Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 47

Sponsored Links

47

_ga full 47 nan nayi editing na qara yawanshi,banson numbers din littafin yayi yawa,idan na samu damar qara wani anjima zaku jini in sha Allahu_

Cikin jirgin ma daga kujerarsa saita aysha,hakan ya bashi damar samun kusanci sosai da ita,yayin da asma’u ke zaune can baya,duk wani motsinsu idanunta na kai,yana sane yake sake narkewa ayshan,yayin da kunya ta cikata,gaba daya khaliphan ya canza tun daga zuwansu legos zuwa yau.

Related Articles

Baqinciki ne cike a qirjin asma’u yayin da take kallonsu,kota ina khalipha ya yagawa hamid,koda can dinma tana sane da hakan,kawai rashin kudi da bata taba zaton khalipha nada shiba shinya janyo mata komai,ga dukkan alamu sun nuna babu wata matsala tattare da ayshan,ko waye kai ka kalleta kasan bata da damuwa,sai taja numfashi ta kuma fito dashi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa,zuwa yanzu ta soma gajiya da zama da hamid din,babu wata alama dake nuna zai sauya,kai babu ma batun sauyi saima sake tabarbarewa da al’amura sukayi,baya ga shegen maqonsa,rashin sanin darajar aure da iyali,sai kuma ta gano wata mummunar dabi’a data fi komai daga mata hankali,wato hamid yana neman mata,matan ma ya rasa wadda zai nema sai ‘yar aikinta kafira ba musulma bama,sannan a yanzu haka yarinyar na cikin gidan duk data kamasu amma ya murje idonsa yace karta soma kuskuren korarta,tana ji tana gani ta barsu,Allah ya sani tana son hamid,saidai maganar gaskiya ba zata iya rayuwar takura da mammaqo ba,abu na farko daya sanya ta guji duk wani saurayi a baya data fuskanci babu dandalen arziqi tattare da shi,tunin daya soma konno mata kai ta dinga wassafa da kimanta yiwuwar faruwarsa,zai yiwu kuwa?.

Da wannan tunanin har jirginsu ya iso kano bata sani ba,koda suka fito daga airphort din sai tadan qara sauri ta cimmusu
“Na gode khalipha sosai,Allah ya qara arziqi” ta fada cikin murmushi,cikin mamaki suka dubeta,khalipha shi ya soma kauda kai,ya kama hannun aysha sukayi gaba sannan yace
“Ba donke nayi ba ai,albarkacin princess humaira kika ci” sosai maganar ta daketa,amma saita share ta sake takawa ta cimmasu
“Ko zaka sakamin number dinka don Allah,bai kamata ace bama zumunci ba,abinda ya faru ya riga daya faru insha Allah kuma bazai sake faruwa ba” murmushi yaso.ya subuce masa saboda kalaman rainin hankalin asma’u,sai ya saka hannu ya amshi wayarta da take miqo masa,har ta soma murna taji yace
“Riqe maza don Allah,da wannan wayar kike amfani?” Saita kada kai tana sakin murmushi
“Kiyi qoqarin canza wata don Allah,saura kadan ta jimin ciwo….muje princess” ya fada yana sake riqe ayshan da kyau,binsu kawai tayi da kallo baki bude,wato bai manta duk wani abu data taba yi masa kenan ba?,anya wannan tafiyar zata zama da sauqi kuwa?.

Aysha kam rasa bakin magana tayi,sauyawar asma’u lokaci guda?…..sauyawar asma’un ba abu bane mai sauqi ta santa sarai,wala’alla tana kwadayin abota dasu ne kamar yadda halayyarta take nason abota da suk wani mai kudi,dason ace tana da kusanci dashi ko kuma ta sanshi.

Sanda suka isa gida ta tsammaci zasu shiga sashen anni ne dafarko,sai taga yayi fuska ya kara wayarshi a kunne
“Anni mun iso,amma zamu dan huta kafin mu shigo….ohk” ya fada yana sauke wayar,hada ido sukayi saiya dan basar yana cewa
“Bana son in shiga na soma karo da fuskar wadan can yaran,don haidar ya gayamin maryam ma tazo,so daga yau babu zaman cin abinci a cikinsu” ya fada sanda suka shiga falon.

Qarfe takwas na dare tana zaune gaban annin cikin ado da qamshi ta nannade jikinta da farar laffaya kamar amaryar da aka kawo yau,shigowarta kenan sashen shima gajiya tayi da laqai laqai din khalipha ta gudo yana wanka donta qagu tazo taga annin,nasiha take mata mai kwantar da hankali kan yanayin haduwarta da mahaifiyarta,ta kuma bata shawarar ci gaba da addu’a,sosai duk wani qunci na zuciyarta ya zabge tun a lagos,kukawar data samu wajen khalipha ba qarama bace,taa zauna taayi nazari sosai tun a can,har ta dinga jin kamar tayi aiki da shawarar basma,saidai mahaifiya tafi gaban wasa.

Daganan wata hirar daban suka shiga yi da annin,aysha ta dubi dakin annin sai taga duka baiyi mata yadda takeso ba
“Anni…dakinki kwana biyu yayi kewata gaskiya” murmushi ta sako cikin jin dadi
“Ba dakin kadai ba har masu gidan,haidar cewa yake yayi zaton kwana daya ko biyu xakuyi sai kuka wuce haka” dariya ayshan tayi,kafin tace wani abu akayi knociking qofar dakin anni ta bada izinin shigowa,matashiya ce wadda a qalla ta kusa sa’ar rahama,ta qaraso dakin idonta akan aysha,da qyar take magaba kana kallonta kasan irin yaran nan ne da sakalci da tabara yayi musu yawa,bawai rashin wayo ko dolanci ba alamun rashin kwab’a tun daga quruciya.

Tana magana da anni amma idanunta qir kan aysha lanqwasa yatsunta,hada ido sukayi da ayshan saboda tsabar kallon da take mata yasa taji a jikinta
“Sannu” ayshan tace mata ganin sum hada ido,duk da a qa’ida itace zata soma mata.magana a matsayinta na wadda tazo ta samesu kamar yadda annabi ya koyar
“Yauwa sannunki” ta maida mata tana dauke kai ganin ayshan ta gane kallon qurillar da take mata
“Ya khalipha ya dawo ko?,naga kamar motocinsa”
“Eh ga matarsa nan aishatu sunanmu daya” duban ayshan ta sakeyi sannan ta dauke kai sai kuma tayi shuru.

“Yaushe zaki koma makaranta ne?,kamar kuna tsakiyar karatu ne ko?” Anni ta yanke shurun tana tambayar aysha,dan murmushi tayi
“Gobe…gobe in sha Allah,saboda muna da c.a goben da azahar”
“Batayi candy bane?” Maryam ta tambaya tana duban anni cikin salon dake nuna raini qarara
“A’ah,masters take hadawa” sai ta dan sake kallon ayshan again sannan ta dauke kai tana cewa
“K’nnnnn” a yadda taga shekarun ayshan tayi tsammanin ko degree na farko batayi ba bare aje ga masters,saboda ita gatanan har yanzu degree din taqi haduwa saboda wasa da sakarci data saka a gaba.

Lokacin cin abincin yayi don haka tare suka sauko gaba dayansu,basu kai ga wajen dining ba khalipha ya shigo falon,yayi kyau cikin fararen qananun kaya long sleev shirt da trouser shima fari,idanunshi kan aysha,saidai a dakenshi ya shigo saboda yasan wadanda zai taras a wajen,dan satar kallonshi tayi kadan,ita kanta saiya mata kwarjini ya cika mata ido,hakanan yayi mata kyau sosai,gaidashi sukayi ya karba a dake yana basarwa,fasa hawa dining din anni tayi ta dawo ta zauna a falon tana maraba da khaliphan,saboda haka mutum uku ne a wajen,rahama,maryam da amal,kowacce kanta na fisga tana cin abincinta ba tare data dubi ‘yar uwarta ba,saidai dukkansu kunnensu na wajensu anni.

Nan tasa a kawo mata abincinta,hakan yayi masa sosai,tana ci suna hira,shi da ayshan dukkansu ba wani yunwa suke ji ba,don basu jima da shiga ba tayi musu girki suka ci,wanda ya jima baiji dadin cin abinci irin na yau ba.

Haidar ne da mus’ab suka shigo falon suna tafe suna musu da alama wani abu suka gani,harararsu khalipha yayi
“Hala bakusan muhimmancin sallama bako da zaku shigo da surutu a bakunanku” dukkansu basu san ya dawo din ba da basuyi wannan katobarar ba,shafa kai mus’ab ya soma,yayin da haidar yace
“Afwa yaya,mantuwa”
“Next time..” Bai qarasa ba yayi shuru suma kuma sun fuskanci me take nufi gargadine saboda haka suka ce
“In sha Allah” haidar ne ya qarasa gefan aysha yana murmushi
“Shuru anty kunyi tafiyarku?”
“Ai gashi mun dawo ya haidar”
“Gwara kam don wallahi ba qaramin missing dinki mukayi ba,duk gidan dadinsa sai a hankali” ya fada yana murmushi,dubanshi khalipha yayi,wani abu yadan taba ranshi
“Duk mutanen dake cikin gidan ba mutane bane sai ita kadai?”
“Ba haka bane yaya,antyn ….”
“Ohk idan ta wuce makaranta gobe saika bar gidan”
“Da sauri haka daga dawowarku?”murmushi kawai aysha tayi,sai ya juya yana tambayar anni me aka dafa
” jeka ka gani” ganin wadanda ke kan dining din yasashi dukan kafadar mus’ab
“Dalla jeka debo mana abinci,wadancan ‘yan zaman dumama kujerar sun wani cike wajen,haka zaka je kana cin abinci suna qarema bakinka kallo kamar wasu mayu”, can qasan ranta aysha tayi murmushi,a yanzu ta riga data san me yasa haidar din ke yawan mita akai,a baya mamaki take kan me yasa sam ba hadauwar jini tsakaninsu,ba shakka ma badon uwa ta gari da Allah ya basu ba zuwa yanzu ko kusantarsu dangin ubansu basu isa suyi ba,saidai uwa ta gari da Allah ya basu ya santa zakayi zaton komai bai faru ba,mus’ab na girmama haidar kamar yadda haidar ke bawa khalipha girma,yana game a wayarshi ya isa wajen yaja plate ya zubo musu ya sauko dashi,da yake sau tari sukanci abinci kwano daya idan lokacin cin nasu yazo dai dai,annin ta riga ta saba musu da haka tun lokacin quruciya.

Da d’ai d’ai amal da rahama suka dawo wajen bayan sun gama cin abincinsu,banda maryam data wuce daki tana amsa waya
“Tashi mu wuce” khalipha ya fada bayan ya miqe tsaye
“Tun yanzu?dare baiyi ba da yawa” Rahama ta tambaya idanunta na kansu
“Mun dawo daga tafiya akwai gajiya da take buqatar a wareta” khaliphan ya fada yana hade fuska kamar ya manta anni na wajen,aysha kaman ta zura da gudu haka taji saitaja mayafinta ta sake rufe kanta
“Anni sai da safe”
“Allah ya bamu alkhairi,mu tashi lafiya ayshatu”
“To anni” haka kawai taji kallon da suke binta dashi bai mata ba,tana sane tace
“Anty rahama,sister amal saida safe…..kinsan ya khalipha da son jiki tausa yace yana so” aysha ta fada can qasa saitin rahama wanda tafi kusa da ita,ta yanda idan ba rahaman da amal dake kusa da itaba babu maijin abinda tace,saidai ta makaro,tuni khalipha dake tsaye ya jiyo abinda ta fada din,wato itama ta iya tsokana kenan da cusa haushi ko?,dukkansu zuciyoyinsu kamar zasu fito,basu sake magana ba har suka ida fita daga

Shi ya fara shiga sashen,ya fada saman kujera ya ware hannayensa kan makarin kujerar yana dubanta sanda take shigowa,gab da zata wuceshi ya sanya mata qafa take ta harde tayo kanshi gaba daya,hannunshi yasa ya tallafeta cikin jikinsa
“Me zaki wuce ciki kiyi?,kefa kika ce tausa zaki yimin ko?” Cikin mutsu mutsu ta girgixa kanta tana son qwatar kanta saboda riqon tsauri da yayi mata
“Ohk,yanxu kuma don kinga babu idanunsu zaki canza magana kenan?”
“Kai ka sani na dinga musu haka”boyayyen murmushi ya saki
“Over act kikayi,tunda kuma kika sakamin rai saikin yi,dama am too tired” dage mata yayi kan sai tayi masa idan ba haka ba shi zaiyi mata,da qyar ta kubuta bayan data fake masa da bata karanta komai ba,bedroom ta gudu,ta jima zaune a can sai data dai daita mode dinta sannan ta fito,kanta na a qasa tace
“System dina pls ta rannan…”
“Wadda na kamaki kina kallon fina finan soyayya?” Ya tambayeta ba tare daya dubeta ba,saita kasa amsa mishi
“Nayi seezing,bana so ki sake amfani da ita” mamaki ne ya kamata,me tayi da zai mata seeizing na system?,itakam bata sani ba,saidai koma meye yafi gaban haka saboda haka batace komai ba kawai ta juya ta samu wani guri can daban ta xauna tana duba abinda ya kamata ta karanta.

Sha biyu saura na dare ta tura qofar bedroom din,ga mamakinta saita sameshi zaune dirshan saman gadon da system a gabanshi,tayi tsammani yayi bacci ne,taqi shigowa da wuri don kada abinda ya faru jiya wanda batasan ya akayi ya faru ba ya sake maimaituwa,ta farka ne kawai ta ganta cikin jikinshi,wanda kuma da alama itace ta baro side dinta ta dawo nashi.

A hankali take takowa har zuwa bakin gadon,ba abinda zata yi sai kwanciya kawai,don haka ta aje litafanta kan bedside din dake daura da ita,ta zauna a side dinta ta hada tafukan hannunta ta soma addu’ar kwanciya bacci,bayan ta gama ta hura ta shafe jikinta sannan ta maida duka qafafunta saman gadon,gyaran murya taji yayi wanda ya danja hankalinta,saidai bata juyo ta dubeshi ba
“Bacci zakiyi?” Ya tambayeta yana ci gaba da aikinshi,kanta ta gyada sannan tace
“Eh”
“Gobe zaki koma,hira ya kamata muyi” ya furta a dake kaman bashi yayi maganar ba,dan boyayyen murmushi ta saki
“Cikin wannan satin nima zan koma so ba lallai mu sake haduwa kafin sannan din” ya kuma yin maganar yana kashe system din,rasa amsar sa zata bashi ya sanyata yin shuru,bai sake cewa komai ba shima sai daya kammala komai ya dauke daga wajen sannan ya jingina bayanshi sosai da fuskar gadon bayan ya kara pillow
“Dame dame kike da buqatar tafiya dashi?”
“Babu komai,ina da komai” ta fada cikin sanyin muryarta data bada wani amo da salo ma daban saboda shurun dare da yanayin duhu duhun dakin,wanda hasken wayarshi daya haske fuskarshi mai saye da gilashin qarawa ido gani ya haska fuskarshi sosai,dan yatsanshi ya saka ya gyara glass din sosai sannan yace
“Come closer” daga kanta tayi ta dubeshi,yanzun ma kamar bashi ne yayi maganar ba hankalinsa nakan wayarshi,tsahon sakan goma kafin ta matsa kadan ta rage tazarar dake tsakaninsu ba mai yawa ba can,pillow din dake gefanshi ya dauko ya maida side din da take sannan ya nuna mata inda yake nufi da yatsa ba tare da yace komai ba,a hankali ta zauna inda yace din,tana gab dashi don tana iya jiyo fitar numfashinsa,wanzuwar pillow din a wajen kawai shiya hana cinyoyinsu gogar juba,wayar hannunshi yayi mata nuni da ita saita maida kallonta kai,tana kallonshi ya tafa (www.rahamalls.com) ya shiga,ba dadewa link din ya bude,jerin kayan da store din na rahamalls suke saidawa ya bude,kaya ne babu wanda babu a kai,yaci gaba da dubawa har yazo bangaren computers
“Dubamin…wacce ce tafi kyau?” Ya fada yana scrolling down,da ido ta dinga bin hotunan system din tana kallo,dukka bata banxa ba wadda batayi kyau ba,dai dai kan wata ash tace
“Irinta maman hunaifa….”sai kuma tadan kame bakinta batasan cewa a fili ta fada ba
“ohkey”ya fada yana shiga page din gaba wanda dinkakkun kayan maza suka bayyana,yayi order din wanda zaiyi ya kashe data dinsa,har a lokacin tana zaune a wajen
“bayan na tafi?,me zaki dinga tunawa dani?” So take ta daga kanta ta kalleshi tada da wanne yanayi yayi maganar,amma nauyi da kwarjinin idanunsa dake bisa kanta sun hanata dagowa,a sanyaye tace
“Babu”
“Ni kuma akwai” ya fada kana yayi shuru yana ci gaba da dubanta,batasan sanda ta furta lafazin
“Mene shi?”
“Yanzu nake so ki barmin abu daya da idan na tuna zaici gaba da debemin kewa duk tsahon lokaci” hannunshi ya miqa mata sannan ya kafeta da idanunshi sai ta dan tsaya tana kallon hannun nashi,ya qagu yaji dumin jikinta mai dadi,tunda ya taba dandanashi sau daya har yau feelings din yaqi barin jiki da qwaqwalwarsa.

A hankali ta dora tafin hannun nata itama saman nashi kamar yadda ya buqata,sosai ya rintse hannun kafin ya jawota ta fada jikinsa yasa hannayensa ya rufeta ruf yans jin dumi gami da shaqar daddad’an qamshin turarenta dake tashi a jikinta,dukkaninsu kowanne yana iya jiyo bugun zuciyar kowa,ba wanda yake wani qwaqwwaran motsi a cikinsu kowa yayi luf jikin dan uwanshi.

??????????????????

A kunyace take hada dan abinda tasan tana buqata wanda dashi zata tafi wudil,ta rasa me ya fisgeta jiya har ta amsa tayin khalipha,duk inda yabi saita kaicewa ganinsa,har ya kammala uzurinsa cikin dakin ya rigata fita,batasan meye manufarshi ba akanta shima me yake nufi?,abu guda ta sani har sukayi aure suna kallon juna ne a matsayin wa qanwa.

Riga da skert ne a tamfa a jikinta,qafarta plat takalmi ne mai igiya wanda mahadi ne da jakar hannunta mai azabar kyau da tsari,hijani ta sanya mai hannu iya gwiwa,wanda yake hade da niqab,saita saka glass din da kanyi amfani dashi lokaci zuwa lokaci domin ado,harabar gidan take takowa bayan sunyi sallama da anni,yau duka cikin mutanen nata babu wacca ta gani,kodon da wuri ta fito oho.

Motocin khalipha ta gani jere a harabar gidan,tayi zaton wani guri zashi shima,saita dan tsaya tana duba ta inda zata hangi malam shehu,don wani lokaci shi ko haidar dama wani ke kaita.

Dai dai lokacin khaliphan ya fito da dan sassarfa daga sashen ma’aikatan gidan,da alama wata ‘yar ganawa yayi dasu,yana tafe yana duba agogonshi,caraf ya kamata tana satar kallonshi,ta kalleshi ita kanta batasan yakai sau nawa ba,shigarsa ta yau ba qaramin kyau tayi masa ba,haka uwa uba take jin wani ba dadi gami da wassafa adadin kwanakin da zata dauka kafin ta sake ganinshi.

Dauke kanta tayi ita ala dole saita tayi pretending kan cewa bashi take kallo ba,wani sashen na gidan daban ta maida kanta tana kalla,saidai haka kawai zuciyarta taqi biyota,ji tayi an riqe jakar hannunta,abinda ya sanyata waiwayo kenan ba tare data shirya ba,yana tsaye gabanta ita yake kalla,saidai fuskarsa a dinke take,ya mata kwarjini sosai,hakan ya sanya gabanta faduwa,da hannu ya mata nuni data wuce,jakar daya riqe ta kalla alamun ya sakar mata,sai ya dage kafadu yana gaya mata ina ruwanta,sakin jakar kawai tayi tayi gaba,da sauri nasir yaronshi dake riqe masa muhimman abubuwanshi duk sanda zasu fita ya matso da sauri zai karba saiya dakatar dashi.

Gab da zasu isa wajen motocin haidar ya faka tashi motar ya fito,tuni ya riskesu,cikin girmamawa ya gaida khalipha
“Barka da safiya yaya”
“Barkanka….ina fata ka kammala yadda ya dace?”
“In sha Allahu” ya amsa yana murmushi yana duban aysha sai ya kallo khalipha
“Na fito da motane na kaita?”
“Na hutashsheka yau” ya fada yana bude mata murfin motar da kanshi
“Yaya ni nake kaita dama ai,yauma bansan da wuri zata koma bane shi yasa na fita” tsayawa yayi da abinda yake ya zubawa haidar ido,shakka ta dan shigeshi,don khalipha ba daga nan ba wajen kwarjini,ko dan uwanshi namiji ya zubawa ido sai yaji ya a jikinsa
“Sorry yaya….” Ya fada yana hade hannyensa waje guda
“Anty Allah ya kiyaye hanya,asha L…..” Sai ya juya da sauri yana dariya zuwa cikin gida,cikin zuciyarshi yana tuna hirat da sukayi jiya shida anni bayan barinsu khalipha wajen
“Haidar….kayi a hankali”
“Me ya faru anni?” Ya tambayeta yana tsayawa da bare bayan wayarshi da yake
“Yayanka ya fara kishinka ne” idanu ya zaro
“Kishi anni akanme?” Murmushi ta saki
“Akan matarsa” idanunsa a waje yaci gaba da duban annin yanason yaji qarin bayani
“Ya kamata ka janye jikinka zuwa yanzu,saboda ya fara soyayya,kasan kuwa illar da soyayya kewa wanda ya fada cikinta ba tare daya sani ba ba kdan bane,zaiyita abubuwa gq zaton na wanda yake kallonsa ko yana cikin hayyacinsa,saidai ina lamarin ba haka bane,shi sha’anin soyayya ya wuce duk tunani” ta qarashe maganar tana tubawa kanta da nata masoyin alhj sa’id,da irin gwagwarmayar da suka fuskanta kafin su cimma gaci
“Lalle ya khalipha ya hau network,ni anni kawai ina respecting din anty saboda na jima banga mai shekaru irin nata dake da hankali da nutsuwa kamar haka ba,sannan tausayinta nake ji tun daga randa na fuskanci tayi shigen tamu rayuwar,uwa uba ina taya yaya kishi ne saboda nasan halin sa’o’inmun nan,suna qyalla ido suka ganta ita kadai ba wani gefanta tsaf zasu iya yiwa ya khalioha shigar burtu….hajjaju anni da alama an tuna da,ya kamata na sanarwa mus’ab harma da ya khalipha muzo mu kwashi darasin soyayya….” Ya qarashe yana dariyar zolaya,daquwa ta watsa masa
“kaci gidanku,tashi ka bani waje ja’iri” yana dariya ya bar wajen yayin data bishi da kallo,na shakka soyayya bata tsufa,don har kwanan gobe bata fasa son sa’id dinta ba,da wannan tunanin haidar ya qarasa cikin gida,lallai zancan annin ya tabbata,tunda suka taso da yayan nasu basu taba ganinshi yana soyayya ba,ah lallai abun zaiyi matuqar armashi,zaiso yaga ya za’a buga wannan game din mai qayatarwa.

*mrs muhammad ce*??
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button