Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 45

Sponsored Links

Tsayawa sukayi cak daga ita har Daddy saboda girma da mamakin da furucin nasa ya basu amma shi ko a jikinsa miqewa ma yayi ya shige bedroom ya rufo qofar.
Hawayene suka fara bin kuncinta tace “muje Daddy” girgiza mata kai yayi da sauri yace “bazaayi haka ba Umaimah ya kamata mu daina yanke hukunci cikin fushi saboda munyi a baya bamuga ribarsa ba qarshe ma sai tarin nadama da fargar jaji da ya sanyamu kiyi hqr kibi umarnin mijinki yafi komai muhimmanci kinsan har yanzu ba daidai yake ba sai kinyi hqr da yanayinsa kafin ya koma normal”

 

Sanya hununsa yayi a aljihunsa ya dauko kudi Riyadh da batasan adadinsu ba ya miqa mata yace “ki kasance me hqr aduk inda kika samu kanki Umaimah komai yayi farko yanada qarshe” komawa tayi ta zauna saman kujera tayi watsi da kayan hanunta tare da kwance Shurafah ta rungumeta a qirjinta tasaki kuka me ciwo tana jinjina yanda zaman nasu zai kasance miqewa tayi ta shiga dakin yana kwance saman bed din yana sauraron qira’ar Shaikh Sulaiman yanabi a hankali ta zauna gefen gadon tare sanya hanunta ta dan daki cinyarsa kadan.

Related Articles

 

Wata zabura yayi ya miqe zaune tare da watsa mata wani mugun kallo yace “meye kuma na zuwa ki dameni wato bakiji abinda na fada miki ba ko?” Share hawayenta tayi tace “Don Allah kayi hqr kabarni nabi Daddy banajin dadin rayuwar qasar nan ni kadai” murmushi yayi na isa yace “bakyajin dadin rayuwar qasar nan ke kadai ko? Hmn tashi ki bani guri”

Kallonsa tayi da manyan sexy eyes dinta da suke cike da qwallah ta bude baki zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace “silent pls nayi waya da reception kije ki karbi key din dakin kusa da wannan banason takura” miqewa tayi ta koma parlourn ta hade kanta da gwiwa taci gaba da rera kukanta cikin tausayin kanta wai yau ita Hameed yake kora daga sashin sa ta fada tare da miqewa ta nufi reception din suka bata key din tare dayi mata jagora har dakin shima suit ne kamar wanda Hameed din yake ciki larabawa akwai tsafta dakin sai zuba qamshi yakeyi tayi ajiyar zuciya ta haye gadon ta kwanta.

 

Yinin ranar gaba daya bataga Shurafah ba itama bata nemeta ba tunda tasan idan taje ma rashin mutunci zata jawowa kanta haka tayita harkokinta ita daya saidai tayi waya a kawo mata abinci idan taci ta sake waya azo a dauka haka har dare yayi ta miqe ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro alwala tayi sallar isha sannan ta tashi ta murzawa jikinta mai ta fesa turarenta ta zura rigar baccinta ta haye gadon taja blanket tayi kwanciyarta.

 

Cikin bacci taji ana danna Bel din qofar ta miqe tare da tambayar “waye?” Cikin muryarsa mai kama data wanda yakejin bacci yace “waye kike tunanin zaizo gurinki a daren nan?” Ajiyar zuciya tayi ta bude dakin ya shigo tare da qarewa dakin kallo har ya sauke idanunsa akanta qirjinsa ya buga da qarfi ganin yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta itamma kallonsa takeyi ganin yanda ta kafeshi da idone yasashi saurin dauke nasa idon cikin son nuna baiji komai ba a yanayin daya ganta yace.

 

“Na lura baki damu da yarinyar nan ba tun safe rabon daki sanyata a idonki amma tunanin qaramar qwalwarki bai baki cewa kije ki duba lfyrta ba” kawar dakai tayi ta fara takawa cikin takunta na isa da ko in kula komai na jikinta yana girgiza ta haye gadon taja bargonta ta rufa batare da tace masa komai ba saboda ta lura da take²nsa idan ta gaba da nuna masa damuwarta akan abinda yakeyi mata to ya samu qofar wulaqantata kenan ita kuma ko kadan bata dauki wulaqanci ba toma banda tsabar rainin wayo irin nasa meye yake sabo a gurinta game dashi da har zaiyi tunanin zata jure wulaqancinsa saboda shi.

 

Matsawa yayi jikin gadon ya janye bargon data rufa dashi ya kwantar da Shurafah a gefenta yace “ki tashi ki bata tasha banason ake barmin yarinya da yunwa” kuda bakwa gurin idan kun samu arziqin motsawa to itama ta motsa wani takaici ne ya tokare masa maqoshi ya haye gadon a fusace ta miqe da sauri zata sauka ya cafkota da sauri ya hadata da jikinsa suka kama kokawa ta tureshi ta miqe da sauri ta nufi parlourn da sauri ya sake cafkota yace “wlh idan kika fusatani zakiji a jikinki” buge hanunsa tayi tace “ka ficemin daga daki banason ganinka dacan kaine kake sani nake bata nonon ko kuwa biyana kake da zaka titsiyeni saina bata”

 

Sakinta yayi da mamakin irin rainin dake tsakaninsa da Umaimah juyawa yayi ya fice saboda yanda zuciya ke fuzgarsa ya afka mata amma bayaso so yake ya nuna mata ko babu ita zai iya rayuwa so yake ta gane kuskurenta na banzatar da rayuwarsa ta watsar da lamarinsa har tabada qofar faruwar komai.

 

Dakinsa ya koma ya zauna tare da dafe kansa so yake ya saba da rayuwa shi daya babu mace so yake ya tursasa kansa da zuciyarsa sabawa rashin mace saboda ya lura fahimtar raunin rayuwarsa akan Umaimah ne yabawa iyayensu da ita kanta Umaiman damar yi masa duk abinda sukeso so yake ya tursasawa zuciyarsa yakiceta a ransa “meyasa ban bari sun tafi da Daddy bane wai?” ya fada yana miqewa daga inda yake zaune ya shiga cikin dakin ya fada saman gadon yanajin wani irin sha’awar kasancewa da ita yanason jinsa a samanta yana sarrafata amma yasan yin hakan qara bata damar cigaba da sarrafashi yanda takeso ne gara ta gane shine mijin kuma a qarqashin sa take hakan zaisa ta rinqa girmamashi rauninsa bazaisa taci gaba da bada qofar cutar dashi ba.

 

Inda tunaninsa ya tafi kenan ita kuwa yana fita ta mayar da qofarta ta datse ta koma gurin Shurafah data rarrafo tanason sakkowa daga gadon ta jata jikinta suka kwanta tare da sanya mata nono da haka bacci ya daukesu koda gari ya waye ma bai nemesu ba suma basu nemeshi ba kowa harkar gabansa yakeyi har yamma sannan ya shigo dakin a parlour ya tarar dasu ta baje kayan wasa sunata wasansu da Shurafah bai sami ko arzikin dagowa ta kalleshi ba ya qarasa gurin ya zauna yarinyar ta tafi ta haye jikinsa tana tsalle²nta ya rungumeta a jikinsa yace “barka da yamma lovely baku iya zuwa gaisuwa ba saidai azo muku ko?”

 

Miqewa Umaiman tayi ta nufi daki tasan ita yake taqala da mgnr kuma bai isa ta kulashi ba tasa qafarta ciki yace “ki shirya kizo muje ki rakani asibiti” tabe baki tayi tayi shigewarta dakin ta kulle tayi kwanciyarta a ranta tace “bazani ba” yafi awa daya yana jiran fitowarta amma shiru ransa ba qaramin baci yayi ba ya miqe ya shiga dakin ya taddata kwance…..

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/24, 2:43 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *G.U*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button