Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 16

Sponsored Links

Dafata taji anyi taja numfashi tace “Yaya bakiyi bacci ba?” Murmushi tayi tace “banyi ba Aneesah kawai inata hasaso irin farin cikin da zan kasance a ciki idan na samu Abdu ne gashi kyakkyawa gashi da hatimin nasara gashi ɗan manya” lumshe ido tayi tace “Hakane Allah ya mallaka miki shi Yaya” amsawa tayi da Amin kowacce ta kumayin shiru.
Wayarta taji tana ring ta zarota ta duba number Abdu ce taja ajiyar zuciya ta sanyata a silent ta gyara kwanciya tanason ɗaga wayar amma batason Hasina ta fahimci dawa take wayar wannan tasa taƙi ɗagawa test ta rubuta masa ta tura masa tace _“Mun riga mun kwanta Yaya Hasina kuma tananan”_ amsa ya dawo mata da ita da cewa _“Ina ruwana My Bestie kina nufin saboda Hasina bazanji muryarki ba?”_
Kashewa wayar tayi gabaɗaya ta koma ta kwanta bataji daɗin abinda tayi masa ba saidai hakan shine kawai mafitarta.

 

Washegari da wuri Ƴammatan suka shirya suka fice daga gdan Sagir wani saurayin Hasina shine yazo ya ɗauke su suka shiga gari kamar yanda Hasina ta tsara haka yinin nasu ya kasance sakaje suka canzo kuɗaɗensu Sukasa a account ɗin nasu rabawa biyu sukayi ɗaya account ɗin Hasina ɗaya na Hanisa a ranar har BVN saida akayi musu kafin huɗu sun gama komai nan Hasina ta sallami Sagir ya tafi su ka hau Sahu suka nufi wani ƙauye da ake kira tanagar suna isa sukayi Sa’a malamin ya gama ganin baƙinsa suka shiga suka zauna bayan gaisuwa da ɗan wasa da dariya ya dubi Hanisa yace Hasinatu wannan ita ce ƴar’uwartaki?” Da dariyarta tace “eh Mal itace bakasanta ba fah ashe” dariya yayi yace “yo inafa kawai dai na gane ta ne da kamanninku saidai tafiki kyau fah Hasina kawai dai hasken kine yafi nata fitowa” murmushi sukayi Hasina tace “ai hasken ma tafini nidai dayake ina ɗan shafe²” shiru suka ɗan yi yace “yanzu meye ke tafe daku ko ta amince zatayi rayuwar ne?” Dariya Hasina tayi tace “Mal kenan kanason ayi rayuwa ita wannan ƙyaleta ina wani saurayi na dana taɓa kawo maka sunansa kayimin aiki akansa?” Jinjina kai yayi yace “Idan ban manta ba kamar sunansa Abdul-Ahad ko?” Cafewa tayi da cewa “yawwa Mal shi fah wato a kwanakin nan gaba ɗaya ya juyamin baya baya sanyani a komai nasa abubuwa da yawa da suka shafeshi saidai naji a gurin Hanisa gatanan dake itan aminiyarsa ce to yanzu wani lbr jiya da daddare take bani iyayensa sun matsa masa sai ya fitar da matar aure kuma ni yayimin alƙawarin aure so fahimtar da nayi kamar ba da gaske yakeson aurena ba Ni kuma aurensa nakeso da gaske”

 

Murmushi Mal Wada yayi ya ɗauko ƙasar sa da yake bugu da ita yayi zanensa ya shafe ya sake yin wani ya kuma shafewa saida ya zana sau bakwai yana shafewa sannan ya ɗago duk ya haɗa zuffa ya zubawa Aneesah da kanta ke ƙasa tana chat ido tsayin lkc Hasina tace “Mal ka kafeta da ido bakace komai ba” jinjina kai yayi yace “Wato Hasina lamarin akwai ƙura a cikinsa tabbas a baya kinso samun guri a zuciyar Abdul-Ahad Amma fah yanzu a halin da ake ciki kwata² babuke a lissafinsa hasali ma ko zancenki baya ƙauna ke in taƙaice Miki ma matarsa ta gabata gareshi…..”
Wata zabura Hasina tayi tace “Innanillahi nashiga uku na lalace Mal kayima Allah kayi wani abu wlh da gaske nakeson Abdu bazan taɓa yarda ya kufcemin ba wlh Mal har kisa zan iyayi akan Abdu….” Ɗagowa Aneesah tayi da sauri idanunta cike da hawaye ta dubi malamin gabanta na faɗuwa tace “Yanzu kai bakada yanda zakayi Mal don cikar burin ƴar’uwata?” Sunkuyar da kansa yayi yace “Muna da damar yin addu’a ne da roƙon Allah kusanto da nesa tazo kusa amma bamuda ikon rusa ƙaddara bare canzata Hanisa wannan abun saidai kuje kuyi addu’a ku rungumeshi a yanda yazo kunyi sakaci yanzu haka an ɗaurawa Abdu Aure da…..” Shiru Mal Wada yayi ba Hasina ba hatta Hanisa faɗin an ɗaurawa Abdu Aure saida yasa jinin jikinta daskarewa zuciyarta tayi wata muguwar bugawa data sanyata dafe ƙirjinta ta lumshe idonta tare da cije leɓenta ta latse kiran da yakeyi mata tun zuwansu gurin tama kashe wayarta gabaɗaya.
Maimakon ya kasance Hasina za’a riƙo jiri ne ya ɗebi Hanisa saida Hasina tayi saurin riƙe ta tana kuka tace “kada ki faɗi ki nakasa kijamin ciwo biyu Aneey tabbas Abdu ya cuceni ya yaudareni ashe dama haka akeji wlh tallahi sai yasan ya yaudareni saina fitineshi na hanashi kwanciyar hankali da matarsa”…………..

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:33 PM] Oum Hairan&Affan: *WATA KARUWA*

 

*OUM HAIRAN*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button