Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 32

Sponsored Links

This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_

_in kinason novel dinan, zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 for those da basu da account ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

Related Articles

 

Tsaki tayi tana kokarin warware daurin zaninta tace “wa kuwa, Hamida mana” wani irin taka birkin dayayi saida ta tsorata tasaki namijin goron hanunta tadafa kirji tana kallon ko ina tana zare ido tace “innahu min sulaymana, wa innahu Bismillah rahmani rahim, kai meya faru haka? Kasheni zakayi?” da kyar ya iya gangarawa gefen hanya yay parking yajuyo ya kalleta yace “wace Hamidan?” hararanshi tayi har lokacin kirjinta nawani irin masifaffen bugawa batadawo daidai ba tace “dan ubanka kana neman kasheni a hanya sanan kuma kana tambayata wace Hamida, tunda munada wata Hamida ne bayan wanda kasani ai shikenan nidai tada mutafi ka kaini gida akwai shirye shirye agabana” Kasa koda kunna motar yayi yajuyo yana kallon Kakan, hararanshi tayi tace “nidai yanda nake cikin farin cikin nan bazan bari bakin cikin ka yabata mini raiba, kaga tafiyata ka jika motarka da ruwan bunu ka tsoma tayoyin motar aciki kasha ka cinye shege mai kama da ifiritu tsabagen bakar mugunta” tabude motan tafita tana surutu ta tare keke napep ta shige tana ballama motar Faruk harara kaman idanunta zasu zazzago kasa.

 

Akofar gidansu aka sauketa tafito tana soka hannu a lalita tace “nawane kudin ka Malam?” “dari biyu ne Hajiya” hararanshi tayi tazaro dari dakuma naira hamsin tace “dari da hamsin zan baka yaro tsadarka tai waya nagadai ba wuyan fetur akeyiba” ta mikomai kudin karba yayi ganin tsohuwa ce yace “to shikenan Allah sa musu albarka” Ameen tace tajuya tabude gate ta shiga cikin gidan, Mama tagani a tsakar gidan da Baba dabasu dade da dawowa daga rakiyan Anty Lami da mijinta ba, dauke kai tayi tai kaman bata gansu ba tai hanyar sasanta, da sauri Abba yabita yace “daga ina kike Umma?” “inda ka aikeni” tafada atakaice tana kokarin bude kofar sasanta, zai biyota ta juyo fuska adaure tace “karka sake ka shigomin sasa ka wuce kacema Haleema a shirya gobe zanyi baki, manya manyan baki kuwa, sanan kabata kudi tai cefane, sanan katuromin Hamida yanzun nan ina jiranta” tana maganan ta rufo kofarta ta wuce ciki abinta, shiru Abba yayi yanabin kofar da kallo kafin ahankali ya saukar da ijiyan zuciya ya juya ya shiga dakinsu dan Mama tabar tsakar gidan, labulen falon ya yaye yaga Mama na kokarin shiga corridor yace “kirama Kaka Hamida zan tafi gidan kaji ni” ahankali takaraso inda yake tsaye tana kallonshi ganin damuwa karara sosai akan fuskarshi, hanunshi takama ahankali takai kan bakinta ta sumbaci hanun kadan tace “karka damu Umma zata sauko okay” gyadamata kai yayi yakai hanun nata kirjinshi ya rungume yana kallonta nayan sakanni kaman yanda itama take kallonshi asanyaye cikeda tausayin shi, saida yadanji dama dama sanan yasaki hanunta ahankali yace “thank you best wife, natafi” murmushi tayi tace “Allah kaika lafiya yakawo kasuwa best husband” kiss yama forehead dinta sanan yawuce yatafi itakuma takoma ciki, dakinsu tabude ahankali suka hada ido da Hamidan da har lokacin bata cire hijabi ba tana zaune kan gado kirjinta bai dena dukan uku uku ba, sai harba ido take kaman wacce tai kisan kai, Ihsan na gefen ta tana homework sai Zainab data gama gyara waken ta turesu gefe ta bude wani littafi tana dubawa, duk dagokai sukayi suna kallon Maman banda ita data saukar da kanta da sauri kasa tana wasa da yatsunta ahankali, da sauri Ihsan ta ajiye byron ta sauko daga kan gadon tace “Mama biscuit din dakikace zaki bani” hanun Ihsan tarike tace “muje yana dakina” sanan ta kalli Hamidan dataki dago kai tace “inkinga dama kije Kaka na kiranki” tana fadin haka tai gaba abinta, Zainab ta gimtse dariyan dake cinta saida taga Mama ta wuce sanan tasaki dariyan da sauri Hamidan ta kalleta da idanunta dasuka cicciko da kwalla, hararanta Zainab tayi tace “Allah ya tsagamin baki sainaki dariya ni” sauka tai daga gadon da sauri Zainab ta tashi itama daga kasa tana kallonta tace “wai ba cewa Mama tayi Kaka na kiranki ba eh hajjaju” harara ta watsama zainab din da manya idanunta tawuce tafita daga dakin ahankali tai sasan Kaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button