Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 4

Sponsored Links

0?4?

 

Qarfe daya ta fito daga library dake cikin makarantar don ta qarasa masallaci tayi sallah,tattaunawa suka sakeyi da sauran dalibai ‘yan uwanta kan lacuture din da suka gama yi,qoqarinta da yadda kanta keja yasa yawa yawan dalibai ke maqale mata saboda ta sake ganar da su abinda basu fahimta ba,ta kammala alwalar tana gab da shiga masallacin wayarta tayi tsuwwa,dakatawa tayi ta ciro tana duba mai kiran,gwaggwo asabe ce take kiranta qanwa ga mahaifiyarta,mace daya tak da ko a baya tayi qoqari wajen ganin ta taimaki rayuwarta,tana daya daga cikin jerin jama’ar da bazata mance da su ba cikin rayuwarta,gefe ta samu ta jingina da wata bishiya dake wajen bayan ta katse kiran ta kirata da kanta don kada ta cinye mata kudi,gaisawa sukayi bayan ‘yan tambaye tambayen lafiyar juna da suka biyo baya tace da ita
“Indo hala bakisan malam baida lafiya ba ko?”
“Kai haba?,tun yaushe gwaggwo?”
“Sati kusan biyu kenan,har a asibitin cikin gari ya kwanta,amma alhamdulillahi yanzu jikin nasa da sauqi an sallamoshi yau kwana uku yana gida ma”
“Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bashi lafiya,in sha Allah zan shigo garim cikin qarshen satin nan,kiyi masa sannu kafin na iso”
“Zaiji,saikinzo Allah ya kawoki lafiya”
“Ameen gwaggo na gode,ki gaishemin da su lami”
“Zasuji” daga haka ta kashe wayar ta maidata cikin jakarta tana sauke ajiyar zuciya,ta tabbata ba don gwaggwo asaben ba babu lallai tasan da rashin lafiyar malam din,ta rasa wanne irin baqin abu ta aika har baqin jini yake bibiyarta wajen danginta na uwa da uba?,me tayi musu haka da kowa ma bai damu da rayuwarta ba?,a hakan ma takan iya cewa alhamdulillah da yadda ta tsinci kanta a yanzu akan shekaru kusan bakwai zuwa goma baya da suka shude,wanda abun yayi tsananin da har bata marmarin tunawa?,saidai har yau akwai wawakeken tabo da gibi cikin rayuwarta wanda batasan ranar da wannan gibin zai cike ba,batasan randa wannan babban jigon zai rabeta ba,batasan yaushe zai waiwayo ya dubi rayuwarta duba irin na idon rahama ba kaman yadda sauran ‘ya’ya ke samu daga wajen uwayensu,da wannan tunanin ta qarasa cikin masallacin ta tada sallarta.

Related Articles

????????

Cikin nutsuwa ya kammala sanya maballan t.shirt dinsa wadda kudinta ya kama naira dubu biyu ita da wandon jeans dake jikinsa,har ya dauki turarensa zai fesa sai ya tuna,maidashi yayi wajensa,ya sake miqa hannu ya dauko wani daban wanda kallo daya zaka masa ka qiyasta kudinsa bazai wuce naira dubu guda ba idan yayi wuta ya fesa a jikinsa,duk da qarancin kudin turaren kuma bai cikin jinsin irin turarukan da yake mu’amala da su amma hakan bai hanashi jin dadin qamshinsa ba,saboda turare ne sanyi dake fita a hankali ba tare da ya daga hankalin wanda yake shaqa ba.

Gaban mudubi ya qarasa yana duban kansa,sai murmushi ya subucewa fuskaraa,duk da arhar kayan amma sun masa kyau
“Gwanjo” ya fada yana shafa gaban rigar dake jikin nasa zuwa saman cikinsa,yana tuna can wani lokaci baya daya shude,wani zamani da yayi tafiyar ruwa da dukkan farincikin rayuwarsu,wani qarni wanda basu taba tsammanin zaya wuce babinsa ya shafe kaman bai taba wanzuwa ba cikin littafin qaddararsu ba,tunanin ya saka ya zarce da sake gyara sumarshi da tayi matuqar yi masa kyau.

Kafin ya kai ga aje comb din hannunsa aka turo qofar dakin hade da sallama,mahmoud ne ya shigo idanunsa na kan khalipha,daga gani tambayoyi ne fal cikin qwaqwalwarsa wanda tun kafin ya zauna ya jefo masa daya
“Me haka ne malam?,ban fahimceka ba” juyawa yayi yana ci gaba da gyara kansa kafin ya bashi amsa
“Na zaci shigata kawai ta isa ta baka amsar abinda yake faruwa ko?”
“Wai har yau baka haqura ba?,baka kuma daina ba?” Ajjiye comb din yayi ta tako kusa da mahmoud din ya dauki qaramar vivo din dake aje kusa da shi ya bude bayanta ya soma qoqarin sanya mata layi
“Na sake haduwa da wata,kuma na fuskanci kaman wannan karon ina tare da nasara” dariya sosai mahmoud din ya bushe da ita harda kwantar da gadon bayansa saman gadon khaliphan,san dariyar mahmoud din bata dameshi ba saima yunqurin kunna wayar da yake bayan ya kashe nashi tsadaddun guda uku ya jefa cikin wata ‘yar kyakkyawar briefcase dake nuna alamun da ita zai fita
“Me yasa kake wahalar da kanka ne babu gaira babu dalili my man…..ka saki kudi kawai ka auri duk kalar macen da kakeso kada ba jinsinka bace ba ‘yar qasarka ba,kowa ya sani cewa mata yanzu kudi kawai suke so,mai kudi suke nema koda baida hali koda bai cancanta,koda ba saurayi bane koda ba kyakkyawa bane,koda jahili ne,to bare kai da babu abinda Allah bai baka ba,c’mon muhammad khalipha ka aje wannan game din a gefe ka fuskanci reality,ba irin matan da kaketa serching a yanzu,baka gani duk inda ka soma farauta daga qarshe sai kaga no signal?”.

Hannu yasa ya dauki briefcase dinsa tamkar bada shi mahmoud ke magaba ba ya doshi qofar fita ba tare da yace masa ci kanka ba,hakan ya sanya shi miqewa da dan tsallensa ya biyo bayansa,saidai bai sake biyo ta kan wancan maganar ba ya sauya topic,yasan ko yaci gaba ma ba amsa zai samu daga gun khaliphan ba
“ka rakani mu shiga na gida anni”
“Daga nan ni sai inda na nufa,idan ka fito daga wajenta ka kwashe su jibril duka ku wuce kamfani na tadda ku a can,ni da mota daya zan fita,bana buqatar gayya” ya fada yana gaba yana ci gaba da dubo lambar sabuwar budurwar tashi don ya sanar mata da tahowarshi.

Yana fita duka suka taso inda yake,da hannu ya tsaidasu kafin ya daga kai ya dubesu
“Mota daya ta isheni da driver,zaku jira mahmoud tare zaku tafi,zan taho daga baya” kai auka jinjina suna janyewa,yayin daya bude motar da kanshi ya shige gidan baya,drivan motar ya shiga ya tasheta suka bar harabar makeken gidan.

Layuka biyu suka rage kafin ya qarasa layin gidan nasu ya bashi umarnin ya saukeshi ya kuma jirashi a nan,ba musu ya tsaya kaman yadda ya umarceshi,ya bude ya fice.

Sannu a hankali yake takawa,shi kansa yana jin dadin takawar da yake,saboda ko banza ya motsa gabbansa,ba kamar baya ba da motar ita ta zame masa qafafunsa,sauqin abun daya bai da lalaci,duk safiyar duniya sai ya shiga dakin dake bangarensa,wanda ke cike sa nau’in qarafuna da na’urori na motsa jiki da qara lafiya.

Plashing yayi bugu biyu ya katse,shi kansa sai da dariya ta subuce masa
“Shame on you khalipha,wai yau kaine da yin plashing,Allahu yahdik” ya furta a zuciyarsa yana sakin murmushi gami da ranqwashin tsakiyar kansa,fitowarta ita yasa ya maida hankalinsa ga qofar gidan,tayi kwalliya sosai cikin atamfarta
“Sannu da zuwa” ta furta tana wuwwulga ido kaman mai neman wani abu,amma sai ta basar saboda jin kanta da take a mace mai aji
“Yauwa barka da fitowa”
“Ina kuma abun hawan yau?” Ta tambaya kai tsaye tana dubanshi,wani abu mai kama da mamaki yaso mamayarsa amma sai yayi hanzari kau da shi yace
“Kinsan qarfen nasara bashi da tabbas,yau yaqi tashi kawai sai na yanke na taho a na haya”
“Kan bala’i,ana wata ga wata” ta furta qasa qasa,sarai ya jita amma sai yace
“Na’am,me kika ce?”
“Babu komai,shigo daga ciki” ta fada ranta a alamun bace,bai musa ba yabi bayanta har setting room din gidan,duk da cewa ba baqonsa bane gidan da zuwanshi kusan na uku kenan,kallon farko zuwa na biyu zaka yankewa maxauna gidan ajin rayuwar da suke ciki,ba alamun suna cikin talauci,dukkan wata alama ta rufin asiri akwaita a gidan,kaman yadda ya tsammaci akwai tarbiyya gwargwado gidansu khadijan.

Nan ta masa sauki ta gabatar masa da abun motsa baki kamar kullum,saidai abinda ya fuskanta abinda aka kawo masa jiya idan ya sake zuwa yawansu da tsadarsu kan ragu,idan cake da doghnout da lemo yaci to zuwa na gaba doughnout da lemo kawai zai samu,yasan bai taba baiwa khadijan komai ba,haka itama bata taba roqarsa ba,saidai amma ya lura duk sanda sukayi sallama zai tafi ba tare da ya miqo komai ba yakanga bacin rai qarara a fuskarta,har idan ya koma gida ya kirata da zummar gaya mata ya iso bata dagawa,saidai duk ya share wannan bai sanyashi a babin komai ba.

Tun kafin aci talata da laraba a hirar tasu ta gyara zamanta tare da sake lanqwashe murya
“Ammm….dama muhammad akwai maganar da nakeso muyi”
“Ina saurarenki” ya fada yana harde qafafunshi waje guda tare da zuba mata idanunsa,haka nan taji ya mata kwarjini,abinda take yawan tunani kenan,me yasa yake yawan cika mata ido,wanda wannan dalilin yasa tun zuwansa na farko dana biyu data fuskanci ba kalar wanda take lalube bane ta kasa masa bayani,janye qwayar idanunta tayi cikin dakiya tace
“Dama…..biki zamuyi na wata qawata,so an fidda anko nakeso ka yimin” janye yatsansa dake saman lebansa yayi ya dan motsa jikinsa kadan sannan yace
“Kaman nawa ne kudin how much?” Sai da tayi rolling qwayar idanunta sannan tace
“Dubu talatinma is enought,idan son samu ne kuma 40k” murmushi ya qwace masa saidai iya shi da zuciyarsa,ba kudin data tambaya bane suka bashi mamaki don ba matsalarsa bane,don a yanzun haka akwai ninkinsu a wajensa,wanda ya fito da su ne yau dan ya mata kyauta matuqar ta sake tsallake yau din bata nemi komai daga wajensa ba,mamakinsa shine yadda yarinya budurwa da bata rasa ci sha da sutura daga gidansu ba take iya duban qwayar idon namiji ajnabinta ta roqeshi kudin da zata dinka suturawa jikinta haka kanta tsaye ba kunya,tamkar ta bashi ajiya ne,kai yake kadawa a hankai zuciyarsa na gaya masa bata gama cin jarabawa ba ba shakka
“Ya naji kayi shiru ne?” Ta tambayeshi tana dan bata rai gami da fiddo ido waje
“A’ah babu komai,kawai….gani nayi kudin basuyi yawa ba?” Tsaf ta dinke girar sama da qasa
“Just 30 to 40k dinne sukai yawa?,ko iyawa ne ba zaka yi ba?,thank god da ba’a gaban qawayena bane da nake cika musu kanka da naji kunya” murmushi ya saki yana miqewa tsaye
“Ba zakiji kunya ba in sha Allahu zan shiga na fita,amma sai kin danmin haquri kadan kinsam abinka da almajiri mai nema”
“Ba damuwa indai zasu samun,amma kar su wuce nan da one week don Allah” ta qarashe maganar a shagwabe,kai kawai ya iya jinjinawa mamaki na kasheshi,haka tayi masa rakiya har qofar gida yau cike da kulawa sannan ta juya ta koma,shi kuma yaci gaba takawa yana juya abinda ya faru tsakaninsa da khadijan har ya isa bakin motar,wanda tuni driver ya bude masa ya shige shi kuma ya maidata ya rufe sannan ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar unguwar.

“Ashe duk kanwar jaa ce?” Ya fada qasa qasa cikin sigar tambayar kansa da kansa bayan ya ciro sabbin kudaden dake aljihunsa ya qare musu kallo ya watsasu cikin wata ma’ajiyar dake motar ya maidata ya kulle yana sauke ajiyar zuciya,kansa ya shafa sau biyu yana kiran sunan Allah sannan ya maida idanunsa ya lumshe yana aje numfashi

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *DAURIN BOYE*

*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(home of expert and perfect writers)

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button