Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 1

Sponsored Links

……. 1

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Wanan novel din kirkirarren labari ne.

“au Khaleel ne shine kawani tsaya a bakin kofa bazaka shigo ba” murmushi dake kara fito da kyanshi yayi ya shigo dakin da gudu yaron dake jikin matar yatashi yayo kanshi da muryan shi irin ta yara yace “Uncle Khaleel” tsalle yayi hakan yasa kakkyawan matashin dake sanye da Shadda sky blue wacce akamai dinkin 3quater daya kara amsan cikakken jikin shi yadau yaron ya shilla shi sama yace “my boy” sanan ya sakko dashi ya zauna akan kujeran dake falon yana sunnar dakai ahankali yace “ina yini Mama” tashi matar da akalla zatakai 45 tayi tareda daukan plate din data gama bama auta abinci aciki tai murmushi tace “Khaleel manya bazadai mubar yar kunyan nan bako, ai shikenan bari naturo ma ita” ya kalli Auta wanda tuni ya maida jikin Khaleel din filin wasa tace “Oya Auta kadai san ba wajen ka Khaleel yazo bako, tashi mutafi ciki” noke kai yayi yaron yace “oh’oh” tabe baki tayi ta wuce sama abinta. Khaleel ya kalli yaron saida yafara jujjuyawa ya tabbatar daba kowa adakin sanan ya kalli yaron ahankali yace “My Boy where is Anty Aisha?” sauka yaron yay daga jikinshi yafara tafiya sanan yace “cana dacinta cana cifan citso” shigowan wasu yara kyawawa guda uku mata biyu sai namiji daya yasa yay shiru da sauri suka yo wajen Khaleel atare suka gaidashi “Ya Khaleel welcome” murmushi yamusu yaja kumatun wacce tafisu girma yace “Hello my fatty Fatima” sanan yaja kumatun dayar wacce ita kebi mata yace “Hello my skinny Maryamu” sanan yaja kumatun dayan namijin yace “Hello my Hafiz Ibrahim how was the madrasa today?” kasan cewa islamiyan su 3 narana ake zuwa ataso su 8 nadare achan suke sallar la’asar, magrib, da issha’i atare yaran sukace “Fine Uncle Khaleel” suna mugun son Khaleel Shima haka yake sonsu, Chocolate din daya kawomusu ya basu nan sukamai godiya cike da murna suka tafi sama dan nunama mummy.
Yaye labulen dakin Mum tayi hakan yasa ta juyo da sauri, wata faran budurwa ce dabazata wuce 22 ba, doguwa ce sosai amma batada kiba, zaune take akasan dakin su tana tsifan gashi. Haba Mama tarike tace “eyye yau iskanci naki ne yatashi ko meye kin bar bawan Allah shikadai har yanzu a falo” dan turo baki tayi a shagwabe batare datace komiba, kwafa Mama tayi tace “yo ai shikenan bari nacemai yatafi abunshi” da sauri ta mike tsaye tace “uhmm damafa umm” Mama ta juyo tace “dama me?” shiru tayi tana wasa da yatsar ta dan murmushi Mama tayi tace “will u get out of this room my friend” dogon hijabin ta dake kan gado taja tafita daga dakin tsayawa tayi anan corridor tasa hijabin sanan ta wuce, kada kai Mama tayi tace “andai kusa nan da 4 weeks ne mumuku auren kowama ya huta fitinan nun yara” ta shiga dakin Ibrahim rike da hannu auta dan jimai haddan dazai bayar gobe.
Tunda take sakkowa daga stairs yake kallon ta harta karasa sakkowa ko kallon inda yake ba tayi ba ta wuce kitchen abinta fridge ta bude ta ciro zobon data hadamai da yamman nan mai sanyi wanda yaji cucumber da water melon, ta daura jug din akan tray sanan tasa karamin glass cup akan tray din tadau tray din tafito ahankali take tafiya kaman batason taka kasa wanda dama haka tafiyan nata yake karasowa gaban shi tayi da sauri ya mike ya karbi tray din hannu nata wanda dama haka dabi’an shi yake, tunda tasan shi bata taba kawomai abu ta ijiye da kanta ba dan da sauri yake tashi ya karba. Ganin ya karba yasa ta dauko table ta ijiye agaban shi ahankali hannu tasa ta karbi tray din, hannu shima yasa ya sake karban tray yayi yana kallon kakkywar fuskarta wanda kwayar idonta yake kasa dan taki yarda su hada ido, cikin wata irin murya wanda ita kadai yakema muryan nan aduniya yace “My Eesha” kin amsawa tayi saima sakinmai tray din datayi. ahankali yadan tsugunna ya ijiye tray din still yana kallon fuskar ta tashi tayi fuuu zatabar wajen hakan yasa ya rike gefen hijabin ta chak ta tsaya batare data juyoba hakan yasa ya sauke ajiyan zuciya tareda yin taku biyu yazo gaban ta, sakin Hijabin yayi yay folding hanunshi a kirjinshi yana kallon fuskarta dahar lokacin taki kallon shi, cikin wani irin tattausan murya irin na lallashin mai fushi kuma karamin yaro yace “My Eesha” kin dago kanta tayi saima yatsun ta datake ta wasa dashi, kallon upstairs yayi ganin babu kowa a saman yasa yakara matsowa dab da ita ahankali yace “My Eesha please look at me” saida tai kusan 10 seconds sanan tadago idanunta dake kyalli sabida yanda hawaye ya cika su tam, hakan bakaramin tadamai da hankali yayi ba Kara tausasa murya yayi yace “am sorry” ajiyan zuciya ya sauke kaman shima zaiyi kukan sabida yanda hankalin shi yatashi “My Eesha nabar wayana a office ne nadan fita waje just to come back na tarar da Zainab tai picking call dinki, wlh trust me I don’t have anything to do with her please am sorry Saheeba” hawayen ne suka shiga gangarowa sosai lumshe idonshi yayi ahankali kafin ya budesu ya kalleta sosai idanunshi sukai jaa cikin wata irin karamin murya yace “please ki share hawayen ki okay” ahankali tasa bayan hanunta ta goge hawayen tas, ajiyan zuciya ya sauke sanan yace “kin yafemin my Eesha?” gyadamai tayi hakan yasa yay murmushi sosai yace “to adan kalleni mana” ahankali ta dago manyan idanunta ta kallai tareda sakin mai murmushi daya lobar da dimple dinta ciki sosai wani sanyi yaji har karkashin zuciyan shi ita tafara yin gaba sanan yabita a baya tsugunnawa tayi ta tsiyaya mai zobon a cup sanan ta koma ta zauna akan kujeran dake facing nashi daukan cup din zobon yayi yakai bakin shi yasha wani irin sanyi da zobon yayi ga dadi mai sanyaya rai lumshe ido yayi ya kwankwade duka yasake karawa ya shanye yasake karawa hakan yasa ta ware ido cike da mamaki, daga mata gira yayi yace “my Eesha bazan iya forming ba gaskiya is too sweet” kyalkyacewa tayi da dariya Jin horn din mota yasa ta tashi da sauri yana kallon agogo karfe goma harda minti biyar cikeda rashin Jin dadi yace “oooohh wai su Abba harsun gama hiran dawuri haka ne” dariya tamai tareda mai gwalo ta tashi da saurin tayi kitchen hakan yasa yaciro car key din shi daga aljihu yarike a hannu daidai lokacin tafito da baban goran Eva dake cike da zobo tasamai a ledda binta yake da kallo harta karaso gaban shi ta ijiye akan table sanan ta dago batare data kalleshi ba tace “good night” dadan gudun ta tayi sama saida takai karshen stairs sanan ta juyo ganin ita yake kallo har lokacin yasa ta wara ido tace “go” make mata kafada yayi hakan yasa tasake murmushi tace “go” kara make kafada yayi yaki tafiya bude baki tayi zatai magana daidai lokacin anbude kofa ta arce da gudu ta shige dakin su. Daukan ledan goran zobon shi yayi ya sunnar dakai yana dan sosa keya kaman mara gaskiya yace “welcome Abba” kallon shi mutumin yayi from head to toe sanan ya girgiza kai yay gaba abunshi hakan yasa kaman wanda aka hankada yay hanyar kofa “Khaleel” yaji muryan Abba hakan yasa adan firgice ya juyo yace “naam Abba” Hawa stairs Abba yafara yi sanan yace “tell ur Dad sun chanza time din meeting din daga 9 zuwa 11 :30” ahankali yace “to Abba sanan ya bude kofa yafita, motar shi ya shiga gate man ya bude mai yafita daga gidan. Gidaje uku ne duka tsakanin su yay horn aka budemai gate, parking yayi ya shiga ciki babu kowa a parlor hakan yasa ya wuce sama, direct dakin Mum ya wuce bata ciki hakan yasa ya kwanta kan gado ya lumshe ido fuskar Eesha ke mishi yana, bude kofa da akayi yasa yadan bude ido kadan yace “Ammi” batare data kalleshi ba ta zauna agaban madubi tana share ruwan dake fuskarta, ahankali yasake cewa Ammi juyowa tayi ta harareshi tace “look Khaleel please kabarni nai bacci nariga nasa Ilham ta kaima abincin ka daki, ka girma amma wlh kafi kaninka fitina” dan yatsine fuska yayi yace “Ammi I don’t want food I want another thing” ajiye cream din da Ammi ta dauko tayi ta juyo fully tana facing dinshi sai a lokacin ta lura da damuwan dake kan fuskar shi hakan yasa tace “mekake so to?” dan murmushi yayi sanan ya sosa kai kaman mara gaskiya yace “Ammi kinsan u are d best, u always brings me first, my one and only sweet Mama” murmushi Ammi tayi tace “Khaleel bangane wanan sweet mouth dinnaka ba just tell me wat do u want” kara sosa kai yayi tareda noke murya yace “please Ammi kima Dad magana Yama Abba magana please, Ammi nidai gaskiya arage tsawon bikin nan tunda dai next week zata gama exam basai ayi bikin upper week ba” yakara she maganan yana kallon fuskar Ammi data kafeshi da ido baki sake. Ahankali yasake cewa “Ammi naaaaa” ahankali yaga Ammi takai hannu tana kokarin ciro slippers din kafanta hakan yasa yay jumping daga gadon da gudu yay waje yakucan cin karo da Dad da sauri ya matsa yace “sorry Dad” ya bar wajen da sauri ya shiga dakin shi yana haki.

Related Articles

Visit mamanshakur.wordpress.com for all my write-up
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button