Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 14

Sponsored Links

14…
Tashi tayi tazo gabanshi da sauri, hawayen dake zubo mata ta share cikin muryan kuka tace “please help, ya kwance min jakana, credentials dina and everything are inside” baice mata komiba ya koma cikin mota ya kunna motar yabi guy din daketa gudu yana kokarin shiga wani layi gaban shi yasha da mota ya fito da sauri Guy din yajuya zai kara guduwa, taku biyu yay ya riko guy din ranshi abace da daga hannu zai wanka mai mari da sauri yaron yabashi jakar yace “dan Allah mallam kayakuri wlh yunwa yasa nai hakan, kayakuri dan darajan Allah” shiru yayi dan yaron yabashi tausayi duka duka bazai wuce 22 ba, anatse yace “idan kanajin yunwa kamata yayi kaje kafita ka nemi aiki kasamu kaci abinci stealing daukar abun wasu ba kyau, hakki zai bika” wallet dinshi yaciro daga aljihun bayan wando ragowan cash din dayake dashi yaciro yabashi sanan yabashi card din Abba yace “kaje address din company nan zansa abaka aiki kaji” tsugunnawa yayi yaron yanamai godiya murmushi yamai yace “tashi katafi don’t worry” daidai lokacin ta iso wajen dan tun dazu take tsaye tana kallon abinda yafaru. Tafiya yaron yayi shikuma Khaleel ya mika mata jakar tareda bude mota ya shiga, yana kokarin tada motar ne tace “thank you so much, am grateful, ammm by the way am Farida Maikano and you?” dago kanshi yayi ya kalleta sai alokacin ma ya lura da fuskarta black beauty ce yarinyar tana sanye da doguwar riga na lace orange dakeda rantsin baki, ta yana black gyale akanta, murmushi tasake mai tace “u really help me wlh credentials dina duka suna ciki nagode ko” murmushi yadan mata batare dayace komiba ya kunna motar zai tafi da sauri takara matsowa jikin motar kaman zatai kuka tace “baka fadamin name dinka ba and u are going is dat fair?” murmushi yasake mata ganin yanda takeda surutu sai ta tunamai da Ihsan ahankali yace “just call me MK” kaman mai tunanin tace “MK, MK Mk?” tasake kallonshi alamu tambaya ahankali yace “zaki iya kirana Muhammad” murmushi tamai tace “wow MK nafiso, Muhammad na tsofaffi ne” murmushi yasake yi dan dukta cikashi da surutu yace “bye” girgiza kai tayi tace “please dan tsaya kaji dan Allah” Jakarta ta bude taciro wani memo ta rubuta number ta da sauri ta yagi paper ta mikamai tace “please please ka kirani this is my number kaji, dan Allah” ajiye mai tayi ajikinshi ganin yaki miko hanunshi sanan tamai bye, tafiya yayi haka tabi motar da kallo baki abude saida motar yabace sanan tace “gosh he’s so handsome, jibi muscles dinshi bumbum, awwwn my superman” Ta wani lumshe ido.
[6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button