Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 14

Sponsored Links

MIJIN MALAMA
Paid book
1 and 2 pay 1k to join us 0811923761615
She is too young a lokacin da Ubangiji ya amshi ran mahaifiyarta Fulani. Majeederh ba zata iya cewa ta shiga maraici ba sbd Abbu ya ɗauke mata dukkan wani nauyin na uwa ya haɗa da na shi na uba. Yarinyar da aka haifa lokacin mutuwar Fulani wacce take bin Majeederh ta amsa sunan Aaliyah, motsin kaɗan Aaliyyah zata ce Anty Jeederh domin ita ta kewa kallon uwa mahaifiya, Albarkaci kyauttukan da Majeederh ke samu tun lokacin ƙuruciya har zuwa matakin girma ya taimakawa Abbu wajan rushe gidan shi tare da gina wani sabo rayuwar ta fara sauya musu, ba sauyi mai yawa ba.
After 20yrs
Shekaru sun ja a lokacin da ta kammala karatun secondary wanda ya yi daidai da ƙara yin saukarta ta uku, lokacin tana da Shekaru Ashirin, Ruma kuma Sha Takwas, Raihana nada shekaru Sha Bakwai. Sai Aaliyyah mai shekara Sha biyar. Filin taron cike yake tab, da manya da ƙana nan mutane, sarakuna da ƴan siyasa, sai kuma masu kuɗin jiyar da suka ƙara sawa taron ya yi armashi. Zazzafar Musabaƙa ake gabatarwa tsakanin makarantar su Majeederh Ahlul Madar, sai Nurul huda, a lokacin ne duk wacce ta lashe zata amsa sunan Gwarzuwar Jiha kuma babbar malama wacce zata dinga wakiltar Ƙasar jihar bakiɗaya.
A hankali ta ɗago kanta inda take tsaye tana bin tarin tarin jama’ar da suke wajan da kallo, ta na jin idanunsu a kan ta. Ta samu kanta cikin wani irin faɗuwar gaba, wacce bata taɓa jin irinta ba. “Malama Majeederh, ke muke saurare” aka ƙara maimaita sunanta a karo na babu adadi. Ta rufe ido tare da mai da kanta ƙasa cikin nutsuwa da kamala ta shiga rera karatun Alkur’ani mai tsarki wajan ya ɗauki shiru sai sautin muryarta dake ta shi. Wannan shi ne karo na uku da Malama Majeederh ke jan ragamar musabaƙar makarantar su, wacce ta zame abin alfahari wannan gaɓar ne kuma idan ta samu nasarar lashe wa zata samu zarafin zama gwarzuwa a garin su, kuma ta zama cikakkiyar Malama.
Kammala karatun na ta mai cike da Tajwid da makarujil-huruf ba tare da gyara ko tini ba ya sanya wajan ya ɗaukar kabbara. Ta lumshe idanunta hawaye ma su zafi tun bayan rasuwar Fulani ya samu damar fitowa daga cikin kyakkyawan Idanunta. Gabaɗaya ta cika burikan mahaifiyarta aure kawai ya rage mata a yanzu. Kyaututtuka ta samu hadda kujerar makka Governor dake mulki a lokacin ya amshi sunanta tare da yi mata al’ƙawarin samar mata da scholarship a ƙasar waje. Ba ta yi wata murna ba har suka isa. Mami ce ta riga kowa shiga gida, hakan ya sa ta shiga har ta cire mayafin jikinta ta ajjiye ƴar fos ɗin tata tare da dawowa parlour ta zauna. Tana zama sassanyar muryar Majeederh mai cike da nutsuwa da kamala babu hayaniya a cikinta ta ratsa kunnen Mami. Sauran ƴan-uwanta na biye da ita. Aaliyyah, Ruma, Raihana.
Mami ta dubi Majeederh dake ƙoƙarin shigewa bedroom ɗinta ta ce.

“Wai lafiya na ganki ba kuzari? Kamar kazar da ƙwai ya fashewa?” Mami ta faɗa furta hakan lokacin da take kallon Ruma dake faɗin. “Babu mamaki baƙin cikin na samu saurayi take mini a wajan taron candy da musabaƙar su” Mami ta kalli Ruma tana riƙe haɓa ta ce “Bana son sharri da rashin ta ido Ruma, Majeederh ba yayarki ba ce? Ina ruwanta da saurayinki?” Ruma ta haɗe rai sosai ta ce
“Mami da ruwana mana, salon kawai ta shafa mana baƙin jini duk kyan nan nata fa bata taɓa yin saurayi ba, ba a taɓa cewa ana son ta ba”
Mami ta ce “Allah Al-hakkamu, akwai abin mamaki ace mace kamar Majeederh shekaru Ashirin amma babu mushinshi ni gaku nan ƙannenta shirin kai ku ɗaki muke” Raihana dake tsaye tana cire mayafi ta ce “A to idan abun ya gagara, kawai sai ta auri ɗan da zan haifa”
Wani irin fashewa da dariya Ruma ta yi hadda riƙe ciki ta ce “Amma Raihana kin fi ɗan iska iya iskanci, ki ce kawai tsohuwo zaki aura masa” Aaliyyah ta ja tsaki tare da tura baki ta shige domin bata da ikon magana yanzu Anti Jeederh zata mata faɗa wai tana rashin kunya bayan su ma rashin kunyar su ke. Zuciyar Majeederh sam babu daɗi she’s just 20yrs ita ba taga girman da tayi da har za a fara mata surutun bata da saurayi ko ba tayi aure ba. Jiki a sanyaye ta shiga bedroom tare kwanciya akan gado. Wayarta ta fara ringing ganin sunan Latifa Omar ya saka ta amsa kiran.
“Latifa” ta kira sunan bayan ta amsa sallamar ta. Latifa dake zaune kusa da mahaifiyarta ta ce “Malamarmu ya gajiya? I just want to say, congratulations! Kin zama babbar malama kamar yadda Abbu yake muradi” Majeederh ta lumshe Idanu ba tare da ta ce komai ba, ita kaɗai ta san wasiƙar jakin da take karantawa a zuciyarta. “Majeederh”
Latifa ta sake kiran sunanta jin ta yi shiru ta ce “Lafiya kike kowa?”
“Allhmdu lillahi”
Cewar Jeederh murya can ƙasa domin bata fiya son surutu baz musamman idan bata cikin yanayi me daɗi.
“Me damunki? Dole akwai damuwa a tare da zuciyarki Majeederh tun ba yanzu ba na fahimci abin da zuciyarki ke muradi” Majeederh ta ja pillow ta rungume tana buɗe manyan Idanunta farare tas da su cikin sauke numfashi tare da nuna yadda abin ke cinta ta ce. “Latifa ba ni da kyau ne?” Mamaki ya kama Latifa ainun domin ko ita da take mace wani lokacin da ƙyar take kai zuciyarta nesa wajan ɗauke ganinta akan Majeederh. “Duba madubi yanzu? after zan kira na ji result” Ta na faɗin hakan ta kashe kiran. Majeederh ta yi shiru tana tana tunanin maganar Latifa Omar ta mance rabon da taga fuskarta a madubi. Ita ɗin ba ma’abociyar ganin kanta a madubi ba ce. Ta miƙe tsaye tana ajjiye wayarta cikin tafiyarta ta nutsuwa ta ƙarasa wajan madubi Idanunta rufe sbd tsoran abin da zata iya ganin wanda zai sanya ya zama dalilin da maza suke gudunta.
Aaliyyah dake tsaye tun ɗazo ta yi murmushi tana leƙa yayar tata ta ce
“I have never seen a beautiful as someone as you” ta ƙara kallon ta ta ce “Wallahi Anti Jeederh ban taɓa ganin macen da take da kyau, kuma take ɓoye kyan nata ba, da ace Maza na ganin ki kamar yadda muke ganinki da tuntuni kin manta da yin aure, ko sau ɗaya ne ki cire liƙab ɗin kema Kiyi saurayi su Anti Ruma su daina miki gori” Majeederh ta buɗe ido tana sakin kyakkyawan murmushi akan fuskarta ta dafa kafaɗar Aaliyyah ta ce
“Kin damu ne?”
“.….Sosai Anti Jeederh, ai gori suke miki ni kuma bana jin daɗi, ina son ki riga su yin aure..”
“Uhm Aaliyyah”
Cewar Majeederh domin asirin ciki sai hanji maganin cuta Allah. Aaliyyah ta ce “Please mana Anti Jeederh jibi idan za mu je ganin lefen Widad zan miki light make up na yi miki ɗauri mai kyau, sau ɗaya dai ka da ki sanya abaya ki saka lace ko atamfa”
Majeederh was just smiled. Kafin ta tsorawa kanta idanu ta cikin madubi ta ce. “Aaliyyah kyau masifa ne an taɓa faɗa miki haka?” Ta girgiza kai ta ce “No at all, me ya sa Anti Jeederh?” “Akwai mazan da kyau ke ruɗar su, baya barin su susan halin da zuciyar su ke ciki, da gaske so na gaskiya su kewa mace ko kyanta ya sa suke santa?”
“More explanation please” Aaliyyah ta faɗa da mamaki domin bata gane ba. Majeederh ta kwasu chocolate guda uku a hand bag ɗin jakarta, ta farke guda ɗaya ta ajjiye, kana ta ajjiye guda ɗaya wacce bata farke ba. Sauran ɗayar ta riƙe hannunta. “Ɗauki ɗaya na baki” Aaliyyah ta dinga kallon chocolate ɗin daga ƙarshe ta saka hannu ta ɗauki wacce ba a buɗe ba. “Me ya sa ita?”
“Sbd ita ce a leda, kuma yadda ledar ke ƙyalli ta ban sha’awa” Majeederh ta harɗe hannu a ƙirjinta ta jima kafin ta ce
“Duk iri ɗaya ce fa?” Aaliyyah ta tura baki gaba ta ce “To ni dai Anti Jeederh wannan ta fi” Murmushi kawai ta yi ta ce “Wannan shi ne illar mace mai kyau, ta na saurin jan hankalin namiji sosai, da yawa sbd kyanta suke so sai an yi aure a fara samun matsala, shi kuma kyau sam baya tabba ranar ɗaurin aurenki ma mijin da zaki aura zai iya ganin wacce ta fiki kyau, to da ga nan yabar ganin na ki kyan sai na ta, duk wanda yake so na tsakani da Allah ko ban buɗe fuskata ba dole watarana ya bayyana a gabana da soyayyar shi, aure kuma lokacin ne let them do, idan sun samu ma su auren su ok” Aaliyyah ta sauke numfashi sbd samun kwanciyar hankali da bayanan Majeederh, ko babu komai ta san cewa ba baƙin jini Anti Jeederh ta yi ba kawai lokacinta ne bai ba.
“…Ya Allah..” Ta ce tana duba tsantsar kyan da Ubangiji ya yi mata, fara ce tas irin farin Fulanin Usul, gashin Idanunta dogwaye sun kwanta luff har saman fatar Idanunta, girar fuskarta har haɗewa take sbd tsabar yawa kuma bata askewa. Gashin kanta jaa bashi da duhu sosai kuma ƙaƙƙarfa irin na cikakkun Hausawa. “No”
Ta ce sanda Idanunta ya sauka a ƙirjinta domin duk wata baiwa a nan Ubangiji ya gama sauke mata su. Ita kanta mamaki take balle kuma ɗa namiji, ta riƙe jikinta sosai jin tsigar jikinta na tashi akwai abin da take tsananin so da ƙauna tun kafin ta kai wannan matakin, a lokacin bata san mene ba har ta dawo ta sani ta fara yin azumin kare kai. Misalin 8:30 na dare bayan idar da sallar Issha duk suna zaune a parlour suna cin abincin dare. Tuwon samo bita ne, da miyar kuɓewa wacce ta ji bushasshen kifi ƙamshi sai ta shi yake. Abbu ya gyara zama bayan ya wanke hannunsa ya ce “Rumana ki mini Hawwa’u”
“To Abbu” ta miƙe tare da shigewa Bathroom ɗin Majeederh ta sameta zaune saman ladduma hannunta riƙe da azkar tana dubawa ta yi murmushi ta ce “Malama Uwar malamai, don Allah ki taimaka ki samu mijin aure domin mu dai ba zamu jiraki ba” ko motsawa Majeederh ba ta yi ba balle ta ɗaga kanta. “To kyakkyawar gidanmu Abbu na kira” ta juya bayan ta sanar mata. A hankali ta rufe azkar ɗin ta miƙe tsaye hijab nata har ƙasa kai tsaye main parlour ta nufa duk suna zaune. “Abbu, Mami barka da dare” Mami ta ce “Ai na ɗauka waya kike sai na yi tunani baki da wanda zai kira, ashe ɗan gado ake”
Ita dai Majeederh couldn’t speak. Abbu ya ce “Ki fara shirye-shirye scholarship ɗinki ya kusa fitowa zuwa Al-Azhar University” Ta ɗago kai da sauri gabanta na faɗuwa ina take jin Al-Azhar University? Ita yanzu gabaɗaya ma at her age ba karatu take buƙata ba, ta samu iya wanda ko wacce mace take burin samun wanda zai riƙe ta har zuwa gidan mijinta. “Hawwa’u”
“Na’am Abbu” “Ki na ji na ai ko?” Ta jinjina kai alamar eh kafin ta ɗago kai kaɗan ta ce “Abbu Al-Azhar fa a Egypt take, Abban Latifa ya ce aure za tayi, Abbu ni ma ka barni na yi…,”
“Na barki ki yi me?” Ya tambayeta a ɗan hassale. “Ina jinki” ta yi shiru Mami ta ce “Tana nufin kabarta ta yi aure ita ma, wanda ba shi da ko saurayi shi ke maganar aure”, Aaliyyah ta ce “Ai wani ya zo zai auri Anti Jeederh Abbu yana ya kore shi wai ba yanzu za ta yi aure ba sai ta gama makaranta, kuma ina ta yi candy” Mami ta riƙe baki ta ce “Aaliyyah Uban naki kike so ki ce yana kurarwa Majeederh samari?” Aaliyyah ta girgiza da sauri ta ce “A’a Mami ba haka nake nufi ba, su Anti Ruma ne suke mata gori wai bata taɓa yin saurayi ba, kuma ai Abbu ke cewa samarin nata sai ta gama makaranta har su Master su P.h.n.d”
Abbu ya yi gyaran murya tare da cewa “Haka na ce, tsarina kenan ba ita kaɗai ba har ke” Ya juya kan Majeederh dake tsugune kanta a ƙasa ya ce “Karatun iya secondary bai isa ba, idan kuma kina da wanda yake son ki da aure ki sanar masa gobe ya zo ya saman sai na yi miki auren idan shi kike so” ganin ran Abbu ya ɓaci sosai ya sa Majeederh cewa “Ka yi haƙuri, Abbu to ka kai Raihana kaga ita akewa refitin a ss 1 take na bar mata scholarship ɗin” da sauri Mami ta ce “A’a, Raihana da Rumana duk aure za su yi, idan da rabo sai su yi karatun a ɗakin mazajen nasu” Abbu ya kaɗa babbar riga yana cewa “Shawarar da na yanke kenan, idan har ta kawo mini wanda zata aura gobe ni kuma zan aurar da ita” Ya yi waje abinsa. Majeederh ta miƙe tare da shigewa bedroom tana zuwa wayarta ta ɗauka ta kasa zama ta shiga lalubar number waya da ƙyar ta iya gano number kira uku ba a ɗauka ba, ta ƙara kira ana biyar aka ɗauka. Ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kafin a hankali ta ce “Assalamu alaika”
An ɗauki tsayin daƙiƙo kafin ace “Wslm, lafiya?” Ta zare wayar ta duba number data kira. Imran dai tasa sani wanda yake mutuwar son ta shi taga sunan shi raɗau a saman screen ɗin wayar. Jin shiru ya sa Imran ya ce
“Majeederh ina da abin yi please, lafiya? Me ki ke da number ta?” A diriri ce sbd rashin sabo da magana ta ce “Uhm Abbu ya ce ka turo wai”
“…. Na turo me…” ya faɗa was abin da ta ce. Ta san ya gane rainin hankali ne, ko kuma har yanzu yana jin zafin kurar karen da Abbu ya yi masa. “Am listening”
“Magabata” Imran ta tuntsire da dariya sosai ya ce “Goodness, ni aurenki? For God sake?” Ya tsaya da dariyar da yake ya ce “Majeederh ai ni bana da burin auren mace mai shekaru ashirin ko sama da haka, kwanaki ma da na ce zan aureki sbd kina cikin age ɗin da nake son amaryata ta kasance, amma gsky yanzu kin mini tsofa” tunda ya fara maganar Idanunta akan Madubi yake kasancewar ba a jima da kawo nepa ba, tana jiran taga ta ina ta fara tsofa a shekaru ashirin shi ne har mace ta fara tsofa?. Imran ya ce “Oh baki samu labarin Raihana nake so zan aura ba? Ko ɓoye miki suke? Ai kullum sai na zo wajanta zan ce kuma ina gab da shirin turo iyaye, am sorry Majeederh Abdul’aziz Khan, amma akwai solution idan zaki amince muna haɗuwa tare da ɗaukewa juna sha’awa da kewa sbd wallahi jikinki ba ƙaramin ruɗata yake ba, ina aurar ƙanwarki ke kuma ina keɓewa dake…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button