Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 10

Sponsored Links

10….

Gyara zaman kujeran motan yayi yadan kwantar da kujeran ya rungume wayan sosai a kirjinshi yana tunanin dan uwanshi, shi karan kanshi he’s missing him, he miss his twin Brother so much, tunane tunane yadinga yi harwani irin bacci mai dadi yay gaba dashi acikin motan.
Kiran Sallan asubahi dayaji yatayar dashi daga baccin dayay awon gaba dashi, ahankali ya bude ido gabaki jiyayi duka jikinshi namai ciwo, yana kallon inda yake yatuna acikin mota ya kwana, dan gajeren tsaki yayi yabude motar yafito ya rufe ya fita daga asibitin ya sallaka titi dan masallacin yana ta dayan side of d road ne.

Saida yajira rana tafito yasakeyin raka’a biyu sanan yafito daga masallacin, wani dan mini supermarket dake gefen mosque din ya shiga yasai brush da tooth paste yafito ya tsallako yadawo cikin asibitin yana tafiya ahankali yay wani irin kyau yana lumlumshe ido alamun bacci bai isheshi ba, shigowa cikin asibitin yayi yy hanyar dakin da aka kwantar da ita, da sallama ciki ciki yabude kofar dakin datake, babu kowa adakin saima gadonta da aka gyara, anyi mopping tiles din kasa sun bushr sai sheki suke, karasawa ciki yayi yana karabin ko’ina da kallo yaja kujeran ya zauna yana kallon TV dakin dayaga an kunna yana tashar CNN, karan bude kofan bathroom yasa yadago kai da sauri wata nurse ce daban tafara fitowa tana kallon cikin bayin, shima kofar bayin ya tsare da ido ya kosa ya ganta, ahankali tafito kanta akasa tana wasa da kumbunan hanunta dasukai wani irin haske, kana ganinta kasan wanka tayi an bata doguwan riganta da aka wanke mata a laundry tasaka yamata kyau sosai, fuskarta babu komi looking natural, kanta babu dan kwali dan nata tun aruwa yabata, kafafunta na cikin wani white slippers dasuka bata tasa, tai wani irin kyau cikin sea blue gown din kaman wata amarya, tunda tafito idanunshi ke kanta bayako kyafta ido harta karaso wajen gadon kafafunta na harhardewa, jitake kaman zata fadi, nurse dince ta kalleshi tace “good morning Sir” gyadamata kai kawai yayi batare dayace komiba, ta kalleta yanda ta tsaya bakin gadon tana wasa da kumbunan har lokacin tace “ki zauna magani zan baki” ahankali ta zauna kaman wacce ke tsoron zama akan gadon, daukan magungunan tayi nurse din tabata tasha da kyar sanan tadau coffee da asibitin suka hada ma patient dinsu dayake arufe yanada zafi sosai ta bata tace “finish it okay” gyadamata kai tayi hakan yasa tai murmushi ta kalli Aabid dake kallonta kaman zai cinyeta tace “Sir your wife is very beautiful” wani irin murmushi yayi yana kallon fuskar nata harda dan kada kafa yace “oh yeah she is, right Jewel?” da sauri tasa hannu tana sosa idonta ko kadan batajin dadin yanda suketa kallonta batada dan kwali batada hijabi jitake kaman ta nutse akasa sabida kunya, murmushi nurse din tayi dake kallonta tace “shy, shy” ta kalli Aabid tace “Dr is coming, he will examine her first before discharging her, dama you’ve cleared all d bill babu abinda zaka biya kuma kawai sallaman ki zaiyi” gyadamata kai yasakeyi batare dayace mata komiba tajuya tafita daga dakin ta rufo musu kofan.
Juyo dakai yayi ya kalleta yanda har lokacin take rike da cup din coffee sai sunnar dakai takeyi, ahankali yatashi daga kan kujeran ya matsar da kujeran baya yay kneeling akasa agabanta har kafafunta na gogan kirjinshi da sauri ta daga kanta ta zaro ido cike da tsoro, murmushi yamata ya zare cup din coffee daga hanunta ya ijiye akan side drawer yana kallon fuskarta, hanunta yakama ahankali kaman yana kama kwai da sauri zata fisge hanunta yarike gam da sauri yana girgiza mata kai yace “no please” yay maganan yana kama dayan hanun yana kallon fuskarta itama shi take kallo kirjinta nawani irin bugawa idanunta sun cicciko da kwalla, murya chan kasa yakirata. “Amatullah” marmar tai da idanunta dake shirin fitar da ruwa, ahankali yace “your brother is on his way to come and pick you, and I don’t want you to go batare dana bayyana miki sirrin dake rainaba” shiru yayi yana kallonta itama shitake ta kallo he could feel yanda kirjinta ke bugawa daga veins din hanunta, kara kwantar da murya yayi yace “I love you Amatullah” wani irin bugawa da kirjinta yayi yasa tafashe da kuka sosai dan ko kadan ta tsani soyayya ita babuma abinda ta tsana irin aure, tsoron maganan aure ma take barinma soyayya, ko wanan ma daya ganta haka sa’a yaci batada lpy kuma batasan ina takeba da tuni tasan yanda tayi ta sabe, hanunta yadan matsa yana kallon yanda take kuka da muryanshi datai rauni sosai yace “I just saw you jiya and am completely blown away, I love every single thing about you Amatullah tunkafin ma ki bude ido, the way am connected to sunrise tun ina yaro I’ve always said maybe akwai wani abu da Allah ya tanadan mini a irin lokacin ne, wen I was small nasha mafarki na tsinci my Jewel acikin ruwa, ashe hakane, the first time I saw you was d yamma, the first I saw you acikin ruwane, your face was glittering yana wani irin haske as bright as the moon acikin ruwan nan, and right there, just right there nasan you are mine, nasan you are the one, deep down I felt this force of attraction dat keep pulling me towards you, I fell for you the very first time I set my eyes on you, please Jewel I know you are not married cus u don’t look married, will you give me that honor to become your life partner? Zaki aureni my Ama?” a tsorace tana kuka sosai ta shiga girgizamai kai, shiru yadanyi yana kallon yanda take kuka tana girgiza kai, ahankali kaman wanda ke tsoron ta yace “I have ur Mum’s number, inkina tsoron fadamusu ne nakira nafada mata ina sonki?” da sauri ta girgiza mai kai hakan yasa yace “please be my wife kinji Jewel nakamu da tsananin sonki, will you be mine forever?!” da sauri ta girgiza mai kai kanta akasa, dan lumshe ido yayi yabude su kadan ya daurasu akanta yace “an miki mijine, are you engage?” da sauri ta gyadamai kai dan kawai yarabu da ita, tsayawa yayi chak yana kallonta sosai yaji zuciyarshi tamai wani irin zafi kaman an watsamai rushin wuta, ahankali yace “saisa bazaki aureni ba because u are engage?” gyadamai kai tasake yi da sauri, da sauri ya lumshe ido yana kokarin saita bugun heart dinshi kafin ahankali yabude su ya daurasu kanta idanun sun kada sunyi ja, cikin wani irin harsh voice yace “bazaki aure shi ba, and if you do saina kashe shi, koma wakika aura I will kill him!” da sauri ta kallai yanda taga idanunshi sun chanza kala yasa ta saukar da idanunta kasa tafara karanto addu’a, wanan wani irin mutum ne Allah yahada ta dashi, ahankali yasaki hannayenta yace “you are my wife Amatullah kifadama kowa haka, and zaki gani saina aurek…” ringing da wayarshi yayi yasa yay shiru ya ciro wayar daga ajihun shi yana kallo ganin bakuwar number ce yasa ya dauka batare dayay magana ba yakara wayan a kunne, daga ta chan bangaren akace. “Umar Faruk Abdullahi mai kaji ke magana, am at d hospital reception daka turamana address din” ahankali ya mike tsaye yana kallon yanda take hawaye yace “okay, am coming” katse wayar yayi ya kalleta ahankali yakarasa jikin gadon yawani irin fizgota tsaye saida tai kara. “wayyo Mama” sata yay ajikinshi yay cupping face dinta yana wani irin kallon fuskarta, itama kallonshi take dan ayanda yarike fuskarta dole ta kalleshi, ahankali ya daura forehead dinshi kan nata yana breathing fast fast kaman yanda takeyi itama kaman zata suma, cikin wani irin voice mai taushi da zafi yace “you are Mrs Aabid Amatullah” dan sassauta rikon daya mata yayi kafin ahankali yay hugging dinta so tight yasa kanta a kirjinshi yay hugging nata well ya lumshe ido, salati kawai take tunda take bata taba hugging namiji in her life ba, gidansu ma gabaki dayan yaran babanta mata ne sai Ya Faruk dayake dan kanin Abba and maganan kirki ma baitaba hadata dashiba, bayanta ya shafa kafin yama soft virgin gashinta kiss ahankali ya chusa hancinshi a gashin cikin wani irin murya data kasa gane ko kuka yake komeyake oho yace “I love you Amatullah My Jewel” shiru yayi ya chusa hancinshi cikin gashin yana shakan kamshin ruwa dayake idanunshi sunyi ja sosai, yakai kusan 2min sanan yasaketa dan sosai yakejin yanda hawayenta suke jikamai gaban riga, kallon idanunta yayi dayaga harsun kumbura sun baci da hawaye, yakai yatsarshi ya sharce mata hawayen datake yace “I’m sorry for hugging you, I couldn’t control my emotions, and I feel better danai hakan” kasa sakinta yayi shi kanshi yarasa wani irin so yake mata he just don’t wanna let her go, wani irin bakin ciki yakeji idan yatuna anzo tafiya da ita, he just don’t want this moment to end, betaba sani haka akeji wen you are in love ba, sake hugging dinta yay akaro nabiyu dudda yanda take kokarin ta kwace kin bata chance din yayi da muryanshi datai rauni sosai yace “please stop crying Jewel, your Dad told me a kano kuke I will come, keep yourself for me for me and you” sakinta yay ahankali yaciro handkerchief daga aljihun shi ya share mata hawayen daya gama wanke mata fuska kafin ahankali yya bending over yama forehead dinta light kiss yay shiru batare daya janye bakinshi daga kan forehead dinba yana sauraran yanda take kuka, cikin wani irin cool calm voice dakenan chan ciki yace “I love you so much Amatullah, your brother is here bari na shigo dashi” janye bakinshi yay ahankali idanunshi sunyi jajir shi kanshi baimasan sonta ya shigeshi hakaba baitaba sanin kana iyason mutum jiya yau son yakaru ba ahankali yajuya yafita daga dakin tareda rufo mata kofa. Fashewa tai dawani irin shegen kuka idanunta sunyi jajir.

Related Articles

A reception yaga Faruk tsaye yana danna waya yana sanye da complete kayan sojoji daya karamai kyau da kwarjini, hanunshi rikeda waya yana dannawa, dailing number daya kiranshi dashi back yayi yana kallon sojan dayaji aranshi shine, ringing wayan Faruk yayi hakan yasa ya dago kai neman me kiranshi, hada ido sukayi sukama junansu kallon kallo kafin Aabid ya daga wayarshi dayay dailing number shi ya nunamai, shima daga wayan yayi ya nunamai hakan yasa sukadanyi murmushi Faruk ya karaso wajen yana jan jakan ya mikamai hannu yace “thanks, we appreciate your hospitality” murmushi kawai Aabid yayi yace “let’s go” yay gaba Faruk biye dashi abaya bude kofan da akayi yasa ta dago kai da sauri Ya Faruk ne ya shigo dakin sanye da kayan sojojin s
dasuka mai kyau sosai yawani irin kafeta da idanu yana kallonta, itama kallonshi take ahankali kafin ta dauke kai, ahankali yatako yazo gaban gadon shikuma Aabid ya tsaya jikin kofa yana kallonsu, tsayawa yay agabanta ya sauke baban bag din hanunshi a gefe yana kallonta, murya chan kasa yace “ya jikin?” gyadamai kai tayi batare datai magana ba hakan yasa yay shiru yana sake kallonta yana nazarin idanunta dasuka kumbura sosai, ahankali yace “why are you crying? Meke miki ciwo” hanunta da aka sama ta drip da aka cire ta nunamai tace “zafi yakemin” hanunshi ya mika ya karbi hanun yana kallon wajen dayadan kumbura daidai lokacin aka bude kofar dakin aka shigo nurse ne da Dr, sunnar da kanta tayi Dr yakaraso jikin gadon yace “My patient takosa ta tafi gida” yay maganan yana gyara stethoscope din jikinshi ya dubata sanan yacire yana murmushi yace “good to go” ya karbi file dinta daga hanun nurse yay yan rubuce rubucen shi na discharge summary sanan yamata prescribe maganin da za’a siya mata, karba Faruk yayi sanan Dr yamusu sallama yafita daga dakin nurse biye dashi, jakar hanunshi Aliyu ya bude yaciro mata dogon hijabin ta baby pink ya mika mata da sauri ta karba tasaka hijabin a zaune bakaramin kyau yamata ba hijabin mai hula dakuma hannu, glasses dinta yamika mata ta karba tasaka ahankali, yabata wani flat shoe na cikin jakan ta saka, sosai Aabid ke wani irin kallonta dan tamai wani irin mugun kyau, hada jakan Faruk yayi yarike yamika mata hannu kallonshi tadanyi kafin ta saukar da kanta kasa ta mika hanun hanunta dake rawa ta rikeshi sanan ta sauko daga gadon ahankali kaman me tsoron saukowa, juyowa Faruk yayi da murmushi kan fuskarshi ya mika ma Aabid hannu yace “thank you so much, Abba yace amika gaisuwar shi, Allah yabada lada, mungode da dawainiya” murmushi yamai yabashi hanun yace “bakomi, ina zaku yanzu?” dan shiru Faruk yayi kafin yace “we are going home, Abba yace nadawo da ita gida straight bazata koma gidan bikin ba, airport zamu yanzu” da sauri yace “I can drop you guys” dan murmushi yayi yace “no you don’t have to worry, taxi na jirana awaje, thank you so much” gyadamai kai yayi ahankali yanadan Satan kallon Hamida da kanta ke kasa har lokacin, hannu Faruk yasa yabude kofan yasakai yafice yana rike da ita sosai yaji zuciyarshi nawani irin breaking yana kallonta hoping ko zata dago kanta su hada ido, ya zuba hannayenshi a aljihu amma har suka fice daga dakin bata dago kantaba wani irin jingina yay da bango ya lumshe ido zuciyarshi yamai so having wani iri yakeji da baitabaji ba in his life, kasa daurewa yayi yabude idanunshi dawani irin sauri yaja kofar yabude yafita daga dakin harda dan gudunshi he wanna see her one last time, yafita bude kofar reception din yayi ya tsaya akan stairs din wajen daidai lokacin Faruk yabude mata bayan motan zata shiga da sauri ya kwala mata kira. “Amatullah!” da sauri daga ita har Faruk suka waigo, hada ido yayi da ita kirjinshi nawani irin suya ahankali yasakin mata wani irin murmushi mai ciwo ya daga mata hannu alamun bye, da sauri ta dauke kak ta shiga cikin mota tana watsa da bakin hijabin ta Faruk yarufe kofan ya juyo yamai murmushi ya dagamai hannu ya shiga gaban motar mai taxi din yaja motar suka tafi sukabar haraban asibitin, motar yabi da ido zuciyarshi namai wani irin rawa rawa har saida yadena hango motar ya lumshe ido, ahankali yabude idon ya sauka daga ya wuce ya shiga motarshi ya kifa jikin kujera yakai kusan 3min kafin yadago yatada motar yaja yabar asibitin da kyar.

Ihun daya cika gidan dashi yasa Mami ta farka daga baccin datake firgigit da salati. “innalillahi wa innailaihi raji’un, Abie, Abie” firgigit magidancin da akalla zaiyi shekaru 60 shima ya farka yana kallonta yanda Mami ta firgice tana kokarin zira slippers yasa shima sauka daga kan gadon kafin ma yasa nashi bathroom slippers din har Mami tafice daga dakin da sauri tafita tai dakin tabude dake facing nasu, wutan dakin akashe sai ihu yake yana kuka, da sauri Mami ta kunna wutar dakin tai kan gadon, yana kwance sai ihu yake yana juye juye yana kuka idanunshi a rufe, da sauri takarasa jikin gadon ta zauna tana bubbugashi. “Son, Son, Aadil, Aadil” da sauri baban nasu ya karaso ya zauna ta wuraren kanshi yasa hannu yadagoshi ahankali yana kiran sunanshi shima. “Aadil” ganin bai bude idoba har lokacin wani irin kuka yake yasa yanuna ma Mami bottle water shi da ake ajiyemai a gefen bed dan yana tashi yasha ruwa cikin dare, da sauri Mami ta dauka tabude, hanunshi ya mika mata ta xubamai ruwan kadan yashafamai a fuska yana kiran sunanshi. “Aadil, Aadil” bude idanunshi yayi yana kallon ko ina nadakin yana jujjuya idanunshi, da sauri Mami ta matso kusa dashi takama hanunshi tace “am here Son, menene? Mekake so eh? Mekema ciwo tell me” tashi yayi daga jikin Abie yafada jikin Mami yasaki kuka ya rirriketa kanshi narawa yana kuka sosai, shafamai kanshi dataji yay zafi ta shiga yi tama kasa magana sabida yanda gabanta ke faduwa, tsugunnawa Abie yayi agabansu bayan ya sauka daga gadon ya shafa kanshi yana kallon fuskarshi yanda yake kuka ashagwabe, cikin lallashi yace “is okay, are you missing Aabid, zance yadawo gobe okay” fashewa yay da kuka sosai harda shesheka yarike Mami gamgam yana girgiza kai, shafa kanshi Mami tayi ta dagoshi handkerchief dinshi Abie yamika mata ta karba ta sharemai wuyanshi da fuskarshi tace “menene? Mafarki kayi? Why are you crying like this, tell me menene” cikin kuka sosai kanshi na rawa yace “s…she..she” da sauri Mami tace “she? Wace she? Menene kuma she Aadil?” fashewa yasakeyi da kuka yace “Mami I want to see her take me to her, Abie” ya kalli baban su yana kuka sosai yace “Abie take me to her” da sauri Mami tace “wane Aadil? Wazamu kaika wurinta? Who are you talking about” fashewa yayi dawani irin kuka yana jan rigan Mami cikin kuka sosai yace “shee” hawaye Mami ta share tana gogemai nashi tace “kaga Aadil dan Allah kadena kukan nan is not good for you, u had a dream I guess, bamusan waye she ba, but zamuyi addu’a ko my Son” make mata kafada yayi yana kuka sosai yana wani irin nishi yana make mata kafada yana tura Mami yana komawa baya ganin haka yasa Abie yahau gadon yana kamashi ganin yana neman buga kanshi yace “Aadil come, a ina she din take to mukaita wurinta? Why are you looking for her, dena fushi zamu kaika wurinta, fadamin who is she eh my Boy?” cikin wani irin kuka yana kallon Abie da idanunshi dasukai ja yana lumlumshe ido yace “she, Abie She, she, Abie I want to see her” da sauri Abie yace “to dena kukan zaka ganta, zamuje but saikasha magani sai muje wurin she, zakasha ai ko?” da sauri ya gyadama Abie kai yana dafe kanshi dakemai wani irin ciwo yana lumlumshe ido kanshi na kokarin tunano mafarkin daya gamayi yanzun nan, fuskar Hamida yagani tazo dakinsu ta tsaya abayan labule shikuma yana kan gado yana buga game din race awaya, dan bude labulen tai kadan ta kwalamai kira tana dariya sosai. “Aadil” da sauri yadago kanshi amma saita koma bayan labulen baiga fuskarta ba, make mata kafada yasakeyi yaki tasowa yacigaba sake lekowa tayi tana dariya sosai takirashi. “Aadil” da sauri yadago kai da gudu takara buya abayan labule, ahankali ya ijiye wayan yatashi daga gadon kanshi na rawa yana sanye da clean white t-shirt danshi mayen white ne baya yadda yasa wani kaya ko Mami tabashi inba white rigaba, da wani fine common flag 3quater daya tsayamai agaban gwuiwa kadan, kafanshi sanye da slippers white yataho kanshi na rawa bakinshi na zubar da miyau yanadan lankwasa kai yana leken labulen yana turo baki kaman mai shirin yin fada yana hararan labulen kaman dan yaro yace “who…who are you?” makemai kafada tayi tacikin labulen tace “oh’oh find me and know me Aadil” cigaba da tafiya yayi harya karaso jikin labulen yana hararan labulen yasa hannu yaja labulen da karfi da gudu tana dariya sosai tajuya zata gudu ya damko hanunta dan juyowa tayi kadan ta kalleshi one side din fuskarta yagani tana sanye da glasses fari, zaiyi magana yaga ta fizge hanunta ta gudu da gudu shima yabita amma koda yafito harya sauko kasa bai ganta ba hakan yasa yadinga kuka cikin mafarkin yana nemanta.

_Wanan littafin is a pure, clean, sweet, mesmerizing, warm, twisted love story dabaku taba ganiba, trust maman Shakur kullum sabon Salo nake kawoma makaranta littatafai na_ .

 

Alhamdulillah anan nakawo karshen free pages din littafin _IN BANI_
In kinason cigaba da karanta littafin nan mai suna _IN BANI_ danjin yanda zata kaya Zaki tura 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting.
Zaki iya turo katin MTN ta watsapp number na kaman haka 07012181461, for any enquiry you can contact me through my watsapp number 07012181461. Thank you lovelies. I love you and I appreciate your support.
_🌹IN BANI 🌹_

 

_M. Shakur_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button