gona dole zaaje kunyar ƙarshe wannan shine dalili na farko da yasa taji a ranta zata iya rabuwa da Habeeb rabuwa ta har abada.
Ƙofa ta nufa tana shirin fita ta juyo ta dubi Hudais dake bayan Baba Larai kawai sai taji wani kuka ya ƙwace mata ta matsa takai hannu zata kwanceshi, Baba Larai batayi mata gardama ba ta kwanto mata shi Hajiyan ƙofa tayi saurin karɓeshi tana cewa “Allah ya kiyaye ya ƙara raɓar jikin wannan annamimiyar matar maci amanar ƙauna kekam kin cika butulu…..” Wani kallo tabi Hajiyan ƙofa dashi ta juya ta fice da sauri Hajiyan soro na ƙwala mata kira amma bata juyo ba saboda Zuciyarta ta riga ta gama ƙeƙashewa batajin daidai da second ɗaya zata iya ƙarawa cikin wannan ahlin gara ta fita kamar yanda suka shirya tozartata dayi mata ƙazafi.

 

Abin takaici da mamaki wai maigadin da komai a gidan ita keyi masa shine ne cewa da ita “Ummah tagai da Assha” wai harda cewa yake “aje aci gaba da tallan Burkutu…..” Ko tana cikin hayyaci itan ba ma’abociyar kula kowanne shirme bace bare yanzu da takejin jiri na ɗaukar ta bata iya gane komai kawai daɓa ƙafarta takeyi ko ina.
Batayi aune ba batasan meye ke faruwa ba kawai saiji buɗe idanu tayi taganta a gadon asibiti hannunta da ƙafarta nannaɗe da bandeji, ta rinƙa raba idanu tana kallon asibiti da wani irin yanayi na rashin tabbaci.

 

Ji tayi ance mata “sannu!” Ta karkata akalar idanunta kan wanda ke mgnr cikin yanayi na rashin madafa ta zubansa idanu tanason tuno inda ta sanshi shi ta kasa tunawa ganin yana nufota yasata janye injin idanunta daga kansa ta zubawa selling idanu, hakan ya bashi damar matsowa har inda take ya zubanta idanu a hankali yace “inane yanzun keyi Miki ciwo?”
Shiru tayi masa brain nata na tariyo mata dalilin faɗawarta wannan halin ta yunƙura zata tashi da sauri mutumin ya riƙe ta tare da ƙwalawa wata nurse kira suka taimaka mata ta tashi zaune ta dubesu cikin rashin hayyaci tace “kwanana nawa anan?” Kallon juna sukayi namijin yace “biyu” cikin tashin hankali tace “Na shiga uku ɗana Hudais ina yake a wanne hali yake yanzun?” Babu me amsar wannan tambaya tata domin basusan komai game da itaba har gara ma Dr Amin shi yanayiwa yanayinta kallon sani amma ya rasa gane inda yasanta, kalmar ta ɗaya ta sanyashi jin wata faɗuwar gaba ta ɗarsar masa.

 

Hawaye ne ya rinƙa zubo mata wani na bin wani ta ɗago cikin kuka mara sauti tace “Don Allah ku taimaka min ku faɗamin halin da Hudais yake ciki inajin tsoron kada wani abu ya sameshi gashi mahaifinsa baya gari….”
Dafa gefen gadon Dr Amin yayi yace “Kiyi hƙr kinga yanzu bakida lfy ƙafarki akwai ciwo sakamakon accident ɗin da kika samu kuma abinda ke cikinki yana samun barazanar zubewa idan kika cika takurawa da tunani komai zai iya faruwa” batace masa komai ba kuma bata daina kukan da takeyi ba ta kwantar da kanta a cikin cinyarta can ta ɗago tace “Wai nan ɗin wanne gari ne?” Nurse Zainab ce tace “Kina ne Abuja ko kinsan wani anan?” Da mugun sauri ta dago tace meye ya kawoni Abuja…..” Maganar ce ta shaƙeta saboda irin kallon da Dr Amin yake yi mata ta kawar da kai ta fara ƙosawa da wannan mugun kallon nashi da ta rasa dalilinsa.

 

Kwanciyarta Nurse Zainab ta taimaka mata ta gyara Dr ya fita yana cewa Zainab a bata kulawa zanje gda na ɗan huta idan na dawo za’a kwance wannan bandejin aci gaba da treatment din ƙafar a kula sosai” jinjina masa tayi ya dubi Beebah yace “Madam ko kina bukatar a taho Miki da wani abu?” Baisamu arzikin ko daga hannu ba hakan ya tabbatar masa wannan duk inda ta fito miskilar gaske ce bai takura kansa da son sai yaji daga gareta ba ya juya ya fice yanajin wani irin yanayi me nauyi game da ita a zuciyarsa saidai shi da kansa gargaɗin kansa yake yi domin yanayi ya nuna itan matar wani ce ko kuma sakin wani ce.
Da wannan mutuwar jikin ya isa gdansa ya buɗe ya shiga yayi parking ya fito ya nufi kofar da zata sadashi da asalin cikin parlourn gidan ya buɗe ya shiga babu kowa a parlourn don haka kai tsaye ya nufi sama acan ya jiyo hayaniyar yaran ya isa ya bude dakin nasu sunata wasansu suna ganinsa sukayo kansa suna “Oyoyo Dad” kama hannunsu yayi yana musu yar gajerar dariya yace “Ina Mom ɗinku?” Ƙaramin ne ya karyar dakai yace “Yau Mom hutu takeji tace kada mu dameta” yasan ƙiriniyarsu shiyasa ya saki hannunsu yace “Ok kuje kuyi alwala bari nayi wanka nazo muyi jam’in sallar Azahar” shigewa ciki yaran maza guda biyu sukayi da gudu yayi murmushi ya nufi ɗakin uwargidan nasa ya buɗe tana kwance a gado tana latsa waya tana ganinsa ta tashi tanayi masa murmushi ta tarosa tayi hugging nasa tare da kissing ƙirjinsa tace “your are welcome my jannati” shafa kanta yayi yace “Welcome sweeter ya fama da ƙiriniyar yara?”

 

Rausayar dakai tayi tace “Sun dameni habeebty shiyasa nace suje suyi playing games su barni na huta” Safeenah kenan macen gaske ta samu lambar yabo wajen iya kula da miji matsalarta ɗaya baƙin kishi ko kaɗan bata ƙaunar taga wata mace ta raɓi mijinta wannan yasa bata ƙaunar duk wani abu da zaisa mijinta yaji a ransa ta cancanci yayi mata kishiya, ta gwammace ko zatasha wahala itadai tasha indai zata rayu da Dr Amin ɗin ta ita kaɗai, wannan kenan.
Jansa tayi har bathroom sukayi wanka suka fito yaje sukayi sallah su da yaransu sannan suka zauna cin abinci sunacin abincin zuciyarsa na gurin petiant ɗinsa yarinyar ta tsaye masa a rai, yanason jin dalilin barowarta gda shikam yanayinta yana nuna masa duk inda ta fito babban gidane batayi masa kama da matar yara ba.
To yau ɗin ma bai iya bawa Safeenah labarin petiant din tasa da baisan sunanta ba sai ita ce tace “Nikam Sweeter ya labarin yarinyar da kace tsautsayi yasa ka bigeta a Kano Amma ka kawota asibitinka saboda ka bata kulawa?” Numfashi ya sauke yace “har yanzu babu wani labari game da itan saidai yanayi yana nuna itaɗin matar wani ce Inma mutuwar aure tasa ta baro gidanta ko kuma wata babbar damuwa to koma dai menene inason ta kara samun sauƙi sai muyi magana a nutse”
Jinjina kai tayi tare da cewa “To Allah yasa muji alkhairi” amsawa yayi da Amin ya miƙe yace “inajin bacci zanje na ɗan kwanta hudu ki tasheni” itama miƙewa tayi suka tafi ɗakin tare suka kwanta suna ƴar hirarsu ta ma’aurata har bacci ya ɗauke su.

***********

Kwanan Habeeb ɗaya a Lagos hankalinsa ya dawo gida saboda yinin da yayi yana kiran wayar Beebah tana ring amma ba’a ɗagawa, gashi duk wani wanda zai samu bayani ta gurinsa ya kira wanda ya ɗaga ne zaice masa kawai ya dawo gida babu lafiya wasu kuwa basa ɗagawa, lkcn da Najeeb da Hajiya Kilishi suka sanar dashi gidan babu lafiya dare yayi nisa don a kallah lokacin sha biyu ta wucce.
Dole tasa ya kwanan zaune sai wajen asuba ya samu bacci barawo ya ɗauke shi aikam babu shiri ya tashi saboda ko a mafarkin baiga alkhairi ba karfe takwas jirginsa ya daga sai Birnin Dutse yayi saa kuwa Najeeb na jiransa kai tsaye gdansa ya nufa dashi cike da tausayin halin da aminin nasa zai zama a ciki, shidai ya hakikance duk wannan abun da akace ya faru koda Habeeb kamawa yayi da idanunsa yanda yakeson yarinyar nan bazai taɓa yanke hukuncin da Mai Martaba ya yanke wa auren su ba.
Tun daga babban parlourn ya fara fuskantar tabbas gidan ba lafiya lau yake ba domin kuwa babu wata alama da take nuna an gyara shi yau, haka ya kutsa sashin Beebah yana ƙwala mata kira amma shiru yanda yaga ɗakin a hargitse kayanta duk a baje a kasa yasa gabansa faɗuwa ya juya ga Najeeb yace “Batada lafiya ne?”

 

Sunkuyar dakai Najeeb yayi ya riƙe kafaɗarsa da ƙarfi ya jijjigashi yace “Ka sanar dani meye ya faru da Wyf bayan tafiyata?” Janyewa yayi yace “kazo muje cikin gida zakaji komai” to dake neman bayani yakeyi baiyi musu ba yace “nasan ma bazai wucce suna can ba” da wannan suka fita suka nufi gidan sarautar suna zuwa ya fita a motar ko parking Najeeb bai gama yi ba ya shige ciki yana ƙwalawa Kilishi kira, tana ɗakinta tanaba Hudais madara taji kiran nasa gabanta ya yanke ya faɗi tasan yau hauka ne a gidan harsai anyi kamar ayi masa turu.
Miƙewa tayi ta fita yana ganin Hudais a hannunta yace “Ina Wyf ɗin take Kilishi jikin nata ne ya matsa ne?” Sunkuyar dakai tayi hawaye ya zubo mata tace “Tabbas Habeebu Wlh tallahi Habeebatullah bata cikin mutane masu dauɗa da zunubin zina amma kash abin tur da Allah wadarai anyi amfani da wani saurayi da kuma shaidar da maigadin gdanka ya bayar an kitsawa Mai Martaba ƙarya da gaskiya akan cewa tun lkcn daka tafi London Beebah ke kawo maza gidanka sai jiya asirinta ya tonu Habeeb Mai Martaba yayima Beebah korar kare tare da aron bakinka ya datse igiyoyin auren dake tsakaninku, bayan haka kuma ya karɓe Ibrahim daga gareta, wlh tun jiyan da abin ya faru na baza mutane su lalubomin ita don na hakikance wannan ƙazafi ne ƙage ne……….
[5/19, 7:59 PM] AM OUM HAIRAN: _*B

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button