Hariji Book 2 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 2 Page 29-30

Sponsored Links

29&30
Securities da suka firfito patrol ɗin dare suka ci karo da wannan incidence ɗin,lokacin ɗaya saura na dare,Ba wanda baisan Adnan ba,duba fa yanayin kashamarsa ga alheri duk wanda ya gani a bakin get sai yayi masa nasibi,kuma kowa yasan nabeela yikeso
Don haka da sauri a ka wuce female hostel ,saidai anje ɗakin su beelan ance ta tafi dinner ,sauƙinta ma ɗaya a cikin large lecture hall ɗin makarantan suke dinner ɗin,Aikawa akayi a kirata daga nan aka sunkucesa suka shige dashi asibitin cikin makarantan *sick bay*

Abun haushi ,koda aka shaidawa beelah abunda ya faru batajin ko ta damu,kuma ƙiri da muzu tace itafa bazata zo ta fasa rawanta ba,so take aci a siɗe partyn da ita…ƙarshe dai ƙudrat wata yoruba gal dake azaban son Adnan ita ta zauna dashi zuwa safe …

*Tashin hankali wanda ba’a saka maki rana…*

Related Articles

Kusan ƙarfe ukun dare ƙuliya ya shigo ƙasar ,saukansa kenan a airport ,baiso yaransa su san dawowarsa ba,sai kasantuwar yayi dialing wayar son bata tafiya,Abun Almara dukkan yaran da matan haka suka biyo drivers suka taho tarbansa
Sosai abun ya basa mamaki sun haɗe kansu gwanin ban sha’awa ko don sunji labarin zai sake aure ne ohhhoooo .
Sai dai ina son?
amsan da ya ƙagara samu kenan daga garesu,saidai ya alaƙanta hakan da rashin jituwarsa da matan gidan sakamakon yanda ya fifita shi fiye da sauran duk yaransa .
murmushi yayi gamida ƙoƙarn kautar da wannan baƙin *taɓon*

a daga ransa saboda tunosa ba wani alfanu face taso da tarzoma ,allah ya bani ladan haƙury amma,Tabbas sainayi maganin dukkan yafaɗa a ransa yina cije duk laɓɓansa

A na zuwa gida ya tadda delicious na jiransa koina clean sai ƙamshin tulare da girki masu daɗi ke tashi
sai dai a cikin iyalansa ya zauna yayiwa duk yaran kyautan million biyar biyar saboda farincikin tarbarsa da sukayi

Kasa haƙury amaryan tayi saida ta magantu
“ƙuliya kuɗin nan yayi yawa ,kana sangarta yaran nan da yawa duk cikansu ba wanda yakai 18 ,bayan duk kuɗin da ake basu,wannan ai sai na baya su kasa samun komai…

miƙewa banufiyar dakeda yara biyu tayi
to sannu ƴar baƙin ciki ,ko da yike bai kamata inga laifinki ba,duba da inyamuri wajen son kuɗi,to wannan dukiyar ubansu ne in basuci ba wa zai ci?amma fa ga shawara ,tunda daɗin ta kinada gindin haihuwa kya iya zuwa ɗaka ki silluɓo naki mu gani,amma yanzu bar masu ɗiyoyi suyi iko…

hayyayaƙowa duk sukayi,kafin ya miƙe cak ya shige part ɗinsa ,idonsa a runtse yaje ya ɗauko zugegiyar dorinan da ya saba zanesu dashi in sun fara dambe,aikuwa ilai yina shigowa suna sarkewa da dambe
Yaronne suka kwarma ihu
“mama ,abbah da bulala ,ku rabu kar ya zaneku”

da sauri suka cika juna gwanin ban kunya yaransu na kallo

“Gidana ba filin yakin badar bane,da kulum maqota zasuna shigowa rabon faɗa ,to yanxu darene ba wanda zai shigo sai tsumagiyata ya rabaku.

Haƙury suka bashi,saidai kobi ta kansu baibi ba
abu ɗaya ke sanyaya masa rai,in ya tuno ya kusa auran ummy tazo ta amshe aikin girkin da adnan ke masa

oh ina adnan ɗina yake?Allah yasa yina waje nagari,oh rabbb
Atake tausayin adnan ɗinsa ya sashi sakko da hawaye akan dakalin kuncinsa ,da sauri ya ɗauki wayarsa yina ƙara neman lambar ADNAN
amma har ya shige ɗakinsa ba nasara…

*Ayi haƙuri dani again and again plz*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button