Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 38

Sponsored Links

38

 

Farin bayanta yake iya gani wanda dogon gashinta ya sauka,tana ci gaba da tajeshi yana miqewa,da fari ya danyi mamaki yayi tsammanin jinnu ne sukeso masa yawo da hankali,saida ya saukar da idanunsa zuwa santala santalan cinyoyinta zuwa qafarta ya tabbatar ba aljana bace amma kuma wacece?,bai gama wannan tunanin ba ta ankara da mutum a bayanta can bakin qofa a tsaye cikin baqaqen suit,wani irin kadawa hantar cikinta tayi,ta zabura gami da qwalla qara ta shige bayi ta danna key tana karanto addu’o’in tsari,ba inda ajikinta baya rawa yana kakkarwa,kasa tsaiwa tayi saboda tsabar tsoro da rudewa saida ta samu gefan bathtube ta zauna,tuni hawaye suka fara tsatstsafo mata,yau ta shiga uku ta lalace,dama akwai aljannu a gidan?,don ta tabbatar tayi imanin babu mai shigowa inda take,bugu da qari ma waye zai iya shigowa dakin da tun daga falo ta sanya mauqulli har dakin gadon,saita barke da kuka mai sauti tana ci gaba da addu’a gami da qanqame jikinta waje daya.

Daga inda yake tsaye haushi ya cikashi taf,wannan wanne irin abu je?,daga ganin mutum shine zata wani zabura kamar taga aljani ta shige bandaki?,wai wace ma har ta samu lasisin shigo masa daki ta bararraje haka?,anya anni ta sani?,Allah yasa ba daya daga cikin yarancan bane da suke addabarsu da bibiyar rayuwarsu.

Parlour din ya koma ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon yana dafe da goshinsa da hannu daya ya zaro wayarshi ya lalubi lambar anni,bugu daya ta daga,sai yayi qoqarin saisaita temper dinsa
“Anni,wace take amfani da bedroom dina?”
“Bedroom dinka?,wace banda matarka,aysha ce”
“Aysha kuma?” Ya tambaya cikin mamaki
“Eh ita,wani abu ne?”
“A’ah,ta tsorata ne kawai ta shiga toilet tayi zaton wani ne” yayi saurin fada don karta dago wani abu
“Aifa aysha ba baya ba wajen tsoro,saika gaya mata wane ai” daga haka ta katse wayar,jifa wayar yayi gefanshi sannan ya miqe qafafunshi ya soma zare takalmin qafarsa da socka din duka gaba daya,ya rage daya daga cikin three in one suit din dake jikinsa ya sassauta tie dinsa sannan ya sake komawa dakin,tsai yayi yana qarewa dakin kallo,komai a tsaftace yake,sai towel bressier da pant dake kan gadon,sai kayan gyaran gashi dake saman madubi da cumb din data watsar waje guda saboda tsoronta,dauke kanshi yayi ya shigo ciki sosai ya doshi toilet din.

Daga can taji ‘yar qara alamun an sake bude qofar bedroom din,wani tsoron ya sake kamata,sautin kukanta ya sake qaruwa sanda taji ana taba qofar bandakin,yana iya jiyo sautinta kadan kadan,haushi ya kamashi,wanne irin tsoro ne da ita haka,knocking ya fara yi saidai maimakon ta bude sake firgicewa tayi,gabanta yaci gaba da bugun uku uku,ta duba duk bandakin ba wajen tsira,kuma ta tabbata ko ihu tayi ba wanda zai jiyota cikin gidan,ganin ba alamun zata bude sai kukan banza da takeyi ba tare da yasan me takewa kukan ba ya sanyashi bude bakinsa,cikin muryarshin nan yace
“Bude mana” saboda tsoro sam bata iya tantance muryar waye ba,sai kawai zuciyarta ta bata muryar aljanu ce,cikin sautin kuka tace
“Wallahi bazan bude ba”
“Kwana zakiyi a ciki?”
“Nidai kuyi haquri don Allah”
“Mu suwa?” Ya tambayeta cikin qosawa,bata bashi amsa ba sai dif da tayi,ganin tana neman bata mishi lokaci yasa ya koma inda ya aje kayan hannunshi ranshi fal takaici,ya lalubi muqullansa daya amsa a hannun anni ya koma yana gwada na toilet din,jin ana alamun budewa ya sake sawa ta tsure,saikawai ta qarasa shigewa cikin bathtube din ta takure waje daya tana dana sanin zama abangaren ita kadai,dama tun dazun take jin motsi,dazu kuma musa’ab ya gama bata labarin ya taba gamo tsohon gidansu,tana ta dariya da tsokanarshi duk labarin ya dan bata tsoro kadan ashe da gaske yake

Sai daya gwada muqullai kusan uku abinda ya sake gajiyar dashi sannan ya dace dana bandakin,a hankali ya tura qofar ya shiga,can ya hangota ta takure gu daya,gashin kanta da bata samu damar daurewa ba ya bazu ko ina har fuskarta,daga kai tayi cikin tsoro ta dubeshi,sai a sannan ainihin siffarshi ta bayyanar mata,khalipha ne sosai tsaye cikin bandakin,sanye cikin baqaqen suit,saidai a yanzu ya cire sun glasses din dake fuskarshi,ya sake haske da kyau,sumar kanshi data fuskarshi luf da ita tana fidda wani sheqin baqi,ya sake murjewa hakanan idanunshi sun sake kyau,daga tsoro sai yanayin ta ya sauya zuwa kunya da fargaba,ta tafka babban abun kunya,bugu da qari tuna abinda ke daure a jikinta kawai ya sake sawa hankalinta ya tashi,kamar ta bace ya daina gannta haka taji,sai kawai ta maida kanta taci gaba da dunqulewa waje guda gana pretending din firgitar dazu ce bata saketa ba
“Saiki tashi ki koma ciki ki bani waje zanyi wanka” ya fada yana dubanta,duk da qoqarin kauda idanunshi da yakeyi amma hakan ya gagara,jin idanunsa take yake ko ina akanta,batajin zata iya motsawa ta wuce haka ya gabanshi
“Ki tashi matsoraciya kawai ko har yanzu baki gane wane ba?” Ya tambayeta yana harde hannunsa a qirji,shuru tayi don bata da amsar bashi
“Ko ba zaki tashi ba sai nazo na daukeki da kaina?” Jin haka ya sanyata zumbur ta miqe,saidai da qyar take iya daga qafafunta ta fito daga cikin bathtube din ta raba ta gabanshi zata fice daga bandakin,caraf yayi ya riqo hannunta yana sani,a firgice ta dago kai suka hada idanu,saita soma neman wajen buya,wanda abin dariyar jikinsa takeson shigewa ko zai daina kallonta,ba shiri ya saketa yana dariya cikin ranshi,bai fasa kallonta ba har sai data fita din sannan ya koma ya rufe bandakin da muqulli ya dawo ciki ya tara ruwan wanka.

Hawaye ne ya sake qwace mata takaici na cinta na ganinta haka da yayi,gashinan shi yanzu ya saka muqulli ya kulle kanshi zaiyi wanka amma ita asirinta abayyane,qwafa tayi ita kadai tana zumburo baki.

Haka ta shirya tana qananun hawaye a gurguje don kada ya sake fitowa ya taddata a haka,duk da haka bata fasa yin kyau ba,doguwar rigar buba ce ta atamfa shadda baqa mai matuqar kyau da tsada,an mata zanen jajayen flowers manya a jiki,bata nemi dan kwali ba saita yane kanta da madaidaicin jan mayafi bayan ta hade gashinta ya bada jela daya data sauka har bayanta.

Har taje zata fita sai kuma ta kasa,bai kamata ba,ba wani magana da sukai tsakaninsu koda ta sannu da zuwa ce,saita koma kan kujerar falon ta zauna tana murza tafin hannunta a hankali tana tuna yadda abun ya faru,dama tun dazu a tsorace take da labarin mus’ab,shi ya sake tunzurata ta sake tsorata.

Idanunsa lumshe suke ruwan na ratsa jikinsa,tabbas haka ne kowa yabar gida gida ya barshi,wani dadi yake ji gashi a gida,Allah Allah kawai yake ya koma wajen anni susha hira,a hankali ya tuna abinda ya faru dazu mintina kadan da suka wuce,murmushi ya saki abun yana son bashi dariya,bai taba sanin matsoraciya bace har haka bayan sanyin da yasan a baya tana da shi ba sai yau,kai ya kada kafin ya dauraye jikinsa ya fito.

Tunani kadan tayi sai ta miqe ta fice zuwa cikin gidan,ya kamata ace tayi masa wani abu da zaiji dadi,tunda bata jin gidan sun tanadar masa wani abun don ba alamun suna da masaniyar zuwanshi a yau,ta tabbata da anni zata sanar mata,haidar da mus’ab ne kawai a falon suna shigo da jakankuna,dariya mus’ab ya sa yana dan satar kallonta,har ta wuceshi ta share sai ta tuna abinda taji yana cewa anni dazu na suprise,sai ta dawo da baya tana dubansa
“Zan rama fa,kaci bashi ne,yaa haidar harda kai aka hada baki ko?” Ta fada tana duban haidar,murmushi yayi yana daga hannu sama
“Nikam babu ruwana bansan me akeyi ba,yace min ne kawai nazo na rakashi airphort” kai ta jinjina tana wa mus’ab sign na alwashi ta wuce kitchen.

Duka ‘yan aikin ma ciki sun kacame da aiki
“A’ah duk girkin meye wannan?” Ta tambayi baba atika
“Mai gida yayi zuwan bazata kinga dole a tashi a shirya masa lafiyayyen abinci” hakanan taji cewa dutynta ne wannan,ita ya kamata tayi masa wannan karramawar,koba komai ta dan nuna dan wani yanki na godiya kan kyautatawarsa a gareta,duk da baikai ya kawo ba amma zata kwatanta
“Bari ku gani,wannan girkin naku ai lokaci zai dauka baku gama ba” cikin qanqamin lokaci ta hado duk abinda take buqata ta dora,ta koma gefe ta niqa abarba tayi mishi pineapple juice wanda kafin ta garma dan qwarya qwarayar girkinta ya dauki sanyi.

Mintina talatin ta gama ta shirya komai kan wani faffadan tray mai azabar kyau,ba wanda yawunshi bai tsinke ba a kitchen din(harda ni mai rubutun ??).

Tana goge hannunta da zummar idan ta gama ta fita da abincin amal ta shigo,kana ganinta kasan bata jima da yin kwalliyar ba cikin dinkin lace
“Wai baba atika me kuke dafawa baqonmu,qamshi ya cika gidan amma shuru baku gabatar masa da komai ba?”
“Ai aikin uwar masu gida ne,gashinan da kanta ba saqo ba” baba atikar ta fada cikin murmushi wanda hakan yaja hankalin amal zuwa wajen aysha wadda take sake jera kwanukan,cikin yaqe take kallonta,nutsatsiyar kwalliyarta wadda girkin da tayi bai bata ta ba,yadda ta jera kayan abincin da qamshin da suke fiddawa,wani abu mai nauyi taji ya tokare qirjinta,sai ta kasa cewa komai ta juya ta fice cikin sanyin gwiwa.

A nutse take fitowa daga kitchen din zuwa falon,shi ta soma hangowa a gefan anni wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba wadda bata taba jin irinta ba,bata sani ba ko hakan yana da nasaba da abinda ya faru dazun?,fuskarshi fes,kyansa ya sake fitowa sosai,ganin yana niyyar juyowa ya sanyata dauke kai da sauri ta maida kan anni,dubanta yake sanda take tahowa din,sai yaga kamar an canza ta gaba daya,shidai yasan ba wannan ayshan ya tafi ya bari ba wata ce daban,abinda tayi dazun ya dawo mishi,sai yace da anni sanda ta iso wajen tana aje kwanukan
“Yaushe humaira ta koma haka?” Yayi subutar bakin fada ba tare daya shirya ba,sam anni bata fahimci tambayar tashi ba,tayi tunanin kyau da gogewar data qara yake nufi,saita saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,miqewa tayi tana cewa
“Sannu takwara,ki kai masa saman teburi,fita zanyi nima dubiya,drivan ma har ya iso” ta qarasa maganar tana miqewa,sai ya dubeta
“Ba hira kenan anni,kamar ma baki kewata ba?”
“Ni bance haka ba saikai khalipha?,watanka nawa?” Ya gane qorafi takeson yi masa,mafi a’ala kuma yayi shuru kar allura ta tono garma
“A dawo lafiya”
“Allah yasa,ya kamata idan ka huta kaima kaje ka dubashi,don yanzun ma tare dasu haidar zamu je”shuru kawai yayi yadan sadda kanshi,da alama baison zuwa wajen amma bazai iya musa mata ba,miqewa aysha tayi ta amshi jakar hannunta ta bita da ita a baya,suna zuwa qofar falon ta amsa
“bar aikin da ba lada kije kiyi na lada,ki kula da mijinki” kunya kaman zata nutse,kalmar saita mata banbarakwai,ba wanda ya fado mata a ranta a lokacin sai maman hunaifa da baban hunaifa,saita dinga jin girma da wani alfahari na shigarta kadan kadan,wai itama fa matar wani ce akwai igiya a kanta,hakanan taji tana son ta gwada yanda matan aure keyi,juyawa tayi zuwa cikin falon,har ta isa kanshi na qasa da alama tunani ma yake,bata tankashi ba ta kwashe kwanukan zuwa saman tebur wanda motsinta yasanyashi daga kai,saiya tsinci kanshi da binta da kallo,qamshinta daya buso zuwa hancinsa yaji ya burgeshi,ci gaba yayi da kallonta ba tare data sani ba yana jin qimarta na qaruwa cikin ranshi,zaman da sukayi da anni kafin fitowarta labarinta kaf duka kan ayshanne,irin kulawar data samu daga gunta ya tabbata ko shine iyakar abinda zai mata kenan,sai yaji tausayinta ya kamashi,lallai mahaifiyarta batasan baiwar da Allah yayi ma rayuwarta ba na samun nutsatstsiyar diya.

Sai data shirya komai sannan ta daga kai da niyyar duban me yake,sai suka hada ido,murmushi ya sakar mata saboda harga Allah bazai iya boye jin dadin kulawa da anni data yi ba,tamkar an dorawa zuciyarta wani abu haka taji,bugun zuciyarta ya sake yawa,idanunta ta lumshe tana qoqarin maida masa martanin murmushin nasa,sai kuma taji kunya ta mata dabaibayi,yanayin daya ganta da abinda ta masa dazu suka fado mata,ji take kaman qasa ta tsage mata ta shige ciki,a nutse ya taso har zuwa inda take tsaye,yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna,saita motsa kadan ta matsa daga kusa dashi.

Ganin shuru batayi niyyar zuba komai.ba bayan shi kuma yunwa yakeji sai ya sanya hannunshi da niyyar bude flask din dake gabanshi,tare hannunsu yaje kai saboda arashin tunanin budewar da akayi yazo daya a qwaqwalensu,da sauri kowanne ya janye hannunshi,khalipha ya dunqule nasa hannun yana jin wani irin abu na masa tafiyar tsutsa a jikinsa
“Uhmmm,a sanmin naci” ya fada qasa qasa ganin taqi ta sake motsawa,sai da tayi qoqarin controlling hannunta dake rawa sannan ta iya zuba masa komai ta miqa masa
“Ka dawo lafiya ya hanya?” Ta fada cikin amfani da irin salon maman hunaifa,wanda ba qaramin kyau yayi mata ba fiye da tunaninta
“Alhamdulillah” ya amsa yana sauke ajiyar zuciya,sai tayi niyyar wucewa,ba haka yakeso ba,hakanan yaji bai gaji da ganinta ba awajen,kwalliyarta ta tsaru,sosai adon yabi jikinta
“Zama zakiyi naji me kika bayan bani nan” ya fada yana kai lomar farko bakinsa,saiya kasa ci gaba da maganar da yayi niyya,dadin abincin na kai masa ko ina,hakanan ta zauna a kujerar da ya nuna mata wadda itake facing dinsa,kanta na qasa shi kuma yaci gaba da cin abincinsa
“A ina kika koyi girki haka?”
“A gida” ta amsa masa a ataqaice
“Tun yaushe?”
“Can da dewa” daga haka bai sake cewa komai ba,yayin da sautin muryarsa daya tambayeta da ita taci gaba da amsa kuwwa a kunnenta,sai take jin kamar ba muryarsa ba,komai nashi ya sauya.

Shiru ne ya ratsa wajen,baka jin komai sai qarar cokalinsa da kuma hayaniyar masu aiki dake can cikin kitchen,daga wata kusurwa ta falon kuma amal ce rakabe tana duban abinda ke faruwa ta bayan labule,agogo yayi niyyar kalla sai ya hangi gefan skert dinta da batasan ya fito ba,qaramin murmushi ya saki cikin ransa yake cewa
“Barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba,lallai hali jini yake bi” a hankali ya sauke idanunsa kan hannunta da take wasa da farcan hannunta da yasha jan lallenta ya koma marroon,tafin hannunsa ya dora a hankali samansu ya damqesu kadan yadda ba zataji zafi ba,da hanzari ta daga kai ta dubeshi don sanin dalilin faruwar hakan,murmushin dake shimfide saman fuskarshi saiya qarasa narkar da ita,qwayar idanunta kawai ya kalla yasan tambaya takesoyi
“Amal” ya furta kamar mai rada ta yadda idan ba ita din dake wajen ba bawanda zai iya jiyo me yake cewa
“Amal kuma?” Ta tambayeshi cikin mamaki,kai ya gyada
“Banason ki dinga nuna rashin sabo ko baqunta tsakanina dake” maganarshi ta dawo mata randa take da kwana guda a gidan,kai ta gyada masa alamun ta fahimta,qoqarin dai daita kanta tayi ya dubeta
“Bani labari dame dame ya faru bayan bani nan” ya qarashe maganar yana miqewa a nutse tare da nufar inda ya hangi amal,aysha ta bishi da kallo a sace tana ganin kaman ya qaro salo da yanga,kominshi shima ya sake sauyawa.

 

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*ko kuma*
07067124863

*mrs muhammad ce*??
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button