Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 27

Sponsored Links

27

*Dimbin godiya a gareku masoyan da basu manta halacci da alkhairi*????????????

_Alhamdulillah,wato haka rayuwa take,a duk sanda ka dage kan ka karya wani ko kaga bayanshi matuqar Allah na tare da shi aikin banza kake,matuqar zuciyarsa a tsarkake take zaiyi wuya kaci galaba a kanshi,koda dukka mutanen duniya aljanu da bil’adama masu taimaka maka ne wajen ganin durqushewar wani,a sanda ake fafutukar fidda litattafanmu kota halin qaqa,sai hakan ya zame mana tamkar wata silar alkhairi a garemu,a lokacin ne wasu jama’a ke ninka farashin da muka sanyawa kowanne littafi namu ninkin baninkin su sayeshi a haka saboda sanin daraja da mutuntuka,da kuma zuciyar da bata manta alkhairin mu a garesu a baya,DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI_

Related Articles

 

 

 

Qarfe sha daya na dare ta fita da kwanukan da su baba asabe suka ci abinci,ta bari ne zuwa sannan tana zaton ba kowa falon,idan ma sun dawo daga wajen dinner din tana tsammanin kowa ya tafi makwancinsa,ganin yadda kitchen din yake a hautsine sai ta kasa tafiya ta barshi haka,ta tsaya tana kikkintsa shi tare da gyara abinda zai gyaru a sannan tunda dare ya riga yayi.

A haka lantana daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta tadda ta
“Lallai indo a gaisheki da qoqari,amarya guda da gyaran kitchen?,lallai” ta fada tana kama habarta alamar mamaki,da murmushi a fuskar aysha ta juyo ta kalli lantanar
“Banda abinki lantana wannan kitchen haka komai a hautsine,ta yaya zakuji dadin yin aikin?” Baki ta dan tabe tana aje farantan hannunta
“Wallahi gajiya nahi aisha….tun safe kana tsaye…ka gyara a bata,kowa kuma da kiran da zai maka….dama kuma kece mai juriyar,nikam nayi iya yina na gaji”
“Allah ya rufa asiri”
“Amin….ai gwara kiyi mana ma na bankwana,zamuyi kewarki wallahi indo” inji lantana tana nuna alhininta a fuskarta zuwa zuciya,sun saba da ayshan saboda sauqin kanta,hakanan sau tari takan amshe ayyukansu tayi idan tana da lokaci,ba ruwanta da qyamar mutum ko girman kai,ba kamar asma’u ba da basu taba jin dadinta ba,ayshan bata ce komai ba sai murmushi da tayi,wanda banda lotsawar da kumatunta yayi ma ba zaka gane hakan ba,kama mata lantanar tayi suka soma gyaran tare.

Basufi mintuna goma ba suka soma jiyo tashin hayaniya daga falon gidan,a hankali muryar anty safiyya tafi ta kowa fitowa
“Mu zasu nunawa iskancin banza iskancin wofi…mu zasu nunawa arziqi?,dama tun ranar kamu nake kula da take takensu,kai tun ranar kawo kaya,ina ruwanmu da wani familynsu ko arziqinsu,abinda muka sani kawai shine mun basu auren ‘yar uwarmu,hakanan muma ba’a talauce suka ganmu ba bare suyi mana dagawa” ta qarashe fada tana huci
“Ke kinga yadda suke wani daddaga hanci da kallon kowa d’ai d’ai kamar kansu aka fara kudi,kina fa gani da muka shiga yiwa ango da amarya liqi sauka sukayi daga kan stage dinfa….” Anty kubra ta fada cikin jin haushi itama
“Su taka a hankali mi tsaf zan kora musu jawabi wallahi…ai muma ba tsiya suka ga tana binmu ko?….koma tsiyar ce a haka dansu yaga yarmu yace yana son aure” anty hajja wadda take qanwace ga momy ita ke binta ta fada.

“Kowa ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa….tun daga yanayin halayyar yaron ya kamata su gane kowanne tsuntsu kukan gidansu yakeyi,don dai kai kawai baka isa ka fada bane baka da ikon gin magana” lantana ta fada,itadai aysha bata ce komai ba,tunda ba huruminta bane,har suka kammala ta wanke hannunta ta yiwa lantana sallama ta juya tabar kitchen din.

A kacame ta tadda falon,asma’u na kumfar baki anty safiyya nayi,da alama wani abun ne ya sake faruwa,tana jin anty safiyya na cewa
“Nikam babu matar data isa na sake jera kafada da ita bare ta wulaqantani bayan Allah bai wulaqantani ba,kije ku qarata ke dasu ke kika zabarwa kanki…banda shi mara mutunci ne har yace ki baiwa yan uwansa haquri sannan ya saurareki?” Cikin kuka asma’u tace
“Kinji ko mummy….wallahi ki mata magana,kinga zata jawo min matsala ko….nasan halin hamid wlh tsaf zai tsiri fushi da ni qarshenta ma sai wani satin za’a qarasa wani abun…nidai ki mata magana kawai”
“Ai na haifu,kuma ‘yar halak ce ni…kije Allah ya bada sa’a” anty safiyya ta fada tana barin falon,ta haura sama dakin da suka sauka ita da sauran ‘yan uwanta.

“Maganar gaskiya asma’u nima fa naji haushi…kuma hamid ya bani mamaki…ban zaci haka yake babu kwalli a idanunsa ba,giyar kudi na dibansa kenan?” Cewar anty kubra wadda sakuwa ce ta asma’un
“Kinga don Allah bana son qananun maganganu,nice dai zan aureshi na zauna da su,kuma naji ina son abina a haka ko yaya yake tunda shima yana sona” ta fadi cikin fada tana tasowa kubrar kamar zata doketa
“Allah ya bada sa’a” itama ta fada tana barin wajen,sai asma’un ta fada jikin mummy tana rushewa da kuka,duk sun hada mata zafi,gaba daya bikin yana neman juye mata,yaqi zuwa mata a dadin rai yadda taso,ga wannan tirka tirka da takeao ta kunno kai tsakanin dangin hamid din da nata,gefe guda kuma maganar aysha har yau na cin ranta,ba kamar yauma da take sake tambayar hamid waye muhammad abdulhakim mai goron,a yadda yake gaya mata waye shi ta tsorata matuqa,tana tsoron faruwar wani anu,tana tsoron kada reshe ya juye da mujiya,batason abinda zai sanya ta kasance itace a qasa har abada,koda yaushe tafison taga itace a sama sama da kowa.

????????????????

Qarfe goma na safiyar washegari suka kammala shirinsu na wucewa takai,a sannan har aliya itama ta iso,ta ishi aysha da tambaya kan maganar data ce zasuyi,murmushi tayi kawai tace
“Me kike ci na baka na zuba?,zamuyi ai”.

Sallamar lantana ita taja hankalinsu
“wani ne a waje yake jira wai an turoshi zai kaiku takai” cikin mamaki aysha ke kallon lanta
“Mu kuma?…takai?” Ta fada tana tunanin waye haka zai aiko?,iya tunaninta bata gane ko waye zai mata wannan karamcin ba,hakan yasa dole ya zira hijabinta tace
“Zo muje aliya inga ko waye” suka fice daga dakin.

Tun daga nesa ta gane baquwar mota ce ba irin ta gidansu ba,saidai bata iya ganin waye a ciki har ta qarasa gaban motar ta tsaya,murfin motar ne ya bude,wani matashin dan kimanin shekaru arba’in ya fito,cikin girmamawa yace
“Ranki ya dade boss ne ya aiko ni….ina fatan kun kammala shiryawa”
“Wanne boss?” Murmushi yayi sannan yace
“Wanne boss ne bayan muhammad khalipha?” Hannunta ta daga
“Ohk….ka koma kawai,zamu bi motar haya” ta fadi tana kama hannun aliyar dake binta da kallon tambaya suka juya.

Tana gab da shiga falon wayarta ta dauki ruri,dubawa tayi K ce ta bayyana kamar yadda tayi serving number dinsa

Numfashi ta aje sannan ta daga wayar ta kara a kunneta
“Me ya faru tsakaninki da sani,yace min wai ance ya tafi”
“Bbu komai,zamu bi motar haya ne kawai….”
“Bai dace ba aysha…maida hannun alkhairi baya fa kenan?”aliyata fada tana tsaye daga gefanta
“Aliya….kin san waye?”ta fada tana kallon hanya ba tare data dubi aliyan ba
“a’ah”ta bata amsa tana girgiza kanta dukka idanunta da hankalinta na kan ayshan
” khalipha ne fa aliya,wanda zan aura”
“Arrrrrrhhhhh” aliya ta fada tana rufe bakinta da tafukan hannayenta duka biyun kamar mai maitsoron kar wani yaji ihunta,idanunta a waje hakanan fuskarta qunshe da murmushi
“How comes sashen….tell me pls” juyowa tayi tana duban aliya,hannayenta harde a qirjinta,fuskarta a hade tsaf
“Khalipha ya saka min shakku mai yawa a kansa aliya….ta yaya zaizo min da wata fuska?,ta yaya zaizo min da wata siga?….a yadda khalipha yazo min aliya ashe ba haka bane….wannan ba yaudara bane?”
“Ya salam…..haba…ni nasan kaman na taba sanin face dinshi a wani waje wlh…kaman ya taba zuwa wajen abba na…oh my god…ina zuwa” aliya ta fada tana zame hannunta daga riqon data yiwa aysha,da sauri sauri kaman wadda zata tashi sama ta koma qofar gida,da idanu aysha take kallonta tana mamakin saurin me take ina zata?,me yasa bata ga alamun jimami ko tayata bacin rai kan abinda khaliphan ya aikata ba?.

Tana nan tsaye kaman sakarya har aliyan ta dawo fuskarta washe da fara’a ta kama hannun aysha ta jata zuwa ciki,a parlour suka ga asma’u zaune sanye da kayan bacci,kaman ko yaushe tana saqale da earpiece a kunnenta da alamu ma waya take,harara ta danqara musu wadda kowaccensu ta ganta,wata fara’a ta musamman aliya ta qirqira tana sake riqe hannun aysha sosai tana cewa
“Kinsan me goro family kuwa aysha?….ai ke Allah ne ya tarfawa garinki nono,dare daya dama Allah kanyi bature…” Ta qarashe fada suna tura qofar dakin ayshan suka shige,hannunta aysha ta cire bayan sun shiga din tana kallon aliya gami da kallon qofar dakin nata kaman wani zai shigo,dariya aliya ta bushe da shi har tana duqawa kadan
“Banson fitina aliya kin sani ko?” Ayshan ta fada a narke kamar mai shirin sanya kuka,bata tanka mata ba sai taja hannunta zuwa bakin gadon ayshan ta zaunar da su a tare sannan ta kalli gwaggo asabe
“Gwaggo kiyiwa aysha fada taiwa kanta fada…mijin da Allah ya bata da don jama’a da dama ne ba zata sameshi ba,bama shi ba gwaggo ko mai gadin gidansa ba zasu yarda ta aura ba….duk bata duba haka ba zata tsaya tana wani goce goce maras tushe ko dalili?,khalipha kaman wani tsanin ki ne na fita daga tsangwamar da kika dade kina fuskanta tsahon rayuwarki,Allah ya sani baki ma sanshi ba bare kiyi kwadayin abun hannunshi koda jama’a zasu fadi hakan,ke kinfi kowa sanin kanki,kinfi kowa sanin wacece ke” ta fada tana duban idanun ayshan kai tsaye sannan ta dafa kafadarta
“So pls aysha….ki nutsu ki fuskanci gabanki kawai….” Ta fadi tana sauke hannunta sannan ta cewa su gwaggo
“Ku shirya da sauri gwaggo….angon ya turo driver shi zai kaimu har qofar gida”
“To ma sha Allahu….kinga mun huta hawa ta haya kuwa” gwaggwon ta fada cikin farinciki,sannan daga bisani tayiwa ayshan dan fada da jan hankali,itakam kawai tana zaune tana jinsu,amma harga Allah tana da fargaba…su asma’u kawai sun isheta isharar tsamiyar talaka da mai kudi bata jiquwa waje daya…masu kudi basa qaunar talaka sam,kansu suke so,isu isu suke mu’amala da junansu,amma koma meye ta miqawa Allah zabinta.

Tana zaune waje daya kawai tunda ta gama nata shirin tana binsu da ido wayarta ta dauki qara,ta duba batasan number ba sai ta daga ta kara a kunneta tayi shuru ba tare data ce komai ba taji waye
“Assalamu alaikum warahmatullah” ta jiyo muryar wata mace dattijuwa,cikin mamaki ta amsa sallamar tana son taji wace
“Ina fata aishatu ce” a ladabce ta amsa saboda yadda muryar ke nuna shekarun mai maganar
“To ma sha Allah….me ya faru na saka khalipha ya turo muku driver ya kaiku,sai naji yana waya da driver yana gaya masa ya dawo kawai?” A take ta gane wace,anni ce duk da cewa baifi sai biyu ta taba jin sunanta daga bakinsa ba,diriricewa tayi gami da tsorata kamar wadda ta yiwa sarko qarya har hakan ya bayyana saman fuskarta,aliya dake gefe wadda ke jin duk abinda ke faruwa saita amshi wayar,gaisawa sukayi sannan tace
“Qawar aysha ce,bamu gane waye ya turoshi ba sai daga bisani….amma yanzun haka ma gab muke da gama shiryawa mu wuce”
“To madalla…na zaci daga khalipha ne…Allah ya tsare hanya…a gaida mutanen gidan”
“Amin zasu ji,mun gode” daga haka ta katse wayar itama aliyan ta sauke tana murmushi qasa qasa,hannu ta saka ta daki bayan ayshan
“Saikin biyani ladan yin lauya….haka zakije ki dinga musu wannan sanyin naki da tsoro?…uwar mijinki ce fa ta kira” idanu aysha ta zaro tana duban aliya
“Ke…uwar mijin wa?…mamana zaki ce,a matsayin yayana yake ni da shi babu zancan miji da mata” idanu aliya ta saka tana kallon ayshan,sai kuma tayi turus ayshan tana duban dakin,Allah yasa su biyu ne su gwaggo sun soma fita da kayansu ana kaiwa mota
“Kaman yaya ban gane ba,yimin bayani….”
“Share kawai” ta fada tana miqewa gami da saba jakarta a kafada,itama aliyan tashi tayi tana rataya tata
“Wallahi baki isa ba yarinya kinyi kadan,tunda kika fara fada dole ki fada duka” murmushi tayi tayi gaba…itama tasan hakanne,ba wani boye boye tsakaninsu,idan ta boye dinma tana da wanda zata gayawa ne daya fita.

A parlour aliya ta toge aysha ta haura sama yiwa mummy sallama
“Mummy zamu wuce…sai mun dawo”a watse ta amsa tana sabgar gabanta,bata damu ba ta miqe ta fito,nan suka ci karo da anty safiyya,da fara’a take dubanta
“yanzu shikenan haka zaki tafi ba dan rakiya?”
“Ba komai anty muna tare da aliya da mero,ga gwaggo asabe ga baaba karima”
“Shikenan….sai ranar lahadin kenan”
“Eh in sha Allahu” ta fada tana duqar da kanta qasa kadan alamar kunya
“To Allah ya nuna mana,don Allah ki gaidasu ,abinne ya hade mana lokaci guda”
“Zasuji anty” har ta juya anty safiyyan tace
“Ammm…aysha zo aliya ta kawo min qararki” waiwayowa tayi ta dawo rana taraddin me ya faru,a tausashe take mata magana
“Bana son inji wata baraka tsakaninki da khalipha,tunda ba wani mugun hali nashi ya boye miki ba sai yanzu ya bayyana,abinda ya farun me yiwuwa haka tsarinshi yake,yaso daukar asma’u amma Allah ya duba ba kalarshi bace bata dace da shi ba sai ya hada tsakaninku,kinsan komai basai na miki bita ba,kuma koda baki fada ba da bakinki kin sani cewa Allah ne ya qwata ya baki,ya lullube asirin komao bada wayon khalipha ko plan dinsa ba,wannan shirin Allah ne,so don Allah aysha banson jin komai”
“In sha Allahu anty…na gode”
“Yauwa Allah ya tsare hanya”
“Amin anty” daga haka suka rabu ita ta sauko qasa ita kuma ta wuce dakin mummy.

Lafiyayyar mota ce data amsa sunanta,hakan ya sanya sukai tafiya mai dadi wanda har mero ta dinga santin ashe hanyar garinsu bata wani rube sosai ba rashin kyawawan motoci yasa suke shan wahala.

Qarfe biyu da mintina takwas suka isa qofar gidan nasu,a hankali aysha take qarewa gidan nasu kallo tana mamakin jama’ar data gani anata shige da fice a gidan,sai tayi tsammamin wani abu ke faruwa don ko kusa ko alama bata kawo cewa bikin aurenta yasa mutane taruwa ba har sai data fito daga motar taga jama’a sun soma yanyameta tare da yi mata maraba lale gami da kiranta da amarya,da mamaki kawai dubansu kamar wasu masu shirin wasan kwaikwayo,kafin kace meye kayanta da aka fito dasu daga booth har an samu masu sunguma sukai cikin gida da shi sannan ita kuma da sauran mutanen da suka tsaya gaban motar suka dunguma zuwa cikin gidan.

Sosai tunani da qwaqwalwarta suka daure da sauyin data taras cikin gidan nasu koma tace a unguwar baki daya,kowa indo yakewa marhaba,kowa indo yake tare,kowa indo yakeson nunawa kulawa,kowa.indo yake so ya raba,kowa ita yakeso ya yiwa magana,shin me ya haifar da wannan gagarumin sauyi haka dare daya?,me yake faruwa ne koko daya daga cikin ire iren mafarkan data saba yi ne tau take yinsu ido biyu,ba aysha kawai ba ba mero da gwaggo asabe da suka san meke faruwa ba hatta da aliya wadda labarin aysha ne kawai ya isketa sai data yi mamakin sauyin data gani.

Mamaki bai sake kamata ba sai sanda inna yelwa ta miqe da kanta ta tareta,ta tareta cikin yanayin da tunda ta budi idanu tasan duniya da abinda ke cikinta bata taba ganinsa ba,cikin kulawa da fara’ar da bata taba ganin makamanciyarta ba daga gareta,da idanu take bin rumfar inna yelwa da ido tunani yana zagaye ilahirin qwaqwalwarta,yadda aka gyara rumfar fes kai baka ce ita bace,aka sabunta ta aka sauya mata kamanni,ta sha leda…ta sha fenti da labulaye harma da kujeru
“Wai meke faruwa?” Ayshan ta tambayi kanta da kanta tana duban aliya kamar ita zata bata amsa,kafada aliya ta daga sannan tace
“Ina zan sani sashen….wannan abun akwai ayar tambaya a kai” tana kaiwa aya wayar aysha dake hannun aliya ta kada qaraurawa alamun shigowar saqo,dubawa tayi don ba komai irin haka a tsakaninsu sun saba
“Karki wani damu da sauyin da zaki gani,anni tayi duk wani abu daya dace saboda ki samu walwala ki sake” aliya ta karanto saqon a fili don mai wayar taji abinda ya qunsa,shuru tayi tana tunani
“Me tayi daya dace?,me ya sauya mutanen nan haka?” Ta sake aikawa da qwaqwalwarta da wannan tambayar,bata kai ga samun amsarta ba matan kawun ta suka soma shigowa,kowacce baki har kunne aka sake sabuwar gaisuwa a gurguje kar inna yelwa ta shigo ta riskesu don ta gargadi kowaccensu da karta shigo bare ta damesu,abun mamaki shine godiyar da suketa sheqa mata kafin kowacce ta miqe ta fice
“Aliya don Allah ki fahimtar da ni abinda ke faruwa mana” ta kama hannun aliya tana fada cikin rudu,don ita har ga Allah tsoro.ma abin yake bata,ko wani abun suke qullawa?,ko wani shiri ne sukayi na daban wanda batasan da shi ba,domin bata tunani akwai abinda zai sauya wadan nan mutanen lokaci guda kai kace umarni ne daga sama
“Babu komai sai alkhairi aysha…karki damu…saqon daya shigo daga khalipha yake,kuma na tabbatar su su khaliphan bazasuyi abinda zasu cutar da ke ba” maganar ita ta kwantar da hankalinta,saidai idanu data sanya tana lura da motsin komai da yadda komai yake gudana,tana iya jiyo shewar cincirindon matan qauyen dake tsakar gidan gidan nasu,sanda aliya ta miqe zata alwala ta daga labule a nan taga manyan tukwanen dake girke a tsakar gidan suna cin wuta,da aliyan ta dawo dubanta tayi
“Na kusa gane abinda anni tayi,anya ba siye mutanen sukai ba?anya ba kudi ne suka sauya komai ba?,aysha shanu biyu aka shigo da su a yanke,ga tarin abinci kala kala a wancan rumbun dake kusa da makewayinku,sannan kowanne cikin gidan nan cikin walwala yake da burin zuwan gobe ranar daurin aure” daga idanu tayi ta kalli aliya sanda take maida pad din data ciri daya zata sauya cikin jakarta
“Hakan ma zata iya faruwa aliya,kin manta ni ba komai bace…zasu iya sadaukar dani saboda abinda baikai wannan bama….” Ta fada tana sauke idanunta qasa qwalla nason qwace mata,dafata aliya tayi sannan tace
“Idan kika lura a yanzu kin zama mai daraja aysha,baki lura da yadda suke kaffa kaffa dake da dukkan lamuranki ba?…dubi kwanukan abinci kin taba gani an jere miki su haka a gabanki daga sashe sashe?,ko wannan ya isa ya gaya miki daraja su anni suka siya miki…kuma ina miki fatan kici gaba da kasance mai daraja ta sanadiyyarsu”.

Sai da suka zo kwanciya bayan inna yelwa ta saka musu maganin sauro an yada musu dandamemiyar katifa da bargo sannan dukkansu suka dago manufar sauyi da suka samu
“Indo ina kika samu miji mai arziqi haka?….ashe dai zamu dandana arziqinki….bama ‘yan gidan nan ba har maqota…kinsan kaf gidan nan babu wanda yanzu bashi da jari mai tsoka?…sannan kaf dinmu mu da maqota ba wanda bai samu sabon dinki ba da zai saka a gobe?bayan manyan buhunhunan shinkafa da aka bi aka raba musu,sannan rumbunan gidan nan uku kowanne cike yake da cima ta ‘yan birni,guda daya yace ayi hidimar biki da shi…saura namu ne muci mu qara idan sun qare za’a dado wasu….ke kanki yasa mun fadi yadda muke bukukuwanmu na al’ada ya biya komai gobe kwana za’ayi ana cashewa,ke ni fa da nake kakarki har kudin liqi sai da aka zubemin in gaya miki,kudina sabbi fil a miqe….” Kanta kawai ta juya daya barin,babu abinda ya burgeta a zubar da inna yelwa keyi,sun sake saida mata dan guntun mutuncin da yayi mata saura,bata sake cewa komai ba tana jin inna yelwar da aliya na sake bugun cikinta tana jin yadda abubuwa suka kasance,mota guda ashe aka yi musu ta saqonsu.

Tashi inna yelwar tayi ta janyo wata babbar akwati ruwan makuba(marroon mai adon dark blue)tana sumbatu
“Ga uban kayan da yace a aje miki indo ko zaki buqata,idan kinzo a baki,kaf karkarar nan da maqotanta ba wadda ta samu adaka irin taki cike da suturu haka,na biye ne saboda masu dauji dai dai nace sai kinzo na danqa miki abarki” kusan aliya ce kawai ta bude tagani,kaya ne aqalla kala goma sha biyu dinkakku,wanda amsa sunansu,takalma jaka mayafai zuwa sarqa da dan kunnaye kowanne kaya da kalar daya dace dashi,kayan kwalliya da duk wani nau’in abu da zata buqata akwai a ciki,jinjina kai aliya take tana qissima tsadar iya wadan nan kayan,sannan a ido kawai kyansu dole ya burge mutum,ba yadda batayibda aysha ta tashi ta gani amma taqi koda motsawa haka ta gaji ta haqura ta qyaleta.

Washegari da dagewar aliya da mero ta shirya cikin a tamfa,duk da cewa ba wani kwalliya tayi ba amma sosai tayi kyau,komai sabo ta saka daga cikin dinkin da asma’u ce ta zabi kayan har zuwa dinkin,hakanan taji tana sha’awar sanya kayan da daddy ne ya dinka mata,ta kasa taba kayan khalipha kwata kwata,komai a sukuku take yinsa,don hatta da karyawar safen da aka kawo musu tea da bread da chips da wainar qwai wanda batasan wanda ya hada ba bata iya ci ba,sosai aliya ta dinga sako hira da zance don ta sako jikinta amma ita kadai tasan ya take jin zuciyarta.

Goma na safe inna kulu ta aika tazo,da fari inna yelwa taso tayi gaddama amma daya daga cikin yaranta maza ya jata daki sukayi magana,batasan me ya gaya mata ba tace suje amma ta dawo kafin lokacin daura aure,tare suka fita da aliya don mero ta koma gida zata shirya kafin lokacin daurin auren yayi,don sai qarfe uku na yamma za’a daura,suna tafe aliya na yaba yanayin gari tare da tambayar indo wasu abubuwan,kusan tasan kowanne waje da abinda yake wajen kasancewarta sha gwagwarmaya ce.

Babu zato ba tsammani suka ga an sha gabansu gami da karta adda a qasa,a tsorace suka ja baya dukansu suna riqe da hannun juna,sai data duba sosai sai taga ashe dan ladi ne
“Indo baki isa kiyi aure ba idan ina raye…kin manta ke tawace?,har yanzu ke matata ce kuma ina sonki,babu wanda ya isa ya rabani dake”wani wawan tsaki taja sannan taja hannun aliya zasu wuce,don ta lura a buge yake ba cikin hayyacinsa yake ba,sake shan gabansu yayi
” na gaya miki ina sonki,babu inda kuma zaki daga nan sai gidana”ya fada cikin salo na maye,isowar wasu matasa wajen suka cakumi dan ladin sukai musu gefe da shi yayiwa ayshan dadi,haka suka wuce aliya na waigen dan ladin
“Waye wai wannan aysha…”
“Tsohon mijina ne”
“Dan ladi?” Kai kawai ta gyada mata,don tunawa da rayuwar datayi da shina qona mata rai yake,dariya aliya ta bushe dashi tana duban ayshan,tana son ta kalleta itama ta tsokaneta amma sai taga ayshan ta basar,da alamu har yanzu ranta ba’a sake yake ba,ganin haka itama ta share har suka isa gidan.

Ga mamakinta a canma jama’a ta samu zoqar ana shirye shiryen yinin biki sosai,a nan dinma maraba ake da ita,duk da bata wani ji abun har cikin ranta ba amma ta dan saki jiki albarkacin gwaggo asabe,saidai duk da haka nata ido,wuni bikinsu suke sosai,tana zaune tana binsu da kallo,lokaci lokaci tana share hawayen fuskarta,koda ace ba har zuciya suke mata wannan hidimar ba,koda ace ba don Allah suke yinin bikin ba,koda ace abun bai burgeta amma zata so ace mahaifiyata na wajen…zata so ace mahaifiyarta tazo…zata so ace tana ganin wulgawarta a wannan bigiren koda kuwa bata farinciki da ganin nata ko auren da take yi.

Qarfe daya na rana zayyanu dan qanin babanta yazo ya kirata,tana jinsu suna ‘yan maganganun kiran itadai ta miqe suka wuce ita da aliya da wasu daga cikin ‘ya’yan qannen umminta,sanda suka isa qofar gidan nasu ya soma cika damqam da jama’a,kusan kowa cikin shadda yake fara,matan kuma sanye da tasu shaddar light purple har zuwa cikin gidan haka kalolin suke,da alama dinkawa akayi kowa da kowa,hakan take kuwa,saboda tana shiga tsakar gidan dake cike da mata suka saki guda a tsakiyar kanta suna yabawa gami da godiya da dinkin shaddodin da aka yiwa kowa a cikinsu,ciki da wajen gidan,aliya ce ta ja mata mayafinta ta rufe mata fuska,kuka ne ya qwace mata,tana ganin komai kamar a mafarki,idan suka kirata amarya sai taji banbarakwai,tana ji kaman da gaske auren gaske zatayi bana samun ‘yanci ba,ba yadda aliya batayi da ita tayi shuru ba amma hakan ya gagara,don ita kanta tasan bata da ikon tsaida wannan kukan,a haka aliya ta matsanta ta mata ta sake sauya wasu kayan,tayi kyau sosai saidai fuskarta duka tayi jajir ta tasa saboda kukan data kasa dainawa.

Kafin lokacin daurin auren gidan ya cika danqam da jama’a,ci da sha ake tako wanne fanni cikin walwala da dariya,saika rantse da Allah tun usuli ita din diyar gata ce a cikin gidan,tun tana kallon kowa cikin mamakin har ta daina mamakin ta zubawa sarautar Allah ido,wato a rayuwa idan kana da shi kaine wani?,kai ne abin so?,kaine abun taqama abun a nuna?,kai akewa biyayya?,kaine abun girmamawa koda baka biyayyawa mahaliccinka?,wadan nan tambayoyin ta dinga yiwa kanta suka dinga kai kawo da amsa kuwwa a kunnenta da kwanyarta.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:02 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO WANNAN NUMBER*
07067124863

*DB*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button