Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 21

Sponsored Links

Kafin takai tsakiyar compound ya cimmata yasha gabanta, chak ta tsaya tana waige waige duk ta rude dan kar wani ya gansu barinma Anty Hindu, arude tahada hanunta biyu 🙏🏿 tace “dan Allah karabu dani, waikai ajjani ni” sosai idanunshi suka xhanza kala ga heart dinshi dake wani irin mugun racing yana duka fat fat fat, gabaki daya yanda take magana yasa yaji kanshi yafara juyawa, ahankali yakai hanunshi daya yadafe kan, da wata irin murya ya kalleta yace “are you my Eesha” girgiza mai kai tayi arude yace “then who are you? Mesa idan na ganki bana iya hakura?” sake girgiza mai kai tana waige waige tace “wlh ni ba wacce kake nema bane, plz go karka sani a wahala” cire hanunshi yayi daga kai yay folding hanun a kirji yana wani irin kallonta, sosai jikinta ke rawa tace “na shiga uku, mallam inkana ma Allah katafi karabu dani” ganin ko gezau baiyi ba har lokacin kuma ita yake kallo kaman wani sabon maye yasa tace “kaji dan Allah katafi bani bace wacce kake nema ba, wlh in aka ganni dakai anan yau na shiga uku” takarashe maganan tana yarfe hannu idanunta sun cicciko da hawaye, ajiyar zuciya ya sauke da muryarshi datai mugun rauni yace “please don’t cry kinji” yay maganan kaman zaiyi kuka ahankali yace “naji zantafi but on one condition” ware ido tayi tana kallon shi, ajiyar zuciya yadan sauke sanan yace “gobe by 4 zanjiraki a bakin layin nan, magana nakeso muyi, inhar bakizo ba zan biyoki har gida” gyadamai kai tayi tana waige waige tace “eh na yarda, naji please katafi Abbana yakusa dawowa” kallon fuskar ta yay nayan sakkanni kaman mai nazarin wani abu ahankali ya tako zuwa gabanta da sauri ta matsa baya, kallon kwayar idonta yayi da sauri ta kawad dakai ganin ya cikamata ido, ahankali yace “please karki kara fita ahaka” yay maganan yana nuna gyalen data yafa, kaman mai rada yace “I don’t like it” yanzu dai tayarda mutumin nan baida lpy me ruwan shi da gyalen ta, “bye” taga ya daga mata hannu, yana fadin haka yawuce ta gefen ta yafita daga gidan yana tafiyan nan kaman Boss.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke ta dafa kirji, tafi minti 5 tsaye a inda take da kyar ta iya daga kafa tafara tafiya ta bude kofar falo ta shiga, hamdala tayi dataga babu kowa sadaf sadaf take tafiya harta kai dakinsu ta bude kofa ahankali dan bataso Anty Hindu ma taji tadawo.

Gab da magrib Farida tashigo gidan a gajiye, Islam tace “Ya lectures yau, sannu yan mass com kunajin jiki” yatsine fuska tayi tace “ni wlh duk am not happy yau lectures yasani yau banga my superman ba” tabe baki Islam tayi tareda kwanciya ta lumshe ido dan har yanzu bata dawo daidai ba, wai wayeshi ne? tsaki tayi ta tashi ahankali tai bathroom dan dauro alwala.

Atare da Farida yau duk suka tafi school dan itama tanada lectures yau.
Wuraren 3 tagama lectures dinta Farida ta kira tace mata ta wuce ita bata gamaba hakan yasa tafara tafiya har tafito bakin gate, Keke napep takeson ta tare tahau. “Assalamu Alaikum my Princess” daukar mai muryan yasa ta juyo murmushi kwance akan fuskarta, wani dogon guy ne mai farar fata, yanada jiki ga saje daya yawaita a fuskar shi, ya sanya wani lallausan yadi brown sai kamshi yake, baki ta bude zatai magana ya girgiza mata kai yana hararan ta dawasa yace “karma kifaramin wanan dadin bakin naki, shall we” Ya nuna mata motar shi, murmushi kawai tayi ya bude mata gaba ta zauna sanan ya zaga ta dayan bangaren ya shiga ya zauna hakan yasa yace “Ya jikin Abba?” wani irin kallo yamata sanan yace “Alhamdulillah yaji sauki” shiru sukadan yi tana wasa da yatsa shikuma yana kallon dogayen yatsun ga fararen dogayen kumbunanta dake mugun birgeshi, jingina yay da kujera anatse ya kira sunan ta “Islam” dago kai tayi ta kallai ganin ita yake kallo yasa ta mayar da nata idanun kasa ajiyar zuciya ya sauke yace “mesa kika zabi azabtar da zuciyata sabida kinsan kece ke mulkata? Islam!” Yasake Kiran sunan ta dawani irin yanayi yace “nagaji inaso nai aure, niba yaro bane, banyi kokari ba tun kina secondary school fa muna tare, please my princess ki yarda naje nasami su Dad ayi finalizing everything kinji” ahankali tace “school dina fa” gyara zama yay ya fuskanceta yace “kina tunanin bazaki cigaba da school bane bayan kinsan yanda nakeson karatu eh princess” girgiza mai kai tayi yace “muna komawa chan zan nema miki University mai kyau kifara yi kinji My Islam” murmushi tamai sanan tace “tom amma please kabari nafara ma Mum maganar kaji” murmushi yamata yace “to naji rabin raina” yawani daga mata Gira, ahankali tace “Ya jikin Abba yaji sauki sosai?” “Alhamdulillah an sallamemu inama ajiye su agida nataho na ganki, I missed my princess so much” rufe fuskarta tayi da hannu sabida yanda yabata kunya, kunna motar yayi yana murmushi yafara tafiya fira sukeyi jefi jefi gwanin ban sha’awa yana shiga kwanar layinsu yay parking dan dama anan yasaba fakin bata bari yakai ta har kofar gidan su, tafito, daga mai hannu tayi shima haka yana wani murmushi jiyayi inama gidan su zasu haka saida yaga ta bude gate ta shiga sanan yatada motar yabar anguwan su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button