Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 5

Sponsored Links

0?5?

 

A hankali take takowa bayan fitowarta daga kitchen dauke da babban tray data shiryo abincin daddy a kai zuwa inda yake zaune yana faman rubuce rubuce cikin wasu takardu,yayin da gimbiyar tasa hajiya sa’adatu mommy ke zaune gefanshi cikin kwalliya tana aikin duba tashar da zata dace da kallonta.

Related Articles

Duk da yawan ma’aikatan dake gidan hakan sam bai damu ayshatu ba ko ya tsone mata idanu,takan bata lokaci aduk sadda take da dama tayi girkin da zata ciyar da mutanen gidan,musamman daddy mutumin dake da qima a idanunta,mutumin da take masa kallon mahaifi,kai tana iya cewa abinda yayi mata ko mahaifin da yayi silar kawota duniya baiyi mata shi ba,don ba zata iya cewa yau ga dadin da mahaifi yake da shi ba.

Gabansa ta aje tray din cikin nutsuwa a ladabce,ya dan daga kansa ya dubeta fuskarshi washe da fara’a
“Sannu indon baffale” murmushi ta saki saboda kiranta da wani suna daya shude can baya cikin tarihin rayuwarta,sai ta duqad da kanta ta koma can baya ta rabe daura da momy,tana jira ya bata dama ta sanar masa tafiyarta qauye da takeso tayi gobe asabar ta dawo litinin tunda bata da makaranta ranar litinin din.

Asma’u ce ta fito daga dakinta sanye da dogon wando da riga ‘yar qarama mai gajeran hannu,sai ta dora top wadda takai har saman gwiwarta,kunnenta sanye da earpiece kaman yadda yake kusan al’adarta kenan ko da yaushe,kanta babu dankwali sai yalwataccen gashinta mai tsaho dake fake cikin ribbom,a shagwabe ta qaraso gaban iyayen nata ta zube a gaban daddyn
“Daddy….tun shekaran jiya ka dawo har yau zuwa fa banga alqawari na ba”
“Hmmm,bake kadai ba,nima shiru nake ji har yau ba’a cemin komai ba,safina ma tayo waya tana jira amma duk daddy ka mana shiru”inji mummy sa’adatu ta fada tana ci gaba da sauya tasha,takaddun ya tattara gefe daya kana daga bisani ya cire gilashin idanunsa yana murmushi
” kowa sai daya min qorafin saqonsa shiru,ayshatu ce har yau banji ta fadi komai ba”murmushi aysha tayi tana sadda kanta qasa,ita awa?,wanne saqo ma ta baiwa daddyn?,iya alfarmar da ya yiwa rayuwarta kadai ta isheta har abada,ta gefan asma’u kuwa fuska ta kwabe tana dan bata rai,ta tsani daddy ya dinga hada yarinyar da su sam,tana ganin bata cancanci jerawa da su ba,yayin da hajiya sa’adatu ta dan tabe baki gami da dauke kai a fakaice,wanda ba kowa bane zai kula da hakan,bai sake cewa komai ba ya kira waya ya bayar da umarni,cikin mintina biyu daya daga cikin amintattun yaran gidan ya shigo jaye da akwati da kuma wata babbar jaka ya dire a falon ya juya ya fice.

Saukowa yayi qasa carfet din ya janyo jakar ya soma kici kicin zugeta hadi da fadin
“Ai gwara na sallameku na huta kada ku cinyeni danye” dukkansu sai da sukayi dariya,kasancewarsa mutum mai barkwanci a wasu lokutan,amma fa idan ya murde sam bashi da dadin sha’ani.

Wayoyi ya fito da su guda biyu irin wanda asma’un ta zaba tace tana so iri daya sak komai da komai,wayace sabuwar shigowa mai dan karen tsada da kyau ya miqawa asma’un,cike da murna da zumudi ta amsa tana jujjuyata ranta fari qal,saidai tuni murnarta ta koma ciki sanda taga ya miqawa aysha irin tata wayar sak,farincikin dake kan fuskarta ya koma bacin rai,ya sake fito da wasu dogayen riguna masu azabar kyau guda shida ya raba musu uku uku,cikin sanyin jiki da fargaba aysha ta miqa hannu zata amsa,yayin da idanunta ya sauka kan mommy da asma’u,mommyn dai ta share kaman bata gani ba,yayin da asma’u idanunta ke kan ayshan,haka ta amsa cikin sanyin jiki tana jerama daddyn godiya da addu’ar Allah ya qaro budi,wasu kayan ya sake fitarwa ya turawa mommyn yana cewa
“Ga kayan su safina nan,saiki san yadda zaki gobe ki aika musu da saqonsu nima na huta”
“Tohm” ta amsa wanda ga duk wanda yai tsai da hankalinsa zai fuskanci ranta a bace yake,muqullin mota sabuwa dal ya ciro ya miqa mata yana fadin
“Ga taki tsarabar saiki barni na sarara” sai a sannan fuskarta ta washe ta koma kaman da,cike da murna tasa hannu biyu ta karba tana masa godiya
“Ta wajenki saiki barwa su asma’u da aysha su ajje tasun ko?”
“Kan uba” kalmar data subuce daga bakin asma’u,motar data jima da ciwa burin daddyn nata yasa mommy ta bar mata shine yanzun zaice wani wai ita da aysha?,wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata yi sharing motar nan da ita ba
“Me kike fada asma’u?” Daddyn ya tambayeta yana mai zuba mata ido don yaso yaji kalmarta ta farko
“A’ah mamaki nake daddy,mun gode Allah ya qara budi”
“Ameen” ya fada yana rufe jakarsa,aysha na gefe baki daya a takure
“Alla ya qaro arziqi daddy mun gode,Allah ya saka da alkhairinsa” ta furta a sanyaye
“Amin aisha….amin” ya fada cikin jin dadi,a tajure take,saboda ji take kaman idanun mommy da asma’u na kanta har yanzu,hakan ya sanya ta miqe tare da fakewa da cewa zata duba farfesun naman kan ragon da takewa mommy a kitchen tayi shigewarta kitchen din,zamanta tayi a can tana duba farfesun tare da sake gyara freezer din da suke zuzzuba kayan girke girke da suke da saurin lalacewa har naman ya nuna,zuwa sannan bata jiyo muryar kowa a falon,hakan ya tabbatar mata sun bar gurin kenan,don haka ta juye naman a warmer ta gyara wajen ta baro kitchen din.

Asma’u kadai ta taras ta nutse cikin kujera,idanunta saman t.v saidai ba ita take kallo ba,ta cika tayi fam,ta soma gajiya da yadda daddyn ke dai daita da ‘yar qauyen yarinyar a komai nata,da kafin zuwanta duka batasan irin wannan ba,ita kadai ta rage a gabansu sai abinda ta zaba ake mata,komai nata daban yake ba tare da an hadata da kowa ba,kallon baqin ciki tabi aysha da shi wadda ta giftata ta nufi dining ta dora warmer din.

Tana saukowa daga wajen mommy na shigowa falon,cikin hanzari asma’u ta miqe ta gyara zamanta sosai cikin bacin rai ta soma fada kaman zata saki kuka
“Yanzu fisabillilahi mommy ni an kyauta min kenan?,babu dama nace ina son abu sai daddy ya hadani da yarinyar nan,yanzu kaman ni ace in saka kaya iri daya da nata,na riqe waya irin tata,mu shiga mota daya tayi driving nayi,mu shiga makaranta a gani ai wallahi sai friends dina su rainani” mommyn dake shirin zama nan wajen tace
“To ya zakiyi husna,sarai kinsan halin mahaifinku,idan yayi niyyar abu babu kai hanashi” ta sake narkewa kaman mai shirin fidda qwalla tace
“Ni wallahi na fahimci kawai daddy ya shurya zubda min mutunci na da ajina,ke ba sai kiyiwa tufkar hanci ba mommy,gaskiya bazan yarda ba nidai kawai ki karbi wayar kya siya mata wata,koni na saka hamid ya kawo mata dai dai ita daga kamfaninsu tunda sun fara qananun wayoyi daga 50k zuwa sama”
“To ai shikenan indai kinsan zaki kawo mata watan,banson ne daddynku ya fuskanci bata hannunta ya daga ma mutane hankali….aysha” mommy ta qwala mata kira wadda ita tuni har ta isa dakinta ma tana shirin daura alwala tayi shafa’i da wutiri,sai ta fasa ta fita kiran mommyn
“Wayar da daddynku ya baku dazu zaki kawomin na ajjiye miki wajena,za’a kawo miki wata wannan bai kamata ki fara amfani da irinta ba tun yanzu” cike da rashin damuwa ta nunawa mommyn inda kayan suke,don tunda aka soma dramer tasan akwai abinda zai biyo baya shinyasa ma bata debe kayan ba,asma’un ita taje ta birkita kayan ta dauko wayar tana jifan ayshan da harara kamar ita ta cewa daddyn ya aikata hakan ko tana da masaniyar zai aikata din
“A’ah dawo ki debi sauran kayan mana ya zaki barsu nan?” Mommy tace da aysha wadda take niyyar komawa dakinta,bata ce komai ba ta dawo ta kwashesu tana fadin
“An gode”.
” ke kawo….zonan mu ga”asma’u ta fada cikin hargagi,ba musu ta dawo da baya ta sake zube kayan a gabanta,hannu ta saka ta bibbirkita ta ciro doguwar riga guda daya wadda bata da kalarta cikin wadda daddyn ya raba musu,gefanta ta jefa tana cewa
“Jeki wannan ta yimin,kamar ma tafi tawa tsada,ina da wata idan na shiga daki zan dauko miki a amadadinta” Tsaki asma’u taja bayan ayshan ta shiga dakin
“Rigima ce fa kawai irin ta daddynku,ita kanta yarinyar na fuskanci rayuwa bata dameta ba,yarinyar data taso a qauye saika dinga siyan kaya na manyan kudi kana bata,harda abinda batasan darajarsa ba ma….miqo min wayar” mommy ta fada tana miqawa asma’u hannu,saita noqe
“Namecy zan bawa ita mommy please” dan zare ido mommy tayi
“Ke bana son sakarci bani nace” cikin shagwaba tace
“Habba mana mommy,kinsan ‘yar waye ne cikin garin nan?,wallahi nasan na bata wannan wayar as a gift ba qaramin daga min aji kyautar zatayi ba” harara mommyn ta watsa mata
“Yar banza,sai shegen son suna da tara qawaye”
“Thank you my mommy,i love you so much” ta fada tana tsalle hadi da faduwa saman kujerar cikin farinciki,ta tabbata gobe zatayi abunda kowacce saita kalleta cikin qawaye,haka nan husna zata sake ganin darajarta da yadda da irin kudin nasu gidan,duk da qawaye ne amma gasa ce sosai a tsakaminsu,kowacce so take tayi abinda zata burge daga,kowacce so take ‘yar uwarta taga ta fita,kowacce so take ta ganta itace a gaba ta baro daya a baya,su kansu basu san cewa abota suke mara ma’ana ba,har hassada da qyashi da kishi ya shigo cikin tarayyarsu yayi kane kane ba tare da sun sani ba,abu daya ne ya hana mommy amshe wayar jin cewa ‘yar wani za’a bawa,kasancewarta mace mai son mu’amala da manyan mutane,tana son a ganta tana mu’amala da wani,wanin ma da yayi suna ya kuma shahara,haka dabi’arta take a jininta take,kusan ba’a qasa yaranta suka dauki wannan dabi’a,za’a iya cewa duk cikinsu mutum daya ce ta banbanta da su,halayenta kusan irin na mahaifinta ne,hakan ya sanya babu jituwa ko alaqa mai qarfi tsakaninta da asma’u,saboda banbancin ra’ayi da hali.

A hankali yake kurbar lemon dake cikin tambulan din qarau na glass sake gabanshi,yayi kyau cikin shigar da yafiyi shigar suit musamman idan ranakun aiki ne,yanayin zamanshi a wajen da yadda yake kai lemon bakinsa lokaci lokaci kadai ya isa ya gaya maka nutsuwar da yake sa ita uwa uba aji da kyau da Allah ya bashi,kusan babu budurwar da zata shigo wajen bata kalleshi ba,masu rawar kan cikinsu kanyi sha’awar dosar sa su taya hajarsu saboda alamun malasa da suke hangowa tattare da shi,saidai basu iya qarasawa saboda kwarjinin da yake da shi suke karya kwana su sauya hanya.

Agogonsa ya sake dubawa ya yarfar da hannu gami da jan tsaki,banda haduwarsu da mas’ood yau ta zama dole baiga abinda zai sashi zaman wajen ba,sam wajen baiyi masa ba,akwai yawaitar cakudedeniyar maza da mata abinda yafi tsana,yana da kishi qwarai duk da cewa kuwa baida qanwa mace,a zahiri zaka ce bai damu da motsin dake faruwa a wajen ba,saidai a badini yana zaune ne yana sake.nazarta da karatun halayyar ‘yammatan zamani,abubuwa da yawa sun faru da suka bashi mamaki suka kuma sake sa mishi tsanar zaman wajen,yana mamakin yadda yammatan ke shigowa,wata tsakiyar maza biyu wata namiji daya,ba wani kunya ko takatsantsan da aka san diya mace da ita,ta zauna cikinsu suci abinci ko abinsha suna hira kaman zasu tafa,wasunsu ma sukan kebe can baya suje susha shisha,wanda shi a wajenshi bata da maraba da taba wiwi da sholisho,hakan take ko a wajen malaman lafiya,zuqa daya ta shishar dai dai yake da ka zauna kasha karan taba sigari guda dari biyu,yana da yaqinin mafi yawansu ba nan suka cewa iyayensu zasu ba,suna iya qarya da sunan mabanbantan wurare da sunan cewa can suka nufa,su binne iyayen har su zo su koma basu fuskanci komai ba.

Dogon tsaki ya kuma ja yana niyyar dauke kanshi wata mota ta shigo wajen,hakanan yaji ta dauki hankalinsa,bawai don kyanta ko bai taba ganin irinta ba,a’ah,hasalima shekararsa uku da hawanta,duk da ba ita yake kallo kai tsaye ba amma hankalinshi na wajen.

kaman a mafarki yaga khadija na fitowa daga gaban motar bayan matashin dake tuqa motar ya zagayo ya bude mata,yana iya ganin sanda ta sauya hijabin jikinta da mayafi sannan ta fito,tare suka jero har zuwa kan daya daga cikin kujeru da teburan dake wajen suna wa juna magana.

Sosai mamaki ya kamashi,don bai tsammaci ganinta a ire iren guraren nan ba tare da wani namiji,da kuma shiga irin ta jikinta,aljihunsa ya laluba sai yaji wayarshi da yake kiranta da ita,yaji dadin hakan,don dama ya taho da ita ne saboda yana da plan din daga nan ya leqa wajenta.

Miscal wajen hudu yana hangota daga inda yake,tana ganin kiran take dauke kanta,daga bisani ta soma tsaki,yana hango saurayin na mata magana kan ta daga,sai a kira na shida sannan ta daga din,sallama ya soma mata ta amsa da qyar tana wani basarwa
“Hala na katse miki wani abu mai muhimmanci….”
“Kusan haka ne,don bacci nake…na dawo daga makaranta na gaji ina buqatar hutu don Allah….ko kudin sun samu ne?”
“A’h…muryarki dama kawai nake da muradin ji”
“Ohk….idan sun samun zaka iya kirana saika gayan ranar da zaka zo” ko kafin ya kashe tashi wayar tuni ta datse nata layin,yana iya hango yadda take yatsina fuska sannan daga bisani ta wurga wayar jaka ta sake tattara hankalinta ga saurayin.

Yana shirin dauke idanunsa ya hangi sanda ya amshi jakarta ya saka mata kudi a ciki,kanshi ya kawar sannan ya miqe tsaye bayan ya ciro wayarshi yaba laluben number mas’od ranshi a bace,shi yasa ya tsani jira,badon mas’ood din ya tsaida shi da alqawarin yana hanya ba da bai zauna wajen har idanunsa sun gane masa abinda ya gani din ba
“Afwa boss,afuwa don Allah”
“Is too late….nayi cancel schedules dina na yau na zauna jiranka duk da muhimmancin da lokacina yake da shi…..saidai wani lokaci kuma idan na samu chance….na kiraka ne na gaya maka karka qaraso baka kuma sameni ba” ya qarashe fada yana shigewa bayan motarshi da jibril ya bude masa sannan ya kashe wayar ya ajeta gefanshi,idanunshi na kansu har sanda driver ya soma jan motar suka soma barin wajen,idanunsa ya lumshe sanyin A.cn dake cikin motar yana ratsashi,sosai zuciyarsa na zafi…dukkan wani hope nashi yana sake raguwa sosai fiye da kowanne lokaci,sunayen Allah yake jerowa daya bayan daya cikin zuciyarshi kamar yadda ya saba duk sanda yaji bacin rai,bai yadda ya zauna zuciyarshi na soyuwa hakanan ba tare daya kira Allah ba.

*mrs muhamma ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *D B*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button