Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 25

Sponsored Links

25

Bin kowannensu da kallo kawai asma’u take sanda suke zayyanawa mummy yadda suka samu gidan ayshan,jin abun take kamar almara,ji take kaman mafarki,tsaye kawai take ta kasa tabuka komai kamar wadda aka zarewa duk wata laka ta jikinta
“Qarya ne….qarya kuke waini zaku zolaya,ta ina yaron oga zai samu irin wannan gidan?,ni zaku tsokana bayan nafi kowa sanin wayeshi,mtseww” Ta fada tana banka musu harara,nusaiba ce tayi caraf ta ciro wayarta ta soma gwadawa asma’un selfie din da suka sha cikin gidan
“Kanbu” asma’u ta lailayo ashar din kai tsaye cike da baqinciki takaici cakude da hassada,zama tayi da sauri gefan gado kusa da nusaiba
“Who is khalipha?” Ta fada tana tambayar kanta,tabbas babu shakka akwai wani daurin boye dangane da al’amarin,tabbas wannan khaliphan ba shine wanda ta sani ba,akwai wani khaliphan boye a bayan khaliphan data sani,ta yaya zata yadda,ta yaya zata amince aysha ta auri wannan khaliphan?bayan duka yaqin da tayi a baya kan hana faruwar hakan,abinda ya dinga kai komo kenan a zuciyarta,cikin fushi da hanzari ba tare data cewa kowa komai ba ta fice daga dakin,tana jin kamar iska ke tafe da ita ba qafafunta ba.

“Aisha….kinga baiwar da Allah yayi miki kuwa?,kinga gidanki aisha?,dama mai kudi zaki aura?” Mero ke fadin haka cikin tsantsar farinciki tana riqe da hannun aishan,sosai takejin dadi kamar ita zata zauna cikin gidan.

Related Articles

Sam bata kawo komai ba tayi murmushi
“Mai rufin asiri dai mero,shima talaka ne kamarmu” idanu mero ta zaro tana dubanta
“Talaka?,alqur’an kada bakinki ya sake fadin cewa shima kamarmu yake,kinsan yadda sama ta yiwa qasa nisa?,to kwatankwacin haka tazarar mu da shi take,kinga gidanki kuwa indo?….bari kigaa a wayata duk da bai dauku da kyau ba” mero ta fada tana ciro ‘yar qaramar torching dinta da mijinta ta saya mata wancan wata bayan ya saida amfanin gonarsa ya samu riba mai yawa.

Dariya take kawai a sanda ta karbi wayar don tana zaton zuzuta abu ne kawai irin na meron,a ido gidan ya qayatar da ita sanda take kallon hotunan,saidai sam bata kawo kanta a ciki ba
“A ina kika samo wadan nan hotunan mero?” Aysha ta tambayeta
“Hotunan gidanki ne da muka je yanzu indo…indo ki godewa Allah,Allah ya miki ni’ima da baiwa wallahi,ba shakka Allah ya fanshe miki wahalarki ta shekara da shekaru,yanzu haka kaf kayan jeranki mun dawo dasu saboda babu wajen da zamu zuba su,hasalima wadanda muka tarar jere a gidan sai namu ya tashi kaman a bola muka tsintosu” dariya sosai aysha ta saki,labarin sai ya nishadantar da ita,don har ga Allah bata yarda da gaske mero take ba,ta daukeshi kawai a shaci fadi ko nishadi takeson sanyata saboda taga alamun damuwa tattare da ita tun dazun kafin su fita,ita kuma ba wannan ne a ranta ba,ummanta take son gani,labarin ummanta takeson ji,kulawa take buqata ta gani daga wajen umminta komai qanqantarta.

Mummy ce ta turo qofar dakin dai dai sanda aysha ke wannan dariyar,dubanta mummy tayi sai ranta ya quntata,tana tunanin tasan komai da hadin bakinta yaron ya lullubesu,ta ayyana a ranta yanzu haka tana dariyar farinciki ne da samun nasara,idanun aysha ya sauka kan mummy sai ta miqawa mero wayarta tana miqewa cikin nutsuwa tace
“Me kike da buqata mummy,da kinyi magana sai nazo basai kinzo da kanki ba” kai ta girgiza ranta na baci,a zatonta tana bacin rai ne saboda aysha sun rufeta,saidai abinda bata sani ba shine tana bacin rai ne saboda ayshan ta samu daukaka da muhallin da autarta bata samu ba,hassada kecin ranta ba tare data farga ba
“Wannan ai yafi qarfin kizo saidai ni nazo da kaina….godiya na taso takanas nayi miki,wato duk zaman da mukeyi dake da yadda muka riqeki ashe ke ba haka bane cikin ranki,kallon maqiyiyarki kikemin,kallon abokiyar adawarki abokiyar gabarki wadda bata son cin gabanki kike min,har ku hada baki da yaron nan ku rufe mana komai sai munje ganin jeranki sannan mu gani,kinsan mai arziqi ne baki gaya mana ba,amma ya zowa a sma’u a wanda baida komai saboda wani baqin nufi dake ranshi,ko ba komai da munsan waye ya bayyana kanshi xamuyi duk shirin daya dace yadda ba za’a ji kunya ba,to na gode da sakayyar da kika yimin Allah ya saka da alkhairi” ta juya tana shirin fita,iya qololuwar tashin hankali aysha ta shige shi,dama ita gwanar hawaye nan da nan ruwan hawaye ya soma layi a fuskarta,bata gane kan me mummyn ke magana ba,me take nufi ne ?batasan sanda ta isa gaban mummy ba ta tareta cikin kuka tana fadin
“Wallahi mummy ba mai kudi bane…talaka ne shima kamata,idan da mai kudi ne anty asma’u ita zata soma sanin hakan,tunda ita ta hadani da shi,ta hanyarta komai ya tabbata har kawo yau…ki tambayeta kiji” ta qarasa fada muryarta na sarqewa
“Ke dalla matsa….dake da asma’un dukanku lusarai ne…kada ma asma’un taji labari…..kunsan waye muhammad abdulhakim mai goro?,kunsan wanne irin arziqi ke gareshi,dukanku baku sani ba,cikin ‘yan sa’o’in aka gayan wayeshi,aisha kin nunan iyakata kuma ina godiya” ta qarasa fada tana kewayeta gami da ficewa daga dakin.

Kuka aysha ta saki har sai da gwaggo asabe sake zaune tana kallon ikon Allah ita da mero suka taso suka riqeta gami da zaunar da ita,tsoro ne fal cikin zuciyarta,ta yaya zata shiga familynsa bayan ya soma dayi mata qarya?,a hakan zai roqeta?,a hakan zai cika alqawarin daya dauka,tana tsoro,tana tsoron faruwar wani abu,don me zai yaudareta,akanme zai ninketa yazo mata da siffar daba tashi bace,yanzu gashi ya hadata da mummyn,ya hadata da mutanen da suka zauna da ita da dadi babu dadi,ba kamar danginta da suka kasa zama da ita ba saboda wani banzan dalilinsu maras tushe wanda baici ace ya shafi rayuwarta ba.

“Ohni sadiya..wai wannan wane irin lamari ne haka yake faruwa?,indo wadanne irin mutanene haka kike zaune da su?,tunda muka zo daga wannan sai wancan?” Cewar gwaggo cikin bacin rai da tashin hankali.

Miqewa tayi tsaye ta dubi su mero
“Ina zuwa” ta fada kawai kana ta fice,da hijabin data idar da sallar azahar a jikinta don haka bata da buqatar sanya wani abun.

Parlourn daddy ta nufa kai tsaye,tayi qoqarin daidaita nutsuwarta sannan tayi sallama ta kutsa kai,su biyu ne zaune a falon shi da anty safiyya,da alama wata magana suka gama tattaunawa ko suke kan tattaunawar,dukkansu shuru sukayi ganin shigowarta falon,kai tsaye ta isa gaban daddy ta duqa tana hawaye
“Daddy don Allah ka kirashi ki bashi haquri ka gaya masa ka fasa bashi aurena,daddy bazan aureshi ba,bazan iya zama cikinsu ba” anty safiyya zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu sannan ya maida hankalinsa wajen aishan
“Saboda me?” Ya tambayeta
“Daddy….yazo min da siffar daba tasa ba,ya yaudareni daddy,wannan ha’inci ne daddy,a haka zanje na zauna da su?” Kasa daurewa safiyya tayi sai data furta
“Aisha,anso kashe rayuwarki ne Allah ya raya ta,an hadaki dashi saboda ana tsammanin bashi da komai Allah sai ya kaiki hannun mai komai din,wannan kadai bai isa ki godewa Allah ba?,wannan abun da kike fada tamkar butulcewa Allah fa kikeso kiyi”da hanzari ta daga kai tana kallon anty safiyya,akwai wani abu,akwai wani data sani kenan game da yadda auren ya qullu?
“Aisha” daddy ya kira sunanta bayan ya dakatar da safiyya
“Me yasa baki gayamin tun farko yadda abun yake ba kika ja bakinki kika yi shuru,kina zaton da an tafi a haka na hadaki aure da shi Allah bazai kamamu ba mu duka?”fada sosai daddy ya dinga yi irin wanda bai taba yi ba,alama ranshi ya baci sosai,kuka ta dinga yi tana bashi haquri,yace sam nauyin bakinta baiyi masa ba,haquri ta bashi da alqawarin ba zata sake ba,daga bisani ya kwantar mata da hankali da bata labarin farkon sanin daya soma yiwa khalipha a rayuwarsa.
“na sanshi can shekarun baya masu yawa ta sanadin faduwar jakar kudadena,kudade ne masu yawa wanda banda kudaden akwai muhimman takarduna harda na kamfani na,sosai na shiga tashin hankali a sannan,saboda matuqar kudaden suka bace a sannan tsaf zan iya shiga talauci bana wasa ba,cikin ikon Allah kwanaki uku da faruwar haka aka kira wayar kamfani na akace ni ake nema kan kudina dana yar,nayi murna sosai na buqaci inda zanje mu hadu da wanda ya tsinci kudin,ba bata lokaci ya bani adress din gidansu,yace nayi haquri,yana da wani uzuri ne da baya barinsa ya fita daga gida da da kansa zai kawomin,nikam a sannan kota kan hakan baibi ba,saboda ko a qafa yace min na tafi wata qasar na amso zuwa zanyi
Sanda na isa gidansu nayi matuqar mamaki,gashi dai gida har gida irin ginin masu kudi da wadata na sannan amma kana masa kallon farko zakasan babu da talauci ta tasamma yi masa raga raga,mamaki na bai sake qaruwa ba sai dana shiga na tadda matashin dan shekara ashirin na jiyyar mahaifiyarsa magashiyyan rai a hannun Allah da qannenshi maza guda biyu,kana kallonsu kasan kuka suka gamayi dukansu,sanda na amshi kudin na tambayeshi nawa yakeso ga mamakina sai yace min babu komai,alfarma daya yake da buqata na biya kudin aikin mahaifiyarsa ta rabu da zafi da radadin ciwon da take fama da shi,na zaci zai buqaci sama da haka,amma sai yace min buqatarsa kenan,matsanancin ciwon suger take fama da shi wanda shi har takai ga ya taba mata qoda za’a mata aiki.

Muna tsaka da wannan maganar saiga ‘yan sanda katsama kanmu,miqewa naga khaliohan yayi yayin da suka yo kanshi kamar kura ta samu nama syka cukuikuyeshi,yayin da yajeta rantsuwa yana fadin bashi bane,matashi dake bayansu yana cewa
“Karku saurara masa,qarya yake ku dakeshi”ni na miqe na musu magana,sannan na tambayi ba’asi,nan dan samdan yace ana tuhumarshi ne da yiwa yarinyar wan babanshi fyade,kuka yake sosai a sannan yana rantsewa da duk abinda yasan me girma ne kan bashi bane,yanayin nagartar yaron ya sakamin tantama kan zancan,naja daya daga cikin ‘yan sandan waje nace ya gayamin gaskiyar magana,na masa alqawarin kudade mai tsoka,nan yace ba shakka bashi bane,amma alhj idris da yaronshi ibrahim su suka biyasu kan kada au saurara idan sunzo su kamashi,daga nan su kaishi kotu ma birsin sukeso yayi,don ya matsa kan maganar gadonsu,a take na gaya masa sunana sai yayi sororo,na kira sauran ‘yan sandan na sallamesu duka da wani abu,nan ibrahim yahau min hauka,nace koya wuce kona makashi kotu kan ya yiwa khalipha qazafi,haka ya wuce don kada allura ta tono garma,kuka sosai ya dinga yi mahaifiyarsa dake kwance tana tayashi,haka qannensa maza guda biyu,a sannan naso jin labarin rayuwarsu amma sai naga bashi yafi muhimmanci ba,lafiyar mahaifiyarsa itace gaba,muka je asibitin na biya duk wani abun da za’a buqata a aikin,hatta da abincin da ita da su zasu ci,cikin nasara akayi aikin aka gama lpy ta kuma samu sauqi,ina da niyya da shirin taimakon rayuwarsu tafiyar gaggawa ta sameni russia,wanda ban dawo ba sai bayan watanni shida,dana dawo su na soma nema sai na tadda sun saida gidan sun tashi,kuma ba’asan ina suka koma ba,dole na haqura da neman nasu naci gaba da saka yarona addu’a,don gaskiya nasp na riqeshi d’ana,saboda gaskiya amana da hankali da nutsuwar da naga yana da ita,uwa uba yadda naga yanason mahaifiyarshi yana tattalinta,nasan lallai sai yaro na gari ne kawai zai hada wannan nagartar”

Dukansu shiru sukayi suna jinjina labarin,yayin da zuciyar aysha ta soma kuma rabuwa gida biyu,
“Kije kici gaba da addu’a ina da tabbas kan khalipha aysha…Allah ya baku xaman lafiya” anty safiyya ce ta amsa ayshan ta miqe cikin sanyin jiki tabar falon.

Sosai ranta ya dinga baci,hassada nacin ranta ba tare data sani ba,ta yaya ma aysha zata samu irin wannan gidan?,wayarta ta ciro ta soma neman tsohuwar lambarsa da suke waya,so take taji ta bakinsa,so take taji dalilin raina mata wayon da yayi tunda fari,saidai amsa daya ake bata is switched off,gani take ma kamar akwai wata a qasa,kaman ayshan ita ta shirya komai,wani irin gumi take ita kadai qwaqwalwarta na kaikawo,hakan ya sanya ta tashi don fitowa daga dakin sukayi kacibus da mummy a bakin qofa,duban asma’un tayi
“Kina jin sunan muhammad abdulhakim mai goro?” Kai asma’un ta kada,sosai ta sha jin sunan ko a bakin hamid ma
“Shine khalipha yaron da zai auri aysha” cikin qanqan da idanu take duban mummy,kamar tana zaton mummyn zata sauya zancan data gaya mata
“Mummy da gaske?”
“Ina wasa dake?” Ta fada itama a dan zafafe,sai kawai asma’un ta kewaye mummy ta fice da hanzari zuwa dakin aysha.

A sanyaye ta koma dakinta,su mero suka zuba mata ido saidai ba wanda ya iya tambayarta komai,bankado qofar dakin da akayi shi yaja hankalinsu su duka suka daga kai suna kallon bakin qofar,gabanta ta qaraso yau qarara muraran take jin haushinta da kishi da ita ba tare kuma da tana da wani sahihin dalili kan hakan ba,wayarta ta cilla mata saman cinyarta
“Ke saka mana number khalipha wadda yake using da ita” a natse ta daga kai ta kalleta,tunda suke da ita yaune karo na farko data kirashi da khalipha sak ba yaron oga ba
“Waye khalipha?”harara ta watsa mata sannan tace
“yaron oga nake nufi”
“Ke da kika soma hadani da shi inaga ke zaki fi kowa samun lambarsa” ta furta anutse sannan ta miqe ta nufi toilet,wanda sanadiyyar tashin nata wayar ta subuto ta fadi qasa,hakan ba qaramin bata ran asma’u yayi ba

Cikin zafin nama da salo na huce haushi da takaici asma’u ta damqo hijabin aysha tana cewa
“Dawo dan uwarki….” Wani wawiyar fincika aysha ta yiwa hijabin nata cikin bacin rai da quna,duk yadda take da mahaifanta bata sake a zagesu,duk yadda suke duk kashinsu dai iyayenta ne,hakanan ba’a sauyawa tuwo suna,wani kallo ta watsawa asma’u,wanda hakan ya dan firgitata,saboda yadda lumsassun idanun ayshan masu kama dana wanda kejin bacci suka bude sosai a yau
“Karki kuskura ki sake zagemin mahaifiya….wannan shine kuskure na farko da zakiyi dana sanin aikatashi a kaina” tuni mamaki ya kashe asma’u,yau itace aysha ke maidawa magana haka gatsal kai tsaye,ayshan dako duka zata kai.mata ba zata daga kai ta dubeta ba,lallai abinda take gudu yana gaf da afkuwa,wato daga jin labarin wanda zata aura har ta soma komawa haka kenan?,lallai dole ta gaggauta daukan mataki tun wankin hula baikaita dare ba
“Ni aisha ni kikewa haka?” Ta fada cikin tsananin mamaki tana nuna kanta,bata tanka mata ba ta juya ta shige bandakin,itama asma’un sake juyawa tayi ta fice fuuu daga dakin zuwa falon daddy.

“Daddy ka dakatar da shi,kar kayi kuskuren aurawa aisha shi,mayaudari ne kuma maqaryaci ne shi,labarin haka yanzu ya zomin,daddy ka dakatar da aurensu” tsai dadddyn yayi yana kallonta ya kafeta da ido harta gama,bai taba tsammanin haka halayyar asma’un take ba sai yau,yaushe ta debo dukkan wadan nan dabi’un oho bai sani ba
“Jeki kiramin mahaifiyarki ku taho tare” ranta ne yayi sanyi,tana zaton zata cimma gaci taje ta taho da mummy,saidai kalaman daya soma furtawa da bude mata dukkan plan din data qulla kan aishan har Allah ya qaddara zata auri khalipha ya girgizata,ga akayi daddy yasan da dukka wadan nan abubuwan?,ya mata tas har hakan ya sanyata kuka mai yawa,tare da qara mata tsanar aisha,sosai yayi mata kaca kaca bai saurara ba,mummy tayi tsumu tana jinsu,ta kasa sanya baki saboda ita batasan ya zasu qarke ba ita da shi.

Haquri ta dinga bashi ta dinga bashi,tare da yi masa alqawarin ba zata sake maimaita kuskure makamancin hakan ba,ya umarceta taje ta nemi yafiyar aysha duk da Allah yayi mata sakayya,bayan ya sallameta mummy ya dirarwa,wanda hakan ba qaramin bacin rai ya haifar ba,ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,ta nuna masa ita batasan meke faruwa ba,ya qalubalanceta ya kuma bata laifinta,haquri itama ta bayar cikin kissa tare da kwantar da kai,saboda bata son wani abu mara dadi ya bullo da zai bata bikinsu,tilas daga qarshe yayi haquri tare dayi mata gargadi mai qarfin gaske ta kuma amsa dukka laifin.

Shigarta toilet din alwala ta daura ko zata ji sauqin bacin ran dake yankar zuciyarta,saidai har ta fito hawaye bai yanke saman fuskarta ba,gefan gadonta ta zauna kai tsaye ta dauki wayarta,wannan karon babu fargaba ta kira mahaifiyarta,gab da zata tsinke aka daga
“Waye?” Aka tambayeta kamar yadda ta saba,alamu dake nuna har yau bata da matsayin da zati serving na numberta
“Nice ummi…Aisha ce ‘yarki”
“Sau nawa zan fada miki ki daina kirana kafin ki gane abinda nake nufi?” Ta fada cikin salon tambaya,kafin aysha tayi yunqurin cewa komai ta ja tsaki gami da yanke wayar,kuka aysha ta saki mai sauti idanunta akan gwaggo asabe,a hankali ta tashi zuwa inda take ta zauna gabanta sosai tana dubanta
“Batasan zanyi aure ba…ba zata zo bikina bare na samu kowacce albarka da diya ke samu a wajen mahaifiyarta duk lokacin data tashi tafiya gidan miji,duk wata matsalata ni kadai na santa,ban taba dan dana dadin uwa ba,gwaggo…ke kadaice fata na na qarshe,ke kadai nake saka ran zan samu amsata daga bakinki…gwaggo…don girma da daraja ta annabin rahama ki gaya min…me na yiwa ummi na?,me na aikata mata haka daya saka ta tsaneni?,meye laifina meye kuma aibuna?” Ta qarashe maganar tana fashewa da kuka mai fidda sauti gami da kifa kanta saman cinyarta,hannu gwaggo asabe ta dora saman kan ayshan,tana jin dukkaninsu basu kyauta,dukansu masu laifi ne,suma kuma suna da tasu gudunmawar da suka taka wajen baqincikin da ayshan ke hadiya,a yau tana jin zata gayawa aysha dalilin wannan wakaci kaa tashin dake faruwa tsakaninta da mahaifiyarta,dukkaninsu a lokacin duk da sunji zafin abun basu zaci zaiyi tsanani har haka ba,ita kanta gwaggo asaben da take ‘yar uwa ga ummin nata abun na bata haushi da takaici gami da mamaki,tamkar sake rabasu akayi bayan wancan dalilin daya zama silar wanzuwar komai
“Na roqeki gwaggo ki fiddani daga duhu izuwa haske,ki warwaremin wannan DAURIN BOYEN,na jima cikin zullumi tashin hankali tsoro da firgici saboda irin qiyayya qarara da nake ganowa daga idanun mahaifiyata….me yayi zafi gwaggo?” Ta qare da sigar tambayar kamar zata shide numfashinta zai tsaya
“Yau xan baki labari indo…yau in sha Allah ba zaki sake kwana da tunanin kin aikatawa mahaifiyarki wani laifi ba” ta fada tana sauke ajiyar zuciya,mero da ita tayi saura a dakin saboda karime tana waje bata shigo ba,saboda kusan itama tabi sahun ‘yan takaici da jimami,dubanta gwaggo asabe tayi
“Zauna mero…..baki zama wata bare ba ko baquwar al’amarin”komawa tayi ta zauna tana tattara hankalinta wajen gwaggo asabe kamar yadda aysha tayi,shuru ne ya ratsa dakin kafin daga bisani gwaggo tace.

“kamar yadda kika sani cewa dangin mahaifinki fulani ne gaba da baya,yayin da mu dangin mahaifiyarki muka kasance manoma ne,har kakanki kafin Allah yayi masa rasuwa ya kasance sarkin noma na qauyenmu,fadan manoma da makiyaya fada ne daya jima yana wanzuwa tsakanin wadan nan mutane guda biyu,fada ne daya janyo asarar rayuka da dama,ya janyo asarar dukiyoyi rashin kwanciyar hankali da lumana,ya kuma janyo gurbacewar mu’amala tsakanin manoma da makiyaya,to wannan abu ya shafi qauyenmu,duk da cewa mu ba’ayi kashe kashe ba,amma rashin jituwa ya shiga tsakani da sabani mai girma,kowa ya tsayawa bangarensa,kowa yana goyan bayan dan uwansa da yake jin labari a can wani yanki an kashe ko anci zarafinsa,hakan ya kawo silar daya zama manoma da makiyaya basa ga maciji a tsakaninsu,a irin wannan ne Allah ya hada soyayya tsakanin mahaifinki baffale da mahaifiyarki,suna tsananin son junansu qwarai da gaske,sam basuyi duba da abinda kaje ya kawo ba,basuyi la’akari da abinda ke faruwa tsakanin jinsin biyu ba,soyayyarsu kawai suka saka a gaba,sanda soyayyarsu ta bayyana,kowa cikin gidansu sunja daga kan daya bazai auri daya ba,duk wata hanya ta rabasu anbi amma sunqi su rabu,junansu kawai suke so,bana mantawa mahaifiyarki ansha jibgarta a gabana amma bata sauya zani ba,a haka suka ci gaba da gudanar da soyayyarsu ba tare da sun yarda da qudurin raba su ba.

Sanda suka tada maganar aure gagarumar rigima ta barke cikin qauyenmu,abu har ya kai gaban alqali,inda yaja kunnen iyayen da su qyale yaransu suyu aure tunda suna son junansu,mai yiwuwa hakan ya zama silar kawo zaman lafiya a tsakani.

Toh tun asali mahaifiyarki macace mai zafi fada da kuma fushi,tana da wuyar saukowa a fushi idan ranta ya baci,hakanan bata yarda a take haqqinta ko waye zata qwaci kanta a hannunsa,tana da riqo idan ka bata mata,saidai takan sauko idan ka nemi yafiyarta,dalili kenan daya sake taka rawa wajen kawo hatsaniya tsakaninta da matar babanta inna kulu,kowa cikin fadin garin yasan ta da wannan hali,hakan ya sanya kaf ‘yan matan qauyenmu ba yarinyar dake kawo mata wargi,mahaifiyar baffale ta miqe ta fadi wannan halaye nata,ta kuma ce ko donsu ba zata bari danta ya aureta ba,ba zata hada jini da ita ba.

An buga sosai kafin daga bisani Allah ya qaddara cewa sai baffale ya aureta,biki akayi sosai kasancewar tana da dangin mahaifiya a nan cikin birni,an mata komai na gata,jeran da babu tamkarsa,hakan ya sake hura wutar kishi a zuciyar faccalolinta tun kafin ta shigo,don duk cikinsu ba wadda ta samu irin gatan data samu,hakanan yadda baffale ke take take a kanta babu wadda ta samu irin wannan soyayyar.

To wani irin zama zance tayi cikin gidansu mahaifinki,tsakaninta da mijinta salamun salamun,zaman lafiya suke da qaunar juna,hakanan yana nuna mata qauna ko a gaban waye,nan fa qananun maganganun cikin faccalolinta da gutsiri tsoma suka soma yawa,kowacce kishi take da ita,saidai sunsan halinta duk wadda ta tareta gaba da gaba ta gaya mata maganar banza tofa itama ranta sai ya baci,ba zata qyale mace ba,suka dinga gutsura magana suna yiwa surukar tasu nuni data saka ido a rayuwar gidan baffale,suka karanta mata da alama ta mallakeshi,kasancewarsa shine qarami hakan yayi tasiri a ranta nan da nan,sannan uwa uba ga kuma kallon da take mata na yarinya mara kunya mara dagawa kowa qafa fitsararriya,nan fa aka fara sa toka sa katsi tsakanin su,mahaifiyarki ita kadai tsakanin faccaloli da uwar miji,amma da yake jarumar gaske ce duk ta iya da su,ta tare iskancin kowa,kuma bata fasa nuna soyayya da kulawa mijinta ba,tana matuqar sonshi hakanan tana kiyaye duk abinda baiso gami da bashi amanna,ta bashi yarda ta sakankance kan cewa bazai taba tozartata ko wulaqantata ba,mu kanmu a sannan mun jinjina mata da irin qoqarin zaman da tayi,a haka ake zaune har tsahon shekara guda,bata taba haihuwa ba sai bari da take yawan yi a kai akai,da wannan kuma suka samu dama suka tasa ta a gaba da habaici da gori,ba uwar mijin ba ba faccalolin ba.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
(08030811300)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button