Hariji Book 3 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 3 Page 73-74

Sponsored Links

73&74
*Alheri writers asso.*
Haka rayuwa ta cigaba da murginawa da dad’i ba dad’i,saidai zuwa yanzu kudi sun fara Zama ma quliya ,ga courses da yike zuwa akai akai ,yaransa har sun Isa shiga makaranta ya sakasu duka,amma sanda Adnan yakai shekaru biyar ganewa yayi in ya bar yaron a hannun matansa to zai iya salwanta,yaro dan amana. Yakuwa daukesa ya fitar dashi waje karatu ,shima yaje yin PhD dinsa ,a rutsutsin ya dawo ya tarar da duk matansa suna laulayi ,bayan ya koma da watanni Abike ta koma gida haihuwa ,itakuma Adama ta haihu a gidanta ,Aka sakawa yarinya suna rufaida,itakuma Na Abike mufida.

Abunda ya fara sakawa quliya shakku akan matansa yanda Sam suka qi turo masa hotunan yaran da suka haifa,sannan ya Kira en uwansa (me -lafiya family) sunce ba’a fada masu haihuwar ba,ya tura abokinsa yaje ya dubo masa yaransa ,an hanashi ya shiga wajensu,Sosai abun ya daure masa Kai ,To a lokacin ya Zama cikin Alqalan da suke Zama a gaban Alqalin ,Alqalai Na wancan lokacin don haka, ransa yaji ta darsa masa wata abu Na dabam,amma ya barshi sai yayi bincike…

*Bayan shekaru sha biyar*

Related Articles

Adnan a lokacin ya gama Isa duk wani munzalin girma,amma har kawo lokacin quliya bai ta6a kaisa gurin danginsa ba,kuma yaron ko ya tambayi quliya mahaifiyarsa saidai ya kama masa en dabaru,amma bazai bashi takamaiman amsa ba,ga matan quliya da suke wareshi a cikin yarorinsu ,a cewarsu adnan shegene ,quliya garin yawon duniyarsa ne ya dirkawa balarabiya ciki ta haife shi,don haka adnan ya taso Sam bashi da sakin jiki da jama’a ,yafi gane rayuwar makaranta fiyeda Na gidansu
A lokacin da Adnan ya samu hutun semester exams ne Na sati biyu,Quliya ya shirya Adnan suka tafi madina,anan ya bayyanar masu da adnan wato 6ataccen magajin masarautan su ,lokacin Sam baya jin larabci sai turanci ,zuwan adnan ya kawo rikita rikita a dangin kafin daga qarshe bayan tsauraran hujjoji da quliya ya kawo suka kar6i adnan cikin gata da so , Sophy tayi murna da dawowar adnan ,don zuwa wannan lokacin dakin kwana ya gagari safiyya saboda makircin kishiya ,saidai ta kwana a katafaren zauren gidan ,ta kulle kanta in asuba yayi maza zasu wuce masallaci ta cigaba da galantoyi a tsakar gida,ta Zama tamkar almajira ,abinci saidai a bata sauran da mutane sukaci suka rage,amma sai gashi dawowar adnan ya karya duk wani qulli ta koma tayi retaining position dinta kamar da,saidai sarki yace adnan bazai komaba,shima ya kamata ya fara koya masa sha’anin Mulki,don haka akayi masa transfer ya dawo school anan madina.

***
Bayan dawowar quliya gida da kwana uku

Yina zaune a living room dinsa yina kallon CCTV system dinsa ta laptop ,yina kallon jaguljagul din kishin matan gidan wani yayi dariya wani yayi tunanin hanyar gyara,dama kuma don haka ya maqala batareda saninsu ba
Abun tsoro!
Cacan bakine ya sarqe tsakanin adama da Abike akan driver mai Kai yara makaranta,wai saidai akoma Kai su Irfan a baya tunda su manya ne,ana shiga hakkin yaran Abike ,Ana kaisu makaranta late.aikuwa Haj. Adama ta buga qasa akan lallai baza a canja tsariba ,don drivern ba bawan gidan yarbawa bane ba
“Au bawan gidan nufawa ne ko? To wallahi sai an canja tsarin nan tunda dai dukiyar ubansu ne ba Na uban wani ba”
“Me kike nufi ? So kike kicewa yarana shegu ko yaya? ”
“Zancen shegu ai kin fini sani tunda duk dubaran tare muke shirya wa”

“To aini Na gode Allah tunda ni gidan marayu Nike zuwa in samo yaran ,ba dakko kwarto nikeyi ba,yina cinmun tsuliya ,a haka nayi ciki Na kawo shegiya matsayin er quliya ba”

“Ahayye to se Mene? Da inje Ina rainon yaranda ba nawa ba ai gwara in San dan masoyina Na haifa yasha nonona,ba yaran wasu ba arnane ko musulmai oho ”

“Nadaiji ba daukan zunubin zina inada aurena kawai saboda kwadayin abun duniya ,gado don shi baya haihuwa…”

Da sauri ya yi pausing videon ,wani irin zazzafan hawaye Na fita masa a Ido,a take yaji ya tsani duk matansa ,wani ziciya ce take raya mashi ya sakesu duka amma da yayi tunanin yaran ,ya zasu tsinci rayuwar su? Kurum sai ya qyale wannan amma yasa a ransa bashi ba matansa har abada , abun nufi su din ba matansa bane ,kuma duk hidimar da zai yi masu ya daukeshi a matsayin sadaka ,amma dole zai qara aure don bazai iya rayuwa ba mata ba

Da wannan tunanin yaje ya auro Nnenna Wanda take nacin sonsa kuma Account ne a wajen aikinsu,don har alaqawari tayi masa akan indai ya aureta zata musulunta.

Amma da yike batada cika alkawari da ta shigo sai ta ki musuluntan. Saima qaton plaza da ta bude tana Satan masa kudi tana dibga kaya ta saka saurayinta ,matsayin manager din wajen,ashe dama ta auresa ne saboda taji labarin yinada kudi kuma bayida banki ,don haka tabbas a gida yike ajiyan kudinsa.

Da quliya ya gane hakan ,sai ya sa aka tottone tsakiyar bed room din kowaccensu ,ya zuba mata maqudan arziki ,da yasan zai sustaining din rayuwar su Dana yaransu da suka roro koda bashi,da rai.don a gaskiya ya fara tunanin komawa saudiyya dingurgum da Zama don ya Lura matan Nigeria basuda kirki Sam,dukkansu yarigada yayi masu kudin goro,.

Kuma bai bari wata tasan wainnan tsubin kudin yina dakin er uwarta ba,yayi hakan dan su samu peace of mind a barshi ya zauna lahiya,suyi tunanin kowacce itace yardajjiyar mijinta,amma sai kuma kowacce akalanta ya koma yanda zataga bayansa don ta nade dukiyar ita daya…gane hakan yasa ya daina cin komai a gidan don yasan zasu iya zuba masa guba ,amma ya yanke lokacin rabuwarsa dasu da zaran ya aurar da yaransu ,don sune vayaso su hofinta .

…Saidai Ana cikin hakan ummi ta 6ullo rayuwarsa ,wannan ya canja masa lissafinsa Na komawa madina amma ya maida Nigeria tamkar zuwan week end

Adnan kam,shaquwarsa da quliya daga jininsu yake,saidai rashin yardarsa ne yike damunsa,musamman yanda yaga
Yana qoqarin maisheshi cook,bayida damar zaman Nigeria .

Ana cikin hakan ,tsohon su quliya shima ya rasu,don haka aka roki quliya yazo a bashi sarautar gidansu,ba tareda sanin kowaba ya tattara ya koma qasansu,saidai in gawurtaccen shari’a ya samu yazo yayi attending shari’ar ya juya. Sam ya fita sha’anin su duka,kuma duk jarabansa irin Na Arab blood ya roqi Allah ya cire masa sha’awar kowata irin diya mace.

Rayuwarsa ta fara tafiya masa smooth ,kafin tsidik sophy sukayi tafiya Kai ziyara kogon hira,A saman kogon wata balarabiya ta bata tuffa,da nufin girmamawa ,ashe akwai sinadarin guba mai tsintsinka jijiyoyi a ciki Wanda in har taci bazai fara yi mata aiki ba sai bayan awanni Sha hudu ,daga nan sai gawa,wannan kuwa makircin kishiyarta ne,cikin hukuncin Allah sai bataci tuffa din da aka bata a wajen masu kasuwancin kogon ba,saima ba wata kuyangarta tayi da taci ita yau bata muradin ci.
Sosai abun yayi touching matar,suna barin wajen ,ta Kira ta a waya ta shaida mata sophy bataci tuffa ba,kuma mutuwar kuyangar a en awanninnan daidai yike da tonuwar sirrin su

Shiru tayi cikin tunanin chanjin salo

Aikuwa suna hanyar komawa gida a saman titin gada,aka turo katafila tazo zata kutsa ta gefensu ta hankadasu qasa ,motar anan take tayi falle falle,kowa Na motar ya mutu har kuyangar,itakuma rudewa ya juyar mata da qwalwa,ta dawo ba uhm,ba um um.

Tunda wannan abun ya faru quliya sha’anin Mulki ya fice mai aka ya ajiye muqaminsa yace a ba kawunsu ,ya dawo Nigeria ,in kin gansa a madina yaje duba sophy ne…

Ta kwashe shekaru hudu tana jinya,kafin a wannan rutsutsin ta yi lafiya ,wannan shine dalilin zuwansa madina kuma…

*Afwan Na rashin update da wuri,jikina yaqi dadine,saida naje asibiti,na sake amsan sabon treatment amma ynx alhmdllh*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button