Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 29

Sponsored Links

“Maman Ibrahim Islam na asibiti fito fito mutafi” arude Mum da Farida data fashe da kuka suka fito daga daki, Mum tace “meya faru?” Anty Hindu tace “baban su yake cemin wai zanga zanga ake a makarantar su, Islam duktaji ciwo mutafi” Hijab Farida ta dauko zata bisu Mum tamata tsawa tace “yanzun nan Sameer zai dawo daga school dawa zai zauna idan yazo? Wuce ki zauna my friend” fashewa ta karayi dawani irin kuka Anty Hindu tace “yi shiru jeki zauna ai zamu dawo, saike kije yanzu dai kar Sameer yadawo ba kowa gidan” fita sukayi sukabarta.

Abba ne ya shigo dasu sukaje dakin Islam sosai jikin Mum yay sanyi bata taba zatan abinda tayi zaiyi resulting to this ba. Tashi Abba yayi yace “bari naje naduba bawan Allah daya taimaketa” Anty Hindu tace “muje nima nagode mishi daga nan” Mum suka bari tareda Islam dake bacci suka fita daga dakin, dakin da aka kwantar da Khaleel Abba ya bude ya shiga, bacci yake, Anty Hindu ne ta kallai sanan ta kalli Abba tace “kaga shine yaron danake fadama ranan nan”. Sake kallon fuskar shi Abba yayi daidai lokacin wayar Khaleel dake gefenshi akan bed yay ringing dauka Abba yayi yaga an rubuta Abba ajiki, Anty Hindu tace “waye?” “baban shine?” Anty Hindu tace “to kadauka mana ka fadamai dansu na asibiti yakamata su sani” fita Abba yayi dan yadau wayar. Bayan yagama wayar ya wuce ya biya kudin komi both ba Khaleel da Islam sanan yadawo ciki, Abba ne yasake kira hakan yasa yafita dan shigo dasu, ba karamin mamaki yayiba dayaga dan Aminin kasuwancin shine, musabaha sukayi tareda kara jajanta lamarin sanan suka shiga ciki.
Tareda Abba da Yusuf Babban Islam suka shigo dakin da sauri Yusuf ya karasa kusa dashi ya zauna Abba yay ajiyar zuciya yace “Allah sawake, ya yartaka dafatan dai babu wata matsala babba” Abban Islam yace “a’a Alhamdulillah bacci ma take, kampanin nanko sun kiraka? abubuwa sunsa na manta ban kirakaba” kafin yay magana Anty Hindu tace “kunsan junane” murmushi dukansu sukayi Abban Islam yace “amini nane muna kasuwanci tare” gyada kai tayi tace “masha Allah” Abba yace “muje ko mudubata” tashi dukan su sukayi harda Yusuf suka shiga dakin da aka kwantar da Islam, ba karamin mamaki Yusuf yay ba dayaga yanda Islam ke kama da Eesha ko wanan ce wacce Khaleel yataba cewa yagani? Ajiyar zuciya yadan sauke yace “bambamcin su kawai shine wanan tafi Eesha jiki kadan” . Gaisawa da Mum Abba yay yamata ya jiki sanan suka baro dakin.

*JARABTA*

Related Articles

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button