Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 30

Sponsored Links

30…

Da magrib yatashi yana karema dakin kallo Yusuf daya gani akan kujeran dakin yana kallonshi, yace “wat happen?” dan murmushi Yusuf yamai yace “kasha uban teargas ne ka sume ma mutane” tashi yay ya zauna yana dan yatsine fuska sabida yanda ciwon kafarshi kemai zafi, Yusuf ya nunamai wata white t-shirt daya fita ya siyomai yace “ga riga kasa ka dauro alwala see dadduma kazo kai sallan asri da magrib mutafi gida dan an riga an sallamemu” rigar ya saka sanan ya shiga bayin dakin ya dauro alwala yazo yay salla.
Bayan ya idar yana kan dadduma wayar Islam dake kan gadon tai kara hannu ya mika ya dauko “My Heart beat” wani irin bugawa kirjinshi yayi dayaga sunan, duk yanda yaso ya hakura yakasa saida yay picking call yasa a kunne daga dayan bangaren Fahad yace “princess inata miki text baki replying, I miss you yau ba muyi wayaba” wani abune yaji ya tokare mai zuciya, “Hello my princess are u there luv?” “mallam karka kara kiran layin nan, an riga an mata miji am her husband to be, so be very careful” yafada cikin fushi ya katse wayar, tashi yay ya linke daddumar yabama Yusuf dake kallonshi baki bude yadau wayar shi batare daya kalli Yusuf ba yace “muje” fita sukayi sanan ya juyo ya Kalli Yusuf ahankali yace “am coming” zama Yusuf yay akan kujerun dake reception din shikuma yay hanyar dakin da Islam take, ahankali ya bude kofar, dayar gajeren sallama dan bama tajishi ba tana zaune kan gado da doguwar riga ajikinta na atampa kanta da bakar hula da aka dan matsar dashi baya sabida bandejin goshin, ta mikar da kafafunta taja doguwar rigar zuwa saman gwuiwowinta tana hura ciwon dataji dake mata zafi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button