Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 30

Sponsored Links

*GARKUWAR FULANI*Cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kerman jiki, ta juyo ta fuskanci inda yake tsaye tare da abkawa jikinshi.

Cikin abinda bai gaza one second ba tamkar gilmawar walƙiya ya janye jikinshi ya kauce gefe.
Hakan yasa ta faɗa jikin show glass ta ruggumeshi gam-gam cikin tsuma da karkarwa tare da sa hannunta duka biyu ta riƙe kanta, tana mai cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil, Auzubikalimatillahi ta’ammati minsherri makalaƙa.”

Tanayi cikin ɗan ɗaga murya mai baiyana firgicin da take ciki.

Related Articles

Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga ƙasan zuciyarshi har zuwa kan lips ɗinshi dole ya taune lip ɗin shi na ƙasa.
Kana sai ya gimtse ya murtuƙe fuska cikin tsare gida yace.
“Karki fasamin abuna!”.
Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta.
Janye jikinta tayi daga jikin show glass ɗin da abkawar da tayi kanshi marfinshi ya ɗan tsage.
Nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe da ƙarfi.
Kana ta tura baki sannan ta juya ta fara tafiya tana ƙunƙunin.
“Allah ya isana banzan al’ada a rinƙa razana mutun anasa hanjin cikina na hautsunewa”.
Baki ya taɓe kana ya zauna bisa kujerar ya jawo tray’n ya ɗibi abincin tuƙeƙen tuwo ne da miyar kase.

Tana fitowa sukayi sahur ɗin a gaggauce sabida lokacin ya ɗan ƙara to.

 

Washe garin da rana bayan anyi sallan azahar.
Ya shigo kamar ko yaushe.
A falo ya samu Ummi da Hibba ita kuwa Shatu tana ɗakinta tana karatu so take ta samu izu uku a wunin yau ɗin.
Gefen su ya ratsa kana ya zauna bisa kujerar zamanshi.
Bayan sun mishi sannu da zuwa ne, ya kalli Hibba cikin kula yace.
“Muhibbat ya azumin”.
Cikin langwaɓe kai tace.
“Da wuya”.
Kanshi ya jinjina kana yace.
“Jeki kira Aunty Juwairiyya”.
To tace tare da miƙewa da sauri ta fita.
Shi kuwa wayarshi ya ciro ya kira Jalal dasu Imaran yace suzo su sameshi a falo.

Jim kaɗan duk suka shigo.
Key ya zaro daga al’jihun tattausan jallabiyar dake ƙasan al’kyabbar jikinshi ya miƙa wa Jamil tare da cewa.
“Ɗauko min briefcase a kan Bedside drower’n.”
To yace kana ya juya ya tafi.
Shi kuwa Ummi ya kalla tare da cewa.
“Ummi me dame kuke buƙata ne?”.
Cikin kulawa tace.
“Akwai komai, sai zam-zam ɗin kane ya ƙare saura baifi gora biyarba”.

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Ba matsala zai isa”.
Lokacin Jamil ya iso. Miƙa mishi jakar yayi, tare da zaunawa gefenshi.
Shi kuwa buɗe jakar yayi.
Murmushi Jamil yayi ganin tana ciƙe maƙil da rafan dubu-dubu sabbi dal-dal.
Rafa huɗu ya miƙawa Jamil hakama Jalal da Imran da Sulaiman.
Sannan ya kallesu tare da cewa.
“Kuje KMC plaza ku zabi kayan sallan.
Sai ya kuma kalli Aunty Juwairiyya yace.
“Aunty Juwairiyya, kuje tare dasu, da Ya Jafar ayi yadda aka saba.
Sannan ku zaɓi abin buƙatar ku.”
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
“To mu gode, kuma za’ayi yadda kace.”
Sai kuma ya kalli Ummi yace.
“Ummi kada ki manta da su Saratu”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“In Sha Allah babu abinda za’a mance”.
Kai ya jinjina kana ya zaro rafan guda biyar ya miƙa mata, sannan ya miƙa wa Aunty Juwairiyya wasu rafofin kana ya bawa Hibba biyu.
Daga nan sukaci gaba da tattaunawarsu.

Washe gari kuwa da safe, suka shirya tsab zasu fita.
Aunty Juwairiyya ta Ummi cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ko zan kirawo Shatu mu tafi tare da ita ne?”.
Da sauri Ummi tace.
“A a mijinta baice muje da itaba mujata mu tafi. Muje dai mu zaɓo mata duk abinda takeso”.
Cikin gamsuwa da hakan tace to.

Hibba kuwa cikin sanyi tace.
“Ayyah Ummi muje da ita”.
Fitowar Shatu ne ta samesu a tsaye cikin shirin tafi yasa ta kalli Ummi cikin sauri tace.
“Ummi ina zakuje?”.
“KMC plaza”.
Ta Bata amsa a taƙaice cikin sanyi tace.
“Nima inzo muje, in samu in fita insha iskan woje”.
Jalal ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Boss ya hana”. Ido ta zuba mishi kana ta juya ta kalli Ummi cikin sanyi tace.
“Shike nan Ummi kuje, Allah kiyaye hanya.”
Amin Amin sukace har sun juya zasu tafi sai kuma tace.
“Ayyah Ummi dan Allah karku daɗe”.
To sukace kana suka fita.

Shiru ta zauna a falon ba kowa hakane yasa ta kunna TV tashar Zee world.
Wani film mai daɗi ta samu sukeyi, sai dai bata san forkonshiba, bisa alamu duk sabone.
Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta.
Tana mgna da Rafi’a.

A haka bacci yayi awon gaba da ita.

Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta.
Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace.
“Ba salla sai kallo da bacci”.
Jin haka yasa ta miƙe zaune tana gyara mayafin kanta.
Shi kuwa tuni ya wuce Side ɗinsa.

Tana idar da salla ta fito. Nan ta samu Saratu tazo, kitchen Suka shiga suka fara aikin yamman.

Sai gab da la’asar su. Ummi suka dawo da kaya niƙi-niƙi. Nan suka ajiye sukayi salla kana suka shiga kitchen ɗin.

Hibba kuwa yashuwa tayi a ƙasa tana birgima kamar bazata kai magriba.

Sai bayan sallan isha’i sun gama aikin sahur ɗin ne.
Suka dawo falo, nan Ummi ta nuna mata ɗinkunanta da aka bada tun Umaymah bata tafiba.
Sosai taji daɗin kayan da ɗinkunan, lallai tana son dogayen riguna Amman tana son surkawa da Shadda, atampa, leshi, musamman Waɗan nan ɗinkunan sunyi masifar kyau. Ko wanne dai-dai jikinta kamar an gwada ta.
Daga nan kuma suka nuna mata gellulluka da hibai da takalma da saraƙunan da suka zaɓo mata bayan sun zaɓawa kansu.
Sun nuna mata nasun ma.
Ummi ta ƙara da cewa.
“Duk zannuwan da abun ɗinkawan kuma an bawa Kabir telen suma duk cikin KMC suke.
Nanda salla dai komai zaizo dai-dai.
Cikin jin daɗi tace.
“Ngd matuƙa Ummi Allah ya saka da al’khairi”.
Amin Amin tace. Kana tace.
“Sheykh zakiyiwa godiya”.
Shiru tayi kamar bataji ba.
Hibba kuwa cikin jin daɗi tace.
Aunty Shatu na zaɓa mana wani Shadda lace mai masifar kyau iri ɗaya na ɗauka mana Royal blue and white Golding color. Nace a tsantsara mana dogayen riguna”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kai kinko kyauta mana”.
Daga nan suka tattara tarkacen suka nufi makoncin baccin su.

Zaune take gefen Ummi tana riƙe da waya cikin murmushi tace.
“Allah ko Umaymah munyi kewarki”.
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“To ko zaku zomin Barka da sallane”.
Da sauri tace.
“Eh Umaymah Allah in ya yarda zamuzo ki tambayan mana shi”.
Cikin dariya Umaymah tace.
“Yoh mace da mijinta sai wani ne zai tambayar miki”.
Cikin sanyi tace.
“Uhummm”.
Ita kuwa Umaymah cewa tayi.
“Ina Umminku?”.
Da sauri tace.
“Gata ta ƙarishe mgnar da miƙawa Ummi wayar.
Cikin fara’a suka gaisa kana Umaymah ta tambayeta ya yaran nata, tace duk suna lfy.
Nan take ce musu ta cewa Shatu ai a saudia zasuyi salla.
Sosai Shatu ta tayasu Murna.

Suna cikin hirar Hadimai guda uku suka shigo da jakukkunan guda uku.
Rusunawa sukayi bayan sun gaidasu ne,
suka ajiye jakukkunan tare da cewa.
“Gashi biyun inji Lamiɗo ɗaya kuma Gimbiya Aminatu ce tace mu kawo miki”.
Sukarishe mgnar suna kallon Shatu.
Godiya tayi musu kana ta kalli Hibba data miƙo mata kuɗi sun kai dubu biyar.
Ta gane manufar Hibba shiyasa ta amsa ta basu.
Godiya sukayi kana suka tafi.

Jim kaɗan Hadiman Hajia Mama sukazo da saƙon Hajia Maman.
Sosai Shatu tayi godiya ta mashi kuɗi a hannun Hibba ta basu.

Nan Hibba ta tattara kayan ta shigar dasu, zata shigar dana HAJIA MAMA tace
“A Hibba barsu zan shiga dasu.”
Gefe ta nuna mata tace ajiyesu anan.

Bayan sunyi sallan azahar sun fito zasu Fara aiki ne ta kalli Ummi tace.
“Ummi bari inje inyi godiya wurin Hajia Mama”.
Cikin tsareta da ido tace.
“Ki bari mana sai ansha ruwa sai in rakaki daga nan kiyiwa Lamiɗo ma godiya.
Duk dai wannan kyauta da yakeyiwa duk ahlin masarautar Joɗa in lokacin salla ya gabato amman muje kiyi godiyar.”
Da sauri tace.
“No Ummi ba sai an rakani ba, zanje ni ɗaya ma, kinga nasa al’kyabba”.
Daga nan ta fice, cike da mamaki suka bita da ido.

Bayan kamar 37 minute ta dawo cike da fara’a sukaci gaba da aikinsu.

Can da suka fito dan yin sallan la’asar,
Ba kayan ba dalilinshi. Da sauri Hibba tace.
“Aunty Shatu kin shigar da kayan ne?”.
Ci gaba da tafiya tayi tare da cewa.
“Maisu ta aiko an kwashe mata abunta dai”.
cikin mamaki sukabi bayanta.

Yau azumi goma sha huɗu gobe 15 in Allah ya kaimu.

Bayan yaci abinci ne ya kira Umaymah nan yake ce mata.
“In Allah ya kaimu gobe iwar haka ƙarfe goma na dare zuwa sha ɗaya jirginmu zai tashi Umaymah”.

“Kai da waye zaku tafi ne?”.

“Nida Dr Aliyu, da Barrister Kamal, sai kuma Ya Hashim da Galadima, da Wambai da Abba na da cimgan ɗin shi”.

Da sauri tace.
“To wai kana nufin kai bazaka je da taka cingam ɗin bane?”.

Cikin sanyi yace.
“Kiyi haƙuri Umaymah dan Allah na roƙeki kada kice inje da kowa, dan Allah a barni mana in huta in na bar ƙasar kam”.

Shiru Umaymah tayi saida taji ya kai ayane tace.
“Shi kenan Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, kuma muna nan tafe”.

Amin Amin yace kana sukayi sallama.

Washe gari kab mutanen masarautar Joɗa masu zuwa Umrah sun gama shirin su.

Bayan ansha ruwa anyi sallan isha’i ne suka shiga kitchen dan aikin sahur, koda ta ɗauko Foodflaks ɗin da akasa mishi abin buɗa baki ko buɗe su baiba.
Hakane yasa Ummi tace to maza ta dafa mishi wani abun.

To tace kana ta juya ta ɗauko, kaza, kwai, dankalin turawa kaɗan, maggi, gishiri, tattasai, attaruhu al’basa mai Curry,
Duk ta matso dasu kusa.
Sai kuma ta ɗebo Kabeji karas.
Ta miƙawa Saratu tace.
“Yauwa Sara goga min su ƙananan, kada ki haɗasu wuri ɗaya, kana ki yayyaka min al’basa sannan ki jajjaga min wata.”
Ta faɗin tana tura mata Attaruhu da al’basan.
Cikin nitsuwa Saratu tace.
“To Aunty ba matsala”.
Ita kuwa Ummi meda hankali tayi kan girkin sahur ɗin.

Wanke rabin kazar tayi, tare da sata a tukunya ta watsa al’basa da maggi da tafarnuwa da citta da kanamfari kaɗan.
Sannan ta rufeshi. Tasa wuta yadda ya kamata.
Kana ta jawo robar dankalin ta fara ferewa tare da cewa.
“Allah aikin nan yana yawa Ummi, kusan wuni muke a kitchen mu kuma kusan kwana shima wai bazaici abuba sai sa mutane aiki”.
Tayi mgnar cikin gajiya da kuma iya gskyar ta, dan muddin kasha ruwa tafa burinka ka samu ka huta.
Juyowa Ummi tayi ta ɗan kalleta tare da cewa.
“A’a ai bakya son hutun tunda kikaje kika samu Juwairiyya kikace ta huta taji da aikin gidanta, nan zaki rinƙa yi, sannan in Hajia Maman ta aiko ki kora Hadiman dashi, ko kisa Hibba ta kaiwa bayi shi.
Kinga duk sun gaji sun daina kawowa, sai Na Gimbiya Aminatu, shi kuma Sheykh yace a dena kawowa tunda kice zaki iya da aikin.
Yanzu da kin bari suna kawowa dai da wata ranama sai munga dama mushiga madafa”.
Sunkuyar da kanta tayi tare da yin shiru kamar bata nan.
Yes ta san duk abinda Ummi ta faɗa hakane.
Ƙarisa feree dankalin tayi kana ta wonƙeshi fes ta ɗaurashi a wuta, ya dafu sosai kana ta sauƙeshi a gefe.
Zuwa lokacin kazar ma tayi lugub, haka yasa ta sauƙeshi ta juyeshi a plate, zare ƙasusuwan tayi duka, sannan ta ajiyeta gefe kusa da dankalin.
Jajjageggen Attaruhu da al’basan da Saratu ke miƙa mata ta amsa.
Cikin plate ɗin dafeffen dankalin ta juyeshi kana tasa kazarma a ciki.
Sannan ta jujjuyasu ta caƙuɗasu da kyau, kana tasa Maggi gishiri ɗan ƙanƙani, sai kuma Curry.
Kwan dake gefe cikin ɗan wani kwanon tangaran ta jawo, ta fasa kwan ta juye cikin haɗin kaza da dankali da jajjagen ta ɗan gwarayasu.
Hibba data shigo yanzu ne tace.
“Yauwa My Aunty dama kwaɗayi ne ya koroni nazo in shiga kitchen.”
Murmushi tayi tare da cewa.
“To matso ki tayani aikin ɗan zuba min ruwan zafi kan Karas ɗincan.
In yayi ɗumi ki juye ruwan cikin kwandon kabejin nan ruwan zafin ya ɗan razana ganyen, sai ki miƙo min shi nan”.
To tace tare da fara aikin.
Ita kuwa Shatu ɗiban haɗin ta rinƙayi tana mul-mulawa kamar Yan boll,
saida ta gama sannan, ta ɗaura man gyaɗa.
yayi zafi ta fara suyasu,
saida ta soyasu duka tasa a Foodflaks kudun kada yayi sanyi ta matsar dashi gefe.

Kana ta matso ta ta amshi Kabeji da Karas ɗin.
Mai tasa kaɗan a tare da al’basa, kana tasa jajjagen kaɗan, ta soyasu, sannan ta ɗauki sauran murmusheshen kazar tasa a ciki kana ta juye Kabeji ta Karas ɗin, sanna tasa Maggi, mintuna biyu zuwa uku ta sauƙesu.
Ta zubawa Hibba da Ummi kana tasawa Sara.
Sanin ya dawone yasa ta shirya mishi komai a tray’n.
Kana ta nufi Side ɗinshi.

Ummi kuwa da Hibba a falon suka zauna suka fara ci suna santi.
Ita kuwa Saratu tattare wurin tayi ta kimtsa komai ta goge sauran kwanuka kana ta tafi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, tuni ya gama kimtsa komai da zai buƙata in yayi tafiyar.
Bai wani ɗauki abu da yawa ba.
Komai na ɗauki shi ya kimtsashi bisa tsari.
A hankali ya taso daga bakin gadon hannu yasa ya shafa cikinsa,
Yunwa yakeji kuma ya gaji da masan shiyasa yau bai kulaba.
Folon ya nufo tare dasa kuɗin dake hannunshi a al’jihun jallabiyarsa.
A hankali ya tura ƙofar ya fito.
A dai-dai lokacin itama ta turo ƙofar shigowa falon .
A hankali ta shiga

Tsakiyar falon ya nufa,
bisa kujera ya zauna, ita kuma kanta a sunkuye ta iso inda yaken.
Ɗan sunkuyowa tayi ta ajiye tray’n kan santa table ɗin, gabanshi.
Kana a hankali ta fara miƙewa zata tashi.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta, da yatsarshi ya nuna mata ta zauna.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“In zauna?”. Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh.

Cikin turo baki ta harari gefen fuskarshi, kana ta ɗan rusuno a hankali ta zauna.
Bakin kujerar dake bayanta.
Cikin muryar ƙunƙuni tace.
“Bacci nakeji”.
Bai kulata ba, sai ma gyara zamanshi da yayi ya nuna mata plate ɗin gabanshi.
“Cikin cinna bikin sama tace.
“Bana gane kurmanci”.
Juyowa yayi ya watsa mata narkakkun idanunshi da bata iya gano meke cikinsu cikin nata.
Karon forko kenan data ga zahirin yadda kalar ƙwayan idonshi suke, sosai kwarjinshi da haibarshi ya danne tsiwarta, a hankali ta matso kusa da inda yake.
Rusunawa tayi har ƙasa a hankali ta buɗe plate ɗin data shirya mishi Chechen balls da ganyen Fork ta ajiyeyi mishi gefen plate ɗin kana tasa hannun zata ɗauki flaks alamun zata samunshi tea a cup ɗin.
Yatsarshi manuniya ya ɗan ɗaga tare da kaɗa mata ƴatsar alamun bai sataba.
Yamutsa fuska tayi tare da turo baki cikin yin ƙasa da murya can cikin maƙoshinta tace.
“Karkaci ma in kaga dama”.
Ta gefen idonshi ya kalleta ba tare da ya juyoba yana kallon yadda takeyin mamul-mamul da lips ɗinta,
Gyara zamanshi yayi tare dasa hannun ya ɗan ɗauki Fork ɗin Chechen ball ya ɗan soka
kana ya ɗago alamun zai kai bakinshi sai kuma ya maida cokalin ya ajiye.
Ɗago kanshi yayi ya zuba mata ido na 3 second kana ya nuna mata idonshi tare da lumshesu alamun ta rufe idonta tako gane abinda yake nufi.
Cikin gunaguni tace.
“Nifa zan tafi bacci nakeji, ba sai na rufe idona a nanba zan tafi kaci abinci k”.
Shiru tayi ganin kallo da yake mata da mayun idanunshi.
tura bakin tayi tare da sunkuyar da kai kana ta murguɗa bakin.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, numfashin ya ɗan fesar kana a hankali ya muskuta ya gyara zamanshi, kaikaicewa ya ɗan yi yasa hannunshi cikin al’jihun jallabiyarsa. rafan dubu-dubu sabbi dal-dal ya fito dasu guda shida.
Miƙo mata su yayi.
Hannunta ta miƙo a hankali ta amshi kuɗin.
Gyara zamanshi ya kumayi kana yasa yatsunshi biyu ya jawo ɗaya plate ɗin ya rufe ɗayan.
Tsuke fuskarsa yayi da kyau tare da kafeta da ido cikin kakkausar murya yace.
“Yau zanyi tafiya daga yanzu, zuwa ƙarfe biyu. Duk inda naje inada lbrin gidan nan duk abinda zakiyi zan sani, duk motsin masarautar Joɗa.
Saboda haka ki kiyayi kanki da yiwa mutane tijara,
Bana son fitsara da rashin sanin darajar manya, ki tsaya matsayinki, bana son shishshigi cikin al’,amuram rayuwata.
Ki kuma kiyayi murguɗa wannan bakin fitsarar in ba hakaba wata rana in kin murguɗa minshi bazai dawo dai-dai ba haka zai zauna a murguɗe a karkace, Allah ya nuna miki matsayi da darajar miji.”
Ƙasa tayi da kanta tare da cewa.
“Kuɗin na meye ne”.
A daƙile yace.
“Na yagawa ne, kije ki yaga ki zubdasu”.
Kallonshi ta ɗan yi ganin hankalinshi baya kantane, ta miƙe tsaya ta juya ta fita.
Shi kuwa bayanta yabi da wani irin kallo.

Sosai yaci Chechen balls ɗin dan yayi daɗi sosai, kuma gashi rabanshi da abinci tun jiya iwar hakan, dan haka yaci iya abinda zai iya ci, kana ya miƙe yaje yayi wonka ya fara shiryawa.

Ita kuwa Shatu tana fitowa a falo ta samesu gaba ɗayansu harda Ya Jafar da Aunty Juwairiyya da kuma. Su Jalal da Hajia Mama.
ganin hakane yasa ta ɗan juya ta nufi falonta bedroom ta wuce taje ta ajiye kuɗin sannan ta fito.
Gefen Ummi ta zauna kusa da Hibba suka ɗan fara hira da Hibba ko inda Mama take bata kallaba.

Can ya fito cikin shigarsa ta yau da kullum.

Da sauri Jalal ya miƙe ya amshi ƴar Kekkyawar jaka ta maza dake hannunshi.

Dai-dai lokacin kuma Ya Hashim ya shigo tare da cewa.
“Sheykh mu tafi lokacin yana ƙurewa”.
To yace kana ya kalli Ummi, Mama, Aunty Juwairiyya, Hibba, yace.
“To zamu tafi”.
Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa.
“Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy”.
Amin Amin sukace.
Ƙwayar idanunshi ya ɗan juya ya kalli inda take ba tare da kowa ya gane ya kalletanba, kana suka juya suka tafi nan su Jalal Jamil duk suka fito dan sune zasu kaisu Airport.

Daga nan suka tafi sha biyu dai-dai jirginsu ya tashi a international airport Ɓadamaya.

Sai kusa ƙarfe ɗaya su Jalal suka dawo,
Sosai suka mamakin wannan karon Ya Jafar bai ce zaibi Sheykh ba.

Haka dai rayuwa tai-ta juyawa sa’a da wuni yau azumi ashirin ne aka kai wanda bahaushe ke cewa an gama goma na wuya za’a shiga na ɗokin salla.
Tunda Sheykh ya tafi baiyi mgnar da kowaba a cikinsu har yau kwanansa biyar.

Yana can ƙasa mai tsarki ibada tayi daɗi baya tuna kowa baya tuna komai sai kusanci yake nema da yardar mahalinsa.
Ko bacci Allah ya yaye mishi sai yayi baccin awa ɗaya zuwa biyu a wuni daga wannan kuma ya gamsu.

Kullum a a masallaci yake kwana.
In gari ya waye sai yayi walahanshi yayi karatun awa biyu, sai ya tafi gidan ƙanan Sitti dake nan Madina wanda shidasu Baba Kamal duk nan suka sauƙa.
to a nanne zai ɗan yi bacci.

To yau kuma shine daren da za’a fara tuhajjudi kuma sannan yaune suka baro Madina suka iso makka.
Kai tsaye gidansu Sitti suka wuce.
Nan suka samu itama Sitti da ahlinta sun iso, Umaymah ma da Haroon yau suka iso.
Kana Ibrahim ma da ahlinshin sun iso daga ƙasar Cairo sosai Sheykh Jabeer yaji daɗin hakan.
Yau ɗin kuma
Yana ɗaya daga cikin dararen da ake tsammanin laylatul Ƙadir.

Kasan cewar babbar zuriya yake.
Sheykh Jabeer Ali, ɗane ga Sheykh Ali jikan Sheykh Abdulkareem kenan,
Wanda sunanshi aka sawa Jabeer.
Yana matuƙar son Jabeer sosai.
Hakan yasa tare suke shiga harami tare suke fitowa.

A nan gida Kautal kuwa hada-hadan jama’ar musulmai na tafiya bisa tsarin addinin musilunci kowa na shirin salla da kuma tarban wannan kwanaki goma na ƙarshe.

Yau miyar shuwaka sukayi da tuwo.
Suna gama kimtsa komai ne suka dawo falo.
Tv suka kunna suna kallo, suna ɗan hira.
Gyara zama Ummi tayi tare da cewa.
“Lallai yau in munyi garaje zamu makara”.
Da sauri Shatu tace.
“In sha Allah bazamu makara ba, wannan uban bindigar da kukace in lokacin sallan Tuhajjudi yayi zava bugata ai zata tashemu”.
Hibba ce ta ɗan gyara kwanciyar ta, tare da cewa.
“Kalli lokacin shabiyu saura yanzuma za’a fara, Ummi kai mana Tashar Saudi”.
Ta ƙarshe mgnar tana kallon Ummi da Rimote ke hannunta.
To Ummi tace kana ta. Juya musu tashar.
Inda suka samu tuni sun fara sallan Tuhajjudi.
Inda ake nuna harami kai tsaye.
Shiru sukayi suna kallon yadda haramin ya cika yayi maƙil da al’ummar Annabi.
Kab an nitsu bakajin komai sai sautin muryar limamin dake karatun al’ƙur’ani cikin zazzaƙar murya mai daɗin sauraro.
Koda aka tafi ruku’u gaba ɗaya a tare aka sunkuya hakan yasa abin yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali.
Sun jeru tamkar zanen fefeyi.
Hakama da suka tafi sujjada.
Musamman da yake cameran ɗaukar sama akayi.
Suna ɗagowa kuma aka juya cameran ya fuskanci limamin da sauran mamu na sahun forko wanda duk manyan malamai ne.

Cikin wani irin kallo Hibba ta miƙa da ƙarfi tare da…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button